← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 170

Sashe 101

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta amsa masa babu da kai sannan ta juya ya fice. Ajinsu ta koma ta zauna a kujerar ta hada littafanta ta saka a jaka sannan ta kufa kanta a teburin da take karatun domin kowa da kujerarsa, haka take bata da sakewa a makaranta saboda suna mata kallon bare, gashi ita kuma ta kasa sakin jiki da saba da kowa, a kullum idan ta shigo makarantar tana maida hankali tayi abun da ya kawo ta ne, wannan ya saka take daga cikin students masu kwazo da saurin gane abu idan aka fada, ko aka yi musu bayani, secondly lessons din da ake mata a gida yana matukar taimaka mata sosai, sai dai sauran daliban da suka maida hankali kamar ita sun fita experience domin sun fara daga farko ne ita kuma ta hau abun ne daga sama.
Tana jin na kada ƙaraurawa ta goya jakarta da sauri ta dauko cake din da Ummi ta yi mata dake karkashin table dinta ta fice cikin zumudi ta nufi gate, a ka'ida idan za a fita daga makarantar sai anyi signed daga mai daukar har dalibai idan kuma School bus ce zata kai su gida zai sun yi shi ma mai tukin yayi da nufin shi ya kai su gida. Ita ta fara saka hannu a inda ta saba, sannan security ya nufi inda motar Ameer take ya kai masa littafi ya karba yayi sign din. Sannan ta bude front seat ta shiga yana kallonta sai ta sakar masa murmushi.

“Ya karatu?”

“Ba dadi”

Ya rage idonsa yana kallonta, he can't lie tana da kyau duk yadda zai misalta abun ya wuce tunaninsa, ba ma kamar yanzu da yake ganin nishadi da murna a fuskarta.

“Why?”

“Bana son karatun ni ai, Ummi forced to do so”

“If you don't want babu wanda zai saka ki dole, you can tell her”

“Ko na fada mata ba zata bari na zauna a gida, kuma Ya Maleek zai yi fada he hate me so much”

Ta dan bata fuska ta turo baki, irin batawar da ya kara mata kyau domin a shagwabe ta yi maganar. This is the second time da ya ji abubuwa suna burgeshi akanta, far'arta da kuma bata fuska ko wanne kyau yake kara mata. Ba dan ya tabbatar ita din ce yarinyar da ya gani a can duniyar ba mai matukar kazanta da datti da ko za a hade kur'ane a rantse masa ba zai yarda ita ce aka gyara ta zama kyakkyawa haka ba, har wani abu nata yake burgeshi, yarinyar fa ganin bera a kanta ya saka shi amai, gashi a yanzu ko yar minister ba zata gwada mata kyau gashi ba, domin an gyara mata shi ya kwanta lum ya kara baƙi sai sheki yake kamar ba nata ba.

Ta bude dan box din cake din ta saka hannunta ta gutsira cake cin ta ci. Yanzu kuma bakinta yake kallon yadda take motsa shi a hankali tana cin cake din, ta dago ta kalleshi sai ta dauki karamin spoon dake gefen box din ta saka ta dibi cake din ta kai masa saitin bakinsa. Ya kalli cake din sannan ya kalli fuskarta.

“Akwai dadi ka ci, na aje ban ci ba saboda kai, ban yi break ba”

Ya bude baki ta saka masa ya fara taunawa, ta aje spoon din ta saka hannunta ta fara ci.

“Akwai dadi?”

Ya daga mata wani irin kallonta yake kamar ya hadeta. Ta sake daukar spoon ta diba ta kai masa a baki ya karba ya ci, sai ta aje ta saka hannu tana ci.

“Ni bana ci abinci da wannan”

“Why?”

“A garin mu da hannu muke cin komai, ya fi dadi”

Ta saka saka dauka ta kai masa a baki, wannan karon da hannunta ta kai masa. Sai ya dan tsaya kallonta sannan ya bude bakin ta saka masa.

“Ummi ce ta yi min yayi dadi sosai”

Cak ya tsaya da taunawar da yake, fuskarsa ta canja daga ba yabo ba fallasa to ba yabo, hannu ya kai ya dauki tissue ya zuba ragowar a ciki ya sauke glass ya jefar. Wani iri yake ji ace mahaifiyarsa tana raye amman be taba cin abincinta ba ko sau daya, be san yadda girkinta yake ba.

“Tambaye ni abun da kike so, zan tafi”

“Kai zaka kai ni gida ai, na fadawa Ummi ba school bus zata maida ni ba”

Ya juyo ya kalleta kamar ya ce wani abu, sai kuma kwarjininta da ya cika masa ido ya hana shi kin cewa komai. Ya maida hankalinsa gaba ya jaya motar suka kama hanya, ko da wasa be sake kallon inda take ba.

“Ka yi fushi kuma? Saboda na baka cake din Ummi? Why do you hate her?”

“Why don't you ask her why she hate me from first place?”

“She didn't, tana sonka sosai Ameer”

“Kuma ta bar ni? Ita tace ki zo ki ba ni cake? Ki siye ni da kalamai?”

“Aa bana karya, bata ce tana son na baka cake ba, daman ni abincina daga cake sai biscuits ko fruits, tana yi min cake kullum”

Yayi shiru be ce mata komai ba, sai hawaye da suka cika idonsa.

“I'm sorry”

“You shouldn't”

“Ummi tana sonka sosai”

“Waira ke yarinya ba ki san komai ba”

Ta tari numfashinsa.

“Na san komai, na san komai tun kamin Ummi ta fada min na san komai”

Ya kalleta

“Taya? Wannan dan iskan Maleek ya fada min ko?”

“Ni bana hira da Maleek, he hate me shi ma kuma ni na fada masa, na sani ne ssboda ina iya sanin abun da ya faru da mutum”

This time around dariya yayi.

“Waira kina tunanin kin fini wayo? Kina iya sanin abun da zai faru miyasa kike tambaya waya koya min busa?”

“Be zama lallai ka sani ba, amman idan na rumgume ka zan iya sani”

“Then what are you waiting for?”

“Stop the car”

Ya samu guri ya faka gefen titi sai ta bude gefenta ta fita ta zagaya inda yake ta bude masa.

“Fito”

Samun kansa yayi da bin umarninta ya fito daga motar, sai ta rumgumeshi ta rufe ido, saman kanta yake kallo hannayensa na zube a muhallinsu, ta kai minti talatin tana rumgume da shi, shi be gaji ba kuma be saka hannu ya rumgume ta ba ko yace ta sake shi, duk kuwa da irin abun da yake ji. Ta dago ta kalleshi da kamar tsoro.

“Eid ya koya maka?”

Ta daga mata kai, ba dan yarda tana iya ganin past life din mutum ba.

“A garin da ka je karatu? Kana yawan busar sarewa amman baka iya mai kyau kamar nasa ba”

“Maybe kin san shi, shi ya fada miki cewar ya koya min”

“Be fada min ba, amman na san shi, shi ďan'uwa ne, na san da cewar shi kadai ya iya busar shiyasa nake mamakin yadda naji kana busawar”

“Na ji wannan sai kuma me?”

“Yau ka kade wata tsohuwar ka kaita asibiti”

“A motata akwai jini maybe kin ga jinin ne, cewa tsohuwa ce kuma wannan kin canka ne kawai, look Waira ke da Ummi ba za ku iya wasa da kwakwalwata ba”

Ya juya zai shiga sai ta ce.

“Ranar da Ummi ta fada maka ita ce mahaifiyarka, ka tafi gurin wata mata Humaira, ka fada mata damuwarka. Jiya kanwarka Fiyya ta shiga ďakinka ta yi magana da kai, kamin ka zo nan daga office kake. Kana shirya yadda zaka bar garin nan ka koma wata duniyar da babu wanda ya sanka ka zauna, ranar da Nimra ta mutu ka zo nan da dare, sa safe ma ka zo, da kai aka kaita makabarta, kuma shi ne zuwanka na farko, wannan shi ne karo na farko da wata ta yi hatsari ka tsaya ka dauketa ka kaita asibiti kuma har ka sakata a motarka, kamin ka zo nan kaje gurin wanki mota, sai ka yi tunanin za su yi zargin ka kashe wani sai ka fasa bada wanki ka zo da motar a haka, kana son ka tambaye ya aka yi na zama haka ya aka yi na iya hausa, ka taba ganina a school bus a lokacin da baka gane ni ce ba, ni kuma ban ganka ba..... ”

Haka ta rika zayyano masa abubuwan da suka faru da bata sani ba, da kuma wadanda ya san be yi maganarsu da kowa ba sai kansa. Tana fara maganar ya juyo yana kallonta da tsananin mamaki har ta kai aya.

“Ya aka yi kika san haka?”

“Wannan shi ne sirrina da ban taba fadawa kowa ba, ina ganin rayuwar da ta faru, ta haka ne na gane Ummi tana dauke da cutar leukemia, ba tare da ta fadawa kowa ba, ta haka na gano yadda take ta boye soyayyarka a zuciyarta, na gano damuwarta na son rayuwa da kai ni na fadawa Iyalanta tana dauke da cutar da take stage 3”

“Duba kike yi?”

“Bana duba, al'adar garinmu kowa yana irin baiwarsa ta tsafi ne, sai dai ni tawa ta sha banban da saura, saboda ana jiran na kai wasu shekaru ne a ba ni sarauta ta sarauniyar matsafa da garin, sai kuma gashi na gudu saboda an zarge ni da kashe kashe wani, alhalin ban aikata ba?”

“Me yasa ba ayi amfani da tsafin an gano ba ke kika aikata ba?”

“Ban tsaya jiran a gano ba, na gudu saboda bana son sarautar kuma a dokar da aka saka min idan na gudu kashe ni za'ayi”

Hawaye ya sauko idonta.

“Ina iyayenki suke?”
Chapter 101 · 0% Book details