← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 53

Sashe 29

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdallah sannan yace abinda nake so da Kai Abdallah ka zauna a garin Nan karka dawo Kd, Abdallah yace Baba bana son Nan state din gwara na koma Abuja,ai Mami tana can tana aure kawai kayi hakuri to ka zauna a Kano ko Hotel ko gida na wani lokaci zaka ga amfanin hakan da nace,Ina da manufa akan hakan,Abdallah ya danyi Shuru sannan yace Baba to aiki fa? Business Dina? Yanzu Ni bani da gado kenan Humaira ta sace komai ta tafi Kuma Mami Bata dauki mataki ba,me zanyi yanzu?,kudin Hannuna Basu fi million Talatin ba,Baba yayi Murmushi yace kaje ku huta da matarka Abdallah akwai dukiyarka da Daddy ya bani wasiyya na baka,da gidajenka komai Yana Hannuna Kuma Ina ta juya maka dukiyarka yanzu ta Kara bunkasa duk abinda kake so kayi da kudin hannunka idan kana bukatar wasu ka sanar min,gidanka na Kano ya tsaru kwarai a GRA komai akwai har masu aiki na zuba maka jiya,Motoci akwai Kaya Abinci komai na Gama ku koma can ku zauna da matarka baza kayi aiki yanzu ba akwai dalilina. Shike Nan Baba Amma sai Na sake 1wk a Nan Hotel din sai mu koma Kano din,Baka da Matsala Abdallah,karka manta karka sanarwa kowa kana Nan,sannan Addua ka riketa sosai,matarka ka dinga yi Mata a ruwa kana Bata tana Sha kullum sannan ka tsaya kuyi ta Addua Allah zai amsa Nima muna can Muna Yi,sannan zanje wajen wani Malamin Sunna ya bamu adduoi ayi Mata,Ba damuwa Baba,Maman Khadija fa? Ai da ita Muka shirya komai hankalinta ya kwanta ai taji yarta na Raye tare da Kai Bata da damuwa tasan komai. Murmushi sukayi Baki daya sannan Baba ya tafi ya koma Kaduna a jirgi. Khadija tace Ni dai ban San kowa ba Abdallah yace idan kwakwalwarki ta dawo ai Zaki sani ai,Ok to muje ka wanke mun gashina ya dameni yau ba a wankeshi ba tun jiya. AsmaBaffa. [12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: TUBABBIYA 46-50 Official AsmaBaffa MEERAH and AUNTY SUMY page dinku ne. Toilet suka shiga tare da kayansu a jikinsu, ta manta zata kunna tap sai ta kunna shower shaaaaa ruwa ya Shiga shararo musu kamar Ana ruwan sama, wani shauki ne ya cika musu zuciya,Hannu yasa a dokin wuyanta gashinta ya watsu a hankali ya shiga kissing dinta ruwan Nan Yan jika su hannunta tasa tare da Rungumeshi a jikinta kamar su dawwama a Haka sai yayi kamar zai kyale ta sai ya sake hade bakinsu yaci gaba da tsotsa sai da ya gaji sannan ya kyaleta idonsa yayi jajir,ruwan ya Gama jikesu da kyar ya daure ya wanke Mata gashinta sannan ya fito tayi wanka,tana Fitowa shima ya shiga jikinsa duk yayi sanyi mace yake bukata. Koda ya fito ya isketa yau har ta shirya Bata jirashi ba,Iyye yau anyi abin kirki Gashi har gashin kin gyarashi Good girl,Murmushi tayi ba tare da tace komai ba ta koma saman bed sabo da ta gaji yau tunda Baba yazo dazu sun Dade Gashi har dare ma yayi,Sai da kyar Abdallah ya samu tayi Sallar Isha sannan ta kwanta, Laptop sabuwa dal iPhone Daya siya yake amfani da ita Yana dannawa zaune a kasa,Tana a saman bed ta zuro da kanta kasa tace kazo muyi bacci Mana Kai baka gaji ba? Wani aiki zanyi sai na Gama kiyi baccinki kafin nazo ya Bata amsa,Kasa itama ta sakko tare da daura Kanta saman kafadarsa tana zuba Masa Shagwaba N...Ni....Allah....uhmmmm...kafafunsa ya mike Mata yace to kwanta anan idan na Gama na maidaki saman bed,Da Sauri ta kwanta tare da yin matashi da Cinyarsa shi Kuma yaci gaba da danne dannensa. Kunna Mana kallo Abdallah,Ko na kunna Miki ma bacci kike Yi,baza ki bani aiki ba kiyi bacci,Bazan Yi ba na rantse kawai ka kunna min pls,American film ya kunna Mata na love me kyau,Ta bada amanna tana kallo aka Fara kissing a film din ta juyo da sauri kamar Zata ballawa Abdallah cinya tace Laaaaa irin abinmu,Yana sani yace me? Yana kashe Mata Ido daya,irin abin da mukayi jiya Wanda kayi min jiya me dadin nan,ka gani wallahi gashi anan anayin irinsa iyyeeee ta furta tana dariya tana Kallon Abdallah tace Ashe Kai Dan gayu ne irin abin turawa kakeyi gaskiya Kai wayayye ne ka Gama wayewa Iyyeeeee ah Lallai na Sallama maka gaba daya,Harda daga Masa babban yatsa,dariya ta bashi sosai akan Kiss kawai take wani yabonsa Haka. Juyawa tayi tare da ci gaba da kallonta sai taga yarinyar film din ta yiwa actor din kyakyawar runguma Babu Kaya a jikinta,Yana rubutu a wani littafi ta kalleshi Harda leka fuskarsa ta kyalkyale da dariya tana cewa gaskiya ka hadu Miji komai irin na Yan Film din turawa kakeyi jiyama fa kayi min wannan abin, to ai kayi Kama da turawan dama,Kallon ya kashe duf tace Mene Haka ina Kallo na me Dadi,kin dameni gwara na Miki irinsa kiji a jikinki,Wutsil wutsil din Shagwaba ta Fara tana narke Masa ita Bata so,Shi kuwa wani shaukin sonta ne da shaawarta yake kwasarsa Yana fisgarsa. Rahmatu ce taga ta Kare musu ta Kira meeting kowa na gidan Yara da Manya suka hallara a babban palonta,Haule da Bilkisu suna Nan da yaransu,Rahmatu tayi gyaran Murya tace Assalamualaykum Yan uwa,Amsa Mata akayi taci gaba Dalilin dana taraku anan ba komai bane face na yanda zamu hada kanmu mu Zama tsintsiya madaurinki Daya,kunga dai Halin da muka Fara riskar kanmu,ya kamata mu dunkule wuri daya,mu hade kanmu,a yanzu bamu da mataimaki ya kamata muyiwa kanmu fada. Bilkisu tace gaskiya Kika fada Zancen munafunci da Hassada ya Kare a tsakaninmu,Yara ku hade kanku,Usman yace ai bakin alqalami ya bushe tunda ba ayi ba sai yanzu da akaji wuya,Firdausi tace wuyace wlh wuya Wanda yaga zai iya yayi mu Kam bamu taso a Haka ba,Haule Amarya tace wlh kuwa tun da Baku kawo Shawara ba sai da kuka ga ta Fara Kare muku,to Yan ragowar kadararmu Ni da yarana bazan taimaki kowa da ita ba,Omar yace ah yo sai yanzu aka san Yan uwa ne, za a wani fito da Zancen Family meeting to bada mu ba,Sagir yace a'a fa ya kamata a duba Maganar Umma Rahmatu mu samu ko duk wata Muna family meeting sannan a ajiye asusu duk wata kowa ya saka wani kudi wannan kudin duk abinda Ya taso a cikin family ko schl,aure etc sai a eba a ciki ayiwa Mutum dashi Kunga an taimaki juna,Su Meenal ne suka hayayyakowa Sagir wlh mu baza mu shiga ba,kwandala bazan saka ba,kaji zalunci kowa yaci gashin kansa ba ruwanmu kowa ya kula da kansa, Haka aka tashi daga taro baram baram sai ma fada da aka kwashi bala'i,Haibici,Gori da zagin juna. Gidan Baba, Mama Tana Palo Hankalinta ya kwanta Khadijanta tana Nan lfy wurin mijinta,Hafsatu ce ta mako kofa Kamar zata balla kofar ta Fado Palon Mama sai da Mama ta tsorata,Bala'i Hafsatu ta Fara wlh Babu Yar katuwar arniyar data Isa ta haifo Mana masifa a gidan Nan,naji ance kamar ciki ko uban Mene dake to kinyi kadan ki Haifo Mana jaraba a gidan Nan,munafuka algunguma,Baba ya daina Haihuwa Ya tsufa,kema kin tsufa in ba jaraba ba da maita har wani ciki kikayi? Tsaye Mama ta mike tace ya bazanyi ciki ba Miji nawa Gwarzo ne, Nima jaruma ce ai ko mun daina Haihuwa sai jarumtaka tasa mun Haihu,Kaine dai baka Haihuwa again sabo da ka tsufa ba karfi baka iya komai ba Dole kaga baza ka samu ciki ba ka Gama naka Haihuwa Eggs sun Kare naka. Hafsatu Hannu ta daga da niyyar zata Mari Mama,Tsawa taji Baba ya buga Mata dake shigowarsa kenan ya kalli Hafsatu cike da tsana yace wlh kina taba min lafiyarta a bakin aurenki,duk ranar da Kika taba ta da niyyar duka ko bana Nan a bakin aurenki,Baki Bude Hafsatu ta tsaya sororo tana kallon ikon Allah,Tsaki Baba yaja Lokacin Mama ta karbi babbar rigarsa tana Masa sannu da zuwa tana sakar Masa Murmushi tace muje kayi wanka ur food is Ready sai ka Huta,Shima Baba Murmushin yake sakarwa Mama na so da kauna abin gwanin Sha'awa da birgewa. Ba Shiri Hafsatu ta fice tana Huci kamar bakin miciji tana Jan kwafa. Abuja Birnin tarayya Mami Yau kwana Uku kenan Bata ga mijinta ya dawo ba Bata San Ina yake ba,Ta shiga damuwa tunaninta ko Yana Kano wurin Uwar gidansa ita ya daina sonta,kishi takeyi kawai, tana zaune a gefen Royal bed dinta tayi Tagumi Afrah da kawayenta sun tafi Wedding party,Tana zaune Shuru sai Yan aiki dake jirga zirga,wayarta ce tayi kara,da sauri ta duba taga Bakuwar Number sai ta daga,Muryar Mijinta taji ya lankwashe Murya Yana makyarkyarta yace Mamin Yara Mijinki ne,Hatsari nayi a mota a hanyar Maiduguri da nace Miki zanje,Yanzu Haka karayara ta ukku a kafa daya,Amma naji sauki gobe za a dawo Dani Abuja a Nan zanyi Jinya,Hawaye ya zubowa Mami tace nidai ka Bari nazo,Alhaji Shehu yace a'a karki zo My love kiyi zamanki da sauki sosai fa gobe Zan dawo nan,ya Dade Yana lallashin Mami sannan ta hakura tana Jiransa gobe. Tunda Alhaji Shehu ya auri Mami ya daina saurarar Uwar gidansa dake Kano da tarin yaransa samari da Yan Mata,sai yayi Wata Uku Basu sashi a idonsu ba,sannan su da talakawa duk Daya,Haka kudin schl ma Baya biya musu gaba daya Makarantar Gomnati sukeyi sai katon gida na Alfarma,mota kuwa kwaya Daya ce a gidansu itama ba me kyau ba,abincinsu Garau Garau talaka yafisu Jin Dadi,Zaluntar su yakeyi Haka Matarsa uwar gida Hadiza take hakuri dashi duk ya tsofar da ita bakin ciki yasa ta tashi daga aiki,yaransa da yawa sun Isa aure Amma yaki Yi musu wasu sun samu mazajen aure wasu mazan sun samu mataye Amma yace Sam bashi da kudi yanzu su hakura sai Nan gaba,da Sunyi magana zai ce Basu da godiyar Allah,gasu a katon gida Amma basa gani,shi bashi da wani kudi,samun nasa nawa ne gaba daya. Mami tasan da Haka Amma Bata tuna Masa da Allah,murna ma takeyi ita amfi sonta ita miji nata ne ita kadai,sai abinda tace ita da yaranta,tunda ya aureta take Kara zugashi Yana Wulakanta Hadiza da yaranta su da shara Daya,Basu da kima da mutunci a idonsa. Saman Bed Abdallah ya Daura Khadijansa Yana binta da mayen kallo ji yake kamar
Chapter 29 · 0% Book details