Sashe 7
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Mami, tace ga key na Gama,Harara Mami ta watsa Mata tare da cewa wlh idan yace baiyi ba,ko an Masa sata sai kinci ubanki a gidan Nan,bace min da gani annamimiya daga ke har uwar Taki. Khadija Hawaye ya zubo Mata ta juyo zata fita tana kuka ji kake gwaf tayi Karo da Abdallah,tana shesheka ta wuce ba tare da ta Dago ko kanta tasan waye ba,sabo da kamshinsa kadai tasan shine. Mami Me ya faru Kuma? Abdallah ya tambaya,tsaki taja tace part dinka ta gyara tunda su Afrah Basu iya ba kana dukar min Yara daga yau indai yayi maka dai dai ka fada min ta Zama Yar aiki a gidan Nan ita zata na gyara maka part dinka. Amma Mami kin San fa Baba uwarsu yake aure ko ba komai kamar kannenmu ne,Bai Dace a sata Yar aiki ba,to wlh indai yayi kyau ita zatayi maka kaji na rantse idan Kuma baka so to Afrah da yaran gida kasan Babu Mai maka. Shuru yayi yace ki bayar a kawo min Abinci na yunwa nakeji nasha aiki a Office Daddy ya sani aiki da yawa. Mikewa yayi tare da tafiya part dinsa,Yana budewa Bai San sanda ya saki Salati ba sabo da tsabar azabar kyau da kamshi da yakeyi kamar Aljannar duniya,Bai Gama mamaki ba sai da ya shiga Bedroom, kitchen da Toilet etc, wow ya furta daya ga kayansa a shirye an wanke an goge gefen Bed,ji yayi kamar ya taka rawa,a fili ya furta wlh tayi Mami itace kullum zatayi min gyara wannan itace sarkin Tsafta ta gidan Nan,ban taba ganin Tsafta Haka ba iya zamana a duniya. Sai yanzu ma ya tuna Bai taba zuwa ya gaida Maman Khadija ba,gaskiya Bai kyauta ba,yau Baba ba a dakin Mama yake ba,Yana bangaren Hafsatu sabo da Haka yau ranar rakashewar su Khadija ce,Wando ne short iya rabin Cinyarta ya kamata,ita Kuma Merry pencil Jean blue da Yar Riga,Ihsan da Yar Ficikar vest da short Wando Ahmad Yana gefe Yana kallon Cartoon Khadija ta mike tare da Ware uban kidan Igbo a katuwar speaker dinsu dake girke a palon,Merry ta mike ta Fara taka rawa suna Mata tafi da ihu har Mama dake gyara ganyen Ogu,Khadija tace yarinya Move let me show you how to Shake your package,ta mike ta Fara jijjiga Hips kamar zai Fado,Door bell suka ji Merry ta bude da sauri ta fadada Fara'arta tace Inna unni? Lfy kawai Abdallah yace Khadija Bata san wani ya shigo ba ma,sai da Mama tace ta rage Volume Sannan ta gane Abdallah ne,rage Vol tayi Amma Bata fasa rawarta ba domin ba kunya ce dasu ba. A sace Abdallah ke kallonta a ransa ya furta yarinyar Nan shedaniya ce sai rawar masifa ai Dole ma ta iya rawa yarinya kullum kida,Sai Mamace tace Abeg Off that music,Kashe kidan tayi Baki daya sannan tazo ta zauna gefen Abdallah tace Sannunmu Inna Unni? Lfy ya amsa Suka hada Ido tana wani yake Kyakyawan bakinta da hakoranta,a ransa yace jiba Dan Baki mitsil sai dariyar tsiya,Ta mike tsaye,Abdallah a ransa yace adon tsoka sukeyi kullum wannan ita ga cinya lukuta da katon Hips har yayi yawa ma,duk a ransa yake magana,Yana zaune ta shiga kitchen ta Hado Masa abinci da kayan Sha ta kawo masa sannan tace yaron Daddy ga abinshi fa,Mama ma tace pls eat abeg u,Dole ya bude abincin pounded yam ce miyar Egusi Tasha Naman rago,ga lemon da suka hada,sai farfesun Kaji,baiyi niyyar ci ba kamshin girki yasa ya fara ci,Loma daya yaji wani dadin masifa da Bai taba ji ba,duk gidansu ba a taba abinci me dadin Haka ba,ai sai ya Shiga ci hankali kwance musamman da yaga tsaftarsu ta zarta tunani,Mama tana ta murna Haka su Khadija ma,Khadija ta zauna a kasa gabansa tana kallon sa kamar Tv Dadi ya rufeta,da ya Dan kalleta sai tace feel Free and enjoy ur food...eat..eat...ok,harararta yakeyi a fakaice Amma ita ba ruwanta,Merry Kuma ta dameshi da lemo daya dan tsaya zata Mika Masa Lemo tana akwai Dadi woo Khadija ta hada shi abincinma ita ke lailayashi Wai dafawa take nufi,Mama tana yes she can cook very well, that's why I like her,she is my Daughter duk sun dameshi,Ahmad Kuma wayar Mama ya karba Yana ta waya da abokinsa Dan Igbo dake Anambra state sai yaren Igbo yakeyi caccacaca.. Sai da ya koshi dam sannan da gudu Khadija ta kawo Masa Ruwa a wani bowl Wai ya wanke hannunsa bayan da spoon ma yaci abincin,Amma Haka ya wanke,tsaftarsu tasa ya zauna a wajensu ya Dade Mama tana ta bashi labarinsu iri iri,Yana gani Khadija zata Yi bacci kamar jaririya ta dawo ta fada jikin Mama ta Fara baccinta,ita Kuma Mama tana shafa kanta tana wani lallabata,Itama Merry Haka tazo ta kwanta tayi matashi da cinyar Mama,ga Ahmad ya wani Kwantar da kansa a kafadarta,Ihsan tana kwance gefe. Sai suka birge Abdallah Shakuwa ce ta daban a tsakaninsu,ya mike ya musu sai da safe ya koma part dinsa. AsmaBaffa [12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: TUBABBIYA 4-5