← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 53

Sashe 51

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sani ba cewar Khadija ta furta tana fari farrr da idonta farare tas. Suna shiga Mami ta karbi jikanta tana musu sannu da zuwa bayan sun gaisa suna Hira akan Humaira sai dariya sukeyi yanda Afrah take fada musu Masifar Humaira, Mikewa Abdallah Yayi yace Office zanje Key din motar Khadija ta Mika Masa yaki karba yace ai Baki Isa ba,ba Haka mukayi dake ba sai kin kaini Office Kika ce yau Ni bazanyi Driving ba,Idon Mami ta faka sannan ta zuba Masa wani fari me Jan hankali,Ya wani lumshe Ido,Mami tace Kai Dalla ka tafi idan zaka tafi ka fiye takura,Mami ki daina shiga Zancen Nan wannan yarinyar Hutu fa akayi musu a schl tace kullum zata na kaini Office shine yanzu zata ce wani kaza kaza,Ga drivers Nan ko gidanka nawa ne da Kai Dole sai ita zata kaika? Kyaleshi Mami na kaishi daga yau bazan sake kaishi ba,Uhm su Khadija an iya driving sai yanga cewar Afrah, ya ranki? Khadija ta bata amsa suna dariya. Khadija ce ta tukashi har Office yace sai ta shiga tasan nufinsa idan ta shiga to sai ya jagwalgwalata sabo da Haka yake Mata wayo shi yasa taki Shiga tana ajiyeshi ta figi mota tayi gaba sai hannu ta Dago Masa tana Danna Masa uban Horn irin tayi gaba ita,Dariya yayi sannan yace zamu hadu ne ya shiga Office. Yaronta Yana wajen Mami ta goyashi Yana baccinsa, can gidan ta yini sai yamma ta dakko Abdallah daga office Suka wuce gida abinsu Ana Shan love. Bayan watanni kadan Abu ta Fara laulayin ciki,Usman sai ji yake da Zainab dinsa kamar kawai, Firdausi ma ciki gareta tare da Merry ta Dr Hussain,matar Omar ce kawai Bata ciki, lokacin Kuma Saura sati daya bikin su Afrah. Khadija ta Zama Busy kamar itace Amaryar kullum gyaran jiki ba ji ba gani, Abdallah dinma ba ganinta yakeyi sosai ba daga gyaran jiki sai gida wurin Mami ko Mama,Mami kuwa itace take daure Mata gindi,King dinsu ko yaushe Yana wajen Mami tana rainonsa. Khadija ta Kara Hankali sosai ta Kara wani girma da Yar kiba tana sheki da walwali tayi wani irin wayewa da gogewa,Abdallah ma Haka wani freshi da kyau yake karawa ko yaushe Yana wani dawowa yaro ga kudi sai Karuwa sukeyi kana ganinsa kasan Jin dadi,kwanciyar hankali da Hutu ya zauna Masa Yan Mata sai rubibinsa sukeyi Amma Ina duk ganinsu yakeyi maza ne Khadijansa itace mace. Yau Khadija tana Wurin wani wajen wankin kafa Tasha uban kyau ga Kaya masu Uban tsada a jikinta kowa ya kalleta sai ya Kara,Abdallah ne ya kirata a waya sai da tayi Murmushi sannan ta daga,Bai Bari tayi magana ba yace kina Ina yanzu Kuma da Rana? Naje wankin kafa ne an kusa gamawa ka dawo ne? Tsaki yaja kadan yace to Ina King? Yana wajen Mami,da mota Kika fita ko Driver ya kaiki? Driver ne Mana Musa,Alright Bari na biyo wlh ko ba a Gama ba tafiya zamuyi na gaji da wannan gyara Haka ko kece Amaryar ai sai haka,Yanzu yaushe rabona dake? Ni dai bazan iya ba ki dawo kawai I need you Now, to kazo ka daukeni mana Mene abin fada,yanzu Zaki ganni coz bukatarki tasa na baro Office. Tana Gama wayar sai ga wata zukekiyar mace ta shigo kace Bata taba aure ba,itama tana uban kamshi da sheki ga da gani kaga wacce Naira ta ratsa hutu da Jin Dadi,Yar gayu ce ta gaske Amma sai Harare Harare takeyi ita kadai fuska Babu Rahma. Ita Khadija tsoro takeji Kar Abdallah yazo yaga wannan budurwa duk da cewar tasan itama fa baa Isa an nuna Mata komai ba. An gamawa Khadija Amma taki tashi sai kakale kakale takeyi,Wacce ta shugo yanzu tace yarinya ki tashi ki bar Nan an Gama Miki idan Baki da aikin yi Ni Ina dashi,Wayar matar ce tayi Kara ta daga tana uban kashe murya Kamar zata Yi sujjada sabo da yanda take girmama me wayar Amma sai Suka ji tana Common My Alim yanzu zanzo ka jirani a airport din pls,sai Kuma ta koma Shagwaba Haba Mana yanzu ka canja baza mu tafi China ba to Ina zamu je? Canada Kuma ka canja? Alright ganinan zanzo in 30mnt. Baki Khadija ta tabe tare da gallawa matar Harara Karaf Suka Ido,Aiko matar ta mike a fusace tayi Kan Khadija dai dai lokacin Abdallah ya shigo ciki Khadija ta fada jikinsa ta saki kuka,hankalinsa ya tashi yayi zaton wani Abu ne ya sameta,Matar dake tsaye tace kinci sa'a marar kunya Ni Zaki Kawowa Raini kin San kuwa wa kike Harara? AMANA ce Matar ALIM Allah ya taimakeki Dana farke miki ciki, Abdallah dariya ta kamashi mace da masifa Haka,yace ke ko Matar Alim kike ko wa wannan tafi karfinki wlh Kika taba wannan duk Kasar Nan Babu me kwatarki, Bana magana da mazan wasu ki godewa Allah na shiryu da Dane sai nayi Ball da wannan yarinyar me Maganar yare, ke Igbo ce ko? cewar Amana,suna Haka Abdallah sai bala'i yakeyi a ciki wurin yace sai yasa an rufe wajen tunda Suka sa Khad dinsa kuka, maaikatan suna ta faman bada Hakuri ,Khadija ganin Mijinta sai ta sake narkewa tana nuna Amana da yatsa Waccen itace ta dinga min tsawa harda cewa Ni tsinanniya ce bani da gata,Har babana dake Lahira ta ambato tana dura Masa ashariya,tace da Mama,Abdallah ransa ya Kara baci yace wlh sai na dau mataki yau baza ki bar cikin Nan ba sai Kinga kalar gatan matata,Khadija Ta Kara karkacewa tace har fa Ina Bata hakuri Ina ce Mata Ina da aure tace ba mijinki ba Surukarki ma taci kaza kazanta.....tana matse Hawaye tace Bazan iya furta irin zagin fitsarar da tayiwa Mami ba, su kansu masu aikin wurin duk sai da karyar Khadija ta daure musu Kai yanda Kiri Kiri take tsaro karya. Abdallah ya Kara fusata ya kalli Amana yace sai kizo ki farke Mata cikin mu gani Kuma kotu ce zata rabamu kinyi furucin kashe mata ta,Baki Bude Amana take kallonsu Yau ga shugaban Yan sharri Khadija Bata taba ganin uwar sharri irin Khadija ba, duk Masifar ta da Saurin fushinta sai mamaki ya hanata magana. Alim ya gaji da jira Driver ya kawoshi daukan Amanarsa da kansa Yana zuwa ya iske Ana ta bawa Abdallah hakuri sai Masifa yakeyi shi sai ya Kai Amana kotu, Alim ne ya shigo kamshinsa Dana Abdallah Suka gaure waje daya suka rikita wurin da kamshi kowa naji da kyansa da kudi,Alim baya son Hayaniya Abdallah ma Haka Yar Masifar da yayi har kansa ya Fara ciwo ya Dafe wajen, Alim Yana ji yasan Amanarsa ta shiryu baza tayi Haka ba,Haka kawai ma wannan Abdallan yazo Yana kalle Masa Matarsa ,hannun Amana ya jawo taso mu wuce sarkin fada zamuyi missing Flight gyaran Nan ya isheni idan Danni akeyi a barshi oya let's go. Abdallah ya hakura ganin kamar ma yasan Alim sai yaja Khadijansa zasu wuce,Khadija ta faki idon kowa ta wara yatsu tare da antayawa Amana zagi irin na ambola,Amana tace yau sai na koyawa yarinyar Nan Hankali,Jin ta Fadi Haka Alim yace zamu Bata ban son fitina kin sani,sai lokacin ta hakura Amma har Lokacin kwafa take ja tana a dakeka a hanaka kuka,Lallai yarinyar Nan yau taci sa'a Amma Allah ya hada mu watarana. Sai lokacin da Suka fito waje sannan Alim ya gane fuskan Abdallah yace ah Ashe ma Kanina ne Abdallah Wai Kaine kake iya masifa Haka Kai da na sani magana ma wahala ce,Abdallah yace ouch...Ashe Kaine Yaya Alim,gaisawa sukayi yace Ina Usman? Yana na nan lfy ai yayi aure,Shegen gari Amma ba gayyata ma,anyway bani number dinsa Zan nemeshi. Abdallah ya bashi number har Yar Hira sukayi kadan sannan yace Dama matarka ce wannan? Amana tace ae Mana Kanina gaskiya matarka ta iya sharri saura kadan na zaneta Allah ya kawoka,Khadija mazaunin driver ta koma ta dinga Danna Horn Wai Yazo su tafi,Gajiya tayi ta fito tace kazo mu tafi kafin na canja Shawara na wuce wurin Mami. Abdallah yace yau kuwa da kin gane kurenki zo ku gaisa da frnd din Ya Usman tare sukayi schl dashi a UK. Lokacin Khadija ta fito tana Jin kunyar karyar da ta yiwa Amana da zagin ambola Amma Haka ta gaishesu,Amana tace daga yau Ni Aunty ce kinji dai mu abokan yayanku ne, amma Mijin Nan naki Yana sonki, sai yau Naga Soyayya irin Tamu cewar Khadija,dariya sukayi gaba daya kowa ya wuce. Gida su Khadija suka wuce tare da kwasar Amarci, anyi bikin su Afrah lafiya an Gama,lokacin Kuma Abdallah yazo da Maganar tafiya Finland zaiyi wani course na 3yrs sannan yayiwa Khadija komai can zasu tafi tare acan zata Karasa karatunta itama. Sallama sukayi da Yan uwa da abokan arziki sannan Suka Wuce Airport ta Abuja zasu tashi. Suna Airport za ayi musu screening sai ga wasu zuka zukan gaske,Mijin yaro danye cakal Haka matar ma,yarone Karami a kafadar Mijin,wani matsiyacin aski da yayi shima kace mawakin turawa ne,tunda yazo wajen yake ta uban Iyayi yanda yake magana abin kallo ne,sai likewa Yar Matarsa yakeyi kyakyawar gaske ce,bashi da kunya Ana gani yake kissing dinta Yana fada Mata sweet words, matar zata tsaya kusa da Abdallah Khadija ta harareta tace ke matsa malama,Allah Baki hakuri matar ta fada a sanyaye,wata Dattijuwa ce ta karaso tana Ramlat Ina can Ina ta jiranku,Murmushi Ramlat tayi tace Mamee Kinga Wanda yace a barki ki Dan huta,Rankwashi Tsohuwar ta zubawa Dan Iyayi tace Muhammadu ka kiyayeni,Mamee Mohammad nake Ni gaskiya ko Sardauna,wannan yaro ka nace Masa ko kunya baka ji kawoshi DaAllah cewar Mamee,Sardauna yace pls karki Goya min da Ni bana son abin tsofaffin Nan naku komai sai kin kawo yawa,Kuma kin San jirgi dai zamu shiga,Mamee Bata kulashi ba taci gaba da rainon Dan Muhammad dinta da Ramlat. Sardauna kunnen Ramlat ya Kama tare da rada Mata yau akwai shagali Allah ya kaimu lafiya, Ramlat tana dariya kasa kasa tace Yesssoo kasan nayi missing naka alot Sardauna ikon Allah Sardaunan Mamee da Ramlat mu kadai, ki daina kirarin Nan da Hausa Na hanaki Yi min Hausa bana son yarana su Fara sanin Hausa Turanci zasu na Yi Hausar sai su tsince ta a gari,Dariya sukayi Ramlat tace karka sa nace sai kayi
Chapter 51 · 0% Book details