Sashe 40
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suna facing juna amma Bata matso kusa dashi ba kowa Yana karshen gado, duk da duhu ne hakan Bai hanasu Kallon fuskar juna ba,Wani kaunar juna tana Kara kamasu, a hankali Khadija ta Dan matso kadan shima ya matso kamar mayen karfe Haka suke jin dumin juna,a tare suke matsawa har suka hadu a tsakiyar bed din,a hankali tasa hannunta me laushi Cikin nasa. Damkewa tare da matseshi cikin nasa Ido ta lumshe tare da matsowa jikinsa ta kwantar da kanta saman Kirjinsa me laushi da kamshi,Hannunsa yasa Yana shafa gashinta a hankali,Kamar baza tayi magana ba sai ya tsinci Muryarta me Dan Karan Dadi tace You are my Final Buss stop,aransa Yana dariyar iya zaro Zancen Khadija Wai final Buss stop, a fili yace You are my Final train station dariya sukayi gaba daya tace Tashar jirgin kasa? Yes ai kinsan yafi Buss tsada,Sai ta canja tace to na fasa Kaine madak atar karshe ta jirgin sama, ok to kece gingimarina trailer dariya tayi sosai tace to Kaine zakin Zuciyata You are My lion, kece Damusa ta, micijiyar rayuwata, gaskiya ban yarda ba snake, You are my Sweet Banana,You are My Apple cewar Abdallah shima. Blanket ta jawo ta rufe su gaba Daya sannan ta koma saman Abdallah ta kwanta ta maidashi katifar harda sakin nauyinta sannan tace Ina da nauyi Dan Allah? Murmushi yayi kana ya daura Hannunsa saman Mazaunanta Kina da wannan kayan ai Dole kiyi nauyi, suna hirarsu ta masoya bacci ya kwashe su. Mami tana fama da ciwonta duk ta rame tayi baki hakan yasa Alhaji Shehu ya tsaneta dama kyawunta yabi ya aureta yanzu Kuma Babu Kyau ga kafarta ta Fara tsatsafo da wani ruwa me wari, Afrah ke kula da uwar tasu sai autarsu, Alhaji Shehu ya Hana ko kwandalarsa ta magani,Mami tana kwance zazzabi ya rufeta Afrah ta Bata magani da abinci sannan Mami ta jawo waya tare da Kiran Alhj Shehu,sai da ta Kira yafi sau goma Bai daga ba,Yana dagawa kuwa Ya fara Bala'i kin dameni ko ni na Dora Miki cutar ne? Uban Kuma me Zan Baki? Hawaye ya zubowa Mami tare da Dana sanin auren da tayi,Nan danta Abdallah ya Fado Mata da Yana Nan da baza ta wahala ba Kuma ba kasar da bazai kaita ba Dan ta samu lafiya,ganin Bata da zabi yasa tace Alhaji kamar ba Kai ba,duk son da kake nuna min Yana Ina? Yanzu akan lalura ta sameni ka gujeni. Dama abinda kika kirani ki fada min kenan? Ke wacce iri ce? To Bari kiji kwandala bazan Baki ba ai Nima badan Allah Kika aureni sabo da dukiyata Kika aureni Dani talaka ne ko kulani baza kiyi ba, Nafa San me nakeyi Kar nake kallonki shashashar banza. Wayar Mami ta kashe Hawaye na zubo Mata Babu tsayawa,Afrah tana gefe itama Hawayen takeyi kanwarsu ta shigo itama ta zauna gefe Babu me lallashin wani,Mami tace ku daina kuka muyi amfani da ragowar kudinmu da Suka rage ko Allah zai bani lfy, Sai dai Mami ya kamata mubar gidan Nan mu tafi Kano ko Kaduna neman magani zaifi araha akan Abuja cewar Afrah, Mami tana rawar sanyi tace ko Maiduguri ku kaini idan Ma Dajin Sambisa ta Kama ku tafi Dani can indai Zan samu lfy. Duk da halin da suke ciki Saida Afrah tayi dariya Lallai Uwar tasu taji wuya. Washe gari Mami ta sake kiran Alhaji Shehu Dan ta sanar Masa tafiyarsu Yana dagawa ta kwantar dakai tare da cewa Alhaji zamu tafi Kano ko Maiduguri neman magani ko Allah zai sa mu Dace,Da matukar masifa yace Ina ruwana ko na daureki? Ku tafi Bauchi ma ko Sokoto Ina ruwana ko idan Kinga dama ki Haura kasar ,Ni dai Ina fada Miki matukar Kika tafi to a bakin aurenki,Mami ta fashe da kuka Yanzu Alhaji Shehu Haka zaka Yi min? Ashe abinda kakewa uwar yaranka Nima zaka min? Ka tausaya min da kudin gadon yarana Zan nemi magani bada naka ba,Tsaki yaja sannan yace Na fada Miki matukar Kika fita a bakin aurenki karki dawo Gidana. Mami tana Hawaye ta fadawa Su Afrah,Afrah tace yaci ubansa ki taso mu tafi wlh Mami so yake ki mutu wlh Kika mutu bashi da asara,Kamar Baki da dangi kamar bamu da kowa a duniya,mu dai Dan Kara Bari mu gani tukun cewar Mami. Mami Haka taci gaba da Zama cuta na cinta ta Gama kwanjalewa tayi baki,kuraje ko Ina ga kafa tana ruwa da wari,Babu Wanda zai ganeta a halin yanzu,Su Afrah ma sabo da wahala da bacin Rai duk sun rame zuciya ba dadi, Yau Mami kwana tayi tana Suma kamar baza tayi Rai ba,sai ihu da wayyo wayyo takeyi,Su Afrah sun zagayeta suna kuka,karshe Afrah ta Kira Yan uwan Mami sun Dade suna kiransu Amma sau biyu suka zo dubiya Babu wani ko wata data Kara zuwa duba Mami,Ranar naka sai naka,rayuwa Dole ko ka guji mutane akwai ranar da naka Dole sai naka ranar cuta kenan. Sunce zasu zo Amma Shuru har kwana biyu Afrah ta shirya ta shiga motar haya sai Kaduna gidan Ubansu Wanda rabonsu da zuwa tunda Mami tayi aure Suka samu duniya sai yanzu da wahala ta kawota Basu da mataimaki,Bata Fara shiga Gidansu ba Family House kawai gidan Baba ta wuce Direct,taci sa'a zai fita Office kenan,Tasha mamaki yanda Baba ya Zama Hamshakin me kudi Haka,komai ba yanda Suka sani ba,Baba tunda yaga Afrah ta rame sannan har tasan tazo gidansa gaskiya ba lafiya ba,tunda Suka tafi Basu Kara waiwayar gida ba ko dangi daga na uwar har na uba. Gaban Baba taje harda Durkusawa har kasa Wanda da ko gaida Baba basayi,da fara'a ya amsa ba tare da ya nuna Mata komai ba,Afrah meke tafe dake ne haka da sassafe? Afrah harda hawayenta tana bawa Baba labarin komai,Jinjina Kai Baba yayi yace to Yan uwan Maminfa? Wlh Baba sunki saurararmu Wai tunda ta samu duniya Bata neme su ba Saida lalura tazo mata. Bari a tura driver ya dakko Mamin Taki da Yar Uwarki ammafa idan ta shirya barin auren nata,Afrah tana murna tace ai ta hakura da auren kawai idan mun tafi ne bamu san Ina zamu zauna ba shi yasa,shiga ciki kici abinci ki huta kawai Inshallah zata samu lfy,Ameen Afrah ta amsa ta nufi ciki Baba Kuma ya shiga mota ya fita abinsa. Rasa Ina Afrah zata nufa tayi, part din Hafsatu ko Part din Mama,tunowa tayi da halin Hafsatu na cin mutunci Amma duk da Haka Part din Hafsatu ta shiga,Hafsatu sai da ta mike tsaye sabo da mamakin ganin Afrah tana Mata sallama da fara'a, dama Hafsatu Bata kaunar zuriyar Mami Nan take taja tsaki tare da dakawa Afrah tsawa uban me kika shigo min part zakiyi? Matsafa masu zuwa wurin bokaye wlh nafi karfinku,shegu Dangin kodaddu gashi Nan halinku na banza yasa kullum Babu ci gaba sai kanjalewa kikeyi fitar min a Palo na Dan bansan da tsiyar da Kika zo min ba. Murmushi Afrah tayi a ranta tana Allah sarki duniya Wai Hafsatu ke zaginta Haka Wanda da Dane da tuni ta Mari Hafsatu Amma duniya ta koya musu darasi sai tace Allah Baki hakuri,Wannan kalma ta bawa Hafsatu matukar mamaki Afrah ke Bata hakuri cab,Firdausi ce ta fito da murna tace laaa Afrah kece yau a garin sannu da zuwa,Hafsatu tsawa ta bugawa firdausi koma ciki Dan ubanki ko na karyaki,sum sum firdausi ta koma inda ta fito Afrah tana daga Mata hannu itama da murna. Ficewa Afrah tayi ta nufi part din Mama tana shiga da sallama merry Ce ta amsa wacce dawowarta kenan Daga Exam sabo da ta Fara University tuni,Murna Sosai Merry keyi da ganin Afrah,Husna ta fito itama zata tafi schl sai Murna Suka tarbi Afrah bayan sun gaisa Merry tace yanzu na dawo Mama ta tafi Asibiti tun 8am Amma anjima kadan zata dawo,Afrah mamaki ya cikata Duk irin wulakantasu da sukayi Amma kalli yanda suke Nan Nan da ita kunyarsu sai ta kamata,kayan ciye ciye da shaye shaye Merry ta kawo mata,dama yunwa takeji bata karya ba ta fito,abincin taci ta koshi sannan ta shiga dakin Merry tayi wanka,Merry tace ta zabi kayan data keso cikin nata tasa kasancewar ba tafiyar hayyaci bace Bata fito da komai ba na Kaya. Bayan ta shirya sai ta Kira Mami ta sanar Mata duk abinda ake ciki da irin karramawar su Merry, Karshe tace idan zaku taho Mami a Hado min kayana kaf a kawo min Baba ya turo Driver. Mami tafi kowa Murna Amma tana kunyar Baba da iyalansa musamman Mama. Hafsatu bakin Halinta Bata fasashi ba sai abinda yayi gaba. Rahmatu da yaransu sun Dan farfado sai rufin Asiri kasancewar yaransu da yawa sun samu aikinyi ga Baba Yana tallafa musu sosai sai asirinsu ya rufu sai dai har yanzu Suna da kiyayyar Baba sabo da asirin da Hafsatu tayi musu,duk abinda Baba yake musu basa gani,shi kam yasan Dan Allah yake musu badan komai ba. Washe gari bayan su Khadija Sunyi Sallar Asuba sai suka koma bacci sai 9am Khadija ta farka tare da zare jikinta a hankali yanda Abdallah bazai farka ba,gyaran inda Yan aiki basa zuwa tayi da kanta ko Ina ya dau sheki da kamshi bed din Abdallah ne kawai Bata gyara ba sabo da Yana bacci,Kitchen ta shiga ta Fara baje basirarta ta fannin girke girgirke,gida ya kaure da kamshi har makwafta suna Iya Jin kamshin girkin Khadija,Sai da ta Gama gwalangwasonta a girkin Kamar na turawa ta shirya a dinning sannan ta koma room dinta tayi wanka tare da daukan wata uban kwalliya ta shirya cikin wata dakakkiyar shadda pupple Abdallah ya dinka Mata a garin Kano da suke yanzu rigace ta wuce gwiwa an zagata gefe da gefe tare da Zani Tasha aiki sosai Fadin irin kyan da tayi Bata Baki ne kamar wata Hajiya Haka ta fito,dauri Kuma irin ture kaga tsiya tayi ta wani cokoshi. Abdallah Kamshin girkin Khadija ne ya tashe shi dama yunwa yakeji,Toilet ya shiga a gurguje ya fesa wanka ya shirya cikin kana Nan Kaya Daya Saba sawa Yana shegen kamshi ya gyara Mata saman bed din kamar mace Haka ya dameshi sosai dama yasan ta gyara ko Ina ya hutar da ita ya gyara yana sakkowa daga sama ya hangota