Sashe 11
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da sauran masu ruwa da tsaki. Ran Mami ya baci matuka,Hafsatu matar Baba sabo da faccalanci sai gata ta suro katuwar jarkar Man gyda Wanda ya Kare a kitchen ta fito tsakar gida fili kamar zararriya da ludayi guda biyu na juya Miya ta Fara kida dam...daram... dam...Dam...dam..kaf...kaf...dum...Dum...ita Kuma kishiyar Mami Amaryar ta fito tana guda Ayyiriri mijin tubabbiya, anan aka Kare,Ina me kudin yau? Yaran kishiyoyi Dana Hafsatu Matan Suka fito suna habaici har da masu dakko farantai manya na silver da cokula suna kida ba ji ba gani,Mami tayi tagumi a daki,Afrah Suka yi mukus a daki,Abdallah ta samansa window ya leko yaga duk abinda sukeyi,yasan Mami yanzu zata zo sai ya sakko yabi ta baya ya figi mota tare da barin gidan Baki daya. Khadija Koda ta gane me suke nufi suna kida ita kanta jikinta rawa ya fara tana tsoron Mami,ga Daddy baya gari,ba Mama da Baba da sauran Yan uwanta,Khadija ta sama ta hango Mami ta fito a fusace tare da fadawa part din Abdallah,ganin baya ciki tasan ya Gudu sai ta nufi part din su Khadija tare da Securies guda biyu tace ku samu kuci uban yarinyar Nan,kuyi Mata mugun duka,Khadija taga Mami ta Mika musu keys da yawa tace idan kofa Bata bude ba ku balla min kofofin Baki daya. Kowa a gidan tsoron Mami Yake ji don Haka masu kida nayi yaran gidan Sunyi mukus,Khadija da Gudu ta sakko tare da fita itama ta kofar baya data bi ta kitchen,a hankali ta lallaba dare ma yayi Amma Haka Daga ita sai short Wando pink da T-shirt Fara bako dankwali ta fito a hankali har ta bi ta dayan gate din na karshe Wanda baza a ganta ba,me gadi na bangaren suna ganinta Basu san me ya faru ba Suka bude Mata kofa ta fice da Gudu tana dariya ko tsayawa batayi ba Titin layin tabi tana tafiya a hankali har tayi nisa da gidan,Hadaddiyar motace ta tsaya a gabanta kadan Baya ya dawo me motar tare da sauke Glass na saitin Khadija,Tana kallo sai taga Ashe Abdallah ne,da sauri ta balle murfin motar ta shige gaba,ya figi motar Suka bar unguwar Baki daya. Mami kuwa suna murda Handle Suka ji kofofi a bude,ta shiga Palo tana zunduma ashar iri iri Amma Suka ji shuru,ko Ina Suka duba shuru ranta ya Kara baci Dole ta hakura ta koma part dinta tana saka irin yanda zata ci uban Khadija da Abdallah kawai. Kida ya saki a motar Khadija harda ihu yessoooo tana Daga hannu sama tana rawa a motar a zaune,Dariya ma take bawa Abdallah ba dama taji kida sai rawa,wani mall tsaya tare da shiga ya siyo Mata katon Hijab har kasa me Hannu Arsh color tare dasu Ice cream da kayan ciye ciye masu Dadi na Yan gayu,Hijab din ta karba tare da cewa tnx,Bai ko kalleta ba ya daura Mata ledar kayan tande tande a cinyarta,Hijab din tasa ya Mata Masifar kyau,ba jira ta bude Ice cream dinta ta shiga shatare da kilishi me Dadin gaske,Da kyar take magana sabo da Dadi,Yago kilishin Naman tayi tare da bashi a Baki gashi tunda Driving kakeyi,ba musu ya bude bakin ta saka Masa Yana ci,Ice cream din ma a Haka take bashi Yana tuki ko Ina zai kaisu oho,Hannunta ne ya goce icecream din ya Bata Masa gefen lips kadan,Yatsanta me laushi tasa a saman lips dinsa masu matukar kyau da laushi,Wani shock Suka ji Baki dayansu. Goge Masa tayi tana tambaya Ina zamuje ne haka? Bai kulata ba sai da Suka je wani Hadadden waje da ake zuwa hutawa da dare cinema ce iri iri,a Nan yayi parking Suka fito ya biya musu Cinema wani Comedy American Film Suka shiga tana rike da ledarsu ta kayan ci, Popcorn ya sake siya musu cikin katon bowl me kyau. Zama sukayi an fara haska film din. A zahiri tunani yake yanda zai bullowa Mami da matsalarta,Khadija kuwa tama manta da wata Mami Kallonta takeyi hankali kwance tana ciye ciyenta kallonta yayi lokacin itama ta juyo Ido suka hada da sauri ta janye idonta a kansa domin kwar jini yake Mata ga kamshinsa me rikita ta tare da kashe Mata duk wata laka ta jikinta. Hannu yasa da niyyar eban poprcorn din itama tasa zata eba hannunsu ya Hadu,wani zirrrr shock Suka ji gaba dayansu sanadin daya jawo Khadija ta rude tare da janye hannunta da sauri ko a jikinsa Abdallah ya ci abinsa suna Haka har Film ya Kare ya duba agogonsa 11pm dare yayi,Muje gida na gaji Abdallah ya furta Yana duba agogonsa dake daure a tsintsiyar hannunsa me kyau da tsada. Khadija tsoro ya kamata Mami tana jiranta kamar zatayi Kuka idonta cike da kwalla take kallonsa,Kallonta yayi taso bashi dariya Amma Bai ce komai ba ya shiga mota tare da jansu suka Fara tafiya,Hawaye ke diga saman Hijab din Khadija dis dis sai sheshekarta yaji kawai,Ba tare da ya kalleta ba yace ya kike so na Miki? Ina Zan kaiki? Khadija tana kuka tace Ni..Ni...dai..zata..duka Ni...ga Mama Basu nan..ok Dan na taimakeki shine Zaki ajiye min kuka Ina laifi ma Dana daukeki,da nasan Haka Zaki min bazan daukeki a mota ta ba,nasan Yanzu Mami tayi bacci ki bi ta daya gate din ki shiga part naku kina sani magana kaina ciwo yakeyi ga zazzabi nake ji Amma kin dameni da kukan banza. Khadija Hawayenta ta goge tayi Shuru tana ajiyar zuciya har suka Karasa gida ta daya gate do Suka Shiga,Mami tuni tayi bacci, lafiya Kowannensu ya shiga part dinsa. Tunda Abdallah ya koma Zazzabi me zafi ya rufeshi sosai Haka ya kwana nannade a bargo Yana rawar sanyi,jikinsa zafi zau,Mami kuwa ko da safe Bata saurari part dinsa ba tana fushi dashi,Haka Bata koma part din Khadija ba tace laifin Abdallah ne daya kulata har ya turata wurin manyan mutane Haka mutane masu daraja ai zaizo ya sameta. Sunday ne ba aiki Yana ta zazzabi har karfinsa ya kare Babu me taimaka Masa,ga ba abinci,Khadija Kuma tana son zuwa ta gyara Masa part dinsa tana tsoron Mami Don Kar tayi laifi sai ta wuce wurin Mami zuciyarta cike da tsoro. Tana Shiga Mami ta gasa Mata Harara har kasa ta durkusa tare da gaishe da Mami sannan ta Bata hakuri akan abinda tayi. Mikewa Mami tayi tace Dan Uwarki Ni saarkice da zanje har part dinku ki kasa bude min,Mami.....kafin tace komai Mami tal kwasheta da Mari tare da rufeta da duka,Afrah ta Miko waya doguwa Mami ta Zane Khadija da ita iya karfinta har yatsa ta fasa Mata jini na zuba,Karshe tace wlh wlh kinji na rantse Dana yafi karfinki aiki na saki Dan matsayinki kenan a gidan nan shegiya Arniya idan Kika Kara shiga safgar Dana saina kashe ki. Key da ta jefo Mata a fuska tashi kije ki gyara Masa part dinsa Kuma kina gamawa ki dawo Nan ki gyara min nawa Dan Ubanki. Tana kuka ta dauki Key din ta fito ta wuce part din Abdallah tana gyare gyarenta har ta Gama ko Ina saura dakinsa ta shiga,tunaninta bacci yakeyi ta wuce Toilet tana ta uban Kuka yasan Maminsa ce ma tayi mata wani abin Kuma ta sata aiki,Sai da ta Gama da toilet sannan ta fito taji Yana ta uban Nishi Yana rawar sanyi Kar..Kar..Kar, da Sauri ta koma ta sawa kofar key Wai Don Kar Mami ta shigo ta kamata tana kula Mata danta. Bed din ta koma tare da yaye blanket din Baki daya da sauri ta rumtse idonta domin daga shi Sai Short wondo surarsa me Jan hankali ta bayyana,Jikinsa ta taba zafi kamar wuta,E-wooooo ta furta da karfi,ur Body is too Hot Yaron Daddy,baki da Magani a Baki ki Sha? Wayarsa ya nuna Mata ta jawo da sauri,,da kyar yace Kira Doctor Hussa ain,Yasa tomprint nasa Haka ta jawo yatsansa tasa a wayar sannan ta bude ta lalubo Dr Hussain. Yana dagawa yace Shegen gari ya akayi? Khadija cikin gwarancinta tace lafiya Babu Abdallah ayi sauri a zo a dubashi shi mutuwa ta kusa zuwa Masa sosai ya kusa mutuwa Doctor ta Karasa tana fashewa da kuka,tace Doctor har kudin break yake bani kudin da yawa dubu dubu wooo idan ya mutu wa zai bani. Dariya ta Kama Hussain dama babban abokin Abdallah ne,Hussain yace ok gani nan zuwa ya datse Kiran tare da kwaso kayan aiki ya taho da sauri,Minti kadan ya Parker motarsa tare da wucewa part din Abdallah,Khadija ya iske ta zuba tagumi tana Hawaye me Bata kudin Break zai rasu. Hussain Yana dubashi yasan bazai wuce jinin Abdallah da yake Hawa ba ko ya ransa ya baci ko hayaniya sai jininsa ya hau kadan,Magani ya zube yace Jininsa ne ya hau kadan,dama Yana yin Haka Bai son bacin Rai ko Hayaniya,Khadija ta kwalla Kara Hawan jini Doctor Innalillahi lahhhhh na shiga Uku na Gama lalashewa Khadija ta Furta tana tafa hannu,Dr Hussain ya dinga dariya dama yasan Khadija tun bikin Baba,karki Damu Khadija Yana Shan magani zai warke Dan iskan yaron Nan baya Jin magana da kike ganin sa ki daina tausayinsa. Khadija tace lala ban Dan yiska bane baya yiskanci ko hannun mace Bata rikewa fa Doctor,to ebo min ruwa ba me sanyi can ba a Bowl na goge Masa jikinsa,Khadija ta ebo a toilet tare towel Karami,Duk abinda Sukeyi Abdallah na jinsu,Jeki kitchen dinsa ki dafa Masa abinci Bari na tasheshi yayi wanka ok. Da sauri Khadija ta shiga kitchen ta Masa lafiyayyen faten Irish potato yasha Kifi ta hada Masa fruit salad tana shigowa da tire ta iske Abdallah har yayi wanka da Sallah Yana zaune gefen bed sanye da farar jallabiya suna Hira da Doctor,Ashe Dr Khadija na fita ya Masa allurar da yake Masa nan take jinin ke sauka Zazzabin ya gudu,Bai son Khadija taga tsaraicin Abokinsa sabo da shi ya taimaka Masa yayi wanka. Tana shigowa Dr Hussain yace na tafi wurin Aiki Ni,Khadija farin ciki ya cika Mata zuciya da sauri ta ajiye tire a gabansa tare da Dora hannunta a saman goshinsa taji ba zafi tace Alhmdllhi mungodewa wooo ya Baki lfy Allah ya karo lfy da yawa da yawa fa. Abincin ta bude kamshin Dadi ya daki hancinsa plate din ta dauka tasa spoon tace ka huta Sir