Sashe 23
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdallah da Khadija zaune suke jikin bishiya Sunyi Shuru kowa Babu tunanin da Sukeyi sabo da Basu San ma su waye ba bare su tuna wani Abu,Khadija ce ta kalli Abdallah tace Khadija yunwa nake ji Ni dai Allah,an bani Madara ka zubar da ita yanzu me zamu ci? Cikina har ciwo yakeyi,kudi Abdallah ya fito dasu a aljihunsa kamar dubu Biyar ya jawo Hannun Khadija ya Mika Mata yace gashi ba sai a siya ba a wajen mutanen Ina da kudi,Murmushi Khadija tayi sannan ta nufi inda taga mutanen yankin na siye da siyarwa,Wani Namiji ne matashi ya tare Khadija yace me zaku siya,Ai ko zumbur Abdallah ya mike ya fisgi hannun Khadija tare da janta Yana masifa wannan mutumin Zaki kula? Keda Zaki siyi Abinci ba kince yunwa kike ji ba? Ae to ai shine yace na tsaya? Hannunta yaja Suka tafi wurin mutanen Koko da kosai suke siyarwa,sai Awara da Bread,Awarar a wajen suke soyata sai ta birge Abdallah ya Mika kudi yace a bamu wannan abin,Me Awara Yar Fulani ta washe Baki tare da cewa ta nawa,Murmushi Abdallah Yayi Wanda sai da ya tafi da imanin kowa Harda Khadija,Me Awara ta Kara washe Bakin daya tunzura Khadija sabo da Kishin Abdallah, Nan take Khadija ta Zubawa me Awara rankwashi tace an fasa siyan Awarar Taki baza a ci ba. Baki Khadija ta turo masa cike da Shagwaba tace Bazan ci ba na fasa siya, Abdallah yace haba dai kefa Kika ce yunwa,To me yasa kayi Mata dariya?dazu Ni ai hanani kayi nayi wa wannan mutumin dariya,Ok to na daina Bari a siya,da kyar Khadija ta hakura suka ce a Basu ta dubu Biyar, Me Awara ta bude baki sai tayi dabara ta Basu ta Dar biyu harda Bread ta Mika musu canji ba tare da tace komai ba,karba sukayi tare da komawa wurin zamansu sannan Suka bude da zafinta ta Fara cin abinta hankali kwance Yana ta kallonta kamar zai hadiyeta,Juyowa tayi Suka hada Ido ta sakar Masa Murmushi lafiyayye sannan ta dauko Awarar da hannunta tasa Masa a Baki,ya bude bakin yaci,a Haka take bashi da hannunta tana ci itama har suka cinye har Bread din,ruwan Tuka tuka Suka Sha sukayi tatil sannan Abdallah yace wanka nake so nayi,Khadija tace Nima Haka Wai mu bamu da iyaye ne da Yan uwa? Baki Abdallah ya tabe Baya iya tuna kowa nasa,itama Khadija Shuru tayi iya tunaninta Bata gano dangi ko daya nata ba,Yar wanne state ce Oho. Me Awarar Suka tambaya a Ina zasu samu suyi wanka?me Awara tace sai dai ku jirani na Gama soya Awara sai muje gidan mu wurin kakata na tabbata zata Bari kuyi wanka a bayinta sai ku shirya ba damuwa,Khadija tace ok sai da ta siyar da Awarar sannan ta jasu gidansu Daga ita sai Kakarta a gidan. Kakar me Awara wacce ake kira da Iya tace Bingel wannan bakin fa Daga Amurka suke? Me Awara wacce aka Kira da Bingel tace Wai Iya wanka suke so suyi Baki ne Basu da ko wajen Zama Dan Allah ki Basu dakin can da babu kowa su zauna tare damu kafin su tafi tunda Suma musulmi ne irinmu, ,Iya ta kalli su Abdallah tace bayin Allah duk garin Nan gida biyu ne na musulmi Daga Nan gidan sai gidan Yar Uwata Kuma muma Hausa Fulani ne,zan Baku dakin kwana da abinci kullum a matsayinkun na musulmai Yan uwanmu. Mun gode Abdallah yace kawai,Iya tace Mata da miji ne ku? Abdallah Bai sani ba yace ae,Farin ciki ya Kama iya tace to shikenan daki guda za a baku,aiki kuka zo Yi garin ko Gomnati ce ta turoku? Nan ma Basu sani ba Khadija tace ae. Iya akwai Tsafta sosai ruwan zafi ta daura musu tare da Hadawa Abdallah ruwan wanka a bayi,Haka ya lallaba ya shiga a tsorace yayi wanka ya fito Yana yatsina fuska shi Bai San bayi irin wannan ba,Khadija ma shiga tayi tayi wanka da sabulun Abdallah daya saka a kayansa ta fito itama. Dakin da aka Basu Suka shiga da kayansu, Khadija doguwar rigar atamfa tasa Amma ba kwalliya ba ko shafa Mai,shima Abdallah Haka ya shirya cikin kananan kayansa farar Riga da Jean Baki,kyau kuwa ba a magana,Bingel ce ta shigo dakin nasu da kowannensu ya rufe jikinsa Yana shiryawa,Bingel ta tattara Kayan da Suka cire har zanen da Suka lullube jiya ta wanke musu karkar tare da shanyasu. Kunu da Nonon shanu Iya ta kawo musu ai kuwa sunsha da yawa sannan Abdallah ya hau Dan gadon Karan ya kwanta bacci ya kwashe shi,Khadija kuwa nata tsafin bana Zama a gidan wasu bane,guduwa tayi Daga gidan aka nemeta aka rasa tana can ta shige gonakin mutanen Kauyen. Baba Yana kulle inda Allah ya taimakeshi Yan sandan Basu taba lafiyarsa ba sabo da girmansa da suke gani,sannan basa zarginsa Sam. Hafsatu da kanta tazo gidan su Mami sabo da suyi tashin hankali an kulle Mata miji,Hafsatu ta kalli inda Mami ke zaune ta furta anji kunya wlh bakiyi ba,ban taba sanin jahila bace ke sai yau,Ke idan ba dabba ba Wai Dan Iskan danki ya bace shine Zaki sa a Kama kanin mijinki uwa daya uba daya,ai ko baici darajar komai ba yaci darajar Mijinki dake kabari a kwance,Sabo da shi bashi da abinda zai muku bashi da amfani,wa ya sani ma ko Dan naki halin tsiyarki da jarabarki ce tasa ya Gudu wlh a sannu sai kinyi Dana sanin rayuwarki,shegiya asararriyar uwa marar tunani, Kai Mami ta jinjina sannan tace kome Zaki ce kice Dana kuma sai mijinki tsohon munafuki ya fito min dashi. Mijin naki azzalumi ya cinye Mana dukiya gidan da kuke ciki na tabbata bashi da kudin siyen wannan gidan harda wani komawa ciki ya sace Mana dukiyar magada,Idan kin Isa ki kwace cewar Hafsatu,Sauran Matan ne Suka shigo Suma Part din Mami Jin fadan yaki karewa,Rahmatu Uwar gida tace a gaskiya Bai Dace a Kama Baba ba,ai gwara ki Kama Hafsatu a rufeta,Bilkisu tace Sam yaro kamar Abdallah Kato Ubanwa zai saceshi kawai dai ya gaji da bakin halin uwarsa ya Gudu,Haule Amarya tace yo Ni a ganina gaskiya Mami ce ta boye danta Dan taga bayan Baba shine za a bullo da munafuncin banza,Afrah dake kwance kusa da Mami ta mike tace a gaskiya ya isheku Kuma wlh Zan dura muku ashariya akan uwata. Iyye...? Sai ki fadawa Wanda Bai Haifa ba wlh kina zaginmu sai na tsinka Miki Mari cewar Rahmatu,Afrah taja tsaki sannan tace aikin banza ai kuwa Hafsatu ta fisgota Suka rufe Afrah da duka ta ko ina Tim tim sai ko Mami ma ta shiga suna ta dukan juna,sarkin yawa yafi sarkin karfi sai ga Mami da Afrah an musu jina jina,Usman da Sagir ne Suka raba fadan da kyar sannan Mami tace sai Naga bayanku wlh a kasar nan. Hafsatu gida ta koma,Mama kuwa tana can gida part dinta Babu abinda takeyi ita da yaranta Daga kuka sai Addua ba Yarta Khadija an daure musu miji,kullum tana police station Allah yasa Usman yaje Suka karbi bailing Baba akan za a ci gaba da bincike, Mama tafi kowa Murna,Hafsatu ma taji Dadi da yaransu. Humaira ba abinda ya dameta sai dai taci ta koshi tayi wanka tasa kayan da takeso ta tafi yawo gari,iyayenta duk Basu San an saketa ba,Mami ta Hana a fada musu,itama Humaira sabo da Mami tana Mata abinda take so Bata so ma a fadawa iyayenta an saketa bare suce ta koma gida,Mami ce tace Abdallah ya bace Humaira zata zauna tare dasu,Afrah sun Zama kawaye da Humaira yawonsu kawai Sukeyi na shakatawa kullum,Mami ce kullum cikin kuka da damuwar rashin danta Yana mace ko Yana Raye Amma taki gane gaskiya ta saduda. Bayan Khadija ta fita ta bar Abdallah Yana baccinsa har yamma likis sannan ya farka Alwala yayi tare da Sallar Azahar da laasar sai yayi rakaa goma yayi Sallama,Ya duba baiga Khadija ba,Fitowa yayi Daga dakin ya tambayi iya Ina Abdallah take? Iya tace wa? Yace Abdallah wacce muke tare? Iya dai mamakin Sunan ya rufeta,tace Kai Kuma ya sunanka? Yace Khadija,ba shiri Iya ta saki dariya Bata ce komai ba tace ai tunda ta fita Bata dawo ba,da sauri ya fita ya dinga zaga gari Bai ga Khadija ba, sai daya shiga daji sosai sannan ya hangota gindin bishiya tana kwance tana bacci a kasa. Yana Murna ya Karasa wurinta Abdallah ya Kira sunanta a hankali ta bude Idonta tare da mikewa zaune tana Sosa Ido,Hannu ya Mika Mata Wai ta mike ya taimaka Mata,Sai da ta kalleshi suka hada Ido sai ta Kama hannunsa tana murmushi ya mikar da ita tsaye tasa takalmanta Suka nufi Gidan Iya,Lokacin Iya har ta Kai musu fura da Nono Tasha sugar,gaskiya sunji dadin furar sai da Suka shanye tas sannan Khadija ta mike zata sake komawa daji,da sauri Abdallah ya mike tare da riketa yace Ina zakije Kuma? Khadija ta kalleshi kawai tace Ni bana son Zama a gida wlh kamar zuciyata zata fashe bazan iya ba,Riketa yayi Kam Wai Dole sai ta zauna,Kokawa suka farayi da ita ta fashe da kuka tana yakushin sa shi Kuma ya riketa Kam,Ganin irin ihun da takeyi yasa ya saketa ta fice da gudu ta koma can Daji ta zauna a jikin bishiya tana sheshekar Kuka. Abdallah ya fito yabi bayan Khadija ya isketa shima ya zauna kusa da ita tana ta kuka saman Kirjinsa ya kwantar da kanta yace to kiyi Shuru mana tunda bakya son gidan ai shike Nan,Amma Zaki dinga zuwa kiyi wanka ko? Murmushi ta saki Wanda ke Kara Mata kyau tace ae da abinci zanzo Iya ta bamu muci, Murmushi yayi tare da zame Dankwalinta gashinta ya bayyana me kyau da tsayi,Ya shafa shi yace Ke Yar India ce? Khadija tace a'a Yar America ce Ni,Hmm Ni kuwa Dan Agadas ne cewar Abdallah sai hirar Shirme sukeyi,Khadija ta Kura Masa Ido kamar ta ganoshi ta shafa gemunsa tace Kai Ina son wannan Sumar taka,tunda ta furta haka take ta shafawa Abdallah fuska da gemunsa tana kwance a Kirjinsa,Shi kuwa gogan tuni abinda yake ji yasa shi ya lumshe Ido tare da tallefe Khadija a jikinsa,Mutanen kauyen Suka taru a kansu Yara suna kallo, wasu cewa suke Yan iska kuzo ku gani,wasu