Sashe 38
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
I'm sorry sarkin Shagwaba kwanta ki huta,Kwanciya Tayi ya gyara Mata kwanciya sannan ya mike da niyyar fita Yaji ta riko Hannunsa tana kwance,juyowa yayi tare da tambayarta ya akayi My Queen? Ina zaka je? Zanje wani Office anjima kadan zan dawo karki damu,Baba ya sani? Ae ya sani shi ya umarceni naje,ok Dan Allah karka kalli ko wacce mace kaji? Ta Furta da kalar tausayi, a hankali ya zauna gefenta tare da Manna mata Hot kiss a lips sannan ya shafa gashinta Yana magana karki damu Babu wata Bayan ke, Ina da kamarki wace zata birgeni, Murmushi tayi tace Tnx a dawo lfy Allah ya tsare,kayi tuki a hankali ka kularmin da kanka. Dadi ya cika zuciyar Abdallah ya amsa da Ameen sannan ya Mata sallama ya fita. Alhaji Shehu ya warke sai dai da sanda yake dogarawa,Sai da ya samu sauki Matarsa uwar gidansa Mariya ta kirashi a waya,Yana dagawa ya balbaleta da masifa akan ta dameshi to baida lfy idan Abinci ne gashi Nan za a kawo shinkafa buhu Daya da Taliya kwali biyu shike Nan abinda Zan iya, to Alhaji kasan ba Mai ba kayan Hadi iya shinkafa da Taliya dame zamu dafa abincin? Cewar Mariya,ga Dubu uku Nan Zan bayar a kawo,bakwa yi min uzuri,ba wasu kudi nake samu ba Amma bakwa godewa Allah,kudin nawa nake samu? Kinbi kin dameni komai kawo kawo,duk irin gidan da kuke ciki bakwa gani. Mariya ranta ya baci Bai San shansu da cinsu ba bare sutura Amma sai fada Mata magana yake,tsakaninsu Babu magana Mai dadi,Hawaye ne suka zubo Mata sabo da irin wahalar data ke Sha wajen daukan nauyin yaranta,Ina zata sa kanta kuka tayi sosai sannan ta kaiwa Allah kukanta tace Allah ka saka Mana,Bata taba Masa Adduar Allah ya Isa ba sai yau,duk wahalar da take sha ta jure Amma zalunci iya zalunci yake musu. Mami kuwa sai abinda tace shi yake Mata ita da yaranta. Yau Saturday yau Kuma Mami ta tashi da Bakin ciki Alhaji Shehu ya auri Mace ta uku,wata ce Yar Ghana Bai fadawa matansa ba sai da aka daura sannan ya fadawa Mami,ita kuwa Mariya baya kaunarta Bata sani ba,da kyar ya shawo kan Mami ta daina fushi dashi,karya ya shirya Mata Wai abokinsa ne Soja zai aureta saura sati daya biki sai aka turasu yaki Sambisa forest ya mutu a can,Amma kafin ya mutu ya bar Masa wasiyya idan ya mutu ya auri Sumayya,Sumayya tsohuwar karuwar Alhaji Shehu ce ta matsa Masa sai ya aureta ko ta tona Masa asiri,Haka Dole ya aureta amma sai ya cewa Mami taimakonta yayi baya sonta. Tunda Alhaji Shehu ya Kara aure sai ya koma kula Mami da Amaryarsa ita kuwa Mariya tana Can banza wofi ko leke baya zuwa inda suke ya tare Wajen Amarya Sumayya da Mami yana sauke musu duk wasu hakkinsu Banda Mariya da yaranta wanda kullum cikin bakin ciki take sai kuka sai Addua. Sun kwashe lokaci a Haka Katsam sai Mami ta Fara rashin lfy sama sama, kafarta ce take ciwo sosai guda Daya, Alhaji Shehu da kansa ya kaita Hospital aka rubuta musu test iri iri Mami taje akayi test Lafiya kalau ga Kuma cuta na damunta a kafa,Asibiti sukaje ba Daya ba Amma duk Zancen Daya ne ba ba a ga komai ba kafa sai kumbura takeyi tayi wani jajir daga Nan sai Zazzabi da kuraje suka Fara fito Mata ko Ina a jikinta,ganin Haka ta Kara firgita. Hafsatu tana zaune tana jiran ciki sabo da boka ya fada kamar fadar Allah, Shuru Shuru Bata samu ciki ba ga cikin Mama Yana ta girma lafiya Lau sai ta koma Gidan Malam tace Malam Banga komai ba har yanzu? Dariya malamin bokan ya fashe da ita yace Ai kin samu ciki tuni,saura kadan ya fito kowa ya gani,kije ki kwantar da hankalinki ga wannan maganin Aljanune suka bayar a Baki ki Barbada a abinci kamar yaji ki cinye Zaki ga aiki, Karya malamin bokan yakeyi sabo da kasa ce ya bawa Hafsatu shi kanshi yasan karya ne baza tayi aiki ba Amma sabo da Hafsatu tayi Imani da shi Bata kokonto akan maganinsa,shi a mahaukaciya ya dauketa ya ebo kasa ya Bata,ita Kuma tayi Imani ta karba a matsayin magani,yanda yace tayi Haka tayi da zuciya Daya,sai Allah yasa magani yayi aiki sai ga Hafsatu ta Fara Amai da tashin zuciya,laulayi takeyi kawai,Ana zuwa Asibiti tana da shigar ciki na Wata daya,Baba yayi murna sosai har Mama ta Taya Hafsatu Murna,Hafsatu sai Murna tana godewa boka harda komawa ta bashi kyauta ta musamman,shi kanshi bokan mamaki ya kamashi yanda ya fada Haka abin ya kasance,Tun a lokacin sai tsoron Allah ya kamashi lokaci guda,Nan take ya tuba ga Allah ya daina tsafi da shirka tare da karya,Gida ya koma cike da Nadama Yana Istigifari kafin ya fara neman wasu Wanda ya zalunta su yafe Masa,sabo da Haka Alumma Kar muyi ganganci wurin a sa ma magani kasan na bokanci ne kace Wai bazai Yi ba Bari ka cinye ko Kash ,Allah Yana iya sawa yayi tasiri tunda Wanda ya Sa maka yayi Imani da abinsa. Abdallah ya Dade Bai dawo ba sai 1pm ya dawo gida dauke da Ledoji tare da tarin wasu takardu Wanda Baba yace ya karba,har Lokacin Khadija Sallah kawai ta iya yi tana kwance tana baccinta ya dawo Bai tasheta ba domin yasan tayi Sallah tunda tana kula da addininta sosai,Wanka yayi ya shirya cikin Jallabiya Fara tas ya shiga kitchen,Me Aiki ya iske Budurwa ce gansamemiyar gaske ga tsayi ga kiba duk tayi bleaching ta lalata Fuskarta can baki Nan fari ta Sha powder tayi kwalliya sosai da sosai Kuma tayi kyau ba laifi Dan kawai ta Bata skin dinta ne shi yasa,sanye take cikin Riga da Skert na atamfa damammiyar gaske sun dameta Bata da wani shape me kyau Amma dai tayi kyanta dai dai ita, har turare ta fesa Sabo da tana son Abdallah ya kalleta ta birgeshi ya so ta koma ya aureta,Maimuna kenan. Ganinsa yasa Maimuna ta diririce ta gigice Gashi da kwar jini dama,duk da Haka data shaki kamshinsa sai da ta lumshe Ido sannan ta mike tsaye sosai kamar wata Soja gansansan a gabansa,Kallo daya ya Mata ya dauke Kai tare da bude fridge yace me kike Yi a kitchen? Queen dita taci abinci kuwa? Fari tayi da Ido farrrr sannan ta Fara karairaya tace Bata fito ba gaskiya Kuma tace Kar muyi Mata Abinci ita zatayi da kanta,muje can part dinmu muyi namu Haka tace,na sani My Queen baza taci abincinku ba ai kin dameni da Surutu cacaca matsa min a hanya yaja tsaki Yana kallonta yanda take Masa fari,a ransa yace Inama Khadija zata Kama Maimuna tana Masa fari da karairaya da taci Ubanta a gidan Nan. Yana fita Maimuna tace sai ka Soni Dole In Allah ya yarda,irin wannan miji Haka ga kyau ga sura gashi fari Kar Kai...Allah yayi baiwa a Nan. Yana Palo Yana Shan Lemo Maimuna tana lekensa daga kitchen tana Jin Dadi a ranta,Mikewa yayi ya dawo kitchen din yasha mamaki daya sake ganinta a ciki Bata fita ba Kuma ba abinda takeyi Yana shiga ya Mata wani banzan kallo ba shiri ta fice da gudu a firgice. Baya shiga kitchen Amma yau sai gashi yana girki da kansa, shi ya dafa musu Jullof din Taliya Tasha Kifi sai kamshi takeyi,Bedroom dinsa ya nufa da abincin inda Khadija ke bacci,ajiye abincin yayi sannan ya duka saitin lips dinta ya shiga tsotsa a hankali kamar a mafarki taji,a hankali ta bude Idonta sai lokacin ya janye Bakinsa Yana murmushinsa me tafiya da zuciyar Mai kallo,Khadija Shagwaba ta fara ajiye Masa tare da turo lips dinta gaba,Hannayensa masu laushi da taushi yasa ya mikar da ita zaune,Kara ta saki kadan washshsh...ka fama min ciwo na,Kalar tausayi yayi tare da cewa eyya...I'm sorry my Queen na manta Majalisi yana cuta, Harararsa tayi da taimakonsa ta mike tsaye da kyar,Daukanta yayi ya kaita Toilet Amma taki yarda ya Mata wanka Kyaleta yayi ya koma Room Yana jiranta. Daure ta fito da guntun Towel Amma sai taga Abdallah hankalinsa ya tashi gaba Daya ya zuba Mata Ido Yana binta da Mayen kallo kamar zai cinyeta,Surarta da kyan skin din Khadija ya ruda shi,dama Yaya aka kare bare ya dandana yaji Zuma yaji Abinda yaji, ganin Haka sai Khadija ta tsorata da sauri ta bude sip inda kayan sawarsu yake a shirye, da sauri ta dakko zanen atamfa tayi daura kirji sannan ta zame Dan Towel din,ta Nemo Hijab Kato tasaka, Harara ya watsa Mata Yana kallonsa ta wani kunshe jiki, muryarsa taji yace Mene Haka Kuma? Wannan ai kauyanci ne,Ni ba a Isa a gidana a dinga daura kirji ba Ana sa Hijab sai ki Bari sai Zaki fita ki saka abinki. Karya Khadija ta Shimfida tace sanyi fa nakeji kamar Zazzabi nake ji ma, ok to sannu kinji Bari kisha magani da pain killer sai ki warke da wuri,Khadija Ido ta zaro tare da kararrabewa zatayi kuka tana Allah..Allah..Ni...na gaji da maganin Nan,Magunguna ya dakko a Leda yace kiyi sauri ki shirya muci Abinci kisha wlh kinji na rantse sai kin Sha kawai salon Kiki warkewa da wuri ance kallonki zanyi ai nayi hakuri ma tun jiya fa ban Kara yi ba,Baki Bude take kallonsa tace au nufinka Nan Hakuri kayi? Yeah idan da wani ne da tuni yayi sau uku sau biyar, Bata ma son Zancen Amma ta daure kamar zatayi kuka tace amma da safe kace Laifin Jaruma ne ba naka ba? Yanzu Kuma kace baza ka hakura ba ai Ni Banga Jaruma tana so ba,dariyar da Bai shirya ba ya saki sannan yace Bari a nuna Miki to Kika fushinta ta gaji da jira sai bara take iya ko Dan kanzo, Khadija ta bashi amsa tana dire diren kafafu na rantse sai dai ta mutu idan taga dama ta tsinke daga jijiyarta ta furta kamar zata cinye Abdallah. Juyawa tayi a Hijab ta shafa lotion sannan da dabara ta saka doguwar rigar material tayi kyau sosai,sai Abdallah yaga tafi Masa kyau ma a Haka,duk motsinta idonsa na kanta,Sallar laasar tayi sannan ya maidata saman bed tare da ciyar da ita abincin shima Yana ci,Idan ya Kai spoon bakinta Yana ta