Sashe 3
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ba a auren talauci,kana me kudi sai me kudi talaka sai talaka,Dana ya auri Yar Malam Shehu ai naji kunya,burina duniya tasan da zamana,so nake duniya tasan Dana ya auri Yar manya. Mami Haka take ta kuri Babu ko sa Allah a ciki,duk abinda zaka dinga kuri ka Dora ranka Kai ba ruwanka da Allah to kuwa Allah zai iya kunyataka a idon duniya,Haka Kuma zai iya kyaleka ya baka abinda kake so ba ruwan Allah. Garin Zamfara kauyen Nahuce Liman fa ya dukufa ya dage Dole sai yaga bayan su Khadija,tsafe tsafensa yake tayi akanta yarinya karama sabo da rashin Imani. Khadija kuwa ta dage sai Kwangilarta take nemowa da yaranta suna aiki sosai,Haka Allah yake ko yaya kayi Abu idan yaso ya dafa ma sai asha mamaki,Khadija da kudin take ci dasu tufatarwa da kudin makaranta wa kannenta,Mama Sai mamaki takeyi kamar Wasa ga Khadija kuwa ta Zama 'yar Kwangilar harkar Noma, tayi katon asusu Ana Tara wasu kudin,ga samari yanda suke tururuwar sonta sabo da tsananin kyawun Khadija,indai kyau ne to a shafa Fatiha kawai a kanta,ga kyan sura da diri,skin dinta wata sumul sumul kasancewar babarsu Yar north Sundance farare ne kwal,Haka Babansu farin bafulatani ne,Khadija round face ne da ita,da hancinta madaidaici baiyi tsini da yawa ba,Idanunta Dara Dara,ga gashi har baya kusan tsakiya,hakoranta kanana kyawawa,ga dimple,girarta me yawa baka,Gata da uban Hips cinyoyi manya,gata da Da tsayi Amma ba can ba,kowa yaga Khadija yasan ta cika mace ta gaban kwatance,Haka su Merry ma kannanta kamar su sukayi kansu kyawawane sosai gwanin Sha'awa. Khadija sabo da zaman kudu rawa wajenta kamar mazari Kuma na Yan kudu takeyi ayi ta girgiza mazaunai,a wani duka kasa tare da rike gefen Riga Babu kunya ko a gaban uban waye Haka suke rawa har Maryam Merry,A kauyen Khadija tana da kawa Abu,Abu yau tazo gidan ba Islamiyya ta samu Khadija da Merry har Ihsan tare da Ahmad sun kunna gidan radio an Sa wakar Wizkid suna ta tikar rawar suna ihu eh...eh...eh...sun cika gidan,yanda Khadija ke rawar zanku kamar kanwar Zlatan,Mama tana aikinta dake itama kudu ta ratsata sai cewa tayi Abu Bismillah ga rawa fa kiyi kema,kunya ta Kama Abu tace ban iya ba,Khairat ta wani duka tana eh....eh...chineke God ah...ah...we dey chill woooo let's dance Abu,Common eh...ehh Merry ma ta jawo hannun Abu Wai sai tayi rawa. Mama tana kallonsu tana dariya harda gyarawa Ahmad rawar tana kalli yanda Khadija keyi maza ka koya kaima,Abu ta bude Baki Jin yanda Mama tace kunya ta rufe ta.