← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 53

Sashe 21

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

muskuta sosai tare da ture Abdallah da mazaunanta tace Malam ka matsa ka tare wuri tana hararsa,Abdallah tsaki yaja ya matsa kadan duk ya faffake wajen ya Saba da harkar manya,kallonsa Khadija tayi tace Kai Bawan Allah kana Kama da wani,Bai kalleta ba yace wa? Khadija tace Wanine na manta sunansa Ni dai,kaima Maiduguri zaka je? Abdallah yace Haka sukace masu motar,Khadija tayi dariya tace Allah irin nawa sunce Wai Maiduguri Zani Ni kuwa nace ae to Wai mece Maiduguri ne? Abdallah irin shegen Nan yace Bank ne fa wajen cire kudi,Khadija tace Kai baka sani bama Ashe wajen Saida lemo ne,muje musha lemonmu a can,Wanda suke motar Ana Jin hirarsu kowa Yana mamaki to su basuyi Kama da Mahaukata ba Kuma,suna ji akace a kawo kudin mota,Sai Abdallah ya zaro dubu goma ya Basu sai sukayi tunanin su biyu ya biyawa har Khadija dama Bata da sisi,Suka dauki kudin mutum biyu suka bashi ragowar kudinsa. Karba yayi tare da maidawa Aljihunsa, mota ta tashi suka Fara tafiya,ko minti biyar Ba ayi ba Abdallah yaja tsaki yace kai me mota Wai ba a zo bane har yanzu? Kowa ya bude baki a motar,Khadija tace aikin banza tun dazu sai tafiya akeyi ko kwana aka ce muku zamuyi a Hanya? Shuru akayi Ana mamakin Anya kuwa masu hankali ne conductor yace yaa ke Hajiya ko ba Borno state zaku bane,Khadija tace Muna shiga uku Muna lalashewa anshe maki Maiduguri kace ae to mu wlh ba Borno state zamuje ba Maiduguri zamuje wurin Shan Lemo,dariya aka kwashe da ita,Abdallah yace Kai...,sai Conductor yace yawwa me hankali fada Mana Kai ai Maiduguri kukace zakuje ko? Abdallah yace yes Bank ba zamu cire kudi,Salati aka saki a motar Driver yace Dalla ku kyalesu Yan rainin hankali suna Bata Mana lokaci gasu lafiya dasu Amma sai wani Raina mana hankali sukeyi, Khadija tace hey Ina zamu ga hankali naka har mu Raina maka shi,aikin banza kanayi, Kuma ka daina zagi namu. Tafiya akaci gaba da Yi har Khadija tayi bacci Abdallah Yayi bacci shima,Basu sani ba suna farkawa ba gida gaba ba gida baya Dajin Allah Amma Abdallah yace shi Dole anan za a sauke shi,Anyi anyi ya hakura yace wlh shi sauka zaiyi Bai San inda za a kaishi ba,Khadija ta farka tana goge baki tace Nima ai wlh anan zan sauka Binka zanyi bazai yuwu a saceni ba,to ae a saukemu a Nan cewar Abdallah,Driver yace Kai ba Azo bafa an kusa Ina zakuje a daji idan ba so kuke ku hadu da yan taada ba?Mene Yan ta'adda? Khadija ta tambaya Abdallah ya Bata amsa criminals,Dole Driver shi zatonsa Raina Masa hankali sukeyi mutane Shar Shar dasu kalar kudi Yan masu kudi kawai ya tsaya a Dajin gefen titi yace ku sauka to,Khadija ta Fara Fita Abdallah ya fita,sun manta ma da Kayansu sai Conductor ne ya tuna ya dauko musu Suka ja motarsu sukayi gaba,Kayansu Suka dauka tare da shigewa cikin Dajin gaba daya sukayi ciki abinsu. Yunwa kishurwa ta damesu ba abinci Allah yasa suka samu wata bishiyar mangoro ta nuna jajir dasu Khadija ta dauki dutse tana jifa ta kasa Abdallah ne ya dinga jifa sai da ya Fado da guda wajen goma,Suka zauna kasan bishiyar Suka shanye mangoron,sannan anan bacci ya sacesu,ko Sallah Basu tunawa da ita,Abdallah cikin Bacci ya Koma jikin Khadija ya manne ba tare da ya sani ba,suna bacci har wurin 10pm dare yayi sosai suna ta bacci a daji,wani sanyi akeyi sosai Wanda yasa suka dunkule wuri daya tare da manne juna,Abdallah kamshi kawai yakeyi ta ko ina sabo da shi Bai Dade Yana galantoyi ba irin Khadija. Sai 11pm Khadija ta Fara farkawa gaba daya Abdallah ya danneta rabinsa a jikinta yake,sanyi taji me tsanani ga duhun daji ko Ina duhu tsoro ne ya kamata ta Kare makalewa a jikin Abdallah sanadin hakan ya farka shima,Zaune ya mike Khadija da sauri ta tashi itama tare da Rike Masa riga Kar ya Gudu ya barta. Sai lokacin ya tuna tare suke da wata,Ba abinda yafi damunsu irin kishurwa,Mikewa Sukayi a Daren suna duba inda zasu samu ruwa ga duhu suna ratsa Dajin Abdallah Baya Jin tsoro Khadija ce ke Jin tsoro kawai hannunta cikin nasa suna tafiya wasu mutane suka Iske a Dajin sun balka wuta suna Jin dumi suna shaye shaye,Kafin su karaso Mutanen Suka mike da sandunansu tare da Adda da ganinsu kasan fulanin daji ne,Wurinsu Suka karasa,su kansu Sunyi mamakin ganin DanAdam da dare Haka a daji. Tsawa Yan fulanin Dajin Suka daka musu kai daga Ina kuke mutane ne ku? Abdallah yace ruwa Muke nema kawai abinda yace kenan ,Torchlight yasa tare da dallewa Khadija idonta yace Kai Kai aradu Ja'e wannan tayi irin Tamu ce, Wanda aka Kira da Ja'e ya mike Yana washe Baki Haka sauran ma suke mike gaba daya suna dariyar mugunta, Daya a ciki shi ya fisgo hannun Khadija kafin ya dauke hannunsa Abdallah ya warwareshi da Mari Wanda sai daya durku she a wajen, Mazan ne sun Kai su goma Suka taso kansu da niyyar dukansu tunda guda Daya yazo Abdallah ya shaki wuyansa ya Fadi sumamme sai ragowar Suka firgita da karfi irin na Abdallah ko Aljani ne sai suka kwashe da Gudu gaba dayansu,Wanda ya sume kadai aka Bari,sai da ya farfado Abdallah yace ruwa Muke bukata ba Shiri Dan fulanin yace rugar mu tana gaba da Dan nisa kuzo na rakaku zaku samu ruwa a can. Khadija na hannun Abdallah ya riketa suna tafiya a hankali har Allah ya Kaisu katuwar rugar Fulani dake Dajin, ruga ce me kyan gaske Tasha korayen gayye da Kuma yayan itatuwa,sai koramu gasu Nan kyau ba a magana hade da Niima. Basu ce gidan wani suke nema ba wata rijiya kawai suka gani Yan Mata suna Jan ruwa da guga a ciki,Direct wurin Suka nufa,Yan Matan ganin kyau da cikar halitta irin na Abdallah tunaninsu aljanu ne ma kawai sai suka jefar da gugan suka kwashe da Gudu zuwa gidajensu,Wanda ya rako su Abdallah ma tuni yayi tafiyarsa gida,Khadija tasan Rijiya suna Jan ruwa da, Abdallah kuwa Bai taba Jan ruwa ba,Gugan tasa ta jawo ruwa cikinsa sai da ta Fara Mika Masa ya tsaya Yana kallo kafin Daga bisani ya karba ya Sha da yawan gaske Itama Tasha suka koshi sannan suka koma can bayan rugar jikin wata bukka Suka Zauna a wurin. Khadija ta kalli Abdallah tace ya sunanka? Abdallah ya tafi tunani sannan yace ban sani ba Nima,Khadija tayi dariya tace tab Kai wanne irin Mutum ne Ni kuwa sunana Abdallah,Yayi Murmushi yace Nice name,Khadija tace ka samu suna ka sawa kanka koma wanne iri ne,Abdallah ya fada tunanin ba Sunan daya zo Bakinsa sai Khadija yace Sunana Khadija sai ko Suka kwashe da dariya Khadija tace ka iya zaben suna wlh. Akwatunansu Suka bude Babu bargo ba komai da kyar Khadija ta samo zanin atamfa guda biyu daya suka Shimfida a wajen Abdallah ya kwanta a Kai,Baki ta turo tare da cewa Kai Khadija ka matsa gefe Mana Ni Ina Zan kwanta,matsawa yayi kadan ta samu ta kwanta a gefe itama Suka lullube kansu da guda Daya zanin,Haka bacci ya kwashesu har rana ta fito Basu sani ba sai lokacin Suka farka suna manne da juna. Zare Ido suka farayi ganin shanu da mutane a kansu Ana ta kallonsu kamar wani sabon watan Ramadan manya da Yara,Tsaki Abdallah yaja tare da Mikewa Yana Jan akwatinsa ya nufi wurin wani katon kogi me kyau ruwansa garai garai Yana wucewa,kamar nutsatse ya dakko brush da toothpaste yayi brush sosai Harda dakko sabulu ya wanke kansa fuskarsa da hannu da kafa ya shafa Mai sai da ya Gama duk abinda zaiyi,sai kallonsa akeyi Ana cewa turawa ne Suka zo,Khadija ma can ta nufa da Bata kayan itama tayi har brush,Fitsari zatayi ta rasa yanda zatayi ga mutane maza da Mata Yara da Manya,Abdallah ne ya tsaya a bayanta yace na kareki kiyi fitsarin,Tana tsugunawa ta saki faya shaaaaaa take tsula fitsari a gefen gogi,Abdallah ya saki dariya yace kiyi a hankali mana,banza tayi dashi kawai sai da ta Gama tayi tsarki komai Sunyi har Alwala Suka koma gefe tare da tayar da Sallah. Basuyi ta jiya ba,Khadija raka'a daya tayi tal tayi sallama,Abdallah kuwa rakaa uku yayi abinsa ya idar, fulanin dake yankin ba musulmi bane Sam,ko Hausa ba wani ji Sukeyi ba sai kadan kadan,jahilai be a yankin gaba daya. Wani saurayi Kyakyawa dashi shi yaga Khadija ta birgeshi yaji Yana sonta,da Gudu ya koma wurin shanunsa tare da tatso Mata madara cikin katon Koko ya kawo Mata,Ai kuwa ta Fara washe Baki Abdallah ya kalleta sai yaji haushi tana yiwa wani dariya duk da Bai santa ba sai yaji kishinta Wanda shi Baya iya gane Mene,Kokon madarar ya kwace tare da jifa dashi gaba Daya har Madarar Suka tarwatse. Khadija tace zanfa Sha Ina so yunwa nake ji,Fuska Ba Rahma Abdallah yace baza a Sha ba ya fisgi hannunta Suka tafi cikin rugar,Mutanen suna binsu a Baya har cikin rugar,Shugaban yankin ne ya tare su a Hanya yace Kai Ina zakuje? Ku su waye ya sunanku? Zaku shugo Mana gari? Abdallah cikin mutanen Nan yace Sunana Khadija,Khadija Kuma tace Ni Kuma suna na Abdallah,Ba Shiri Sarkin garin ya bude Baki tare da cewa kai yaro Khadija Sunan mace ne na musulmi karfa ku Raina mana hankali,Gaku Yan gayu kalar kudi sannan Yan birni Amma zaku Raina mana hankali ko cirani kuka zo? Khadija tace na rantse sunana Abdallah shi Kuma Khadija,mu ba ruwanku damu mu a daji zamu zauna bamuce kowa ya rike mu ba. Dariya mutanen Suka kece da ita,wani yace ai yanzu ba a yarda da bako ko mahaukacine sabo da rayuwa bare ku gaku masu kudi ku zauna a daji Muka sani ko wani mummunan Abu ya kawoku Nan,harda wani cewa Wai sunanka Khadija sabo da rainin hankali. Khadija dake tsaye tace to karku yarda din ance neman taimakonku mukeyi a daji zamu zauna ai Daji na Allah ne,Sarkin yace Ke Daga ji ma yaren kudu ce ke,sabon Musulunta ce ke ko? Tubabbiya ce ke? Tsaki Khadija taja Suka yi tafiyarsu tare da barin mutanen a Nan tsaye kikam. Mami suna murnar bacewar Khadija tare da Humaira dasu Afrah harma
Chapter 21 · 0% Book details