← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 53

Sashe 27

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai da tayi wanka sosai yau cikin Jin Dadi sannan Kuma ta Fara tunanin kunzugunta me zata sa,Yana shigowa yajiyo Muryar ta a Toilet tana kwala Masa uban kira ta rike sunansa Abdallah, Jikin kofar ya tsaya me kike bukata? Cike da Shagwaba kamar zatayi kuka tace Ni me Zan saka a Down Dina? Har ga Allah ya manta yace me fa? Wai Kai to ka manta jini fa,Oh sorry na manta,Pad ya dakko Mata guda da sabon pant ya Dan Bude kofar ya Mika hannunsa ta karba,ta Kara shagwabewa Ni ban San wannan ba Allah ban San ya Zan Saba,Hannu ya Mika ya karba Yana dariya ya Sa Mata a pant din ya gwada Mata yanda ake sawa,Amma tace Sam ita Bata sani ba. Gajiya yayi ya bude Toilet din Baki daya Allah ya taimaka ta daura Towel,ba Haka yaso ba yaso ya isketa ba Kaya,a kasa ya tsuguna yace Oya dafani kina gani jinin Yana Fara digowa kasa Dafashi tayi ta daga kafa ya sa Mata ya shirya ta neat sannan ta gyara Towel dinta ta fito shi Kuma sai da ya Kara wanke Toilet din sannan ya fito. Ta shafa lotion dinsa yanda taga yayi,Wata Yar yaloluwar rigar ya Bata tasa doguwa Amma ba can ba,ta Mata masifar kyau ta fitar da surarta sosai,tana kallonsa yayi sallar Isha a nutse da adduoi,lokacin gashinta ya Karasa bushewa ya taje Mata tare da shafa Mata mayuka masu kamshi ya hada ya Mata parking,shegen kyau tayi ta koma jikin katon mudubin ta tsaya tana ta faman kallon kanta,tana Juyawa,kusan raba dare tayi jikin Mudubi,ko yace ta kwanta baza ta kwanta ba sai ta mike ta koma jikin Mudubi,idan ya kashe light sai taje ta kunna ta koma jikin Mudubinta. Har yayi bacci ya farka tana jikin Mirror,zamuyi fada to indai baza kizo ki kwanta ba,Gobe tafiya zanyi abina na barki ke daya cewar Abdallah,da Gudu Khadija ta Karasa jikin Bed din tace na daina,ok kashe light din ki kwanta,Bayan ta kashe gefe can karshen bed din ta kwanta tare da rakubewa. Muryarsa taji yace ki gyara kwanciyarki idan ba so kike Gobe na barki a Nan ba,da sauri ta mike kafafunta ta gyara,ta Dade Taki yin bacci sai kusur kusur takeyi kamar bera. Hannu yasa tare da dakkota cancak ya maidota gabansa kiyi bacci yanzu Nan kin hanani bacci. Kwana biyu banyi muku posting ba ayi Hakuri biki mukayi shi yasa ban samu time ba. Nasan Fans sun gaji da jira na kuyi hakuri. AsmaBaffa [12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: . TUBABBIYA 41-45 Official AsmaBaffa Zulaihat,Asy TempleRun,Faridasulaiman130,Rukayyatu,Yaseerat Mustapha,Ummu Hamjaf,Anty,Maryam Kabiru,Muneerat Adam,Aisha Muhammad and Aysha AD. A hankali ya rungumeta a jikinsa,Khadija ta saki wata Ajiyar zuciya shima Abdallah haka musamman Daya daura hannayensa saman Dukiyar fulaninta,dama kadan suke jira a hankali yake shafawa Khadija ta lumshe Ido ya Gama tafiya da Imaninta,a hankali ta Furta ya baka ji tsoro ba yau? Dariya ce ta kamashi ba tare da ya shirya ba tunowa da shirmensa da yayi da kanta ta bashi free Amma yaki yarda harda hawaye. Jikinta ta Zame a hankali tana cewa ya Isa Haka ai kaji yanzu,to rannan da kike so fa har fushi kikayi fa Amma yanzu kin hana why? Khadija tace yo dama nifa rannan Wasa nakeyi maka Kuma kace baka so harda kuka Nima yanzu na fasa, Ni din? Ya furta Yana murmushi,Khadija tace ae Mana da waye ba Kai ba, rungumeta yayi Yana Jin kaunarta har cikin bargonsa Haka bacci ya kwashesu Baki daya. Da Asuba ya farka tare da zare jikinsa a nata Alwala yayi ya fita masallaci kusa da Hotel din har ya dawo Khadija tana baccinta Bai tashe ta ba sabo da yasan ba wata Sallah zatayi ba. Baccin shima ya koma sai 11am ta farka fresh da ita Tasha bacci,sai karewa Abdallah kallo takeyi Yana bacci yayi mugun Mata kyau,a hankali ta Dan shafo sajensa tare da Dan gemunsa masu matukar kyau da kyalli,Ga laushi da santsi,Sumarsa ta shafa ta shinshina hannunta wani numfashi taja tare da lumshe Ido sabo da kamshin Dadi Data ji, tana faman tabe taben jikinsa ya bude idonsa a hankali,Da Sauri ta boye hannunta tare da sadda kanta kasa kunya ta rufeta,Kwanciyarsa ya gyara tana zaune Yana facing nata a kwance ya saki Murmushi me kayartawa sannan yace Morning Khad kin tashi lfy,Ba tare data amsa ba ta dire kasa tare da shigewa Toilet da Gudu Wai kunya takeji,yasan Khadijansa ba Haka take ba,tasa Khadijan Bata kunya sosai akan wannan Khadijan marar lafiya. Ta Dade ciki kafin ta Gama komai har wanka sannan ta shiga Kwala Masa Kira Abdallah....wani sanyi da nishadi yake ji idan tana kiran sunansa kamar karta daina tafi kowa iya kiran sunan duk da cewar Hausar Tata Bata fita sosai,Yana sani yayi Shuru taci gaba da kiransa Yana Jin Dadi sannan ya Isa jikin toilet din Yana Murmushi ya Furta ya akayi ne sai kin Karar min da Sunan nawa? Kamar zata narke Sabo da Shagwaba tace kazo ka Sa min pad din yake ko me? Handle din ya murda tare da shiga dauke da pad a hannunsa,daure take da towel ta wani matse kafafunta,Kallo yake binta dashi gaskiya Khadija ta hadu karshe Mace ce ta gaske hakan yake furtawa a ransa,Kamar jiya haka ya tsuguna kasa ya Sa Mata pant da pad sannan ta fito shi Kuma ya zauna ciki yayi wanka,Kafin ya fito ta Gama komai na shafa lotion da turare,Yana Fitowa daure da Dan towel tare da karami a hannunsa Yana goge gashinsa,Ruwa kadan saman tip tsinin hancinsa Yana digowa dis dis,Khadija ta kafeshi da idanu Bai aune ba Yaji harshenta saman tsinin hancinsa ta lashe ruwan tana murmushi,Dariya ta bashi domin ta tsoratashi da farko baiyi zaton abinda zata Masa kenan ba,gashinta ta Sosa sabo da kunya ta koma gefe tana magana kasa kasa ka fidda min Kayan da zansa. Komai baza ki koya ba sai anyi Miki jiyafa na nuna Miki komai,Na manta to Ni bazan iya ba sai nayi zamana Haka,Arabian Gown ya zabo mata ta shirya shi Kuma ya shafa Mata Powder da lipgloss tare da yafa Mata Dan gyalen rigar sai Murna takeyi tana kallon kanta a Mudubi,a Haka ya shirya Cikin pitted jallabiya Fara tas ba karamin kyau sukayi ba,Tana gaban Mirror ya tureta kadan Yana duk kin tare wuri,Dariya ta kyalkyale da ita itama ta tureshi da Mazaunanta manyan gaske,Abdallah yaja ajiyar zuciya tare da shidewa Yana lumshe Ido,Khadija ta kalleshi da sauri tare da tambayarsa So Soft? Kai ya Daga Mata Wai ae,Murmushi ta saki tare da kamo Hannunsa tana shafawa a hankali ta furta muje yawo pls kaji kamar zata Yi kuka. Flat shoe Sea blue kalar rigarta ya Bata tasa shima yasa nasa Suka fita tare da bada key a gyara room din kafin su dawo,wata rantsatsiyar mota Suka nufa mamaki ya rufe Khadija Ina ya samu mota? Ko dama a Nan ya ajiyeta? Abdallah...ta Kira sunansa,naam Khad mene Kuma? Oh yanzu Wai sai naji kana ce min Khad Kuma? Shima suna na ne? Yeah wannan Ni kadai zan na fada Miki,Kai ta jinjina tana murmushinta tace Wai dama Kai me kudi ne? a Ina ka Samu Mota me kyau Haka,gata sabuwa me tsada? Kofa ya bude Mata gaba ta shiga shima ya zaga ya shiga sannan ya kalleta bayan ya rufe kofar yace ae me kudi ne ni,Baki Bude tace to ka siya Mana jirgin sama mu shiga abinmu,Jin kalamanta ya kunna motar Suka bar Hotel din idan mota ta Dan jijjigata sai ta fada jikinsa tare da kankameshi ko ta kamo Hannunsa ta rike Gam. Sannu sannu dukiyar yaran su Rahmatu ta Kare kaf suka shigo siyar da motocinsu Daya baya daya suke Saida kadarorinsu Ana so a kafa sana'a Amma taki yuwuwa kowa idan ya fara Business kamar gaske sai kudin su tarwatse, abinci ma yanzu Ba wani na kirki suke Zubawa a gidan ba yayin da Yan aiki wasu tuni duk sun tafi saura Basu Mutum uku ba,Ganin sun Fara Zama Allah sarki Kawu ya fara taimaka musu da abinci duk wata Amma Bakin Hali irin na Hafsatu sai taje wurin Bokanta yayiwa Baba tsafin da bazai taba taimakawa su Rahmatu da yaransu ba,Haka Bata samu Nasara ba asiri yaki cin Baba sai ta sake dabara tayi asirin dasu Rahmatu da yaransu kaf indai taimako ta hannun Baba ya biyo to baza su karba ba,tayi nasara a Nan duk abinda Baba zai Basu ko zasu mutu baza su karba ba,Hakan yana konawa Baba zuciya duk tunaninsa suna sani suke kin karba,Haka Talauci yace salamu alaikum Cikin gidan iyalan Daddy. Ko wacce yanzu ita take ciyar da kanta ita da yaranta,Gashi Basu yiwa yaran tarbiyar kirki ba,tsakaninsu ba tausayi Babu Imani kamar a kansu aka Fara Talauci kamar Mahaukata Haka suke acting Babu tawakali, Mami kuwa da yaranta tunaninsu dabararsu ta tsallakar dasu,tunaninsu Wani plan da wayonsu ne yasa suka tsallake talaucin. Merry Kullum Khadijansu suke missing sai Addua sun dogara ga Allah yayinda soyayya ta kullu tsakanin Merry da Dr Hussain abokin Abdallah,Har yau Baba tare da Dr Hussain neman su Abdallah sukeyi Addua suke Babu fashi kullum. Wani katafaren Shawarma joint Abdallah ya kaisu shine ya fara Fitowa sannan ya zaga tare da budewa Khadija ta fito,sai kallonsu akeyi domin sun ba da show sun hadu sun Kai a kallesu kamar Ido ya Fado,Yana zuwa yace a sallami kowa dake wajen sai ya Gama sannan,sunji kudi nan Suka bawa mutane hakuri akan su jira Oga zaici Abinci sai ya Gama ya rigada ya biya kudin,inda Abdallah ya farantawa mutane yace kowa a bashi yaci zai biya,mutane gaba ta Kaisu suka watse sai shi sai Khadijansa tana gefensa ba wani ganewa takeyi ba,chicken Shawarma da Beef Burger aka kawo musu sai fruits salad ai kuwa manyan Khadija ta dauke ta shiga ci da sauri sabo da yunwa takeji sannan ya Mata Dadi. Shi Kuwa Abdallah a nutse kamar shine macen Haka yake ci Yana satar Kallon Khadija farin ciki Yana ratsashi,ta ciko baki da Shawarma har ta Bata Mata gefen Baki,yatsa yasa tare da goge Mata ya Sa a Bakinsa ya tsotse,Dariya tayi bakinta cike da Shawarma tana ci,Murmushi ya saki tace da Dadi gaskiya wannan abun ya sunansa? Shawarma ya Bata amsa,Hmm ai tunda
Chapter 27 · 0% Book details