Sashe 17
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
biya ta hakkinta ko Allah ya konashi,sai da ya huta ya sake Wani gumurzun sai da ya Gama jigata tafi karfinsa gaba daya Bata gajiya,sai da kyar ya samu ta gamsu,Jikinsa ya zame ya kwanta wanwar,sai zazzabi ya rufeshi kamar zai mutu,da kyar ya samu ya tsarkake jikinsa ya gudu bedroom dinsa Dan karma ta motsa Mata ta dawo neman Kari,Ai a Daren Abdallah asibiti ya kwana,Ana Kara Masa Ruwa da Allurai,Dr Hussain yayiwa waya yazo ya daukeshi Humaira tana can tana baccinta hankali kwance,Dr sai dariya yakewa Abdallah Yana tsokanarsa,Kwana guda da yini a hospital sannan ya samu lfy karfin jikinsa ya dawo bai tsaya ko Ina ba sai ya gudu gidansu. Part dinsa ya shiga Daddy ya zuba masu gyara suna canjawa Khadija komai na part din,wanka yayi ya shirya fes ya fito Yana walwali ya Shiga kowanne part suka gaisa,sannan ya wuce part din Maminsa ya Dade yaki tafiya,Mami tace Abdallah ka tashi ka tafi gidanka Mana kabar karamar yarinya a kwance a gida ita kadai ai tsoro zata ji,Haka Ango sukeyi? Sai yace Mami zan tafi ne Wasa Wasa har akayi Azahar yaje Sallah ya dawo a Nan yaci abincin Rana sannan yayiwa Mami Sallama ya shige part din su Khadija,Mama ya iske a Palo ita kadai Suka gaisa tace duk sun tafi schl har Khadija Daddy yace taje schl dinta yanzu zasu dawo ka Dan jira su,Dama Haka yakeso Kar ya tafi gidansa Humaira tace ya Mata wani Abu,Humaira kuwa tunda Bata ganshi ba ko nemansa Bata yi ba harkar gabanta takeyi tana chat da waye wayenta masu aiki suna Mata abinda take so. Mama ta kawo Masa kayan ci da Sha suna Hira sama sama sai ga Merry ta shigo da Ihsan sai Ahmad,Abdallah Suka gaisar Abu kuwa tana dakin Khadija tana baccinta ita da Madam Ngozi,Khadija ce ta shigo daga karshe Hijab a hannu da takalmanta tare da safa duk a Hannu ta shigo da Sallama tana Kwalawa Mama Kira,Kamshin Abdallah ne ya bigeta tasan Yana Nan,Nutsuwa tayi ta Karasa tare da Durkusawa ta gaidashi ya amsa Yana Kare Mata kallo yaushe aka canja musu Uniform na musulunci Riga da wando da Hijab,yaji dadin hakan,Ko Uniform Bata cire ba sai Hijab ta cire kawai Hannu ta wanko ta wuce Dining ta cika timbinta sannan ta mike ta shiga Toilet tayi wanka da Brush ta shirya cikin kayan Islamiyya dama suna Sallar Azahar tun a schl Fitowa tayi tana kamshi ta zauna kusa da Abdallah domin ba kowa sai shi kadai Mama ta Basu waje. Khadija ta leka fuskarsa tace Ango Ina Amarya? Banza ya mata kawai,zata Yi magana ya mike ya fice abinsa ya shiga mota ya koma Gidan Humaira,Taci kwalliya cikin kana Nan Kaya ta tsuke za a birge miji,Yana shiga ya ganta ta kwadawa wata dattijuwa Mari wacce ke aiki itama a gidan,Yana zuwa shima ya kwashe Humaira da Mari lafiyayye yace mahaukaciyar Ina ce ke? Kamar wannan dattijuwa Zaki Mara mahaifiyarki ma ta girmeta Amma Kika iya marinta,Kunci Humaira ta dafe tace Kai har ka Isa ka mareni akan wannan kazamar wlh sai kasan Ni ka Mara. Tana kuka ta dauki waya ta Kira Maminsa tace Abdallah ya Mata dukan tsiya,Ko minti goma ba ayi ba sai ga Mami tazo gidan da kanta ta ci mutuncin Abdallah tare da korar Dattijuwar tace munafukar tsohuwa hada kayanki ki tafi kwanan Kauye ai ba shi ya daukoki ba nice to kije na koreki,Tsohuwar tana bada hakuri Abdallah ya Bata kudade da yawa yasa Driver ya maidata gidansu. Haka zaman nasu ya kasance Babu Wanda ke shiga safgar kowa,Humaira sai in tana Sha'awa zata bashi Condom shima ya daina matsawa kansa abinda yaga zai iya yake mata yayi tafiyarsa,Haka har aka maida Khadija part dinsa cikin family House,Mami sai aiki take sata iri iri sannan ta Hana Abdallah zuwa gidan gaida kowa Wai Dan kar ya kula Khadija,Hankali kwance Khadija ke gyara part dinta tayi aikinta da girkinta,sannan gata ga Yan uwanta,Madan Ngozi da Abu sun koma kauye da Sha Tara ta arziki. Daddy ne da kansa ya takawa Mami birki cewar matukar ta Hana Abdallah zuwa wurin Khadija to wlh Khadija zai maidata gidan da Humaira take su zauna tare,hakan yasa ta kyale Abdallah yazo. Amma aiki kullum sai Khadija tayi musu karshe ba godiya zata rankwasheta ko ta mammareta ta koreta,Duk ta Hana Yan Uwan Khadija shiga part din da Khadija take,ta Hana Khadija zuwa part din Mama Haka ta hakura sabo da Kar matsala ta barke. Daddy Yana barin kasar ta Hana Khadija zuwa schl Gashi waec da Neco zasu zana,ganin Haka yasa Baba ya biya kudi masu yawa Za'a zanawa Khadija. Abdallah Bai sani ba sabo da yayi tafiya zuwa Cairo ganin Mami ta takura Masa. Humaira tana zaune Kawarta tazo suna Hira tace ke banza ce me yasa kika yarda aka raba muku Gida da yarinyar Nan,ai ki Bari a kawota kuyi kishi ki hura Mata wuta da kanta zata ce a saketa,ai Haka akeyi Amma kina Nan me kika San sunayi da mijinki,Gwara komai ayi a idonki Kar a cuceki,sannan da wuri zai saketa idan Kika hada Mata wani tuggun. Humaira tace Kuma fa Haka ne Zuly Bari na kira uwarsa ki gani,Kin san fa Abdallah mugun Dan rainin hankali ne,wlh wahala yake bani Aljana ce ta aureshi bashi da lfy sabo da Sam Mata Basu dameshi ba ko tsirara zakiyi Ni wlh Banga wani amfanin aure ba,Gwara Ina waje inci Karena ba babbaka,kawai Dan kudinsa da kyansa nake zaune dashi ko banza duniya tasan na auri miji hadadden me kudi,Zuly tace ai Baki cika ba sai kin Kori kishiyarki ke kadai kike shanawa Babu wata. Nan take tace wannan Mamin tasa algungumar mata ce Bari dai na kirata suka kwashe da dariya,Humaira ta Kira bugu daya Mami ta dauka jiki na rawa tace Humaira ya akayi da fatan ba matsala bace? Humaira taja tsaki tana yatsina tace Mami Abinda nake so a dawo da wannan yarinyar Gidana mu zauna tare so nake na koreta da wuri ya saketa,Amma tana nesa ai za a Sha wahala wurin korarta Nan Humaira ta shiryawa Mami dabarunta,Mami tace Nima Saida nayi tunanin Haka,Kinga Kuma Haka ne, shegiya Tubabbun banza a satin Nan za a dawo da shegiya kici Ubanta da aiki da sauran su,ko rashin kunya ta Miki ki Mata shegen duka. Abdallah jibi zai dawo kafin ya dawo an dawo da ita Dan uwarta cewar Humaira. Washe gari part din Khadija daban a gidan Abdallah dama,Rana tsaka Mami tasa Khadija ta hada kayanta komai,Ita dai Mama Nasiha tayi Mata,Daddy ma sai labari yaji wurin Baba yayi dariya yace Alhmdllh dama abinda nake so kenan yanzu Abdallah zai samu kwanciyar hankali ita Kuma Humaira sharrinsu kansu zai koma,a waya Daddy yayiwa Khadija Nasiha,Mama da Baba ma Haka,Khadija tana kuka aka maidata gidan Humaira,Tunda taga gidan da part dinta ta daina kuka sabo da gidane na masifa wurin kyau da tsaruwa,tace Ahhh Alhmdllhi wooo yanzu Naga wurin Zama,Humaira kishiya ce ba uwar Miji ba ubanka zanci a gidan Nan. Ranar Khadija Part dinta sai da ta sake gyara shi Yana kyalli da sheki lungu da sako,ko Ina kamshinsa daban ne. Ranar Kuma da dare Abdallah ya dawo sabo da Daddy ya sanar Masa komai, part dinsa ya wuce Yan aiki ya iske a ciki Humaira tasa su Gyara Masa ai ko ya koresu yace karsu Kara zuwa part dinsa. Humaira Jin ya dawo Tasha wanka da kwadayinta ta shigo ba sannu da zuwa ba komai ta Fara Complain yanzu zaka dawo ban Isa ka fada min ba,ai jiya kace ba yau ba,Dan Ni ka tsaneni,tsaki yaja kawai ya shige toilet ya barta a nan tana mita,Yana Fitowa yaga tayi Shirin bacci yace Hajiya yau ba kwananki bane,Mikewa tayi da masifa Ni yaushe ka biya min bukatata da zakace kwana na ya Kare? Kwana nawa na Baki kinci yakai 1mnth ban taba bawa Khadija kwananta ba,ko ita ba mace bace? Au to Ni nace karkaje wajen nata taja tsaki tare da jefar da robar ruwan dake hannunta tayi waje fuuuu. Sake sake takeyi yanda zata ci uban Khadija. AsmaBaffa. [12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: TUBABBIYA 21-25