Sashe 31
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Light blue dinkin zamani na Yan gayu yasa duk da cewa Bai fiye sa manyan Kaya ba Amma tunda Khadija ce ta zabo Masa to zai sa,yasha kyau na gasken gaske,yunwa nakeji Ya Abdallah,Nayi order yanzu Zan sauka na karbo,Khadija ta Bata fuska kishi ya kamata ita Bata so gaskiya ya fita Yan matan bariki gasu Nan a Hotel sai sintiri sukeyi suna neman masu binsu. Zan bika Ni muje tare mu karbo ya tsinci muryar Khadija,ya Zan barki ki fita a nan Maza ko Ina anan,Dan mitsil din bakinta ta turo tana kunkuni ai ga Mata Nan su a ko Ina kana fita zasu na kallonka,Me kike cewa Don yajita sarai,Sai tace ba komai tana cuno Baki,Murmushi yayi ya nuna baiji me tace ba ya nufi kofa zai fita,Kafin ya fita tace to ka canja Kaya Mana, what? ya juyo ya tambaya sai Kuma taji kunya tace cewa fa nayi a dawo lfy,Murmushi ya saki kadan sannan ya fita ya Dan Dade sannan ya dawo lokacin Khadija sai fushi takeyi ita kadai maybe wata ta kalleshi. Ledojin abincin ya ajiye Yana kallonta yanda ta Bata rai,lfy? Me ya faru? Murmushin yake tayi Kawai tace ba komai sai Lokacin dabara ta Fado Mata tace uhm Wai garin Nan kuwa da Yan Mata? Abdallah ya Bata amsa Yana taje gashinsa again sosai ma kyawawa ma dasu gasu Nan ko Ina,Baki ta tabe kishi ya kamata ita Bata da kyau kenan sai Kuma tace suna zuwa Hotel din garin Nan Kuma? Ko Makkah ai Ana zuwa Hotel mene a ciki mutane ne fa Basu gane maanar Hotel ba,Masauki ne na Baki kafin Mutum ya bar garin ko ya samu wurin Zama Amma mu Hausawa an maidashi wurin Badala sannan kowa aka gani a Hotel to Kawai Iskanci yaje Yi baza ayi Masa zaton Alkhairi ba. Kamar Khadija zatayi kuka tace to wa yace a dinga zuwa Ana Kai Mata ai gaskiya ne Ana iskancin,kallonta Kawai Abdallah Yayi da mamaki yanda ta dage tana fada,Abincin ya bude Mata Fried rice Tasha salat da kaza,sai kayan jika makoshi gasu Nan,Sai Kuma Hadin tea da chips shima gasu Nan,Na koshi ta furta,da sauri ya kalleta yace hmm Baki Isa ba yarinya Kinga Ina Wasa dake? Kince yunwa sannan kice baza kici ba,wlh Kika sa Wasa baza kiga Su Mama da wuri ba,ban son Shirme,Ganin ransa ya baci ta jawo tana kumbura Baki ta Fara ci kamar zatayi kuka,Better ya furta shima ya shiga cin nasa,sai Gashi Khadija duk ta cinye nata saura kadan ta rage taje ta wanke Hannunta da Baki ta dawo tana Shan Fruits,sai da ya gama sannan ya mike ya wanke hannunsa shima ya Kara gyara sumarsa tare da feshe jikinsa da wasu turarukan Yana Gyarawa Yana ce Mata Zan fita ki kula da kanki ba dadewa zanyi ba,Zumbur ta mike tace Wai Kai a Nan garin Ina ka sani? Sai kayi ta fita yawo kana driving Ina zakaje?. Khad banson zargi ya shiga tsakaninmu wasu Document Baba ya turo Zan karba,Ni ba zarginka nakeyi ba Amma ka tafi Dani,Wurin cike yake da maza bazanje dake ba,Komawa tayi ta zauna kamar zata fashe sabo da fushi. Fita yayi abinsa Yana fita ta zurma katon Hijab har kasa da sauri ta lallaba tabi bayansa a hankali tana lallabawa tana sanda kamar Barauniya,idan taga kamar zai juyo ya kamata sai ta rabe a jikin bango ta kame kamar wata Soja na bin Mai laifi zai cafkeshi. Masu aiki a Hotel din da sauran mutane kowa kallon Khadija yakeyi wasu suna dariya ma,can sai ya juyo zaiyi magana da wani maaikaci da sauri ta buya a bayan wata katuwar flower,yaso yaga Kamar Khadijansa Amma sai ya nemeta ya rasa ya zata gizo idonsa yake Masa sai yayi Murmushi yace Kai gaskiya Ina sonta da yawa har gizo take min yanzu. Khadija tana Dan leko da idonta ta tsakiyar Flower kowa ya ganta sai ta daura yatsanta a saman lips dinta Wai yayi Shuru,wani ne yazo ya tsaya a gaban Flower data boye ya Kare Mata Abdallah,da sauri ta dawo bayan Mutumin ta duka tana leko Abdallah har ya fita Compound na Hotel din,Da Gudu ta bi bayansa sai Kuma ta rabe a wani lungu kadan tana lekoshi zai shiga mota kenan sai ga Wata mota karama me shegen kyau tayi parking wata dalleliyar Yar gayu budurwa ta fito da takalmi me tsini tana taku dai dai,da sauri Budurwar ta karasa gaban Abdallah tana zuba Masa Murmushi,Shima Murmushin yayi Mata me tafiya da ruhin Yan Mata da Alama sun San juna. Da Sauri Kh adija ta lallaba tana tsallen kwado ta fada bayan flowers tabi tanan tana matsowa lokacin Abdallah ya ganta Kiri Kiri,sai yanzu ya gane Ashe itace tun dazu take binsa yayi tunanin gizo take Masa,Yanda takeyi dariya ta bashi sosai Yana kallon wurin da take boye Yana dariya,Sam Bata wannan Budurwar yakeyi ba hankalinsa Naga Khadija. Budurwar tace Wai yau Abdallah ke dariya Haka,kai da ko a schl duk abin dariyar da za ayi baka Yi meke baka dariya Haka ne? Sai lokacin ya kalli Budurwar yace Haneefah ya kk ya kwana biyu? Me kikeyi a Nan? Wani meeting mukazo Yi wlh a ministry namu aka turo mu,ya bayan rabuwa? Tunda Muka Gama University a London sai yau na ganka, I missed u so much,Karaf a kunnen Khadija dake boye bul ta fito ta matso da sauri gaban Abdallah,Lfy Alhmdllh cewar Abdallah,Haneefah tace Abdallah ka gujeni baka da kirki wlh ba irin son da ban maka ba Amma kaki aurena nasan bani da halayen banza. Abdallah a tsorace ya kalli Khadija dake kallonsa kamar zata zabga Masa Mari,Ai ni tuni Ina da aure Haneefah kiyi Hakuri komai ai mukaddarine daga Allah,I'm so Jealous Abdallah wacce me sa'a ce Haka a duniya har naji kishinta ko wace na tsaneta,Ni wlh ba ruwana da matarka ko Mata uku gareka zanje a ta Hudu Sabo da Allah ya Sa min sonka. Ido Abdallah ya zaro Khadija na tsaye yace kiyi Hakuri kawai Haneefah,Kafin tayi Magana Khadija cikin Hausarta da Bata fita sosai tace ance ba a sonka Dole ne Wai kwarto Kana bin Mijin wani,He is My Husband Go and find your Own,He is mine,ah...see me see wahala ko Ana aure dole ehhh? Na by Force? Khadija ta Karasa da karaji,Haneefah tace kaji Yar iskar yarinya Dan ubanki Yar ficika dake Abdallah zai auri yarinya Haka kamarki? Me Zaki iya bashi har Zaki zo kina fada min magana,Abdallah da manyan Mata irinmu masu aji ya Dace....tace Dalla...Dalla....Rufe Mana baki kamar mangalar Donkey, How Dear you talk to me like that, Shi kanshi Abdallah tunda Haneefah ta zagi Khadijansa yaji ya Kara tsanarta, yaji Dadi da Khadija ta Mata Haka ma,Masifa Khadija ta Fara Kaine Marar class ka saya kana fadawa Namiji kana sonsa Yana cewa no kana a'a Kai sai an aure naka,Dole ne ba a sonka Kwarton banza woooo.Haneefah masifa take gani ruwa ruwa wurin Khadija,sai da Khadija ta Gama sannan Haneefah tace sai nayi maganinki tunda baki da kunya,Abdallah kaji kunya yarinya kamar wannan ka aura me zata maka idan ba Shirme ba...kafin ta Karasa Khadija ta damki Hannun Abdallah tare da bude Masa mota ya shiga tace Allah ya tsare min Kai,a dawo lafiya,kayi tuki a hankali,take care of ur self for me. Kai ya Daga Mata kamar wani danta,Haneefah ta tabe baki tace Abdallah Kaji kunya wlh Kyan yarinyar kabi ka aureta Dan tana da kyau shine ya rudeka ai kuwa zaka Sha kwaba,Khadija ta rufe Masa mota tare da daga Masa Hannu tana murmushi shima Haka yaja motarsa,Khadija ta juyo a fusace kan Haneefah tare da tattare Hannun Hijab dinta tace kace dazu me? Tsorata Haneefah tayi Don da Alama Khadija Bata da kunyar uban kowa Kuma taji kamar yare ce ba bahausa ba zata iya komai sai ta kwashe da Gudu da takalminta me tsini tana cankal cankal tayi ciki. Har Khadija ta koma Room dinsu bala'i takeyi tana mita Taki hakura,Har tayi Sallah tana idarwa ta Dora masifarta,toilet tana wanka sai masifa takeyi,Har me gyara room tazo tana Gyarawa dake Abdallah yace mace ce zata dinga gyara musu room ba Namiji ba saboda Matarsa, sai matar tana aiki sai taji Khadija na kunkuni ita kadai,Tunanin Matar itace ta batawa Khadija sai Hakuri take Bata har ta Gama ta fice musu a room. English wear tasa riga da skert tayi matsiyacin kyau,Sai 5pm ya dawo,Yana Knocking taki budewa Wai fushi takeyi ya kula Haneefah dazu sai da ya Dan Dade a tsaye sannan ta bude,Dan bakinta ta cunoshi dama tun farko ya San Nacin Masifar Khadija,Da kyar tace sannu da zuwa,Ya kalleta yana sani yace Dan tayani cire kayana na gaji da yawa,Budar bakin Khadija sai tace mu da muke Yara me zamu iya yiwa manya irinka,Ashe Muna da Rana muma?,Tohhh Abdallah ya furta Yana murmushi yace to ai bani na fada ba ko? Kaine ka sata ta fada min,dama can kana da burin fada min kana neman Hanya sai ga me baki tazo ta fada min,Kaine ka zugata,Baki Bude Abdallah yace au sharri Zaki min kina fa wajen komai ya faru,Baki ta murguda tace waya kayi Mata kuka tsara abinku ai sai ka Fadi abinda manya ke bayarwa Wanda Ni yarinya bazan iya ba,nafa san me nakeyi ai dadin abin ba a girma bane ehe, Dariya Abdallah ya danne yace au Ashe jarumace nake Jin tausayinta Zaki iya Dani Ashe? Khadija ta Masa wani kallo sannan tace nawa kake to,Wai gaba Daya da Shekara nawa ka girmeni? Nawa kake yaro? Mamaki ta bashi Lallai taga makwancinsa da Khadija ko magana da kyar take iyawa a gabansa Amma aure yasa ta rainashi yau shine yaro ma. Ki dai kiyaye Bakinki Dan wlh Zaki sa nayi maganinki gwara ki lallabani naci gaba da daga Miki kafa Kar ki tunzurani ki ballowa kanki ruwa,Murmushi Khadija tayi ta mike tsaye harda rike kugu tace Ruwa? mene idan na balloshi ai sai wanka zanyi a ciki nayi wanki ma sannan na Sha yo wani abin ne a ciki in Banda asha ayi wanka? Khadija Bata gane Hausar Abdallah ba hh. Waccen Yarinyar me Baki kamar Mangala ka fada Mata ta kiyayi Khadija wooo Zan iya cire Mata Kunne, hannunta Abdallah ya jawo tare da