← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 53

Sashe 20

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AsmaBaffa [12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: TUBABBIYA 26-30 Official AsmaBaffa KHADIJA MUKTHAR, HAFSAH,HAFSY and HAJIYA ABOU. Page nakune. Washe gari anyi sadakar Bakwai yayin da kowa ya watse sai iya Yan gidan,Abdallah,Usman,Sagir tare da Baba sune ke hada Kan dukiyar marayu kaf Ana tattara komai sabo da tarin dukiyar Daddy sai dai Alkali da kansa ya raba tafi karfin rabon Yan fake fake,ga Yara jimgim a kanta, Hafsatu matar Baba ta fada wajen malamanta ganinta Abdallah ne akan komai na dukiyar Bata San Shirme take ba,sabo da gulmar da Yan gidan keyi akan gado yasa Baba yace a fitarwa kowa hakkinsa da wuri a huta tunda Allah yasa Daddy ba a binsa bashi,su Rahmatu da Suka hade kansu sunga abin ya wuce tunaninsu baza su Samu damar cutar ba,sai sukayi fada ko wacce tace daga ita sai yaranta,Mama dasu Khadija sai kallon ikon Allah suke suna mamaki gaba daya ba wadatar zuci,son duniya ya rufewa iyalan Daddy ido. Humaira taga Shuru har yanzu su Khadija Basu dawo ba suna family house har an kwashe 2wks Abdallah Bai ce ta koma ba itama Khadija Bata nemi ta koma ba sabo da ko ganinsa Bata yi kullum suna fita Kan harkar Gado. Yau da safe Khadija ta shiga bangaren Mami zata gaida ta,Ko amsawa Mami Bata yi ba sai ma cewa tayi ke Dan Uwarki tashi ki barmin part bana son gaisuwar ko Dole ne shegu Tubabbun banza agololi wlh sai kun barmana gida tunda bana ubanku bane,Ai za a raba gado wlh sai dai Uwarki su San iinda zasu koma gida na magada ne Wanda ya Baku damar Zama a gidan ya mutu sai muga inda zaku zauna,Afrah ta amshe da shegu matsafa munfi karfinku wlh abinda kuka yiwa Abdallah yake kulaki mu Baku Isa ba. Khadija ta zaro Ido tare da furta Allah baka hakuri ta mike ta bar musu part din kamar zatayi kuka,a Hanya taci Karo da Abdallah ranta a bace ta wuce Bata ko kalleshi ba,da sauri ya riko Hannunta tare da jawota gabansa,Kanta a kasa Taki ko kallonsa yatsansa yasa tare da dago habarta ta kalleshi idonta cike taf da hawaye lfy? Ya furta dama kadan take jira sai ta fashe da kuka tare da fadawa jikinsa,Tsigar jikinsa ce ta tashi yarrrrrr da kyar yace me akayi Miki? Mami ce? Kai ta daga Masa tana shesheka tace zagina Yana Yi Wai na miki asiri kana so na,yaushe kace kana Sona Dan Allah? Abdallah ya danyi Murmushi kadan yace bance ba Kam,Khadija tace to ka fada Mata pls baka Sona,Harara ya Mata kadan ya goge Mata hawayen sannan yace jeki shirya Driver ya maidaki gida Kinga kin huta da Mami ko? Murmushi tayi tace to yaushe Kai zaka dawo? Anjima da dare,Ok tace da murna ta wuce da gudu. Khadija tana shiryawa tayiwa su Mama sallama sai gida,Humaira tana ganinta tace Alhmdllh,Saida ta Bari Khadija ta Gama gyara part dinta neat ta Shiga wanka sannan ta lallaba tare da Barbada maganinta kasan pilonta ta fito tana murna. Khadija ta shirya abinci taci ta koshi tana jiran taga dawowar Abdallah Amma Shuru,a Palo bacci ya kwasheta har gari ya waye ko bedroom Bata shiga ba,Hakan baiwa Humaira Dadi ba Amma Haka ta Kuma lallabawa bayan Khadija ta gyara bed ta barbada Mata again lokacin tana kitchen. Hafsatu ta karbo itama nata Maganin Na Bokanta,Suma sauran matayen sun zage wurin neman Mafita,Mami muguntarta kawai take hadawa akan Baba Dole ya kwashe iyalansa ya bar musu gidansu na gado. Yau da safe aka Tara kowa Alkali ya raba gado Babu zalunci,yanda yayi rabo kowa ya g amsu tare da shedu Yan uwan Daddy da lauyoyi tare da Yan Uwan matayensu,an fitar da komai duk hadamar mutum Dole ya hakura da yanda aka raba sabo da ba zalunci,Mami ce kadai take Jan tsaki ita Wai an cuceta tana habaici,Baba dama ya Gama shirinsa zai bar musu gidansu ya koma nasa Wanda Daddy ya bashi na Kaduna kusa da Family House nasu Unguwa Daya suke,Mami da sauran Mata suka dinga bakin ciki cewar ai Baba zalunci yayi a cikin gadonsu ya sata,Mama taji dadin barin gidan zasu huta da Jarabar gidan,Hafsatu kuwa tafi so a zauna ayi ta kwasar bala'i,,Abdallah kuka yayi sosai da wasu samarin ganin Mutuwa me tonon silili Baba ya bar gidansu da iyalansa,Baba motocinsa biyu masu kyau Abdallah ya Kara Masa guda dalleliyar gaske ba tare da kowa ya sani ba. Kowa Dukiyarsa an damka Masa Yara da Mata Kuma an bawa yayyensu manya wasu Kuma iyayensu sun karba,Mami kaf ta tattara na Abdallah Dana sauran yaranta ta karba Wai ita zata ajiye musu,Kowa yayi mamaki duk girman Abdallah Wanda ko dukiyar Daddy ma shike juyata kaf Amma Wai zata ajiye Masa,Wanda Daddy ya bawa Baba a bawa Abdallah kawai Baba boyesu yayi Bai bawa Abdallah ba Yana tunanin sai Nan gaba idan sun samu nutsuwa. Bayan komai ya lafa Yara duk wasu sun Fara baragaza da kudadensu,Hafsatu takanas ta tafi gidan Abdallah Wai ziyara tajewa Humaira,Humaira tayi Mata wulakanci ta shige daki,dama Hafsatu abinda take so kenan ta samu ta lallaba sama part din Abdallah ta saci rigarsa jallabiya da takalminsa ta fito ta gudu gida, Ranar Kuma Abdallah ya dawo gidan shima,Khadija har an kwashe kwana biyar da dawowarta tuni ta kwanta Kan maganin da Humaira ta barbada Mata,Ganin Bata bar gidan ba Humaira ta Fara takaici tana zagin malamin ita kadai,Abdallah Yana wanka a part dinsa Allah Allah yake ya Gama yazo yaci abincin khadijansa me Dadi bai sani ba Khadija yau tun Sassafe data yi wanka ta shirya cikin Arabian Gown tayi kyau ta hada kayanta a katuwar Akwati tana Jin kamar Ana hura Mata wuta a gidan a gigice ta salale da akwatinta ta bar gidan gaba daya,Kuma Bata iya tuna kowa nata in Banda Abdallah sunansa kadai take iya tunawa kawai ta manta kowa da komai,ta manta wacece ita har sunanta Bata sani ba. Bayan Abdallah ya Gama wanka kamar sabon Ango ya fito Yana Murna ya nufi part din Khadija duban duniya Bata Nan,ba inda Bai dubaba na gidan Bata Nan,a gigice ya duba part dinsa ya fada dakin Humaira ta juyo a tsorace yace Ina Khadija,Humaira tace Ina ruwana Zan boye ta ne ko Ni na Aurota,tsaki yaja ya fita wurin masu Gadi Suka ce ai Hajiya karama ta Dade da barin gida tun safe,Mota ya shiga kawai Yana kallon hanya ya tafi Family house,gidan Baba,har gidan frnds ko Ina ya duba ba Khadija ba labarinta,Mami ma cewa tayi ta tafi karuwancinta,gida ya dawo idonsa jajir Yana hawaye ya wuce dakin Humaira dake waya da Zuly suna sheka dariyar murna harda Ihu,Yana shiga shi Yana zargin Humaira domin Khadijansa Bata nisa da gida ba tare da ya sani ba,Wuyan Humaira ya shaka Yana Ina Khadija,Wlh duk inda take ki fito min da ita kafin na kasheki,Humaira tana Kakarin mutuwa tace wlh ban San inda take ba,ban sani ba,Waya ya Fisgo ya fara Tafkawa Humaira Yana tsula Mata,kuka da ihu takeyi Amma taki fadan gaskiya,Mari Saida ya Mata yafi goma,Fuskarta tuni ta kumbura sumtum, Amma Humaira Taki fadan gaskiya dukanta yakeyi yasan wlh da Sa hannunta har sai da ya farfasa Mata ko Ina na jikinta masu gadi da Yan aiki suka shugo agaji yace wlh duk Wanda ya tako dakin Nan na koreshi daga aiki ba shiri suka juya Suka tafiyarsu dama Humaira ta Addabesu Bata da mutunci,Ganin baza ta fada Masa ba kawai sai ya dakko takarda da biro yace me kika yiwa Khadija ya furta da kakkausar murya,Humaira tace ban sani ba ya rubuta Mata na Sakeki saki daya ya cilla Mata takarda yace kafin 5mnt ki tattara ki barmin gidana,fuuu ya fita a mota ya fara neman Khadija lungu da sako,Mama da Baba ma sun bazama,Haka su Dr Hussain Amma ba a ganta ba,tuni Har an bada Sanarwa gidan radio da tv da gaggawa Amma ba labarin Khadija. Humaira kuwa Mami ta Kira a waya tana zunduma kuka ,sai ga Mami da Afrah a gidan taga harda takardar saki,ran Mami ya baci tace Alhmdllh tunda saki daya ya Miki Baki saku ba wlh,zaizo ya sameni tashi muje asibiti ki koma gabana da Zama wlh Dole sai ya zauna dake muje,Humaira tana murna ta lallaba Suka tafi asibiti akayi treating nata Suka dawo Family House Ana gulma labari ya watsu tuni a ko ina. Hafsatu sai Murna take taga Mama dasu Merry na kuka sun rasa inda zasu saka kansu,Su Madam Ngozi duk an tambayesu Basu ga Khadija ba,Abu kamar Wasa har an kwashe 3days Abdallah Yayi kukan fili Dana zuci,kamar zai mutu da bakin ciki,Addua yake ba dare ba Rana,Haka su Mama da Baba ma basa bacci. Mami ta nemeshi Amma yasan akan Humaira ne sai yaki zuwa,Hafsatu tana dawowa daga kauyensu ta samu da dare ta wuce can Bayan gari gidan Tururuwa ta Haka wani Rami ta binne layoyi sannan ta saki wata farar kaza akan gidan tururuwar tayi fuffuka ta fada daji da gudu sai da ta Gama ta dawo gida tace daga gidan Kawarta take. Kwana Uku tsakani Abdallah ma ya fito kenan zai tafi Office tare da neman Khadija sai yaji kansa ya Sara tunaninsa ya kauce kawai sai ya ajiye key din motar a kasa ya taka zuwa bedroom ya Hado kayansa a akwati shima ya fice a kafa ya fita daga gidan,me gadi sunyi tunanin lfy wani Abu zai dubo domin baiyi zaton Abdallah ba lfy yake ba ganin kullum a firgice yake tun bacewar Matarsa. Tunda Abdallah ya fita baibi hanyar titi ba sai dai yayi ta bin lungu da sako Yana garari har ya tsinki kansa a Tasha masu saka mutum a mota suka Fara murna passenger ya samu Suka karbi akwatinsa suna Alhaji Maiduguri zaka je? Drop kake so? Abdallah Yayi Shuru sukace Maiduguri zakaje ko Lagos? Abdallah yace Maiduguri ai kuwa suka ce Drop kake so kawai yace a'a, sai suka sashi a wata katuwar Bus a gidan gaba,Can anjima kafin mota ta tashi sai ga Khadija da Gudu ta shigo tashar da akwatinta futu futu da ita tana zuwa suka tambayeta Maiduguri Hajiya? Tace ae itama aka sa Kayansu a Boot suka sata a gidan gaba ita da Abdallanta,Babu Wanda ya gane Dan Uwansa kamar Baki,Khadija ta
Chapter 20 · 0% Book details