Sashe 5
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mami Ina so next Month zanje Usa,Baka Isa ba Abdallah wlh kaji na rantse ka Gama Masters ba inda zaka tafi Daddy ya Gama shiryama aikinka sannan ga kasuwancinka kanayi,Office dinka ya Gama maka komai sabo da Haka aiki kawai zaka Fara Nan gaba ayi aurenka,Yasan tunda ta rantse ba Kuma canji kawai sai yayi Mata shuru ya mike tare da tafiya part din Daddy. 4:30pm kida kawai ke tashi a gidan na Dj sai rawa ake cashewa Ana ci Ana Sha suna farin ciki anyiwa Hafsatu kishiya karya ta Kare,Tunda motocin Amarya suka tsaya kowa ya gyara Ido zaiga Amarya ga kida na zamani ya cika ko Ina,Lokacin Khadija sun Gama rudewa da ganin gida Haka hadadde Wanda Basu taba ganin irinsa ba ko a mafarki,Mama Da Madam Ngozi suna gaba sauran suna baya Khadija da Merry tare da Ahmad mamaki sukeyi,suna kalle kalle Dai dai lokacin Abdallah ya fito zaije part din Daddynsu, Baki bude ake kallon su Mama domin zaton kowa arna ne basa Sallah musamman Ngozi Tare dasu Khadija. Khadija tuni farin ciki ya cikata a Nan gidan zasu zauna,sai ta daina bacin Rai sai Murna,Jin kida yasa jikinta ya fara rawa Bata San data duka kasa ba tare da rike gefen rigarta ta Fara rawa tana jijjiga Hips Haka Merry ma, Itama Madam Ngozi ta Fara rawa suna tafiya da rawa,Bakin kowa yaki rufuwa,Abdallah daya gansu Saida ya tsaya Kallon ikon Allah don Bai Zaci ita ce Amaryar Kanin Babansu bace,dama ance da yaranta zasu tare,Rashin kunya ta gaske ya gani musamman Khadija da tafi kowa ga tsangalalliya r shiga,itama Mama baza kace Amarya bace,sai Dan Karan kyau kowa sai da ya yaba. Alhaji Karami gidan ya shigo ya Iske Khadija da Yan uwanta suna cashewa,Farin ciki ya kamashi sun saki ransu,Khadija tana ganinsa ko kunyar ba Bata ji ba,Abdallah Yana gefe Baki a bude Yana Kallon ikon Allah,Khadija da sauri ta bi bayan Alhaji Karami ta wuce da gudu Suka jera tare dashi suna Hira,tace Alaji wannan gidan Yana da chau Amma ku akwai kudi ne gaskiya,Gashi kowa ya waye a gidan Yan gayu ne,Sam Khadija Bata kula da Abdallah ba Wanda ke Jan tsaki an kwaso musu arna. Part din Hafsatu uwar gida Wanda yake cike da danginta aka wuce da Mama da yaranta,Hafsatu ganin kyawu irin na Mama gabanta ya Fadi,Bata Zaci Haka ba musamman da akace Mata tubabbu ne,kishi da bakin ciki ya taso mata,ta mike tsaye gayyar tsiya ki tafi part dinku shegu Tubabbun Arna,Nan kawaye da Dangi suka kwashe da dariya,Mama Cikin Hausarta da Bata fita tace wallayi mu dai ba Tanbabbu ne ba,Dariya suka kwashe da ita gaba daya,uban Mene to cewar Hafsatu,ganin Haka yasa Yar Uwar su Daddy taja su Mama zuwa hadadden part dinsu sama da kasa ne,Mama tana sama yaranta a kasa,yasha kayan Alatu Babu abinda Babu a ciki. Abinci iri iri aka kawo musu,Khadija kuwa tana Wurin Alhaji Karami ta makale Masa,Tare suka Isa part din Daddy Baban su Abdallah Wanda shima Abdallah Yana can,Da Sallama suka shiga,Abdallah ta gani cikin rantsatsun kana Nan Kaya yasha uban kyau tunda take Bata taba ganin me kyansa ba,ga kwarjini da haiba,Fuskar Nan murtuk ba Rahma,Har kasa Khadija ta duka tare da gaisar da Daddy,ya Amsa da sakin fuska tare da cewa Ashe kun iso? Cikin Hausarta wacce da kyar takeyinta tace Yes Dad Munzo Kai najiya Dadi wallayi wannan gida me Chau ne, da Ina ta fushi Amma Ina zuwa na daina fushi Kai... Alhmdllh Daddy Munsha rawa yau yaran gidan Nan Yan gayu ne,Hausarta ce ta bawa Daddy dariya yace to Haka ake so ga yayanki Abdallah sunansa,Khadija ta kalleshi ko kallonta baiyi ba,tace Samari sannu fa wooo gaskiya kana da Chau,Daddy wannan yafi kowa Chau sose,Ina kwananmu? Abdallah a ransa sai zagin Khadija yake kawai ta cika Masa kunne da hayaniya,Sabo da Alhaji Karami ya Dan saki fuska yace lfy,Baki Khadija ta tabe tace wannan ba fara'a fa Daddy kullum yaronka Yana fushi aka, Kai ka Zama kana smile Yana da chau, Mikewa tayi Abdallah yabi kafafunta da kallo ya dauke Kai. Bayan sun fito Khadija part dinsu aka rakata ta tana cin Abinci ta jawo hannun Merry suka fito inda masu Dj ke cashewa Matan gida Ana ta shagali,Khadija ta kutsa ciki Ana kallonta wuri ya cika maza da Matan gidan Ana kallon ikon Allah,Lokacin Mami taje ta jawo Abdallah Wai Dole sai yayi liki yanda Hafsatu zata Fi Jin haushi,ala Dole ya biyota Yana kunci,Khadija ta karbi speaker ta Fara magana. Assalamualaikum wooo.. Alhmdllh muna godewa Allah fa daya kawo mu wannan gida me Albarka, I'm so so Happy ganin Mamana a gida iri wannan,we Hope zaku karbe mu, Yan Matan suka Fara tabe Baki suna kus kus Usman da yake saurayi Dan 34yrs yace yess oooo. Khadija ta washe Dan bakinta tace thank you Bro,so Yanzu Dole mu nuna farin ciki da muka zo wannan Family,Haj Ramatu matar Daddy ta farko tace Aiko Dole watarana ku bar Mana gida,Khadija tace baza mu fita ba wooo Muna nan. Merry Ce ta karbe speaker tace we must Dance today Coz we are in Good Mood, Dj play the music abeg. Dj ya saki Sautin wakokin Nja zo kuga Khadija da Merry ka rantse gidan gasar rawa suke,sai da suka birge uban kowa da rawarsu,fili aka Basu gaba daya Ana Shan kallo ba a San sanda aka rufesu da liki ba,rawa suke me a zabar kyau a nutse,sai da suka kayatar da kowa,Ko uban Iyayi Abdallah kasa daina Kalla yayi ya zuba musu Ido,Khadija ta jawo Usman Ciki,ta Figo hannun Sagir da Omar tare da wasu Yan Matan tace Dole suyi Suma,suka danyi kadan Ana ta dariya da liki,Abdallah dai ya kasa motsi,Khadija tazo wajensa tace Dan gidan Daddy kayi liki Mana oya spray the Money for me,Ko kulata baiyi ba,Khadija ta faki idonsa ta fisge kudin ta koma filin ta Fara liki tana Wasa da kudin Yan dari dubu dubu, Abdallah Kuma ya juya ya koma ciki part dinsa. AsmaBaffa [12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: TUBABBIYA 3 Official AsmaBaffa ZAINAB GARBA BUTALAWA page dinkine jinjina gareki da tarin Godiya wajen Kokarin yin Document na dukkan Novels Dina. Fans ku tafawa Zainab Garba Butalawa domin itace ke muku Document na dukkan novels Dina,sabo da Haka masu Sharhi ku kwashe Mata da tafi. Sai wurin 9pm sannan suka Gama shagalin taronsu, Hafsatu matar Alhaji Karami Haushi Wai itama an Mata kishiya karyarta ta Kare,Khadija kuma wurin Mama suka koma,Khadija ta zabi lafiyayyen bedroom dinta,Haka Merry ma da Ihsan dakinsu daya da Ahmad kowanne dakinsu daban lafiyayyen gaske yasha kayan more rayuwa,Madam Ngozi da sauran Dangin Su Khadija da suka rako Amarya Nan suka kwana washe gari Dangin su Daddy suka sauki baki da Kyakyawan Kari na Alfarma, yayin da Hafsatu ke cika tana batsewa tare da habaici akan Dangin Su Daddy Dangin Miji kenan Wanda dama Suma murna sukeyi da aka yiwa Hafsatu kishiya sabo da Bata da mutunci ko kadan. Misalin 9am Su Madam Ngozi suka yi shiri Driver ya maida su Zamfara kauyensu.Daga Mama Sai yaranta hudu su suka rage. Duk yawan Yan aikin gidan Nan Hafsatu ta Hana ko wanne shiga part din su Mama bare suyi musu gyara da girki etc,Ganin Haka yasa Khadija da Merry tare da Ahmad har Ihsan suka zage suka gyara part dinsu sabo da dama tsaftar masifa ce dasu har tayi yawa ma,ga iya girki,kamshin dake fita a part dinsu na daban ne,Haka girkin da Khadija keyi a kitchen ya turare gaba daya estate din da kamshin Dadi,sai gulma akeyi ai yare Dama sun iya girki, Upstairs Khadija ta hau tana shanya Kayansu data wanke a Washing machine daga ita sai 3qutr da Yar bingilar Riga,surarta me matukar kyau ta bayyana,wakokinta takeyi na yaren Igbo, dai dai lokacin Abdallah ya fito shima ta samansa corido Yana Shan juice tare da shakar fresh air, kasancewar Girman Kudu ne Su Khadija basa magana a hankali Waka take rerawa da karfin Wanda Ya bawa Abdallah damar Jin wakar ta,juyowa tayi suka hada Ido,da sauri ta washe bakinta tare da kwallawa da karfi tace Hi.....Harara ya watsa mata,jikinta ne yayi sanyi sai ta share Amma ta kasa hakura ta sake kallonsa tace Ina kwananka? Yatsunsa ya wara tare da antayo Mata Dakuwa Ambola ya wani turo lips dinsa masu kyau da sheki,Khadija ta nuna kanta Wai da ita yake,Yaja tsaki Yana harararta tare da komawa bedroom dinsa,tana Gama abinda takeyi ita ma ta koma ciki. Bayan sun Gama ayyukansu wanka sukayi Suka shirya cikin Gown ta Khadija iya gwiwa ce,Ta merry har kasa Shi Kuma Ahmad gajeren wando ne da Riga t-shirt a jikinsa, Ihsan Kuma Riga da wando masu kyau. Mama Amarya cikin Atamfa Riga da Zani me tsadar gaske,Suna zaune sai ga Alhaji Karami Ango yasha wanka dama gashi Kyakyawan dattijo,cike da girmamawa su Khadija suka gaidashi ya amsa da sakin fuska yace Bari Yanzu Binto Yar uwarmu zata zo ta raka ku part part ku gaisa da kowa na gidan Nan,Zaku ga ba Wanda yazo ya dubaku,Kar ku damu Abdallah kadai ke zaga ko wanne part ya gaisar da kowa sabo da Daddy ne ya saka doka sabo da zumunci Amma sauran duk sun daina shi kadai ne yake bin Umarnin Mahaifinsa shi yasa Daddy yafi sonsa da kowa a cikin yaransa,muma Yan uwa munfi sonsa. Murmushi Mama tayi tare da Mikewa ta Hado Masa kayan abincin da Khadija ta girka iri iri,Alhaji Karami Wanda duk gidan ake kiransa da Baba Bai taba cin abinci me dadin na Khadija ba,ga Masifar tsaftarsu dan ya samu labarin Hafsatu ta Hana Yan aiki shiga part din su Mama. Baba ya kalli Mama yace kuyi hakuri naji Yan aiki Basu zo Nan ba,Mama tayi Murmushi tare da cewa ba komai wooo ai mu bama son Yan aiki ma,da Kan namu zamuyi aikin mu da Chau,Kar a bamu Yan aici Alaji. Murmushi yayi me kyau domin shima yafi son yaci abincin matansa Amma Hausawa duk sun saki jikinsu sai Yan aiki,sai da ya Gama cin abincinsa sannan sai ga Binto ta shigo da fara'a tana kuzo muje kuga gida da kowa na gidan kafin su fita. Tsakanin Merry da Khadija Babu Wanda yasa mayafi Haka Mama ce kadai ta yafa,Kuma tace itama