Sashe 49
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
duk ya tashi hankalinsa Kuma ta Hana aje Hospital Wai ita kalau take,Sai da tayi wanka ta kwanta sannan tace Dan Allah Baby Ina za a samo min Naman ganda shi kawai nake bukata,shi Zan iya ci,ai sai dai naje Wurin Mami itace kadai zata iya Nemo Mana, Abdallah da sauri ya sake tuka mota sai gidan Mami Family House bazai iya musu waya ba, zasu Bata Masa time Khad dinsa ta gaji da cewar sa, Mami suna tare dasu Rahmatu a palo suna hira sai ga Abdallah ya shigo hankali tashe kamar zai Fadi Mutuwa,Suna gaisawa yace Mami akwai Naman Kai a Gidan Nan? Khadija ce Bata da lfy take son ci Baki ganta ba Mami duk ta rame ya furta kamar zaiyi kuka,Mami ta kalleshi sai tayi dariya itama Rahmatu dariyar tayi. Sai Abdallah yaji haushinsu ya za ace mutum Bai da lfy su tsaya dariya,Mami ko har yanzu bakwa kaunar Khadijan tawa ne Wai? Ban gane ba nace Bata da Lafiya Kuna dariya,Kai sarkin me Khadija mu kaf gidan Nan ba Naman Kai,jiya Omar ya kawo da yawa yaran gidan Nan Suka dafe shi Muka ci,Bari na aiki me cefane taje ta siyo yanzu sai nayi Mata cewar Rahmatu, Mami tace ke Kika kulashi ma duk yabi sai fada yake mana. Zama yayi kawai tare da yin shuru Kamar me Nakuda ya rasa inda zai sa kansa sai faman Kiran Khadija yake a waya Yana tambaya ya jikin naki My Khad, hope Baki Kara Amai ba? Yanzu Ina ne yake Miki ciwo? Ita Kuma Gogar tana ta Shagwaba tana Ni Naman Kai kawai nake son ci yanzu bana Jin ciwon komai,Yanzu za a dafa na kawo Miki kiyi hakuri kinji yanzu Mami zata Yi, ok thanks kace Ina gaida Mami dasu Umma cewar Khadija,Zasu ji Inshaallah. Saida ya Gama wayarsa Mami kawai ta zuba Masa Ido tana kallon ikon Allah, Mami Wai Mene sai kallo na kikeyi? Abdallah manya Wai yau Abdallah ne yake Haka akan mace ka manta abinda ka dinga cewa Kai ba macen data Isa ta saka ko ta hanaka? Nace karya ne Amma ka dinga cika Mana Baki kana Mana kurin banza a gidan nan,me Class,me Hankali ba wacce ta Isa to yau gashi,duk ka kasa sukuni kamar Kaine marar lafiyar,An gaishe da Dije ta Ciri tuta, Dariya yayi yace to Mami na canja ra'ayi yanzu na dawo sai abinda Matata tace ai shike Nan ko na janye, Dariya Mami tayi tace to dama ai aikin Gama ya Gama,ka Kaita asibiti bazai wuce ciki ba Mami ta Furta tana Murna Zata Yi jika. Shima Abdallah Dadi yaji yace Mami Allah ciki ne da ita? Kai Ni ka isheni da rashin kunya ka tashi ka bani waje,Mikewa yayi tare da cewa Bari naje Wurin Umma ko ta Gama dafadawa, part din Rahmatu ya koma ya zauna har sai da aka Gama dafa Masa me Dadi ya dauka a flask ya tafi gida. Khadija shi take ta jira dama yana kawowa ta karba ta bude tana Jin Dadi Yana gefenta Yana kallonta ta dinga ci da sauri da sauri tana lumshe Ido sai da taci da matukar yawa sannan ta boye sauran da dare zata cinye abinta, sai gata ta koma Normal har girki tayiwa Abdallah tare da Kara gyara gidan sannan tayi wanka taci kwalliya shima Haka sannan yaci abincinsa Sukayi sallar Azahar Suka kwanta baccin Rana,Abdallah dai ansha bacci sai 4pm suka farka kusan a tare suna kallon juna da sha'awa, Khadija ce Fara Murzashi suna kissing din juna,shima Yana lugwigwitata Basu San sanda Suka raba kansu da kayan jikinsu ba daga Nan Kuma Majalisi ya karbi bakuncin Jaruma tare da Yi Mata kyakyawar sauka ta Alfarma. Bayan sati biyu Khadija kullum cikin cin Naman Kai take,ko Mami ta dafa ko kishiyoyinta ko kuma Mama,sunje asibiti an Basu result cike ne Dan wata biyu, murna kamar Abdallah zai Suma Haka ma Khadija dasu Mami,Abu tuni Usman yace Kar a Kara ce Mata Abu Zainab za Ana kiranta dashi yanzu Abu tuni ta koma Zainab,ta Kara wayewa da gogewa,tayi kiba da kyau,Su Firdausi ma ana can Ana Shan Amarci,Omar ma haka Ana zaune lfy da Jin dadi, Merry da Angonta Dr Hussain Suma. yanzu da Omar da Usman a karkashin Abdallaj suke aiki suna famtamawa,Mami da Kishiyoyinta sai abinda suke so tare da sauran kannai,ga Baba na kula dasu Nan ba wata matsala, Haka rayuwa taci gaba da ja cikin Jin Dadi har cikin Khadija Ya cika wata Bakwai,lokacin Abu dasu Firdausi duk suna da yaron ciki. Khadija Zama da kyar tashi da kyar Amma tana kokarin yin komai da zuwa schl etc,Naman Kai kullum tana ci,Dr Hussain da Amarya Merry Ana can Ana ta Amarci Suma Amma Merry Bata samu ciki ba,Husna ma ta samu miji wani matashi Dan gidan Minister Mahmud kenan, wasu ma a kannen su Abdallah Mata da maza sun fitar da Wanda zasu aura ciki harda Afrah zata auri dan gidan Mariya matar Alhaji Shehu wato Salman, da kyar Mami ta yarda Wai ita baza ta sake hada jini da Shehu ba,sai Baba da Abdallah Suka sa Baki sabo da yaron kirki ne na Gari Kuma. Cikin Khadija ya cika wata tara Mami tace ya kawo Mata Khadija gabanta Kar Haihuwa tazo ba kowa,Abdallah yaki yarda ba yanda ba ayi ba yace shi ya dauki hutun aiki ya daina zuwa Office Sai ta Haihu. Kullum Abdallah Yana gida Yana kula da Khadijansa sai abinda takeso, da kyar take tafiya komai shi yake Mata,Abdallah yau Baba ya aikesu da Sassafe karbar kayan dakin su Afrah da aka turo daga Dubai,da wuri ya lallaba Khadija suka fita shi da Omar. Yana tafiya Bai Dade ba Khadija ta Fara Nakuda,gashi ba uban kowa a gidan,Yan aikin ma duk basa Nan an Basu Hutu sun tafi ganin iyali sati biyu sai sun dawo,Khadija tana ta daurewa ita daya kwal a gida, ta dakko wata katuwar Leda me Kama data Cikin buhun sugar,dama Abdallah ne ya kawota Wai idan zata haihu shine zai karbi Haihuwa,Ai ko ta dakko ta Shimfida abar tayi tumbur ta kwanta a Kai harda tale kafafu Wai ita zata haihu da kanta ta bawa kowa mamaki. Ciwo da yayi yawa sai ta mike daga saman Leda ta Fara zirga zirga,ta yaye ledar ma ta jefar,daga Nan Daya Dan lafa Sai ta dakko ledarta ta sake shimfidawa ta kwanta tare da tale kafafu tana Addua kizo maza Haihuwa cewar Khadija tana ta fada Haihuwa kizo,. Ciwo yana dawowa wannan karon da karfi ya taho sai ta fashe da kuka ta Fara lalubar wayarta zata Kira Abdallah,Waya tana can tsakiyar bed,gashi ta kasa tashi, can Nishi me karfi yazo Mata Wanda Bata shirya ba,sai ga Kan jariri ya Fara yowa waje,Khadija ta barke da kuka zata mutu ita kadai a gida Bata San ya ake Haihuwa ba,ihu takeyi Jin karfinta sabo da azaba ko Makwafta zasu ji a ceceta Ina ba Wanda yaji Allah ya taimaketa ihunta da take dagewa tayi da ya Fado Namiji Kato dama Sunyi scanning tun i, har mabiya ta Fado du lokaci guda Amma ba kowa Bata iya yanke cibi ba,ba karfi a jikinta ko kadan sai da ta Dan huta ta mika hannu da kyar ta iya jawo wayarta tana kwance a kasa wanwar tumbir da ita yaro Yana ta tsala kuka.. Number Abdallah duk Taki shiga ba network,ta Kira Mama ba a dauka ba,Mami ta Kira yafi sau nawa itama ba a dauka ba,Hawaye ya zubowa Khadija ta rasa ma wa zata Kira sai ta Kira Baba tasan maza basa Wasa da wayarsu, Aiko bugu Daya ya dauka yace Khadija ya gida? Baba na Haihu Ni kadai a gida ba kowa jaririn Nan zai mutu jininsa ya tsotse ba a yanke cibi ba kaji shi Yana ta kuka baka ganshi ba Kyakyawa dashi, Baba yace tototo da sauri ya katse wayar ya Kira Rahmatu yace suyi sauri suje Gidan Abdallah Khadija ta haihu ba kowa a gidan. Rahmatu da Bilkisu sune Suka tafi gidan,dama Bilkisu Nurse ce tana aiki a asibiti yanzu,tunda Daddy ya rasu ta karkade result dinta ta koma aiki a asibiti, Mami harda bige kafa garin sakkowa daga bene taji an haihu ba kowa sai fada takeyi Ina Abdallah Yayi ya bar yarinya ita daya zata mutu a gida. Minti kadan su Bilkisu suka karaso abin ya Basu dariya ganin Khadija tumbur a kwance saman Leda,Rahmatu tace kaga Mata masu Haihuwa da jarumta,Nan danan ta nuna musu inda komai na Haihuwa da Suka tanada yake aka yankewa yaro cibi tare da goge Masa jikinsa da Zaitun sannan,Rahmatu tace Allah ya kiyaye Bata wani zub da jini da yawa ba,Bari a Kara rage na marar,Rahmatu ta dinga matse marar Khadija tana jijjigata sai da ta fitar da jinin Nan tas sabo da idan Ana barinsa Yana sa mace ta Dade tana jinin biki da Ciwon ciki,Toilet kawai Suka kaita Suka nade ledar Suka Kai toilet tare da flowshing komai,ba abinda ta Bata ko digo,Rahmatu ta tattara komai tasa a bakar Leda ta daure ta fitar, sai da sukayi duk abin da ya dace,Wurin gashi aka Sha kukan Khadija Kamar za a yankata haka ta dinga kukan zafi, sai da Suka Gama komai duk da dakin Khadija Bai baci ba sai da Suka Kara gyarashi kyal kyal ko Ina ya dau kamshi,Bilkisu ta duba taga Khadija Bata samu Kari ba ko kadan Bata bukatar dinki,Allurai tayi Mata na Karin lafiya da kuzari,sannan ta koma Hospital ta dakko HBv Vaccine tayi Masa, Rahmatu tasa aka kawo lafiyayyen Abinci daga gida Khadija taci ta koshi sai bacci,Jarrin suka yiwa wanka aka gasashi sosai sannan Bilkisu ta Tafi ta bar Rahmatu tana Kula da Khadija,Kafin kace me an cika gidan dam Yan barka har makwafta Ana tururuwa,Khadija tana baccinta Rahmatu ta Hana a tasheta,Mami ma tazo,su Abu kaf dangi da abokan arziki,Abdallah wayarsa Bata Shiga an gaji da nemansa. Rahmatu ce zata zauna tare da Khadija har tayi Arba'in,sai da yamma Khadija ta sake wanka wanka bayan Rahmatu ta gasata sosai tana ta kuka Wai zafi,Har ta shirya tayi kwalliya tasa Riga da skert na Atamfa kamar ba ita ta haihu ba tana zuba Kamshi me dadin gaske, Har Lokacin kuka takeyi,Rahmatu tace kin Dade bakiyi kuka