← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 53

Sashe 6

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zafi ya isheta daurewa kawai takeyi. Part din Haj Rahmatu suka Fara zuwa da yaranta samari da Yan Mata,kamar ba sune suke murna jiya ba anyiwa Hafsatu kishiya Amma ganin kyawun Mama da yaranta yasa suka Fara tabe Baki suna musu kallon banza,Khadija duk surutunta Shuru tayi har suka koma part din ta biyu Haj Aliya itama da yaranta sai Shan kamshi takeyi,jiki a sanyaye suka tafi part din ta Uku Wato Aisha Mamin Abdallah ganin talakawa ko kallo Basu isheta ba kamar ba itace tafi kowa Murna ba jiya,sai Mata ta Hudu Amarya Haulat me yaro daya Saddiq tashi tayi ta bar musu Palon ma Baki daya Dan kansu suka fito,Binto tana Basu hakuri tace gidan Nan faccalanci akeyi sosai Babu me kaunar Dan uwansa Kuma duk Matan ne suke Haddasa fadan. Part din Mazan gidan samari aka kaisu Samarin ba ruwansu sai Jan Su suke da Hira sabo da Maganarsu abin dariya,Bayan sun fito Binto tace saura part din Daddy da Abdallah,sunje Wurin Daddy sosai ya karramasu sannan yace duk abinda suke so ko ya faru su sanar Masa,har number wayarsa ya Basu sannan yace Next week zai tafi Russia zai tafi da Matarsa daya,dama Haka yakeyi duk tafiya idan zaiyi to sai ya tafi da mace cikin matansa,idan ya tafi da wannan sai ya dawo da ita ya tafi da wata. Bayan sun fito suna Murna sai part din Abdallah Yana Palo Yana kallon Ball ganin Binto da Kuma Mama me karamci yasa ya saki fuska ya rusuna ya gaidasu suka amsa yace da Kin Bari ma Anty zanzo har can na gaida Mama ai Bai Dace Ina kamar danta ba tazo gaishe Ni,Babu komi wallayi Khadija ta bada amsa,Next time sai kazo kaga yanzu mun kalli gida da Chau da Chau,A wayance ya Harareta ba tare da kowa ya gane ba. Khadija Bata hakura ba tace yaron Daddy baka da Tsafta a part naka sose ya kamata masu aiki su Kara dagewa kalli tv naka yayi Dirty,Gaskiya Khadija ta fada domin da kansa ya Hana Yan aiki shigar Masa part sabo da sace sace akeyi Masa,Kannensa yake sawa su Gyara Masa sai dai basa Yi Masa yanda yake so sai weekend yake zagewa ya gyara da kansa. Bayan sun fita karshe part din Hafsatu Suka shiga Hafsatu tana ganinsu ta mike tsaye tare da daka musu tsawa ku fice min daga part gayyar tsiya Arna kawai,munafukai zaku ce musulmi ne ku,Babu wata Alama data nuna ku musulmi ne anyi juju tsafi an aure min miji shegu talakawa matsiyata,Binto tace kee Hafsatu ki Kama kanki,sai dai ki mutu aure an rigada anyi shi koma Arnan ne ya rigada ya aura Dole ta Zama abokiyar zamanki,shasha Sha dabba wacce Bata San me takeyi ba. Mama tace ki kyaleta Anty rayuwa ce komi zai wuce wooo,baiwar Allah woo mu musulman asline fa,ki Dena Bata bakinki kina waisting time kowa mafa ya iya fada wooo kawai de Shuru muna Yi maka ammafa woo idan kana fada fada da yawa Haka watarana yarana baza su barka ba wooo,You have to be very carefull ehem domin Nima Matan Alaji ne like u. Fita sukayi tare da komawa part dinsu,Sai Dare Ango Baba ya shigo part din Amarya da Ledoji manya biyu sai da ya mikawa su Khadija nasu sannan ya Haura Samansu bangaren Mama. Kaji ne lafiyayyu da Madara tare dasu fruits,Mama harda Yar kunya,bayan sunci sun koshi sannan Mama tayi wanka da Alwala,kafin Baba ya fito tayi Shirin baccinta cikin Kayan bacci masu Jan hankali tana kamshi gashinta yasha gyara sabo da Mama a waye take Bata tsufa da kwalliya sabanin matanmu wasu na Hausawa da Sunyi Yara sai su daina komai suce sun tsufa,sai Alhazawa su koma neman Matan banza. Baba ma wanka da Alwala yayi ya Sa jallabiya tare da jansu Sallah raka a biyu suka idar ya dafa kanta tare da yi musu adduoi,Bayan sun Gama suka kwanta,Daren yau Suka rayashi da sunna,Wanda Baba ji yayi kamar yau ya taba sanin mace a duniya,Mama ta daban ce,akwai gyara Kai ga iya love a bed,sabo da ba wata kunya ta zage tare da sarrafa mijinta a shimfida ta shayar dashi zumar da Bai taba Sha ba ko a mafarki,Nan fa ya Kara kaunar Mama,sonta ya Kara shiga ransa,ya rude Mata sosai,ita Kuma sai Shagwaba da lallabashi takeyi,kudu ta ratsata sosai take Masa biyayya ba girman Kai irin na wasu mu Hausawa,ga caring da ji dashi,Haka ma Yaranta suke mutuntashi,Baba Bai Gama Shan mamaki ba sai da yaga yana cire Kaya su Khadija ke wanke Masa a washing machine su goge Masa,ga uwar Tsafta ga iya girki,sannan ga addini basa Wasa da Sallah duk da ba wani ilimin addini ne dasu me zurfi ba hakan Bai hanasu addini ba,ga jan mutuncinsu tunda suka fuskanci yanayin gidan sai suka daina shiga shirgin kowa,Dan ma Khadija uwar surutu ce da tsokana kullum sai tayi tsokana ta gudu. Bayan sati biyu sun Saba da gidan sun San kowa lokacin Kuma Baba ya Gama musu komai na makarantar su Ahmad Yana jss1 aka sashi,Merry Ss1 Ihsan jss3 sai Khadija Ss3 Uniform dinsu kala biyar da schl bags da sandal,canvas sai kayan littatafai na karatu,gasu da kokari sabo da suna Jin turanci sosai. Kamar kullum Driver ke kaisu ya dakkosu a motar gidan,Hafsatu ta dinga bala'i ta Hana a kaisu,Har fada sukayi da Baba ga Daddy baya kasar shi da Rahmatu Matarsa ya tafi,Mama ganin ran mijinta ya baci tace karka damu kawai ka Basu kudin taxi sai su tafi ai ba nisa makarantar,bana so kana damun kanka komai zai warware gaba,Baba har Addua ya kwararawa Mama Dan yaji Dadi Bata son Hayaniya tana da hakuri ga biyayya,Bata son ran mijinta ya baci. Tun daga wannan Rana su Khadija ke tafiya schl da kansu,Yau Monday su Merry sun Riga Khadija fitowa gate din gidan,da gudu Khadija ta fito sanye cikin Uniform Riga iya gwiwar kafa green and white sai Hula Green a kanta jelar gashinta har tsakiyar gadon baya tayi Masifar kyau. Tana gudu tana kwalawa Merry kira Bata sani ba Mami ta fito cikin shiri Abdallah zai kaita ganin Doctor dinta za a duba lafiyarta Sabo da Naira ta ratsata,Khadija ce ta bige Mami,kauuuuu kakeji Mami ta kwashe Khadija da Mari,Khadija Bata San sanda ta durkushe a kasa ba sabo da azaba,Mami tace dabba jaka marar tarbiya,Arniya Yar Arna har Ni Zaki hankade Dan Uwarki,Shegu tubabbu masu tuban muzuru,wlh idan bakiyi Hankali ba sai kun bar gidan Nan,Abdallah na jikin mota ya harde hannayensa a Kirjinsa Yana kallo sai Murmushi yakeyi Yana Murna da Alama Maminsa ta birgeshi. Ido jajir da Fuskarta tayi ja abinka da fara haka Khadija ta mike batace Komai ba tace kiyi Hankuri Ajiya ban ganoki ba time din,pls forgive me, pardon me Ajiya Kinga su Merry Ina nema gasu can a wancan Gutsun bishiyar,Jin kalmar data fada yasa Abdallah dafe kunnensa Don kunya yaji,Afrah da itama ta fito cikin shiri ta kwashe da dariya tana bin Khadija da kallon kaskanci tace ke karki Mana batsa a gida Gindin bishiya ake cewa. Khadija tayi tsalle gefe tace wallayi karya ne fa Abu yace Mani Gutsu ake cewa ku dama ance iskanci ne kuke Yi a hausarku,bazan Ce Gindi ba Ni Ina da kunya woooo,Tsaki Mami taja ta shige mota,Afrah kuwa dariya harda rike ciki,Shi kanshi Abdallah dariya ta bashi da kunya. Yana Jan Motar wata lumtsumemiyar gaske su Kuma Su Khadija suka tafi schl tare da Shiga taxi,Merry tace Allah ya Isa da Marin da waccen tayi Maki,Khadija tace Don't mind her God Yana gani ba. Bayan sunje schl sun dawo Baba yace sai Islamiyya na saku gata Nan ba nisa da gidan Nan,sun Gama shiri sun fito da katon Hijab kamar gaske,Mami ta turo Afrah Wai ta Kira Mata Khadija. Gaban Khadija ya Fadi Kar ko Mami taci mutuncinta ko ta duketa,kamar kwai ya fashe Mata a ciki ta Shiga part din Key Mami ta jefo Mata tare da cewa Arniya gashi maza dauki ki gyarawa Abdallah part dinsa,Afrah yasa ta gyara Masa Amma Mami tace ko Afrah tayi dukanta yakeyi yace Bata iya ba,sannan Yan aiki basa Shiga part dinsa sabo da satar da suke Masa,ga Iyayin Abdallah ba a iya Masa,to indai har tasa Yan aiki zasu iya Masa sata, shine yace bari ta gwada Khadija idan har tayi me kyau to Afrah ta huta ya daina dukar Mata yarta. Khadija tace Islamiyya fa zamuje,Ubanki Zakije nace wlh idan Baki gyara ba sai na tattaka ki cewar Mami,saura kiyi Masa sata barauniya,Fita Khadija tayi ta koma sashensu ta fadawa Mama,Baba Yana zaune yace ai yau idan bakiyi ba Khadija na shiga uku da Gori a gidan Nan domin suna bakin ciki da abinda Dan Uwana ke min, Mami zata ce dukiyar mijinsu ne ba Gidana bane,Mama tace kije kiyi Khadija me kyau zakiyi bana so Mijina ya shiga matsala pls,Merry ta fadawa su tafi ita sai Gobe zata Fara zuwa,Part din ta bude ya gaji da haduwa kalar Yan gayu,dama English wear ne a jikinta Riga da skert cikin Kaya da Baba ya musu masu tsada,kasan ta Fara gyarawa tare da canja fasalin zaman kujerun da flowers dake girke a palon masu kyawun gaske,Nan fa ya dau kyalli da kamshi, duk da Haka taji kalar kamshin Bai Mata ba,ta koma da gudu wurin Mama ta kwaso wasu daga cikin nasu tazo ta fesa tare da jona wasu na electronic sannan ta haura Samansa, Sai da ta sume a tsaye tsabar haduwar bed din,Haka ta canjawa Saman ma komai har mazaunin bed din,ta canja new Bedsheet,ta saki Ac tare da sakin kamshi na Bedroom ma daban,ta wanke toilet dinsa tare da shirya kayan wankansa neat,ta kwaso kayansa masu Dirty har Boxers da singlet da Bedsheet data canja,ta zuba a washing machine ta wankesu Kal ta fita can baya ta shanya a Rana kamshin toilet ma daban,lungu da sako ta gyara har fridge da kitchen dinsa ita kanta ya birgeta kafin wani lokaci kayansa sun bushe ta kwaso ta goge Wanda ya Dace a goge,tayi linki me kyau taje Amma Bata taba Masa sip ba kawai ta ajiyesu a gefen bed ta Kara gyare gyarenta ko Mai neat sai ta fito tare da kulle part din ta koma wurin
Chapter 6 · 0% Book details