← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 53

Sashe 18

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Official
AsmaBaffa
RASHIDA ALIYU,FATIMA,HINDAT22222222,KHADEEJAT AHMAD AND SALEEMARH SAEED.
page naku ne Yan albarka.
Koda yayi Shirin Baccinsa itama Khadijan Haushinta yake ji ta jawo anyi Masa Mata har biyu zai mutu,Kwanciyarsa yayi bacci me Dadi ya kwashe shi,da Asuba ya tashi kamar yanda ya Saba yaje ya tashi Humaira tace ita ba yanzu take sallah ba,dama yasan halinta sai taga dama takeyi,Part din Khadija ya wuce ya Yana bude Palon kamshin daban ne,komai daban nutsuwa ta sakko Masa,Bai Gama Shan kamshi da kallon Tsafta ba sai da ya shiga Bedroom dinta,saman Sallaya ya isketa tana raka'atanil fijr, ji yayi ta birgeshi kofar yaja ya wuce masallaci.
Bayan Khadija tayi azkhar bacci ta koma 10am ta tashi ta Shiga kitchen tana hada breakfast tana Kuma gyara part din har ta Gama komai ta fada wanka,cikin Riga doguwa Yar kanti irin roba din nan har kasa take gefe da gefenta tsagace ta kai Rabin cinya,Hannun Vest ne da ita me Dan Fadi,Ta fito da surarta tayi Masifar kyau,Yar kwalliya tayi sama sama ta shafa turaruka,tana Fitowa Palo sai da ta firgita ganin Humaira kerere a tsaye sanye da Riga da wando sun dameta tam Haka ta fito tun daga part dinta zuwa na Khadija Yan aiki suna gani.
Khadija Ta bude Baki tace sannu Sis Ina kwana? Lokacin Abdallah ya shigo ya dau wanka cikin kana Nan Kaya,kyau Kam iya kyau Yana kamshi,Humaira ce tayi tsaki sannan ta nuna Khadija da yatsa tace ki shiga hankalinki wlh karki sake ki gaisheni Dan Uwarki,nafi karfin nayi kishi dake kucaka,dubeki shekararki nawa da har Zaki aurar min miji banza Yar Arna,Khadija da karfi cikin Hausarta da Bata fita tace what? Me? dan Arna ko? Is a lie baka sani ba ask your Husband I'm real Muslim so Ka daina fada min Arna,Oho kice sabon Musulunta ne tubabbu ko?cewar Humaira,Khadija tace noooo....watch ur tongue Ni ba tubabba ba Musuluma ni,Ka daina min masifa fada fada Haka cacaca Nima fa na iya fadan Nan,mijinka Mijina ne,the same muke kiyi biyayyar aure Nima nayi tawa,kina gani na Karami aka to Let me tell you nasan Mene aure da komi wooo,Abdallah gashi ka fada Mata ta daina zuwa part Dina tunda bashi da kunya Yana zagi na,idan ba aka ba gaskiya Zan Rama zamuyi fada,Tsaki Humaira taja tace bagwariyar banza,Uwaka banza cewar Khadija itama ta rama,taci gaba kullum miji Yana wajenka baya zuwa wajena so today girkina miji nawa har 1wk na budurwa sai ki Bari idan Nima yayi 1wk zai dawo waje naki Mayya Ni nace ya aureni? Ban sani ba aka daura Mana aure.
Abdallah ne ya gaji da cecekucensu yace kwanan ko wacce biyu biyu ku kiyaye bana son tashin hankali,Humaira kija girmanki ke Kuma Khadija ban son tsiwa,sannan ba Zan Miki 1wk ba domin an Dade da kaiki gidan miji so wannan ya wuce yanzu 2-2days ne. Gwalo Humaira tayiwa Khadija ta fita abinta,Khadija yarinya ga kuruciya sai ta fashe da Kuka Humaira tayi Mata gwalo wlh sai ta Rama ta tafi da gudu zata fita ta bita Abdallah ya Fisgo Hannunta ta dawo kusa dashi saura kadan ta Fadi ya riketa da karfi,sai kokawa suke tana zillewa tana kwacewa ita da Dole sai ta Rama tana kuka.
Tsawa ya Mata Zan mareki fa baza ki Bari ba tsayawa tayi cak tana Hawaye me akayi Miki da Zaki damu mutum da kuka?cike da shagwaba Khadija tace baka gani gwalo tayi min ai baka kula ba tayi min gwalo Allah sai na rama ta Karasa tana shesheka,Kallonta yayi yace to Rama a kaina, wullu....wullu...Khadija tace tana zaro Masa harshe Wai ta Rama shike Nan ta Kama dariyar da take Mata masifar kyau Wanda ya jawo Abdallah ya kafeta da Ido,Kusa dashi ta zauna a kasa kusa da kafafunsa tace Yaya Ga Breakfast ko kaci wurin matarka? Yanzu fa kike fada akan mijinki kince Kuma naci abincin wajenta bayan kwananki ne? Wasa fa nakeyi Mama tace Kai Yaya nane Hira zamuyi da Wasa sai na dinga baka Abinci kawai Haka ma Daddy yace min fa.
Abdallah yace hakane,Mikewa tayi ta wuce Dining hakan ya bashi damar karewa surarta kallo Wanda ta gaji da kyau komai ta hada, Dining din ya Karasa tayi serving Nasa,ya Dade Bai ci Abinci me Dadi ba Tunda yayi aure sai yau,yarinya Yar 17 Amma tafi Yar 26yrs komai.
Khadija Yana ci ta kafeshi da Ido yace lfy? Murmushi tayi tace Yaya Kaine kyawunka yayi yawa me kyau ne Kai,ka dinga godewa Allah,Murmushin Jin Dadi yayi data yabeshi,suna Breakfast sun Gama kenan Baba ya bugo waya hankali tashe,Abdallah waya na kunnesa Baba Yace Abdallah kayi sauri Kai da matanka ku taho gida yanzu,Tunda Abdallah yaji Haka yasan Wani ya mutu,Bai kawo kowa ba Sai Daddy,Kuka kawai ya fara,Ganin Haka Khadija ma ta fashe da kuka tana tambayar lfy? Kawai dakinta ya shiga ya dakko Mata Hijab Kato har kasa tasa yaja hannunta tare da kashe komai na wuta Suka fito,Part din Humaira Ya shiga yayi yayi ta taso su tafi tace ita a motarta zata taho zatayi Driving Haka kawai baza a takura Mata ba.
Mota yasaka Khadija gaba ya shiga Bai jira Driver ba suka wuce Family House dinsu,Yana zuwa yaga gida a damfare da mutane,manyan masu kudi da Dangin Daddy,ga talakawa makil,Yana Fitowa yaga Gawar Daddy har za a sallace shi,masu taaziyya aka Fara Masa Allah ya jikan Alhaji Yousuf,Baba Yana gefe Yana kuka Haka sauran Yara da Dangi,Ya manta Khadija na rike a hannunsa ma,ta tsage da kuka tana Ihu tace Yaya wlh na manta ban fada maka ba Daddy Yana Ciwon zuciya rannan naji Yana waya sannan Har Aman jini yayi,Baba yace Likitan ma yace shi ya kasheshi farar daya,Basu fadawa kowa ya rasu ba tun jiya da dare sai da aka kawo Gawar Nigeria Nan Baba ya sake fashewa da Kuka,Abdallah wanwar ya Fadi kasa a sume,Anyi anyi ya farfado Ina sai asibiti Khadija Ihu take a wajen Nan maza na kokarin maidata gida tayi tsalle tayi tsalle ta Fadi Tim tana Mijina ne Ni atafi Dani asibitin Dole aka jefata a mota itama aka tafi asibiti,wasu suka tafi asibiti wurin Abdallah wasu Kuma aka sallaci Gawar Daddy tare da kaishi gidan gaskiya.
Dangin Humaira duk sunzo Amma ita Bata zo ba Kuma taji mutuwar Saida Ummanta ta kirata a waya ta dura Mata ashariya sannan tazo gidan zaman makokin,Da taji Abdallah na asibiti ko damuwa Bata yi ba,Mami da kowa sai yanzu suke kukan banza marar Amfani, Hafsatu matar Baba tace Halinka na gari ya bika Oh anyi Rashi wayyyoooo mutuwa baza ta barmu ba wayyoo mutuwa Bata San Wanda zata dauka ba,Rahmatu Uwar gida tace Wai Wai wayyyoooo mutuwa gwara ki dauki Abdallah ko Sagir,Haule Amarya tace ai data dauke Daddy gwara ta dauki Abdallah,Sagir,Afrah da fiddausi Baki daya,Kai gwara a rasa mutane milliyan a Nigeria,Katanga ta rushe,munga ta kanmu,bawan Allah komai ya daukewa kowa,Mami tace ta Allah ba taku ba Mutuwa sai dai ta fadawa yaranku,,Bilkisu itama iskokinta Suka tashi ta Fadi yarab tana Aljanu,yaran gida Mata daga me Aljanu sai me kuka da ihu ansa katon Hijab da carbi,Mazan kuwa daga me Suma sai masu zaucewa,sai masu kukan zuci sai masu na fili,Afrah ce ta shigo ta dawo daga Abuja biki anyi Mata waya,da ihu ta shigo mun shiga uku Mami wayyo Daddy,Wayyo na shiga Uku na lalace.
Mutane suna Bata hakuri Addua akeyi ba Kuka ba,Addua yake bukata kuyi Hakuri Allah sarki ai dukkan me Rai mamacine muma ita muke jira kowa Bai tsallake ba,Afrah tace ku barni nayi ku barni nayi tayi zaman Yan bori tana burburwa sai Aljanu suka tashi faffafa,Merry ta shugo da gudu tana Mami Abdallah woooo ya mutu shima ewooooo miji na Khadija rayi nasa A hannun Allah an tafi asibiti a gani ya mutu ko da ransa,ai Mami itama sai ta sume aka shiga Kwara Mata ruwa likitoci kawai aka kawo gidan suna aikin soke mataye da mazaje da Allurai da karin ruwa,sabo da ga masu Aljanu ga masu Suma ga masu zazzabi kowa Babu lafiyayye a gidan Dr Hussain Yana kan Abdallah a asibiti.
Mami ma an Mata Allurar bacci,Yan zaman makoki Kuma har Humaira fadan halin Daddy suke na gari yayi musu kaza kaza etc Khadijan ma da tabi Abdallah sai Allurai akayimata na bacci aka shimfideta gefe domin ta Hana kowa sakewa Kar mijinta ya mutu.
Chapter 18 · 0% Book details