← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 53

Sashe 13

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanka Khadija tayi tare da gasa jikinta da ruwan zafi sannan ta dauki wayar da Baba ya siya Mata me kyau Infinix Haka Merry ma da Mami ya siya musu masu tsada kowannensu,Mama ta Kira taji ko sun taho,Mama tace sai Gobe zasu dawo gaba daya dangin Baba masu mutunci da karamci sun hanasu tahowa yau,hakan baiwa Khadija Dadi ba ta Matsu su dawo gidan ya isheta ita daya. Bayan ta dawo Daga Islamiyya kitchen ta shiga tana nazarin me zata dafa Masa pounded yam da egusi soup ta hada Masa Tasha naman kaji sai lemo da farfesun beef meat ta Masa Hadi da carrot da sauransu abin Sha'awa. Wanka ta shirya cikin Riga da da Zani Amma bata iya daurin Zanin ba Sam ta dageshi sosai Kuma ta daura saman rigar ta yafa mayafi a kanta abinka da Fara tare da kyau sai tayi kyau sosai a hakan. Tana tsoro da sanda ta shiga part din ba tare da kowa ya ganta ba,tana shiga tasa key Dan kar Mami ta kamata, Yana main Palo ta sameshi saman 3seater Yana kwance da Alama bai warke sosai ba yanayinsa,Sallama tayi Masa tare da ajiye abincin a gabansa tana Sannu ya jiki? Da sauki ya Furta,kasha magani ta furta tana dafa saman goshinsa da hannunta har yanzu jikinka da zafi. Kallo yake binta dashi yanda take damuwa da damuwarsa. Abincin ta zuba Masa a plate ta koma gefe ta zauna,da kansa yaci sosai sannan ta dakko Masa Magungunansa a bedroom ta ballo tana bashi da ruwa Yana Sha ya Gama ta kwashe Kwanukan tare da Masa sai da safe ta tafi abinta. Mami kwana biyu Bata ga danta Abdallah tun tana fushi dashi har ta hakura ta tafi part dinsa domin gano lafiyarsa,ai kuwa taga ya rame Bai samu ya warke ba sosai,a gigice ta Karasa gabansa tana tambayarsa lfy? Yace bani da lfy Mami ki yafe min na Bata Miki...kafin ya rufe Baki tace na yafe maka Abdallah na,Allah baka lfy ai ban sani ba,a part dinsa ta yini tana kula da danta sai data ga ya warware sannan ta dawo bangarenta. Shi kuwa Abdallah murna ta kamashi Maminsa Bata fushi dashi. Washe gari da Yamma lis Khadija ta dawo Daga Islamiyya kenan motar su Mama tayi parking a gidan sun dawo lfy,Abdallah Yana jikin motarsa Yana kokarin shiga zai fita Yaji ihun Khadija Wanda Saida ta tsorata har masu Gadi,Jakar makarantar ta jefar ta dinga tsalle da ihu tare da fadawa jikin Mama da Merry,Baba Yana kallonsu cike da Jin Dadi,Khadija har kasa ta duka tare da Gaida Baba tana musu sannu da zuwa,tsaki Abdallah yaja sannan ya karaso gaban Baba da Mama ya gaidasu a mutunce tare da musu sannu da zuwa suka amsa suna Masa Godiya tare da tambayarsa kowa lfy. Ido suka hada da Khadija Abdallah ya harareta yanda take wani murna duk ta cikawa mutane kunne da surutu,ciki suka rankaya shi Kuma Abdallah ya shiga motarsa ya bar gidan. Bayan sati Uku Daddy ya dawo tare da Matarsa sai sintiri akeyi zuwa gaidashi,Daddy ba abinda yake damunsa irin Rashin hadin Kai na iyalansa,Ga almubazzaranci ganin suna da wadata sai ayi ta barna da abinci ba tattali wata sai tasa a dafa Mata Abinci sai tace ta fasa ci,baza su bawa almajirai ko wasu ba sai su juye a shara,kayan Abinci duk yawansa kwana kadan kowacce zata ce Babu a part dinsu har Hafsatu matar Baba,Haka magani da zuwa asibiti ko Ciwon Kai Suka ji sai Doctor ya dubasu an Tarawa Daddy bills a Hospital kudi me yawan gaske ko tunanin rayuwa basa Yi,idan ba ransa ya zasuyi kenan,gashi duk cikinsu Babu me Jin Maganar wani,Kaninsa Ma Baba Basu daukeshi komai ba,gani sukeyi bashi da wani Amfani a garesu sabo da shi ba wani bane. Sai yanzu yake ganin illar aure auren da yayi Yana saki,wasu Matan ma da ya aura duk sun tafi da yaransu yanzu Kuma Yana mutuwa zasu zo dasu za a raba gado rigima ya Bari ba karama ba,Bai yi Saar auren Mata na gari ba,Basu San rayuwa ba ko kadan kawai Jin Dadi da Hutu Suka sani shi yasa Basu da hankali gaba daya,Abdallah ne daban duk da shima Bai San ta duniya ba Amma yafi su hankali. Daddy yaji Dadin auren da Abdallah zaiyi Amma da yayi bincike abin ba kyau,Humaira ba matar aure bace musamman Abdallah,ga Mami ta dage akan kwadayin dukiyar wasu sabo da Rashin wadatar zuci duk kudin mijinsu da yaransu na wasu take hange,Daddy yasan Hana auren Matsala zai haifar ga Abdallah domin Mami zata iya tsine Masa,Babu irin Nasiha da fadan da Daddy baiwa Mami ba akan a hakura da auren Abdallah a nemi wata,Mami har da kuka za a rabata da danta za a Hana danta ya Mata biyayya,Daddy yace Allah ya Sanya Alkhairi Zan Masa auren Amma ko bana Raye sai kinyi kuka da idonki ta Dalilin wannan auren. Matansa kaf da maza Da Mata yaransa ya Tara wuri daya har da Baba da iyalansa Daddy ya musu Nasiha sosai akan rayuwa da Kuma irin abubuwan da suke Tafkawa Marasa kyau,Ya kallesu yace kun ganni Kuna rainani Kuna ganin kamar bani da amfani a gareku wlh babban katanga ce duk ranar Dana Fadi na Mutu kuka rasani Babu Ni zaku Sha mamaki,rayuwa ba tabbas,Allah ya gani nayi kokarin sauke hakkokina a kanku Amma bakwa ganewa,yanda kuke wulakanta Abinci da sauransu,gaku kune gulma da munafunci ku sai abinda iyayenku Mata suka ce to gaku gasu Nan,duk ranar Dana mutu zakuyi nadamar halayenku, Ina Baku Shawara ku kaunaci junanku,ku hada kanku,Sannan ku dinga aiki da hankali da tunani,ga Dan Uwana Uwa daya uba daya Kuna ganin bashi da amfani na tabbata sai yayi muku ranar da Babu Wanda zai muku ita sai shi. Ku daina ganin ko na mutu ba wani Abu sabo da na Tara muku dukiya to ko nawa Mutum ya Bari kuka gada zasu Kare cikin kankanin lokacin matukar bakuyi amfani dasu ta hanyar data Dace ba,maza da matanku ku yarana nayi nayi ku fito da Wanda zaku aura kunki gaku da yawa kun Isa aure Amma kun Gaza,bazan muku Dole ba iyayenku Mata zasu aurar daku tunda su kuke so ni ubanku ban Isa ba. Sosai Daddy yake ta fada da Nasiha sannan yace sauran yarana da suke kasar Nan iyayensu daban ku shirya duk zasu dawo Gidana da Zama Suma, karshe ya rufe taro da Addua,Baba Yana zaune sai kuka yakeyi sosai Sabo da kalaman Yousuf Dan uwansa Sun rudashi tare da bashi tsoro,Shima Abdallah tsoro ya kamashi Daddy na Zancen mutuwa Hawaye yakeyi,Su Khadija suna gefe da Mama Sunyi Shuru,sauran Yaran kuwa Danna waya suke kawai wasu ma Headphone Suka saka,bayan ya sallami taro daga shi sai Baba Dan Uwansa,Wasu takardu ya Mika Masa yace karbi takardun gidajene guda biyu daya Kaduna daya a Kano idan gidan nan ya dameka sun koreka ka koma gidajenka ne na Mallaka maka kyauta halak malak,Sannan ka kula da Business naka sosai Dana doraka a Kai,shi yasa ban hadaka a dukiya ta ba,na baka kasonka daban babu Wanda ya Isa yace kudin magada ne. Baba ya sake fashewa da kuka yace Yaya nifa ban gane maka ba wannan zuwan,Meke faruwa da Kai Haka? Murmushi Daddy yayi yace ka daina damuwa abinda ya Dace nayi ne kawai tun tuni banyi ba shi yasa nakeyinsa yanzu. Da kyar ya kwantarwa Baba Hankali,Check na millayan talatin ya mikawa Baba yace naka ne. Wasu takardu na gidaje guda biyu ya mikawa Baba yace wannan a Abuja wannan a Kaduna Nan gaba ka bawa Abdallah nasa ne halak malak,ba yanzu zaka bashi ba sai Nan gaba,Sai kudi shima ka ajiyewa Abdallah a accnt naka Nan gaba ka bashi,wannan sirri daga Ni sai Kai sai Allah,karka fadawa kowa. Ban bawa Abdallah wannan Dan nafi sonsa ko don wani abuba na bashine Dan biyayyar da yake min yake maka Dan Uwana,sannan sabo da kyawawan halayensa,na kudurce a Raina duk Wanda yayi Haka Zan Masa wannan kyauta sai gashi Abdallah kadai ya min biyayya. Baba dai Kuka yake kawai kamar mace har ya karbi takardun da Kuma wasiyyar Daddy a rubuce Dan kar ma ace karya ne watarana shi yasa Daddy yayi rubutu da komai ya bayar, Abdallah da Baba sun rasa sukuni gaba daya gani sukeyi Daddy mutuwa zaiyi kawai,kullum Basu da walwala har aka saka ranar bikin Abdallah da Humaira,biki ya rage saura wata daya Amma Ango ramewa yakeyi kawai sabo da Maganar Daddy shi gani yake Daddy mutuwa zaiyi shi yasa yayi azumin kaffara na rantsuwar da yayi kan bazai auri Humaira ba yanzu ya hakura zai aureta Daddy ya daura Masa aure da kansa Kar ya mutu,Yana so Daddy yaga aurensa. Khadija kuwa sai kunci takeyi tana zabgewa Kan Abdallah zai auri wacce Baya so tana Taya frnd dinta bakin cikin auren Dole da za ayi Masa,kullum sai tayi masifa tanawa Mama mita Har Baba ta fada Masa karfa ayiwa Abdallah auren Dole,Baba yace taje ta fadawa Daddy da kanta. Yau da Sassafe Khadija tayi Shirin zuwa wurin Daddy ta fada Masa Kar ayiwa Abbdallanta auren Dole gashi Nan Yana ramewa,Tunda ta shiga sanye da Hijab take sabo da Baba yayi musu fada da nasihar saka Kaya masu bayyana tsaraici ga mazan da ba muharramansu ba Kuma sun dauka duk da watarana suna Dan kin sawa Amma suna gwadawa,Sallama take kwalawa Amma Shuru har sama dakin Daddy Babu kowa,cikin toilet taji kakarin Amai Daddy nayi,baya ta koma Daddy ya fito da waya a kunnensa Yana kiran Doctor a wahalce yace Doctor yanzu fa Ina tunanin zuciyata ta gama lalacewa domin Ko kaki nayi jini ke fita,Baki Khadija ta dafe sabo da a boye take bayan labile tana Jin Daddy na magana saura kadan kwanakinsa a duniya,Doctor Yana kwantar Masa da Hankali Bayan sun gama waya yasha maganinsa sannan ya kwanta saman Bed,a hankali Khadija ta fito yanda bazai kula ba zaiyi tunanin Yanzu ta shigo dakin nasa,Sallama tayi ya amsa Mata da Fara'a yarinyar ta kwantawa Daddy sosai,a gabansa ta zauna a kasa shi Kuma ya zauna saman Bed ta gaidashi,yace Khadija lafiya dai na ganki Haka da Sassafe? Khadija ta dukar da Kai kasa sannan tace Daddy Dan Allah karka yiwa Abdallah auren Dole,baka gani duk ya
Chapter 13 · 0% Book details