← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 53

Sashe 26

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shiga kwalawa Abdallah Kira tana Toilet,Dattijon Mamaki ya lubbeshi Jin Ana kiran Namiji da Khadija,Jikin Toilet din ya tsaya yace Mene? Tace ka bani daya rigar nayi amfani da ita,Yar karamar rigar ya Bata ta linka tayi kunzugunta da ita,Wanda ta cire tasa a bakar Leda Sannan tasa a dustbin ta shirya ta fito,Abinci Suka ci suka koshi sai Lokacin Dattijon ya musu magana. Sannuku Yara,Abdallah yace yawwa,Dan Allah Tsoho me akeyi a wannan gidan? Dattijon ya kallesu Hawaye ya zubo Masa sannan yace Nasan Baku sani ba,Wanda yasa aka kawoku Nan Mashirki ne, kudin tsafi yakeyi,Akwai bokayensa da Suke sashi duk sati sai yayi Luwadi da Zina sannan ya samu biyan bukata,Duk takalman da kuke gani na mutanen da ya kawo ne Mata da maza idan yayi amfani dasu sai ya Sa a kaisu wani state din a watsar dasu,Abdallah Da Khadija Suka ce Sam su Basu gane me tsohon yake nufi ba,Dattijon yayi kokarin Fahimtar dasu Amma Basu gane ba,karshe yace idan an shigar daku wurin Oga to karku ci kome zai Baku kawai iya abinda Zan iya Gargadinku dashi kenan,Daga Ina kuke? Abdallah yace mu dai bamu sani ba,bamu sam mu su waye ba,Duk tambayar da Dattijon yayi musu Basu sani ba,anan ya gano ba kalau suke ba kansu akwai motsi. Khadija tace Daga zuwa Shan Lemo shike Nan aka kawo mu Daji,Yanzu Tsoho Wai Mene Zina? Dattijo ya jinjina Kai yace Tunda Baku gane ba shike Nan abar Zancen kawai muyi Addua Allah ya fitar damu daga gidan Nan lfy,Kai Namiji Ga surori da Zan baka mu dinga karantawa Muna Addua,kema Haka mu dage mu fita lfy,Khadija ita tafi son rayuwa a daji cikin kunci take a gidan Nan sai tace ai Dole mu dage mu bar gidan Nan ba Dadi gwara Muna daji. Allah sarki Yar bishiyar Madaci na,har na tuno da Dan Micijin Nan green Yana saman bishiya kullum Ni kuwa Ina kasa muyi baccinmu ba ruwanmu,Khadija ka tuna Wannan abin da muke ci wannan bishiyar me Zaki? Abdallah yace oh Kanya ko? da sauri tace ae har na tuno Dan katon dutsenmu da muke baccinmu Allah ya tsinewa mutumin Nan da ya kawo mu wannan Dan Iskan gidan muna rayuwar mu me dadin gaske,Dattijo Baki bude yake kallonsu irin alatun dake wannan gida Amma ace gwara Daji dashi gaskiya ba kalau suke ba gasu a Haka kamar masu Hankali. Abincinsu Suka jawo Suka cinye tas tare da wanko hannunsu sannan Abdallah ya dinga jera Sallah tun Ana sa ran aidarwa har aka gaji yaki idarwa kawai zirarata yake tayi ba ko zaman Tahiya,Dattijon Yana ta kallo abin ya daure Masa Kai. Dattijon yayi yayi Khadija ta karbi Addua na karatun Qurani Taki,Sai Abdallah ne ya karba ya Kama Yi ba ji ba gani yaki dainawa, kwana daya ba a waiwayi su Abdallah ba sai da Suka kwashe kwana Uku a gidan Nan sai dai a kawo musu Abinci sannan Oga Shehu ya turo yaransa Kan a Kai Masa Dattijon,Abdallah da Khadija. Ba duka ba zagi Suka tafi dasu zuwa wani katafaren part dinsa Suka samu Oga Shehu ya daura kafa daya Kan a saman lumtsumemiyar kujerarsa Yana karanta Jarida,Tunda ya kalli Khadija Yaji hankalinsa ya tashi ba abinda yake bukata sai ita,Abdallah dai adduar da Dattijon ya Basu yake ta karantawa a zuciyarsa,Oga Shehu ne ya mike ya Kalli Abdallah yace Ku kawo min na Fara gamawa da wannan,Abdallah Bai San me ba yabi bayansa tare da yaransa,bedroom suka shige yaran Suka ja kofa Suka koma,daga Oga Shehu sai Abdallah,Oga Shehu yayi wani surkullensa sannan ya shafi Hannun Abdallah yanda zai kasa magana sai abinda yace shi Abdallah zaiyi,Oga Shehu tunaninsa tsafinsa yaci yace Kai cire kayanka gaba daya komai,Tsirara zakayi,Abdallah yaki,yayi yayi Abdallah yaki ko motsi,a fusace Oga Shehu ya taso da niyyar cirewa Abdallah kayansa Baki daya,Nan Abdallah ya Kai Masa wani mugun duka abinka da Me Aljanu sai ga Oga Shehu ya tashi sama ya Fado kasa Damm....ji kake karas ya karye gida biyu a kafarsa,Oga Shehu ya saki Kara me firgitarwa Wanda gaba Daya yaransa sai da Suka taho da gudu,Abdallah ya fito da sauri Yana zuwa inda su Khadija suke kansa ya Sara ya Fadi a wajen,Dattijon ya shiga tofa Masa adduoi su Kuma Yaran Oga sun ruga dakinsa,Oga kawai ihu yakeyi Yana rokonsu akan su fitar Masa dasu Abdallah Baki daya,Da Gudu mutum biyu suka fito lokacin Abdallah hankalinsa ya dawo jikinsa Yana tashi Family dinsu ya tuna,Danginsa,iyayensa,rasuwar Daddy,Da Kuma farko abinda ya sameshi zai fita office tun daga Nan kamar me makuwa Haka ya dinga tuna rayuwar da sukayi da Khadija tun Hawansu mota har zuwa Kauyen Maiduguri da komai da sukayi cikin rashin hankali sai da ya tuna kaf,to me ya sameshi da har ya kasa gane waye shi da abinda sukeyi da Khadija a daji duk Bai gane ba sai yanzu. Bai Gama tunanin ba Mutanen Shehu suka zo tare da yin waje dasu Abdallah Suka jefa su a mota suka jasu can bayan gari gefen titi suka watsar dasu sannan Suka figi mota suka yi gaba,Oga Shehu Kuma sun kaishi asibiti tuni. Dattijon Nan sai kallon Abdallah yakeyi kamar wani Abu na damun Abdallah Amma Bai ce komai ba yace to Alhmdllh Allah ya fitar damu yanzu Ina zaku je? Abdallah yace Kaduna na tuna family da komai,Dattijon yace Alhmdllh to Ni a garin Kafancan nake suna na Malam Saleh muje Tasha sai ku shiga mota Nima na shiga tawa,Abdallah Ya kalli jikinsa mamaki ya kamashi kamar Mahaukaci ga uwar Suma,ga gemu Haka,Khadijansa ya kalla ya tuna itafa Bata samu lfy ba,tana Nan a rashin kwakwalwarta, Aljihunsa ya duba sai yaga Yana da 5k a ciki da Atm card dinsa guda Daya,Kudin ya cire ya tare Taxi Suka shiga yace a kaishi Bank,Sai da aka Fara Kaishi ya cire kudade masu Dan kauri sannan ya bawa Dattijon dubu Ashirin yayi Masa Godiya yasa me taxi ya Kai Dattijon Tasha inda zai Hau mota,Dattijon ya dinga Godiya da murna,Abdallah yace ba komai Allah ne yasa na warke Kaine sila ta sanadin adduoin daka bani na gode,Khadija ta washe Baki tare da cewa Khadija baka da lfy dama? Shuru Abdallah ya Mata sai da Dattijon Suka tafi sannan ya kalleta yace Sunana fa Abdallah,Baki Bude Khadija tace suna nanefa, Hannunta yaja tare da sake tare musu mota suka Shiga yace Hotel nake so me kyau,Driver yace an gama. Prince palace Hotel ya kaisu sannan ya sallameshi ya tafi shi Kuma yaja Khadija Suka shiga ya Kama musu daki Suka shiga,Khadija sai kalle kalle takeyi ita daji take so Bata son nan. Ki zauna a Nan karki fita zanje na siyo Mana Kaya,Tunda yasan halin da take ciki kawai key yasa ya kulleta a cikin room din ya fita tare da shiga taxi,Aski ya fara zuwa aka tsantsara Masa me shegen kyau,aka wanke Masa kafa tare da yanke Masa farata duk da cewa dama ba kazanta Basu da dirty bayan an Gama,Mall ya shiga ya musu Shopping sosai har Khadija wayoyi masu tsada ya siyo da simcard, hattana pad sai da ya siyo Mata trolley guda ya ciko musu da kayan bukata ya dawo masaukinsu. Khadija sai kallonsa takeyi kamar mayya yanda taga yayi tsananin kyau,askin ya Masa kyau,sai da ya fito daga wanka tana zaune gefe daya ta rakube a jikin bango kamar almajira ta ganshi ta Dago Ido suka hada Ido da sauri ta janye idonta,tana tunanin ita ya ta ganta kamar Almajira shi gashi ya canja,Kuma taji yace ya tuna family dinsa kenan shima zai tafi gidansu ya barta ita kadai kamar yanda Dattijon Nan ya tafi shima. Kuka kawai yaji ta rushe da shi,Gabanta yaje ya tsuguna cikin muryarsa me shegen Dadi yace lfy Khad? Khadija tana goge hawayenta cike da Shesheka tace kaima tafiya zakayi ka barni? Abdallah ya kalleta sosai yace kefa matatace Khadija Kawai Dan brain dinki Bata dawo normal bane,family dinmu Daya dake,gida daya muke,Nima Baki ga yau na Samu lfy ba ko kin manta? Kafata kafarki tare zamu tafi koma inane,sunana Abdallah daga yau kece Khadija. Murmushi ne ya kwace Mata ba tare data shirya ba,shima Murmushin ya saki yace Bari na shirya kema nazo na yanke Miki farce na gyara Miki gashinki ko kin fiso mu dinga Zama a daji? Da Sauri ta daga kai sama Wai ae tafison Daji sannan tace Amma duk inda zaka iya Zama Zan bika ko bana son wajen,Good ya Furta Yana shafa Lotion me kamshi,Cikin kana Nan Kaya ya shirya masu azabar kyau ya gyara sumarsa da Tasha style irin kyan da yayi ba a cewa komai,Khadija sai binsa takeyi da kallo Yana ta uban feshe feshen turarensa,sai da ya Gama sannan ya Mika Mata ledar Abinci take away yace taci,Kallonsa tayi ta kalli abincin kawai sai tace Ni kazama ce ko baza kaci Dani ba yau? Ba Shiri ya zauna gefenta ya fara cin abincin sannan itama ta Fara ci,har suka Gama sannan ya dauko Kayan yanke farce daya siyo,Yana gefen bed a zaune tana jikin kafafunsa a kasa ya kamo Hannayenta tare da daurasu saman cinyarsa, ya yanke Mata faratanta gaba Daya hannu da kafa,Ya kaita Toilet ya fara wanke Mata gashi itama ba wani dirty tunda suna tsaftarsu, Yana wanke Mata taga kumfa sai dariya takeyi,Mene abin dariya a nan? Abdallah ya tambaya Yana dirza Mata gashinta,tace Allah...Allah....wayyo cikina ta Kara kyalkyalewa da dariya harda kwalla tana rike ciki Wannan kumfar ce take bani dariya jiba yanda ta cika min Kai na,sai fadowa takeyi a kasa Kuma aikin banza idan ruwa ya zubo Mata sai ta wargatse ta Zama ruwa ai wahalar banza takeyi ta Kara kwashewa da Dariya da taga wata katuwar kumfa ta Fado ruwa na zuba ta koma ruwa,Kai...Kai...Amma anyi girman Banza kalla wata Katuwa da ita yanzu babu. Shi kanshi Abdallah tausayi take bashi da dariya,sai da ya Gama wanke Mata gashin tas sannan yace to saura kayan jikinki ki cire ki bani su a zuba a dustbin,To ka juya bayanka Mana,baya ya juya Mata sannan ta cire zir sannan ya karba ba tare da ya juyo ba ya zuba a Leda ya daure tare da nasa Wanda ya cire ya fitar dasu ya watsar ko a Hotel din Bai son ganinsu, Khadija
Chapter 26 · 0% Book details