← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 53

Sashe 43

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai a hankali,Mama ta tafasa Mata ruwan magariya ta zuba gishiri tasa Khadija ta zauna a ciki ta Dade Haka tayi sau uku sauki ta samu sosai kusan ma sauran kadan ta warke tayi wanka da brush taci kwalliya cikin Riga da skert na Atamfa itama duk Abdallah ne ya dinka Mata a Kano sun fito da surarta tayi Masifar kyau,Merry Ce tayi mata Daurin me kyan gaske,suna Palo gaba Daya dasu Afrah Ana Hira Khadija ta fito tana zuba Kamshi Afrah tace sai kinyi Amaryar Yaya Allah yaja zamaninki dariya sukayi gaba daya. Khadija ta zauna kusa da Afrah tayi fari da Ido tace ya kikace? Ah na gani wannan fagen sai Yaya yazo zai bada tukwi ci,Khadija ta mike tana cewa Afrah yarinya nifa yanzu Auntynki ce yafi ma ki Fara durkusa mini,Kitchen ta shiga ta hadowa Mami kayan Abinci me ruwa ruwa a katon tire ta shiga dakin ta iske Mami tana Jan carbi,Har kasa ta duka tare da giasheta Mami da fara'a ta amsa kamar me,Khadija sannu da kokari tunda kuka zo kike ta kawo min abinci Haka har na rasa Ina Zan cusa a cikina kofa kwana daya bakuyi ba Baki huta ba,Khadija tana rufe fuska Wai kunya tace Mami ba komai fatanmu Allah ya Baki lafiya,Ameen Mami ta amsa tana Alfahari da samun Suruka irin Khadija,Ashe itace Bata Fahimci Hali irin nasu Khadija me kyau da tarbiya ba,shedan ya rudeta cewar Mami a ranta. Khadija da kanta ta bawa Mami abincin a Baki,Abdallah ya bude kofar zai shigo kenan yagansu a Haka suna Hira tana bawa Mami abincin farin ciki yaa kamashi ya Kara Jin son Khadija sabo dal a ransa a hankali ya koma wurin Mama inda suke tare da Baba suna Hira ya zauna sun Dan Dade sannan ya dawo Palo wajen su Merry,sai ga Su Usman ma sun dawo daga sallar Magrib sun zauna a palon,Merry ta shirya abinci iri iri Ana ci Ana Hira harda su firdausi yaran Hafsatu duk da suna cikin bacin Rai Haka Suka daure. Khadija ce ta fito da tire a hannu ta Gama bawa Mami Su Usman suna ta kallon irin kyau da haduwar data yi a ransu suna Abdallah ya Dace shi kam,a palon ta tsaya suka Fara Hira dasu Omar iyayen surutu Ana nishadi,Abdallah Kuma kishi ya tokare Masa wuya ya hade fuska kamar me su Usman dasu Merry duk sun harbo jirginsa,Khadija ma Tasha jinin jikinta kawai sai ta shige kitchen,Usman ya kalli Abdallah yace Dan iska me zamuyi maka da Mata tashi ka bita jarababbe,Murmushi yayi da sauri Aiko ya mike yabi bayanta. Dawowa yayi yace Merry bani Hijab Kato dariya sukayi gaba daya taje ta dakko wani katon Hijab me Hannu, ya karba tare da iske Khadija a kitchen tana wanke Hannu, tana juyowa ta ganshi ya hade fuska ba Rahma kina ganin maza Zaki fito Haka jiba yanda shigar tayi Miki kyau Kuma ta fito da surarki duk Ana ta kalle min abina, Khadija tace to kayi hakuri saka min Hijab din,Murmushi yayi tare da Sa Mata hijab din sai ta Kara wani kyau,Jambakin yasa Bakinsa ya tsotse shi tas sannan yace to muje,Murmushi kawai tayi suka fito tare sai wurin 10pm sannan su Usman suka tafi gida,Abdallah yace Khadija tazo su tafi an gyara musu part guda a Nan gidan Baba tace baza taje ba ita da Mama zata kwana. Bakin ciki ya Kama Abdallah yace Haka mukayi dake a Kano? Abinda zakiyi min kenan? Mama Kuma ai tana part din Baba,Khadija tace Ni bazan biki ba kunya nakeji,yasan karya take Babu wata kunya da takeji kawai baza ta je bane,ya shirya daukanta ta arce dakin Mami dake kwance tasha magani taji Khadija ta shigo da gudu. Mami ta mike Zaune tace lfy Khadija Haka me ya faru? Khadija tace Mami Wai sai na bisa part dinsa Kuma Ni nace a Nan Zan kwana tare dake shine yace zai daukeni,Mami tace to kyaleshi Ni dama Kinga a katifar kasa nake kwana sabo da bazan Iya sakkowa daga saman bed ba da asuba sai ki kwanta a gadon ai gwara ki huce gajiyar tafiya. Abdallah sai gwada wayar Khadija yakeyi a kashe kawai ya shiga dakin Mami ya hango Khadija har ta shige bargo,Mami tace Kai lafiya ba sallama me kake nema? Shuru yayi Yana Jin kunya kawai ya koma tare da banko kofar kamar zai cireta. Kasa bacci yayi Yana ta juyi ya Dade rabon daya kwana shi kadai,baiji dadin abinda Khad ta Masa ba Amma zaiyi maganinta gobe sai ta kawo kanta da kanta yasan Hukuncin da zai Mata,Itama Khadijan ba wani dadin baccin taji ba ita kadai, kawai Dan tanaso Majalasi ya samu lafiya ne amma da tuni tabi mijinta ko Romance Sunyi. Washe gari tunda tayi Sallar Asuba ta koma bacci sai 10am ta farka lokacin tuni Mama ta tafi da Mami can main Palo wurin Malam me magani,gidan gaba Daya kamshi da sheki yakeyi Yan aiki na aiki ta ko Ina. Khadija wanka tayi taci uwar Kwalliya cikin fitted Gown ready made Black and Golden tayi kyau na fitar asiri tana baza kamshi ta fito Palo ta iske Me magani har ya Gama yiwa Mami Addua a ruwa ya Bata Tasha tare da shafa jikinta ya tafi,tayi mamaki da taga har wanka Mami tayi tasa kaya me kyau duk da jinyar da takeyi,gaishesu tayi gaba Daya har Mama, Khadija tace Mami Ashe har wanka kinyi? Murmushi Mami tayi tace kina bacci da taimakon Mama nakeyin wankan,Jinjina Kai Khadija tayi ta kalli Mama sabo da ta rasa me tayiwa Mama tunda ta gaisheta taga tana ta harararta tana hade Mata fuska. Bin Mama tayi dakinta tace Mama kamar fushi kikeyi Dani me nayi Miki daga zuwana? Khadija baza mu sh irya dake ba,ganin kin dawo gida shi yasa Kika banzantar da mijinki ke ga me Uwa ko shine Kika kwana a nan Kika barshi,nufinki Mami zata ji dadi kina gudun danta kin rainashi?,wlh kina gani idan ya gaji kishiya zai Miki ba ruwana Kuma Nima ba ruwana dake indai baza kiwa mijinki biyayya ba,Haka na koya Miki? Ko Haka Kika ga inayi? Duk mata ba da Haka suka Saba ba wanne halacci ne Bai Miki ba har Kika kawo yanzu,da wani wlh da kin gane kurenki. Mama Bari fa nayi na warke Allah Mama ke kina da fushi da wuri ai hakuri akeyi da Yara Khadija ta furta tana dariya,Mama tace kinfa girma Khadija ya kamata kisani,Yo Mama sabo da Allah Ina na girma kalleni fa, Dan Baki ga wata me aikinmu ba Maimuna Rusheshiya Amma har nice na girma? ba laifinku bane da kuka min auren wuri kuma...Kum..pillow Mama ta dakko ta kwadawa Khadija tana murmushi,da gudu Khadija ta mike tana Bude kofa Sukayi Karo da Abdallah zai shiga wurin Mama. AsmaBaffa [12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: TUBABBIYA 81-85 Official AsmaBaffa Ga page dinku mutanena Rokel, Jikar Kuluu, Fatimahig16, Khadija Usman, Ayman Mrs, Aysha Humairah, Hapcer, Halymatu, Gwabnati and Maman Hajiya. Jinjina gareku manya manya Mum Afnan,Maryam Kabiru,Maryam,Fulatah luv, Aisha Adamu Abdullahi,Khadeejat Ahmad,Hadeeza Mukhtar, Mama zee and Bilkisu Rabiu Ado. Annallaha Ma'assabirin Ina so na Baki page baki da suna sai Annallaha Ma'assabirin ya kamata kisa suna sis, Ina godiya da Sharhi. FLOWER, JIDDER ZARIA and ASYCOOL tsohuwar Zuma Ina Miko gaisuwa. Gefe yaja da sauri Yana dafe da goshinsa fuskar Nan murtuk akan ya kwana shi kadai jiya,Khadija tace sannu Ban gani ba Ina kwana Bai ko kalleta ba bare ya amsa ya wuce ciki wurin Mama suka gaisa sai Hira sukeyi akan rashin lafiyar Mami, Khadija hankalinta ya tashi matuka ganin Abdallah Yana fushi da ita,Haka ta lallaba jiki a sanyaye ta koma can Palo ta zauna ita daya tal,ganin shurun yayi yawa sai ta jawo wayarta tare da Kiran Kawarta Abu suka Sha Hira,tana gani Abdallah ya fito Bai kulata ba ya shige wurin Maminsa. Koda ya fito Afrah ya Nemo ta zuba masa Abinci yayi Break,ya mike zai fita Khadija ta tareshi tare da tsayawa a gabansa tace Me....kafin ta Karasa ya raba ta gefenta yayi tafiyarsa abinsa ya barta Nan tsaye, abin yayi matukar Bata mamaki Dan kawai jiya kadai Rana daya tal Lallai Abdallah,shareshi tayi itama Suka shirya kamar wasu Yan Mata tare dasu Afrah zasu tafi Family House asha Hira,Suna Fitowa bakin gate Abdallah ya fito da mota ya sauke Glass din motar tare da cewa Wa Kika tambaya da Zaki fita? Afrah ku tafi ke ki koma gida,Khadija kamar zatayi kuka tace ai Mami tace naje,tsaki yaja yace sai ki tafi idan Mami ke aurenki ya figi motarsa ya bar wajen. Hawaye Khadija ta Fara sai ga Baba yace Khadija lfy? Baba Abdallah ne yace bazan je Family House ba mu gaisa Dan kawai jiya na Masa laifi, Nima Khadija bani da ikon barinki kije sai Baba ya Daga waya ya Kira Abdallah yace akan me zaka Hana Khadija? wannan ai shashanci ne,Baba nifa ba hanata nayi ba kayi hakuri taje kawai. Yace kije Khadija cewar Baba,murna ta Kama Khadija dasu Afrah suka rankaya Suka je Family House sun Hadu da Yan Matan Ana ta Hira ana shewa. Har dare Basu koma gida ba,har 10pm Basu koma ba,Abdallah yaga sun Dade ransa sai baci yakeyi shi yanzu Khadija Bata sonsa ta daina kula dashi,Yana wajen Mami suna Hira su Khadija suka dawo Mami tace yanzu sai dare Haka kuka taho ai da kun kwana can,Mami Yaya Omar ne ya kawo mu a mota,Ok to,Khadija tana satar kallon Abdallah da ya hade rai,wanka tayi ta fito tare da Shirin bacci sai binta yake da kallo kamar zai cinyeta,ganin irin Masifar Kallon Abdallah, Khadija ta fice Daga room din Direct ta wuce part din da Abdallah yace nasu ne, saman Bed din ta samu ta kwanta abinta tare da kashe light,Abdallah Bai San ta shigo ba ya dawo Yana ta Jan tsaki Khadija ta daina sonsa,wanka yayi tare da Shirin bacci sannan ya Haura saman bed sai yaji ya fada saman Mutum,Khadija ta saki Kara tare da matsawa gefe,Masifa ya Fara Mata ya Zaki zo ki kwanta baza ki fada min ba Ni ban San da Mutum ba. Khadija tace Ni na rasa me nayi maka kake fada Dani Kamar ba Kai ba,a mutane sai ka Fara Yi min
Chapter 43 · 0% Book details