← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 53

Sashe 19

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdallah ko ya farfado idan ya tuna sai ya sake Suma Haka aka kwana daya biyu sannan ya Fara samun lfy da taimakon frnds da Khadija da suke ta Masa Nasiha har akayi sadakar uku Dr Hussain ya Hana Abdallah sallama sabo da yasan Yana zuwa gidan zai sake dawowa gidan Jiya,Khadija ke sintiri taje gida tayi girki taje gidan makoki ta dawo asibiti ta kula da Abdallah ita da Dr Hussain.
Yau kwana Uku Yau Humaira tazo dubiyar mijinta, Khadija lokacin taje gida sai da ta Fara zuwa wurin taaziya sannan ta wuce gida tare da gyara part din Abdallah da Kuma part dinta sannan ta shirya lafiyayyun abincinta iri iri na Yan gayu,Wanka tayi ta shirya Cikin Lace Brown and Golden batayi kwalliya ba sabo da kukan Rashin Daddy da sukayi Babu nutsuwa,Mayafi ta yafa sai tayi Masifar kyau ta fito a wata Hajiya malam,Da Sauri ta shiga Room din da Abdallah yake dauke da Sallama a bakinta,Humaira tana gefensa sai Danna waya take tana murmushi, Khadija tana shiga suka hada Ido da Abdallah ganin Yana hawaye yasa Khadija ta Karasa da sauri kusa dashi tasan Daddy ya tuna, Hannunsa ta rike tare da tsugunawa a gabansa Sabo da Humaira ta tare inda zata zauna,Kayi Hakuri Lokacinsa ne Addua ita zamuna Yi Masa Ok? Kai ya gyada mata kawai Amma ya kasa hakuri,sai da Khadija tasa yayi Sallar Laasar da Addua sosai sannan ya samu Yar nutsuwa ya koma saman bed ya kwanta,Abincin ta zuba a plate sai kamshi ke tashi,Sai gani sukayi Humaira ta mike tana tsaki ta fice abinta.
Khadija tace Alhmdllh dama duk kin tare wuri Ni gaba ta kaini ta zauna a gefen Abdallah tare da cewa to Dan zauna kaci abincin,Kai ya girgiza Mata shi ya koshi,Fuska ta Bata haba ranka ya Dade naje gida Nasha wahala kace baka ci pls ka Dan ci Dan Allah haba me kyau,Daddy Inshallah Yana Aljanna firdausi Yana can Yana Jin dadinsa Kai kana Masa bakin ciki kana kuka,Fadin hakan data yi sai Yaji kamar Daddy Yana Aljanna Yana Nan Yana kuka sai ko yaji sanyi,Khadija taci gaba da Masa kalamai masu Dadi da Wasa sai ya Ware ya zauna saman bed din,Khadija ta ebo abincin tana murna ta Kai Bakinsa ya karba Yana ci,sai da ya koshi dam ta kyaleshi tace saura wanka ko na maka,kallonta yayi da sauri sai tayi Murmushi tare da boye Fuskarta ta Furta Wasa nake maka,dariya ma ta bashi Amma baiyi ba ya shiga wanka ya fito ta dakko Masa lotion dinsa ya shafa ta Mika Masa kayansa Wanda ta dakko Marasa nauyi ya shirya kamar bame jinya ba,Har Bayan sunyi Sallar Isha sai ga Mami da Yan uwanta.
Tunda suka zo suke hararar Khadija suna fadar bakaken kalamai tana jinsu ita dai har suka Gama duba shi suka tafi gida,gefensa ta koma ta zauna har ta fara gyangyadi,gefensa ya matsa Mata yace kwanta,Hijab mayafinta zata cire yace idan wani ya shigo fa? Da kansa ya gyara Mata Mayafin ta kwanta a gefensa,Wani shock suke ji kawai duk tunanin Abdallah na mutuwar Daddy sanda yaji jikin Khadija na gogan nasa wata nutsuwa ce ta shigeshi da farin ciki,tunaninsa ya tsaya cak ya nutsu Sunyi Shuru zuciyoyinsu ke bugawa kawai,Juyowa Khadija tayi suna facing juna, da sauri ya dauke kansa,a hankali tace sleep sleep tana shafa Kirjinsa,gaba daya ta hargitsa Masa tunani Baya son ya Mata wani Abu sai ta Kara girma Amma ji yake Anya zai iya kuwa? tunawa yayi ai ba soyayya suke ba,ba Kuma sonta yake ba sai ya canja tunani,Yana ji tayi bacci abinta a nutse,Dr Hussain ne ya shigo yace Kace shegen a gadon asibitin ma Amarci kakeyi,Gobe Zan sallameku ku huta,Murmushi kawai Abdallah yayi,Dr yazo Wai zai sa Masa Drip ya juya tare da Rungume Khadijan sa a jikinsa Wai baza a sa Masa ba,Dariya Dr yayi kawai ya fita abinsa a Haka suka Sha baccinsu harda makara yau.
Washe gari da wuri aka sallamesu suka wuce Family House Ana ta makoki,Abdallah mutuwa ta dawo Masa sabuwa kuka ya dinga yi Haka duk ya bawa Yan gidan kuka Suma again,Baba ne me lallabashi Yana Masa Nasiha,Yana part din Mami duk yaji kewar Khadija ya Saba kullum suna tare,duk sai yaji ya damu gashi Mami baza ta Bari tazo wajensa ba.
Khadija kuwa tana part din Mama tana baccinta,Abincinta yake son ci gashi baida number dinta,Merry Ce ta shigo tare da kawowa Mami kayanta data sata wanki,Mami na kusa ba dama yace a turo Masa Khadija,Mikewa yayi yace Ina zuwa Mami,a compound ya tsaya Merry tana Fitowa yace Ina Sis naki? Tana dakinta ba kowa ma a part dinmu kaje kawai Mama sun tafi Dubiya makwafta,Part din nasu ya shiga ya gaji da Tsafta kamshi na daban ne,Nutsuwa ce ta shigeshi Har Bedroom dinta ya shiga ta fito a wanka daure take da guntun farin towel ta daure gashinta da wani farin Towel din,Cinyoyin Nan gasu Nan santala santala farare tas dasu hips kamar me.
Kasa dauke idonsa yayi akanta sai data karaso gabansa tace Sannu da zuwa Bro ya jikin? Zauna ga bed Harara ya zuba Mata sannan yace kinzo kina ta bacci banci komai ba fa? Da Shagwaba ya furta sai yayi kyau ya birgeta,Tana shafa lotion ta duka tana shafawa a kafafu tana cewa ai dazu nayi Abinci naka Yana Nan,Shi kuwa hankalinsa Yana kasan mazaunanta data duka Suka fito ta Baya kadan,Sabo da yafi gani da kyau sai ya kwanta a bed din,Yana lekawa Baya gani sosai,tana gamawa ta mike tsaye tana gyara towel din,tace bacci zakayi Kuma? A'a kawai ya iya cewa hankalinsa ya tashi.
Hijab tasa zata sa bra da pant yace oh har wani Hijab Zaki sa Ni ga Dan iska ko? Baki bude tace kayi hakuri badan Kai nasa ba,to cire ki shirya a Haka Dan munafunci,Hijab din ta cire sannan ta dakko Bra dinta da pant ya gansu manya a ransa Yana ayyana girmansu yace Wai ke bakya period ne? Khadija kunya ta kamata tace ae ban taba yi ba wlh har 17yrs ko asibiti za'a kaini?
Sai wasan Haihuwa Kika iya keda wannan Abun take ko wa cewar Abdallah,haba ai Mama tace mun girma ba Wasa yanzu na daina Yi dama Abu ke sani Dole na girma yanzu Matar aure ce ni ta furta tana murmushi,Baki ya tabe tasa hijab ta kawo Masa abinci me Dadi,a hankali ya furta kin San ban warke ba Taya zanci Abinci da kaina? Dama Ita ta Saba ko bawa kannenta a Baki ma, kusa dashi ta matsa Yana zaune gefen bed, ke cire hijab dinnan Yana takura min,Kai da ba ajiki naka yake ba ta Ina zai dameka?Shuru yayi Mata tasan Bai son musu sai ta cire sai Dan guntun Towel dinta a ransa yace wannan Hurul ein din duniya ce Dan dai kawai tayi karama da yawa ne inyi soyayya da wannan ko na batawa kaina lokaci tare da zubar da girma na,kawai ta dinga bauta min shike nan.
Humaira tana can gida tana fushi tare da jiran Abdallah ya dawo,kawai sun barta a gida ko bukatarta baifi sau uku ya taba biya Mata ba,tana huci ta Kira Kawarta Zuly ta fashe Mata da kuka,Zuly tace lfy? Humaira tace Allah ya Isa kun cuceni kun zugani nayi aure gashi ku Kuna ta shanawa Ni kuwa Ina kunshe a gida bana Jin Dadi da Mijina ko kadan Ina bukatar Namiji wlh idan na gaji wurin samarina Zan koma.
Zuly ta sheke da dariya tace Albishirinki dama tazo na samo Mana shegun malamai sai abinda kika ce da Abdallah shi zaiyi wannan Khadija sai ya saketa,gobe zanzo gidan da wuri Hajiya ta,Humaira tace Allah kawata na gode sai kinzo.
Hafsatu zaune take cikin danginta suna zugata,Yayarta tace Kika sake Haka za a raba gado Baku samu komai ba Tunda kin tsaya Wasa tun Daddy Yana da Rai Baki yago Mana komai ba to wlh ki mike tsaye sai fa kin tashi tsaye kin fisgi rabonki idan ba Haka ba gidan Nan kina gani zai Fi karfinku, Hafsatu tace ai nayi Shiri Yar uwa,wannan Dan Iskan Abdallah shine matsalata sai Naga bayansa shine kawai zamu samu lfy,Kwarai kuwa ki tabbata kin dauki mataki cewar Kanwar Hafsatu,Dariya da shewa sukayi Baki dayansu.
Humaira Washe gari Zuly tazo tace Gobe za ayi sadakar Bakwai Mijin naki da Yar Iskar suna can gidan ko? Baki Humaira ta tabe sannan tace suna can maybe sai jibi zasu dawo,wlh Zuly Naga kamar Yana son yarinyar Nan,Zuly ta Ciro wani magani a jaka tace gashi Inji Malam Rai banza,Au sunansa Rai Banza? Kwarai kuwa cewar Zuly ki sawa Khadija a kasan pillow dinta Dan kadan Zaki Barbada data kwanta akai to da kafarta zata bar gidan Nan,Kuma ba family House zata je ba sannan ko Yan uwanta baza ta tuna ba kawai baza ma tasan ita wace bace Haka zata dinga garari a duniya ita ba mahaukaciya ba lfy Ras ba, galantoyi ta farashi yanzu har karshen rayuwarta.
Sannan ko wasu sun riketa baza ta taba Zama ba sannan baza ta Bari ayi Mata magani ba.
Farin ciki ya cika Humaira tace saura na Ogan ya kamata na mallakeshi fa,Zuly tace shi din banza ki fara korar kishiyar nasa me sauki ne,sai Uwarsa Yar iska har ita Zan Kora ta koma danginta can yanda baza ta dameni ba.
Tafawa sukayi suna dariya sai yamma Zuly ta shige motarta ta wuce.
Mami zaune take tare da Afrah,Mami tace Kai Na Matsu ayi Bakwai a raba gadon nan muga kasonmu sai yanzu nake Dana sanin haifar Yara kadan,da nasan hakane ai Haihuwa zanyi da yawa shike Nan da gado me yawa zamu samu mu da talauci har abada,Afrah tace wlh kuwa ai Ni na Matsu a raba na sake siyo dankareriyar mota,Haka suke ta hirarsu ta gado ko Bakwai ba ayi ba.
Rahmatu, Haule da Bilkisu sun hade kansu su Matan su uku da yaransu Suma suna so zasu hada Kai da lauyoyi sabo da kaso me tsoka ya Fado kan yaransu,Haka yaran ma sauran Wanda Daddy ya Haifa dake wasu garin da iyayensu Duk sun zo sai an raba gado zasu tafi,kullum cikin fada da rikici suke,da gulmace gulmace,Abdallah Yana sane da duk abinda ke faruwa shi da Baba basa ko cewa kala,Haka samarin ma kowa ya Dora burinsa akan gadon da zasu samu,Wanda ya mutu shi ya mutu.
Chapter 19 · 0% Book details