← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 53

Sashe 33

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy duk yawan dukiyar Daya Tarawa yaransa ta kare? Wani albarka ne dasu,sai fa Wanda Allah ya zaba shike kudi da kudin gado. Ke Dan ubanki tashi ki bani waje ka jimin yarinya ni Zaki yiwa waazi,tun kafin a haifeki nasan da haka munafuka. Ficewa Firdausi tayi ta Bata wuri tasan Hafsatu baza ta gane ba sai dai idan duniyace zata ganar da ita ta fannin wahala etc. Wahala Su Rahmatu sun Fara karbarta ja,abinci ma yanzu da kyar suke samu,sun koma abin tausayi,wasu Kayansu na sawa masu tsada duk sun Dan siyar da wasu tare da cinye kudin a cikinsu,Ashe wahala ma tana sawa asiri yaki tasiri ta wani fannin,Duk abinda Hafsatu tayi musu na Kar su karbi kayan Baba yanzu yunwa tasa mota guda yake Yi musu ta kayan Abinci sai ko Suka karbe Amma sai da Suka zageshi bayan ya tafi,Haka sutura baya Bari su rasa kamar yanda yakewa yaran cikinsa Haka yake musu abinda suke so dai dai karfinsa,motoci Basu fasa Hawa ba duk da sun siyar da nasu Baba ya siya musu wasu,Masu zuwa schl Bai Bari ta gagara ba ya biya komai,a halin yanzu Allah shine gatansu Baba shine gatansu,dashi Suka dogara shi ke musu komai,duk da basa so Amma Haka suke karbewa,Tunda Baba ya rungumesu Basu da kukan komai,hakan yasa wasu sun daina shaye shaye wasu sun rage Abubuwa da sukeyi Marasa kyau da yawa sabo da komai Sai da kudi akeyinsa Kuma Basu da kudin mutum Dole ya hakura,ko badan Allah ka Bari ba Amma ba a rubuta make zunubi. Da yawa wasu suna so suyi Zina,ko Shaye shaye ko yawon banza inda za a kwaso zunubi Amma Allah Bai Basu kudin yin ba Dole mutum ya hakura ta Dole sabo da babu kudin Yi. Hakan yasa Yan Matan suka Fara tunanin neman mazajen aure,Mazan ma a ciki yanzu sun karbi aikin da suke rainawa da,Baba ya samo musu aikinyi wasu a company nasa wasu Ana Abdallah wasu Kuma aikin Gomnati da murna Suka karba,Wanda hakan yayi Masifar konawa Hafsatu rai,Suma yaran su Rahmatu ba so sukeyi su karbi kayan Baba ba sakamakon aikin Hafsatu na asiri Amma ba yanda suka iya idan ba Haka ba ai da tuni sun tozarta Babu mamaki ma da tuni yunwa tasa sun koma roko a makwafta. Suna tashi Yau Abdallah yace su shirya Kano zasu koma,Khadija tace yawwa yafi Haka ma akan zaman Hotel,Sai da Suka shirya tsab kamar wasu Larabawa Haka Suka fito suna Fitowa Driver na jiransu da motar Abdallah da yake tukawa,Baya suka Shiga bayan sun sa kayansu a Booth,Airport driver ya kaisu suka shiga jirgi Abdallah sai wani kakkare Matarsa yake Yana haba haba da ita. Suna Isa Kano ta dabo tumbin giwa wani Driver daban yazo da fyaleliyar mota ya daukesu zuwa katafaren Unguwar da gidan yake,wani Dankareren gida na Alfarma ya kaisu me gadi ya wangale gate,Tun daga waje Khadija take mamakin kyawu da tsaruwar gidan,motocine zuka zuka masu tsadar gaske guda uku a Compound inda ake parking, Fitowa kawai sukayi,zata ja akwatunansu Abdallah yace ki Bari za a kawo,Palo Suka nufa gidan ya tafi da Imaninsu musamman Furniture da suke gidan ya tsaru kwarai komai Fari ne Kal da Golden a gidan. Khadija ta haura Sama Yana binta a baya,Dakinta ta zaba shima Haka sannan ya Kira Baba ya sanar Masa sun koma Kn. Tunda ta shiga Bedroom Bata fito ba Tunda tayi wanka ta tsantsara kwalliya cikin wando pencil creazy Jean fari tas,tasa Riga pink color t-shirt ba karamin kyau tayi ba ta matse Sai mazaunai manya,Shima wanka yayi tare da sa jallabiya fitted brown yasha kyau Yana kamshi,Key ya dauka na mota ya shiga Bedroom dinta tana cikin Toilet tana Shirya kayan wankanta sai yayi tunanin wanka takeyi ya fita abinsa,Sai Karar tashin mota taji,Mamaki Khadija takeyi na Abdallah Wai ko wanne gari ya sani ne? Zata tambayeshi idan ya dawo Amma ko ya sanar da ita ya wani fice ya barta Danma akwai Yan aiki Mata da maza mutum biyar maza uku Mata biyu shi yasa gidan ko Ina yasha gyara kamshi ke tashi kawai. Yunwa takeji sosai ta Dade tana Jiransa har tayi Sallar Laasar har 5pm ta kusa Amma Shuru Bai dawo ba,abinda ya dameta Matan Kano masu shegen Son me kudi da sunga mutum me kudi ko Yar motarsa me kyau sai a nace Masa a aureshi,aure ba Dan Allah ba suma mazan da sunga Yar Fara sai suje,shi yasa Mata suka lalace da shafa Mai,ta Dade tana Jin labarin Matan Kano burinsu su auri me kudi,indai mutum Yana da kudi to fa ba abinda za aci da halayensa me kyau ko marar kyau sai a aureshi,su kasa yiwa miji biyayya sabo da dama bashi akeso ba,shima Kuma akwai abinda yasa ya aura sai a kasa rike mace a saketa, afwan Mata hakance take faruwa,mace a Dankareren gida ba komai ciki na abinci,ga gida ga mota Amma Babu sutura ba abinci,sai ta Fara kasuwanci ko aikin Gomnati kullum tana titi shi yayi gabas ita tayi yamma sabo da ta tsira da mutuncinta. Mata mu rage burin duniya,Dan kar mace tayi biyayyar aure sai tace Dole sai tayi aikin Gomnati Dan ta gagari mijinta,Bai Isa da ita ba sabo da tana da kudinta idan Bai Mata Abu ba zata siya da nata,in ya saketa ma da gidanta zata koma da yaranta tana bin yaran maza tana lalatasu ko ta koma Yar lezbian tana kashewa Yara Mata kudi.Allah ya kyauta Amma ya kamata muyiwa kanmu fada duniyar Nan ba Zama akazo Yi ba,Dan Aron lokaci Allah ya bamu zai iya karba a lokacin daya ga dama,muyi kokari mu nemi lahirarmu tayi kyau Dan itace matabbata. Duniya Kuma yanzu mata ga bin malamai da sukeyi harda yaran Yan Mata Suma Malam, wasu ma suna haduwa da Namiji me kudi sai akai sunansa wurin Malam Dole Wai sai an aureshi,sai Kuma anyi aure asiri ya karye ya fara cin Ubanta tana kuka da tsinewa maza ai maza tsinannu ne kaza kaza,mace data yi aure 1yr ta Fara zagin maza maganarta kenan maza kaza kaza,ba ayi aure ta hanya me kyau ba Taya zamuga dai dai,tun kafin ayi auren Shedanci yasa darajar auren ta ragu, Allah ya kyauta. Hankalin Khadija ya tashi kwarai da Matan Kano bare Kuma ance suna da kyawawa Suma da yawa sai ta kasa zaune ta kasa, tana Jin Karar motar Abdallah ta gyara Fuskarta tare da Kara shafa turare sannan ta Fara sakkowa daga Steps,lokacin ya bude Kofa ka rantse Yar baturiya ce,Gaba daya yaji sonta Yana Kara ratsa jininsa,ji yake kamar ya saceta Murmushin da Bai shirya ba ya sakar Mata,da sauri ta karaso gabansa da sassarfa,Sannu da zuwa,Ina kaje? Nan garin ma kasan ko Ina? Ko Ina akwai Mata ko? Suna da kyau? Ko dai karyar mutane ne? Tunda take tambayar Bata ko huta ba a jere take jero Masa,Shuru ya Mata Yana kallon bakinta dake birgeshi, Hannunsa ta kalla ta ganshi dauke da manyan Ledoji da sauri tace Ah..sannu woo na barka da kaya ta karba ta ajiye a palon ta dawo da sauri tare da Sa hannunta cikin nasa tace muje ta kaishi Saman 2seater ta zaunar dashi sannan ta shiga kitchen ta kawo Masa Drink me sanyi a glass cup,Gaba daya ya kasa magana ta tafi da Imaninsa ta Masa kyau har baya so ya daina kallonta,Shi Kam Allah ya bashi macen gaske,Da kanta ta bashi lemon ta Sha da yawa sannan ta matsa kusa dashi sosai tare da dafa kafadarsa pls ka fada min tambayata. Wannan tambayoyi ta Ina Zan Fara ma? Dan Allah ka fada min,Ok to dama kusan duk State din Nigeria dai dai wacce business Bai kaini ba tun Muna zuwa tare da Daddy har na koma Ni kadai,sannan dazu naje Zan Miki sallama kina wanka,Abinci na siyo Mana sabo da yau ki huta kafin gobe ki Fara girki. Mata Kuma gasu Nan ko Ina,ke nifa Bari kiji na fada Miki idan Banda ke Babu wacce ta Isa magana ta hada Ni da ita me tsayi,ki tambayi Baba kiji,sannan Dan na fita sai akace Miki Mata nake kallo? Wacce macece ban gani ba,karki manta a turai nayi rayuwa Sannan naje kasashe daban daban. Ina da wacce Zan kalla data wuce ki? Ai duk matan da Zan gani nasan kin fisu sau dubu me zanyi dasu Ina da kamarki,sabo da farin ciki Khadija Bata San sanda ta fada jikinsa ba tana murna tare da cewa Allah da gaske? Sosai ma kuwa da gaske,Fadawa jikinsa tayi gaba Daya ta turashi saman kujerar Suka fada gaba Daya kwance,ta danneshi tana murna sai kace Yar yarinya duk tabi ta cukwikwiyeshi,dariya ma ta bashi sai kace me wasan kokawa. Ba zato ta manna Masa kiss a kumatu sannan ta mike tsaye tace baka ce nayi kyau ba? Kema kin San ba sai na Furta ba yanda nake kallonki kin San kinyi,inama Abu zata zo garin Nan taga yanda na Kara kyau Haka ai da ba Haka ba,Abu tazo ta koya Miki maganganun banza ko? Kai ta girgiza tare da cewa Abu ta ba Haka take ba Ni hausa take koya min,Oya ga abincin nasan yunwa kike ji. Plate ta dakko kitchen ta juye chips da gasashen kifi,gefe Kuma wani hadadden Pounded yam ne miyar Egusi,Zama sukayi a kasa ba tare da sunje Dining ba Suka ci sukayi dam,Bayan Isha Abdallah ya hade cikin kana Nan Kaya zai fita,Khadija tace baza ta yarda ba sai ya tafi da ita,20mnt Zan dawo ba dadewa zanyi ba, Khadija ta makale kafada itafa Bata yarda Dole yace ta shirya su tafi,Tana murna ta shirya cikin Arabian Gown Tasha kyau,Jambaki radau,Fuskarta ya tallafa tare da hade bakinsu wuri daya ya shiga tsotsa sai da ya shanye jambakin sannan yace muje,tana sani taga lips dinsa sun koma red kalar jambakinta duk har gefen lips da rigarsa, sai Taki fada Masa sai dai ta kalleshi tayi dariya kawai. Hafsatu wanke kafarta tayi takanas ta tafi wurin malaminta,Malam nifa yarana maza Biyune kacal duk Mata na haifa ya za ayi na samu ciki nima na haifi wani Namijin ko Uku ne na Samu maza? Shi kanshi bokan yaga Hafsatu kasurgumar Jahiilace wa yake iya bada Haihuwa bare har ma Namiji,Amma a fili Malamin yace zamu duba
Chapter 33 · 0% Book details