← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 53

Sashe 25

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a hankali tare da tura hannunsa a rigarta a hankali Wai Kar ta kamashi, sai da hannunsa ya Kai kansu ya shafo yaji wani shegen laushi sai ya lallaba ya zare hannunsa a fili ya furta ba ruwana Allah ya Baku hakuri,Khadija ta farka Jin Yana magana da sauri ya rufe idonsa Kam tare da yin baccin karya kunyarta yake ji,Khadija tayi tunanin bacci yakeyi sai ta dauki hannunsa ta Dora a saman dukiyar Fulaninta a Haka suka tsaya shi Wai kunya yakeji yayi mukus a Haka idonsa a kulle Wai bacci yakeyi. Jikinsa ne ya tona Masa asiri da ya fara rawa Kar Kar Kar kamar mazari, sai kace Khadija ta samu wani Table ko bench Haka ta dafe shi da Hannayenta Wai jikinsa ya daina rawa tunaninta kamar kujera ko wani Abu marar Rai ne Ana girgizashi,Yana ta rawa karrrrrr ita Kuma ta dafeshi iya karfinta Wai ya tsaya ya daina rawa. Sai tayi sauri ta cire hannunsa dake kirjinta sai ko ya tsaya cak jikin ya daina rawa,sai ta sake Dora hannun nasa Aiko jikinsa yaci gaba da karkarwa shike Nan ta samu abin Wasa sai ta Dora hannunsa a kirjinta sai ya fara karkarwa karrr sai ta cire sai ya tsaya cak sai dariya takeyi tana Haka shi Kuma kamar wani engine ba hutu,har sai data gaji sannan ta daina ya samu lfy ,ya wani matse idonsa tare da baccin Dole,itama tayi baccinta sai da Rana ta fito kwal sannan Suka farka tare da tsintar kansu cikin wani sabon dajin ba gida gaba ba gida baya. AsmaBaffa [12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: TUBABBIYA 36-40 Official AsmaBaffa Yakasai,Mom Haneef,Serky Baby,Mrs Muktar Lambata,Zainab Dinawa,Ummihauwa,Raliya Nura lawal,Ummu Hamdana,Fauzat, Maryam Adnan and Maman Sauban. Page nakune Fans Allah saka da Alkhairi. MAMAN MASHKUR Ina godiya da Jinjina. Khadija ta kalli gabas ta kalli yamma ta kalli gabas sannan ta kalli Abdallah,marartace ta Fara murda Mata,Abdallah yace a Ina zamu samu ruwa to? Sam bai kula da yatsina fuska da takeyi ba na ciwon Mara, Shuru tayi Masa sai yace sauri mu Kara gaba,Suna tafiya Khadija ta dafe mararta tare da durkushewa a kasa,da sauri shima ya tsuguna a gabanta Yana tambayarta me ya faru,Mararta take nuna Masa tana Hawaye,Hannunsa yasa a marar Tata Yana shafawa a hankali,Har ta danyi sauki sannan ya rike Hannunta suka ci gaba da tayi,Abu taji kamar ruwa Yana bin cinyoyinta,tana dubawa taga jini ne, tunani ta Lula ta kasa gane jinin Mene,sai ta fashe da uban kuka harda ihu,tsoro ne shima ya kamashi ganin jini na bin kafafunta sai Kuma can yayi Murmushi yace period kike Yi? Khadija tace Dama kasan sunansa? Abdallah yace yanzu na tuna shi,Zama yayi tare da Yi Mata bayanin jinin Haila da hukuncinsa harda wanka du,Khadija ta sani Amma yanzu Bata tuna ba sabo da Abdallah ya fita tunani a yanzu halin da suke ciki. Jin ba matsala bace sai ta daina kukan,suna tafiya suka hango katon Kogi da ruwa garai garai ba kowa a yankin,Khadija tace muje can ga ruwa na wanke jikina,bishiya Abdallah ya samu tare da ballo musu itacen aswaki Suka Fara goge bakinsu dashi suna tafiya suna Yi har suka Isa wajen ruwan, Kallon Khadija yayi tare da cewa juya bayanki zanyi wanka,Ba musu ta juya Masa baya ya tube kayansa duka ya shiga gefe kadan tare da yin wankansa ba sabulu,Yana gamawa ya saka dogon wandonsa da Singlet sannan yace na Gama juyo,Alwala yayi sannan yace sai kiyi kema,tace to Dame zan shirya kaina na toshe jinin? Abdallah yace ga rigata t-shirt tunda Bata da girma sai ki Sa Haka,pant fa? Yace sai dai tight Dina tunda Dan karamine zai shigeki, Murmushi Khadija ta saki sannan shima ya juya Mata baya ta Dan shiga gefe kadan ta cire kayanta dama skert da rigace a jikinta ta English wear ,Saida ta Fara wanke kayanta da pant din tas a ruwan sannan ta matsa wani wajen baya kadan ta wanke jikinta fes ta dauki tight din Abdallah Dan mitsili tare da linka Yar rigarta tasa ta shirya tsaf tayi kunzugunta dake tana da Hips sai ta cika Wandon daf,Rigarsa tasa sabo da tafi Tata tsayi har Rabin cinya ta kawo Mata,Fitowa tayi ta shanya kayan data wanke jikin wata bishiya,Abdallah ya kalleta ba karamin kyau tayi Masa ba,sai ta birgeshi rigar tasa ta amshi jikinta. Suna zaune kowa yayi Shuru suka hango bishiyar Guava tayi manya manya da cashew gasu Nan sun nuna,Zuwa sukayi Suka tsinko da yawa sai da Suka cika cikinsu dam sannan kayanta sun bushe sai kawai tasa skert din pant din Kuma da rigarta ta rikesu a hannu sannan Suka bar wajen. Mami zaune take saman Makekiyar Kujera ta nutse tana kada kafa duniya na Kai Mata,Alhj Shehu ne ya shigo tare da Zama kusa da Mami ya kalleta sannan yace Hajiyata ya akayi ne? Murmushi Mami ta saki domin ta yarda da Alhj Shehunta yanda yake nuna Mata kauna ba a cewa komai,Su Afra sai Abinda suke so shi yake musu sosai yake rikesu. Baba har yanzu Bai hakura ba,Kuma baiyyi fushi ba neman Abdallah da Khadija yake ko Ina a fadin Nigeria,Ita Kuma Mami tana can duniya ta samu ta daina neman Dan nata ma gaba daya,Mama ma Addua sukeyi sosai akan Allah ya Bayyana Abdallah da Khadija,Hafsatu Kam ba ruwanta ganin Baba Yana Business Kuma Allah ya dafa Masa yanzu Yana samun kudi suna Jin dadi sai take ganin kamar abinda tayiwa Abdallah shine ya jawo Baba yake samun kudi,tunaninta da Abdallah Yana Nan da Baba bazai samu kudi ba,Bata yi tunanin duk abinda Allah ya tsaga zaka samu duk duniya Babu me hanawa,Haka idan baza ka samu ba idan duk duniya naso ka samu baza ka samu ba wannan a rubuce yake. Ciwon marar Khadija ne ya dawo sosai,Kasa tafiya tayi,Abdallah ya tsuguna a kasa tare da cewa hau na goyaki,Da Sauri ta Dane bayansa har murna takeyi,tana bayansa ya mike tsaye yaci gaba da tafiya da ita Basu San ma Ina Suka nufa ba, suna tafiya har dare ya farayi ba gida gaba ba gida baya,Wasu gungun Yan Daba ne Suka yanko kwana kicif Suka ci Karo dasu Khadija tana bayan Abdallah tana baccinta, Yan daban ne Suka kece da dariya tare da furta aiki ya Kare basai mun wahala ba yau,ranka ya Dade a sanarwa Oga Shehu ga dai dai shi an samu,Abdallah kallonsu yakeyi kawai har suka ce Kai sauke wannan yarinyar a bayanka,Bacci takeyi Dan Allah karku tasheta baiwar Allah cewar Abdallah,Surutu ne ya farkar da Khadija ta tsorata da ganin mugayen mutane Haka dauke da muggan makamai ba shiri ta sakko kasa daga saman bayan Abdallah,Ogan su ne yace Kai muje Mana, Abdallah zaiyi musu Khadija ta girgiza Masa Kai Suka bisu,Yan daban Suka tasa su a gaba tare da tafiya dasu salin alin. Khadija tana rike da Hannun Abdallah Gam ta kalleshi suka hada Ido tare da sakarwa Juna Murmushi Mai kayatarwa domin yamma tayi lis yanayin garin yayi Dadi sosai suna Jin dadi,Yan Daban Nan suna satar Kallonsu yanda suke wani nishadi kamar ba kamasu akayi ba,ba ruwansu Basu San me duniya ke ciki ba, sai da sukayi tafiya me tsananin nisa Amma ko a jikin su Abdallah basa gajiya,sai can Suka hangi wani Dan karamin gida me kyau a cikin Dajin,gidan suka Karasa su Yan Daban sun gaji sosai da kyar suka iya karasawa sannan Suka kwaso lemuka da Ruwa suka Sha abinsu,Khadija tace muma a bamu musha,Ogansu ya gasa Mata Harara sannan yace Kai ya sunanku? Abdallah yace Sunana Khadija,Ni Kuma Abdallah cewar Khadija, Sigari Ogan ya kunna Yana bulbula hayaki yace Kai Baba wannan Yan rainin hankali ne Amma zanyi maganinsu Tiger dakko engine Nan kowa ka zana Masa Tatoo na sunansa daya fada Dan ubansu. Wanda aka kira da Tiger ya dakko Machine din Tattoo Nan take ya Kama Hannanu Abdallah Damtsensa ba Imani ya kafa engine ya Zanawa Abdallah Sunan Khadija a Damtsensa,Haka ya samu itama Khadija a Damtsensa ya Mata round da suna Abdallah da Capital letter ko wannensu,Abdallah baiyi ko gezau ba,Khadija ce ma tayi Kuka sabo da zafi,suna zaune gaban Yan Daban Nan Suka ji Karar Mota,Wata dariya sukayi tare da furta gafa Oga nan yazo zamu Sha Kudi,Oga Shehu ne yazo tare da escort dinsa suna take Masa baya,Yana shigowa ya kalli Abdallah da Khadija farin ciki ya kamashi irin Wanda yake bukata,Kudade masu yawa ya bawa yaran nasa suna ihu suna Masa kirari,Khadija ce ta matsa kusa da Abdallah tare da rada Masa ya kamata na canja kunzugu na Kar ya Bata Ni, ok Ki Bari a samu wuri cewar Abdallah ya furta Yana Murmushi. Kai ta jinjina gaba Daya Oga Shehu sai kallonsu yakeyi kamar maye ganin Basu damu ba harkar su sukeyi,da wasu ne da tuni sun Fara kuka Amma su ba ruwansu. Yaransa yasa Suka shakawa Su Khadija Wata Powder tuni suka zube kamar gawa suna bacci Nan take suka zuba su a mota sannan Suka ja motar suka Kara gaba,Tafiya sukeyi dasu Basu tsaya ba sai da Suka shiga cikin garin Maiduguri sannan suka nufi wani katafaren gida na Alfarma Katon gate aka wangale musu motar ta danna ciki tafiya akeyi a cikin gidan kamar zasu je wata uwa duniya sai da akayi tafiya me nisa sannan motar ta tsaya,wasu yaran Oga Shehu ne Suka zo tare da fitar da Abdallah da Khadija daga motar Suka shigar dasu ciki,takalman mutane ne iri iri gasu Nan da kayan sawar Yara,Manya,Yanmata da tsofaffi gasu Nan Harda na Almajirai da talakawa,wasu takalmin ma da Leda aka daure,Ba kowa cikin wani katon Palo sai Dattijo a rakube jikin bango,ciki aka shigar da Khadija tare da Abdallah dake kwasar bacci. Ruwa da Abinci yaran Oga Shehu suka kawo suka yi tafiyarsu,sai Dare misalin 11pm Suka farka daga baccin da Sukeyi,Mamaki ya kamasu ganinsu cikin gida me kyau Haka,Dattijon Nan dake karatun Qurani Suka gani Yana zaune gefe daya,Abdallah yace Dan Allah inane Toilet? Dattijon ya kallesu sannan ya nuna musu,Abdallah ya shiga Toilet yasha gyara sai kyalli yakeyi ta Bature,Harda yin wanka da sabulu me kamshi ga sababbin brush Nan da Toothpaste ya dauki sabo yayi ya shirya tsab yayi fresh sannan ya fito,Khadija ma ta shiga Haka tayi wanka da brush sannan ta
Chapter 25 · 0% Book details