← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 53

Sashe 9

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

troble,Ok karki fadawa Baba da Mama tare da kannenki pls,Promise me, Kai ta jinjina tace I promise this is a secret between me and u,but if that man repeat what he did to me again I swear to God bazan rufa asiri ba Dole na fada whole duniya ma suji,da kyar Abdallah ya lallaba ta sannan ta tafi part dinsu. Kansa ya Dafe bayan ta tafi yace wannan zata sani Ciwon Kai ko Ina wani Nonon kirki ma a kirjinta oho,tsaki yaja ya nufi part din Maminsa. Yaje wurin Mami zaici Abinci yaga abinda baya so suka dafa,cike da Shagwaba yace haba Mami kin San bana son Taliya fa,tashi kaje inda zaka ci kaci Amma wlh na gaji da iyayinka,baka cin na Yan aiki na zauna dafa maka kana min Iyayin banza,yunwa yake ji sosai kawai sai ya wuce part din Su Khadija yasan Dole zai samu Abinci me shegen Dadi. Da Sallama ya shiga Mama Tasha wanka kamar zata gasa, a ransa yace Dole ta Haifi masu kyau,ga Tsafta kamshi kawai ke tashi a ko Ina na sashen wata nutsuwa yaji da farin ciki Yana ratsashi,ga kida na tashi na zamani,Khadija tana saman Dining da Allo a hannunta tun na kauye na makarantar Allon Liman, tana Alu am Baki wau zal,kamar tana Waka,yayi mamaki da ya ganta da Allon gargajiya. Mama Bayan sun gaisa tace Khadija kawo Masa abinci ko Baki Gama girkin ba? Khadija tace saura kadan na Gama, Ok in kin Gama ki kawo Masa,Abdallah yace Mama kice tayi sauri yunwa nakeji,Mama kiyi sori fa Khadija kinji Yana Jin yunwa,Ki ajiye Allon Nan ki tafi kitchen. Bedroom Mama ta haura sama wurin Baba,Merry ta zauna kusa da Abdallah tace Brother sister Khadija tayi Saurayi last week a schl English teacher ne,tace tana sonsa,Abdallah yace Allah ya taimaka tare da jawo Hannun Ahmad kusa dashi ya zauna Yana tambayarsa schl suna Hira, kitchen Khadija ta koma tana girkinta tana wakokinta na Igbo,Tana aikinta Abdallah yunwa ta dameshi,yace na gaji Bari na duba ko ta Gama,Kitchen din ya Shiga da sauri ya dauke idonsa a kanta sabo da sanye take cikin wata Yar bingilar Gown cinyoyin Nan baka baka a waje luwai luwai dasu ga uban mazaunai kamar tayi ciko, kamshinsa kadai yasa tasan shine ya shugo,Da sauri ta juyo tace almost done Bro Abdallah,Baki ya tabe sannan ya bude Fridge tare da dakko yogourt,da sauri Khadija ta kwace yogourt din a hannunsa tare da furta pls Kar ka Sha wannan yanzu zan Gama remain just 5mnt,doguwar kujera ta jawo Masa zona a Nan kafin na Gama, zuba min Haka zanci kin dameni da surutu kina sa min Ciwon Kai,Dole Haka ta zuba Masa Chinese fried rice din wadda Tasha Hadi ga soyayyun Kaji tare da hadin couslow ta shirya komai a katon Tire me shegen kyau,yanda ta shirya komai abin Sha'awa kamar a resturant komai tayi Masa kwalliya yanda zai kayatar,Haka ta shirya na Baba ma,Zai dauka tace a'a da nauyi zaka wahalar da kanka gaka Dan gayu Ni na fika karfi fa akwe karfi gareni ta dauka da sauri ta Kai Masa Dining Yana kallon ikon Allah,tafiyar ma ba a hankali takeyi ba ko Ina na jikinta motsawa yakeyi,Merry ta zuba mata da Ahmad sannan ta zubawa kanta ta Gama komai ta dawo Palo ta zauna tana cin abincinta,Merry tace sister kizo ki bani a Baki,Mamaki ya Kama Abdallah dake dining Yana cin nasa sai Santi yakeyi a ransa,shi kanshi cewa yake yare sun iya girki ya manta Suma Hausawa ne. Yana kallo Kadija ta daina cin abincinta ta dawo wurin Merry kamar ta samu jaririya Haka ta dinga bawa Merry abinci a Baki katuwa da ita,Ahmad ma yace a Baki zata bashi ta hadasu tana Basu har Ihsan sai da suka koshi sannan Taci nata ta koshi,cin abincin ma da sauri ba wata yanga,Tana gamawa ta mike ta wanke Kwanukan da aka Bata,ta gyara ko Ina Abdallah Yana mamaki kamar engine Bata Hutawa ko kadan daga wannan sai wannan ,Ita kuwa Khadija mamakin yanda yake cin Abinci da yanga Yana yin komai a nutse Sai ya birgeta,muryarsa taji yace yau Baki gyara min Bed room ba? Maminka ya manta Bai bani key din ciki ba,kayi Hankuri tomorrow by God grace Zan Jara maki, ok kawai yace ya mike ya bar musu part din. Da dare ta Karasa aikin daya Bata na cike Forms tana gamawa ta shirya komai,washe gari Monday Sunyi Shirin schl ta fito da papers din ta Kai Masa har part dinsa Yana bacci Bai tashi ba ta ajiye a gefen bed din kawai ta fito Suka wuce schl. Sai 10am ya tashi yaga takardun yasan itace ya duba Handwriting nata me shegen kyau ne ya tafi da Imaninsa gashi ta cike dai dai yanda yace ba kuskure ko kadan,Yaji Dadi ta taimakeshi ya huta. Daya je office kawai yaransa ya mikawa,sai Kuma Na Computer da za a shigar da kowanne form ciki a cike a system,Gama sa Application din bayan sun dawo daga Islamiyya ya tura Afrah ta Nemo Khadija,Da sauri sai ga Khadija tana Haki da Alama gudu Tasha,a ransa yace Bata rabo da gudu,Laptop din ya bude yace zo ki gani,kusa dashi ta zauna duk kamshinsa ya kashe Mata jiki ya fara nuna Mata aikin da zatayi a Laptop,ita Kuma kawai fuskarsa me kyau da yanda yake motsa Bakinsa take kallo gaba daya Bata Jin me yake cewa,sai da ya Gama maganarsa yaga Bata ma san me yake ba shi take kallo. Tsawa ya buga Mata kina kallona Haka kamar baki sanni ba,Na tsani kallo Mind ur Business,Jiki na rawa tace I'm sorry Kaine kana da Chau ne Yaron Daddy kamar Kaine ka halicci Kai naka,komi naka Yana da chau, Harara ya watsa Mata tare da cewa Zan mareki wlh, Yi Hankuri na daina,oya fada min me na koya Miki yanzu,da sauri ta kalleshi domin Bata iya komai ba,Biro ya kwala Mata a kanta ta saki Kara kadan,koya Mata ya Kara yi har ta gane komai sannan yace dauka Laptop din ki tafi da Ida idan kin Gama ki kawo min gobe nake son aikin kafin ki tafi schl,Ok tace tana cewa dama na iya Computer sosai a Anambra. Kallonta yayi suka hada Ido tayi dariya,yace see ur mouth ai kece Anambra din komai kice wani Anambra kwana Nan zan Fara zaneki a gidan Nan kina yawo da jiki a bude a gidan Nan shi yasa Usman ya tabaki,Baki ta rike da karfi tace pls kayi Hankuri Ni dai ban iya sa manyan Kaya ba,bazan iya ba zafi suke min da kaikayi, Kuma yanzu bazan Kuma zuwa part dinsu ba na rantse kaga ba zai sake taba min No...kafin ta Karasa fadar Nono Abdallah ya mike tare da daukan charger zai zaneta, gefe ta matsa, Mami ta shigo farin ciki ya kamata Abdallah zai Zane Khadija,Sai taga Ya shaudawa Khadija daya a jiki da sauri ta fada jikinsa ta rukunkumeshi gata Dama da karfi Suka bangaje Mami ta fada kujera rikica gijif, Khadija ta kwace da Gudu Abdallah ransa ya baci Wai tayi kokawa dashi ya bita Yana so ya kamata yace sai ya zaneta ta rainashi,Palon suke zagawa,Mami takaici ya cika ta,da sauri ta dauki Laptop din da zatayi aiki ta gudu tana dariya. Abdallah yace sai na balla yarinyar can idan na kamata Yana huci,Mami tace Dalla rufe min Baki kun Gama rungumemiyarku to an dai kusa bikinka ka sani domin an Gama komai Daddy Yana dawowa ranar biki za a sa. Allah ya kaimu Mami ya furta zuciyarsa na Kuna,Mami na fita yace wlh na rantse ko sama da kasa zata hade bazan auri Zabin Mami ba nasan ba Zabin kirki bane,sai nasan yanda Nayi aka rusa auren Nan,za a cuceni da kuruciyata Ni Abdallah ai gwara a aura min wannan tubabbiyar Khadija. AsmaBaffa. [12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: TUBABBIYA 6-10 Official AsmaBaffa Khadija Dandume,Innaro,Y@rb@iwa and Jidder Zaria page nakune kuji dadinku. Mami Waya ta Kira Daddy tare da sanar Masa fa Abdallah ya samu Mata,Daddy ya fara Murna dama duk yaransa ba Wanda yayi aure yace ai Next wk zasu dawo ko Dan wannan Shirin biki,sannan ta waya ya sanarwa Baba da wasu Yan Uwansu maza takanas Suka tafi Neman auren Yar Kawar Mami wacce a Makkah Suka hadu,Yan Asalin Ethiopia ne Amma a Nigeria Kano suke zaune,Hamshakan masu kudi ne Kuma jinin Sarauta. Babu matsala iyayen Amarya Humaira Suka Amince Nan aka Basu kudin komai na Aladarsu tare da saka ranar aure 3mnths masu zuwa,Murna wurin Mami ba a magana,Su Kuma sauran kishiyoyin bakin ciki sukeyi zai auri masu kudi,Hafsatu matar Baba da suke faccalanci na masifa har wajen Mami tace Dan tsokana tace Anga kudi tir da so bana Allah ba,akan kudi za ayiwa da auren Dole,fada Suka yi da Mami sosai sannan ta dawo part dinta. Mata da samari kuwa murna sukeyi zasu Sha biki na kece raini,sai shirye shirye suke, Maman Amarya Humaira tace Humaira zata zo tayi 3wks a gidan su Mami sabo da su Saba da Dangin mijinta kafin ayi aure,Mami duk tabi ta haukace kamar wata shugaban kasa ce zata zo gidansu,duk aikin gyare gyare Khadija take sawa tayi na taryar babbar Bakuwa.Shi Kuma Ango Abdallah Sam ba abinda ya dameshi. Humaira da kanta tace ta fasa zuwa baza ta zo ba sun Gama wahala a kanta. Yau ta Kama Sunday gaba daya kowa Yana gida Mama,Merry,Ahmad tare da Baba sun tafi can Adamawa Dangin su Baba zasuyi kwana biyu Wai ganin Yan uwan miji,Khadija kuwa Mama tace ita ta zauna a gida. Su Mama basa nan yau Sunday tana part dinsu ita kadai ta Gama aikace aikacenta tana zaune tana kallo Nollywood Chanel tana kallon Nigerian film,Door bell taji,sanye take cikin Riga da skert na Atamfa tayi Masifar kyau kanta ba dankwali gashin Nan gashi nan a baya yaraf, tana budewa taga Abdallah ya shigo ransa a bace,Ita kanta taji tsoro,Good Day Bro ta furta tana Sosa wuyanta. Abdallah yace Ina Mama? Cike da gwaracin Hausarta ta bashi amsa Basu Nan sunje Adamawa sai jibi zasu dawo Ni Kai Ina Nan part din,juyawa yayi ya tafi abinsa,a tunaninta abinci yazo nema sai ta shiga kitchen ta Masa miyar jajjage Tasha Kifi tare da dafa Masa farar shinkafa Tasha green beans
Chapter 9 · 0% Book details