← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 53

Sashe 15

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Afrah duk anbi jirgi an tafi sheda Daurin auren Yayansu,Khadija kuwa part dinsu ta koma Dakinta inda Abu ke zaune tana kwalliya sai ji tayi Khadija ta rushe da uban kuka,Abu ta saki powder ta tarwatse tace nashigesu ke Kuma lfy? Khadija tace Daddy zai Masa auren Dole shike Nan ya daina dariya,Tsaki Abu taja tace banza sai kiyi ai har kullum baza ki hankali ba Khadija,Kinaga yanda yake washe Miki Baki Ana muku hoto kice baya sonta munafuki Yana son Abarsa kina Nan Zaki ji ya dirka Mata ciki ta haihu, gwara ma ki daina batawa kanki lokaci muyi wasanmu Ina ruwanmu mu Dan anyi Masa auren Dole. Khadija tace anjima rawa za a Sha a gidan Nan,wlh zamu cashe a gidan nan ai Ni ko Dan rawar Nan ma na daina fushi gwara da aka Masa aurensa,Abu tace ahaf aikin banza kin Sa na fasa Hodata Yar dari uku da Hamsim wlh sai na dauki Taki kin biyani,Khadija tace taf sai dai na karbo Miki kudi wurin Abdallah ki siya wata. Kano can masallaci Yan Daurin aure suka Sheda An daura Auren Abdallah Yousuf da Humaira A.A.Sani Kan Sadaki Naira dubu dari biyu,Ba a Gama murna ba Suka ji an sake bada Sanarwa An daura auren Abdallah Yousuf da Khadija Adam akan Sadaki dubu dari biyu,ko Shi Abdallah daga sama kawai yaji abin Kamar a mafarki,bakin ciki ya kamashi shi ya tsani Mata biyu a duniya tun daga kan abinda ya gani akan Daddy dinsu ya kudurce a ransa ko baya son mace ko wanne Hali gareta matukar ya aureta to ita kadai zai zauna da ita ba kishiya sabo da yaransa,Kar a samu matsala,Shi Kuma Khadija za a bashi yarinya karama me ta iya idan Banda wasan Yara,ko girkin ma kawai dai Dan ta Dan iya ne da Tsafta,Abokansa suka yanyamesa Ana Ashe da biyu dazu suka dinga pics suna soyewa Ashe munafunci ne abin Amma ba a buga Iv da Khadija ba, tuni masu kaunarsa sai Murna ake tayashi Mata biyu lokaci guda,Haka su Daddy ma dasu Baba Ana ta murna tare da Baban Humaira baiji komai ba sai Murna yake ya aurar da Humaira ya Huta da halayenta na banza duk da Yana sonta sune silar lalata Mata tarbiya Amma yaji dadi ya aurar da ita,Humaira da Mamanta tare da dangi tunda Suka ji su biyu aka aura sai suka Fara balai an yaudaresu wlh da hakane baza su bada yarsu ba,an tona musu asiri,An Basu kunya kamar Humaira za a hada da kishiya,Nan fa aka dauka Ana ta cacar Baki su Humaira harda Ihun kuka da zazzabi,Uwarta ma Haka sai kuka tana Mami ta cucemu. Afrah ta fashe da kuka data tabbatar Khadija agola ake nufi sai ta makowa Mami waya Wanda Basu San ma me akeyi ba,Mami tace Hello Afrah an daura tana murna,Kukan Afrah taji tana Bata labari a Nan take Mami ta sume aka kwasheta sai asibiti,Maman Khadija kuwa dama ta sani da ita akayi Shawara Da Daddy da Baba tare Suka yi Shawara. Gida tuni ya dauka kafin kace me zance yaje ko ina,Khadija Bata San me akeyi ba suna ta uban Wasa da Abu a bed room,ganin masifa ta barke a gidan Madam Ngozi sai zaga Palo take tana ewooo....Yarinya Karami Khadija aka yiwa aure heeeeeey Hausa people woooo ahhhh...Mama Abinci ta kaiwa su Khadija tace zata kulle su da key Kar su yarda ko motsi suyi fada akeyi a gidan,Khadija Bata San me ba taga har ruwa duk an kawo musu mama tasa Key an kullesu a daki su kadai,duk Basu San me akeyi ba,Yan Daurin aure na dawowa bala'i ya balle a gidan Mata garin habaici Suka Fara kokawa da dukan juna wannan Mata da danginta waccan ma Haka aka fara da fashe fashe har da masu dauko ludayin Miya,wasu an fasa musu Kai,wasu fuska da hanci etc,Afra ta makure Nana firdausi Yar Hafsatu budurwa suna ta kokawa,maza Sunyi Sunyi a raba fadan yaki,sai da Daddy ya Kira Yan Sanda yace duk su kwashe Masa su sannan aka samu lfy akayi solving case kowa na Jin haushin kowa Daddy yace duk wacce ta Kara magana akan auren Khadija da Abdallah Bai yafe ba,Haka aka ci gaba da biki. Sai ga Mami ta tashi an dawo da ita daga asibiti tana shugowa ta Fadi a tsakar gidan ta Fara gunjin kuka tana tsinene,Allah ya tsine maka Alhaji Karami Kai ka auro Mana su,shege tsinanne,an aurawa Dana Talauci,za a shafa Mana talauci,wayyo..wayy....yoiiiii ta daura hannu a kanta ihu take Wanda har makwafta suka zo,bacin Rai kamar zai kashe Daddy,Abdallah,Baba,mami ta Gama tona musu asiri an cika gidansu,Mami Bata hakura ba Ta samu Kayan Dj ta farfasasu kamar ta haukace,Daddy yace Kar Wanda ya kulata,har gaji Dan kanta ta Gama,tace In kin Isa Mama ke da yarki ku fito wlh sai na kashe ku,in yaso na Mutu a prison. Abdallah wurin Daddy ya koma yace Daddy saki Mami Dan Allah,Daddy yace Sam Sam abinda ta shuka a sannu zata girbi abinta Abdallah Nan Ya Masa Nasiha akan rike matansa da adalci. Securities ne Suka Kori Yan kallo da kowa gida ya koma tsitttt kamar anyi mutuwa,abin arziki ya Zama tsiya,Mami wani tunani Tayi danginta Suka zazzageta akan abinda tayi tare da Bata shawarar banza,Wata da suke ce Mata yashuwa tace ke banza ce ai yanzu ba Haka akeyi ba ai an waye,kawo kunnenki kiji....sai suka kwashe da dariya sannan Mama tayi wanka ta cakare ta biya masu DJ Kayansu ta dakko wasu masu DJ din gida Kuma ganin komai ya lafa aka ci gaba da shagali musamman da kida ya fara tashi a gidan,Daddy da Abdallah kawai Murmushi sukayi Baba yasha tsinuwa wurin Dangin Mami,Amma yaga zasuyi kida yace kai da wata a kasa. Khadija tana bacci duk Bata San me akeyi ba ita da Abu,kidane ya tashesu sukayi wanka Khadija ta sake shiri cikin lace light blue. Mama ta budesu tace kuzo kuje ku cashe Kuma,ke Khadija Zaki ji Ana cewa kema matar Abdallah ce karya sukeyi karki kulasu kuyi bikinku kawai. Khadija tace to dama Ni Ina ruwana iyakaci idan an kawo Amarya naje na mata dukan tsiya Abdallah Zan ramawa. AsmaBaffa [12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: TUBABBIYA 16-20 Official AsmaBaffa Wannan page naku ne masu Sharhi. MAMAN KHALIFA,MAMAN AFFAN,OUM AMATULLAH,HAUWERH ZD,MMN BASMA, HAUWA IBRAHIM YARO,MAMAN SADEEQ,JEEDDAH LUV,MAMAN FATEEMA,SILENT QUEEN,WACY BABY ,MRS A and KHADIJA ALAD. Lace din light blue ba karamin kyau yayi Mata ba fitted Gown ta fitar da surarta kasa ta baje,Madam Ngozi ta Mata Gogoro me shegen kyau,Abu ma cikin Atamfa Riga da skert sun Mata kyau kamar ba daga kauye ba,Merry da Ihsan sun canja Material me kyau Suma,Khadija sauri take taje wurin kida Bata San bala'in da akayi dazu a kanta ba,Abdallah yasha sabon wanka ya fito da Frnds nasa da yawansu,Khadija duk inda tayi sai taga Ana kallonta Ana nuna ta Ana gulmarta,Ango na zuwa wurin da Mami ta kirasu Wai Yazo suyi musu liki yanzu za a kawo Amarya Humaira gidan, gobe sabon shagali za ayi sannan a Kai Amarya Humaira,Khadija dama tuntuni tasan duk kalar kayan Ango da zaisa shi yasa duk kalar tasa Baba ya dinka Mata,sai dai Bata san yanzu zai sa kalar kayan taba sai suka sake yin anko ita lace shi wani arnen Yardi light blue,kowa daya gansu sai da yayi zargin dama can suna sani sukayi hakan har Mami,Data kalli Khadija sai data ji kamar ta hadiyi zuciya ta mutu,dannewa tayi kawai da kyar sabo da shawarar danginta. Abu ganin su Mami na filin rawa tace bamu da kudin liki ki tambayi Mana Abdallah naki Mana,Abdallah Kuma tuna Maganar Daddynsa da Khadija da tace yayi tunani wannan sirrinsu ne sai ya bashi tabbacin Khadijan ce tasa Daddya ya aura Masa ita,sai yaji haushinta yaji tsanarta zata jawo Masa auren Mata biyu,Khadija Allah sarki Bata San komai ba Merry Ce kadai ta sani Amma Mama tace karta fadawa Khadijan. Khadija ta kutsa ta cikin abokan Ango Suka Bata waje sanin Amaryace da kanta,Kusa da Abdallah ta tsaya da karfi tace pls Bro kudin liki Dan Allah ka bamu muyiwa Mami,Hararar da Bai taba Mata ba ya watsa Mata ba shiri ta ja baya,Dr Hassan Yana kallo sai ya mikawa Khadija Yan 1k bundle guda,tace Sunyi yawa fa Dr niba Amarya ba zanyi liki Haka a banza ka Bari sai bikina Nima yazo,Karaf kunnen Abdallah,Dr ma yayi mamaki da Bata sani ba,sai ya bigi cikinta yace kina Ina duk auren da aka daura Miki yau,Dariya tayi tace nifa Mama a daki ta kulleni da key bacci Nasha da kawata ban San Ma anyi komi ba sai kida naji shine muka fito rawa. Dr yace Allah sarki to ki bawa kawar Taki Mana gata itama Kyakyawa Haka,Abu harda Jin kunya an yabeta, Abdallah ya tabbatar Khadija Bata sani ba Kam gaskiya tunda har yaga ta iya rabar kusa dasu Mami tana musu yayyafin kudi,Sai harararta sukeyi,Afrah kuwa da kawayenta da Suka shiga Nan ma Khadija ta Fara musu liki sai Afrah ta take Mata kafa da takalmi me tsini sai da tayi Hawaye ba shiri ta fita daga filin,ta Dade a tsugune sannan Dan maita irin ta Khadija ta koma filin Nan tace a samusu Kida ita da Merry da Abu yau farin ciki zasu nunawa Abdallah,Merry kawai kallon Khadija take da tausayawa. Aka saki Sauti Khadija ta fara rawar bajinta Wanda gaba daya aka koma kallonta domin ta birge kowa ka rantse sai da tayi training,Ana ta ganinta a Amarya marar kunya ita Kuma Bata San komai ba,Duk Wanda zai Mata liki sai Mami ta Hana matasa naso har wasu Matan Amma Mami ta Hana,Abu ta shige ta dinga zuba Yan dubun da Dr Hussain ya sake Bata,Abdallah ya mikawa Merry kudin a boye taje itama wasu Matan da mazan suka rufeta da liki,Ana Haka sai ko akace Ga Amarya Uwar gida Humaira ta iso,zo kuga Murna wurin Mami tare da Danginta,Kowa yasan Amarya ta hadu ga kyau Amma da ka kalli Khadija kasan ta zarta a komai. Kawayen Amarya da Yan uwanta sai yatsine yatsine suke an tsaya da kida Ana ta nuna musu Khadija ta fito zasu fita daga gidan ita da Abu Wai yawo zasu je ita Bata San tana da aure ba,tuni
Chapter 15 · 0% Book details