Sashe 42
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadija sun Gama shiri wanka Suka dauka sosai Yasha wani yarda sea blue me laushi shara shara ita Kuma lace ne itama sea blue and Black sunsha kyau kamshi kawai Sukeyi ta ko Ina,Driver ne ya kaisu Airport Suka shiga jirgi sai Kd,suna Isa Driver na jiransu sai gidan Baba,Khadija Dadi da murna takeyi kamar zata Yi hauka, Family House Suka Fara zuwa kowa yayi mamakin ganin Khadija da Abdallah,tunanin kowa sai ya yafi akan Dama ba bacewa sukayi ba turai suka gudu karya ne,sai da suka gaisa da kowa sai suka koma Gidan Baba Hafsatu ta fito kenan tayi Ido Hudu da Abdallah Nan take sai ta Fara surutai ta haukace gaba Daya ta hanyar surutai da sambatu iri iri. Dariya Hafsatu ta kyakyace da ita tace yiiiiiiii nice na yiwa Abdallah asiri ya haukace ya bar gida,nice nayiwa Su Rahmatu asiri da yaranta su tsani Baba su daina son abin Hannunsa Yana Nan a cikin Gidan Daddy na binne jikin bishiyar Guava ,cikin dake jikina na asiri ne Haka Hafsatu ta dinga tonawa kanta asiri da irin tuggun data Kulla,Yaranta sai kuka sukeyi suna riketa Daga Nan ta fice tare da shiga Family House Nan ma ta dinga sambatu tana tonawa kanta asiri karshe sai ta Fara shiga makwafta gida gida tana tonawa kanta asiri sai Kuma ta shige cikin garin ta bazama duniya tana tsince tsince. Kowa ya cika da mamaki Ana sallallami da gulma,Baba kasa motsi yayi Harda Hawayen takaici,Mami kuka tayi,Sai yaran Hafsatu dake kuka cike da kunyar halin Uwarsu, asirin da Hafsatu ta furta ta binne Baba da kansa yaje family House ya tono shi aka lalata abin, Family meeting Baba ya Tara kowa da kowa a Family House su Rahmatu da yaransu Har Mami dake halin jinya,Abdallah da Khadija kowa Yana Nan Baba ya bude taro da Addua,sannan yace Alhmdllh kowa yaga abinda ya faru da Kuma yanda rayuwar family dinnan ta kasance Tun Dan Uwana Yana Raye,Abu me Dadi da marar dadi ya faru,ya kamata mu hadu mu gyara,Kunga abinda Hafsatu ta aikata ga yanda ta Kare,Haka Mami gashi yanda Kika dawo,kin manta da kowa Akan kin shiga daula ke Zaki wa Allah wayo kina gudun talauci,Abdallah da bakwa son rayuwarsu da Khadija sai gashi a halin cutar da suke ciki ta rashin tunani a Haka suka rayu tare har suka warke abinda Allah ya tsara ya rigada ya tsara. Baba sai da ya Basu labari komai Akan Mami da Kuma bacewar Khadija da Abdallah,sannan karshe yace ku Kuma su Rahmatu duk gadon da kuke gadara dashi gashi yau Yana Ina? Ko ba komai kunji a jikinku Kuma rashin bawa yaranku tarbiya ne ya jawo tun suna Yara sun Saba da kudi Basu san babu ba yau waye yaji jiki? kun taba tunanin zasu Kare? Ya kamata mu Kara nutsuwa musan inda rayuwarmu ta nufa mu dage mu nemi lahirarmu tayi kyau. Usman shine Babba yace Alhmdllh Baba mu mun gane gaskiya tuni,sannan Abdallah Muna tayaku murnar samun lafiya,hakika munyi farinciki,Kuma munga rayuwa munga Ishara Dole Baba da muke ganin ba komai bane yanzu bamu da gatan da ya wuceshi gashi duk mun samu aiki har Muna kokarin Nemo matayen aure Matan Kuma suna da mazajen da zasu aura Alhmdllh mu gaba daya da muke family House mun gane gaskiya Allah ya shirya mu,karshe Ina Kara bawa Baba hakuri da Kuma gode Masa akan abubuwan da yayi Mana,munyi Masa abubuwa Marasa Dadi Amma Bai kalli hakan ba ya kula damu Allah saka da gidan Aljanna,Ameen gaba Daya aka amsa. Rahmatu ce ta mike tace Dole mu godewa Allah mu godewa Baba domin munci kwal ubanmu mun karbi tafka iya tafka Amma hakan yayi sanadiyyar gane kuskurenmu Madalla da samun Mutum Dan uwa Managarcin kanin Miji irin Alhaji Qarami Baba Allah ya saka,Ameen aka amsa,Haule ma Amarya ta mike tace tofa bayin Allah Dole mu hada kanmu Baki daya mu Zama tsintsiya madaurinki Daya Yara su Zama na kowa ba gulmace gulmace da munafunci an Zama Daya,Mami Allah ya Baki lafiya dama kinfi kowa iya tsiya, Baba Allah dai ya biya,Murmushi akayi aka amsa da Ameen,Sai Bilkisu itama tace bani da bakin magana sai dai nace Allah ya saka da Alkhairi Allah ya hada kanmu ya bamu Zama lafiya da kaunar juna,Ameen aka amsa. Mami tana Dan ciwonta tace Gaskiyane Haule nafi kowa neman rigima a gidan Nan,Dan Allah kowa ya yafe min musamman Baba,Dana Abdallah da Khadija tare da Mamanta na kuntata muku ku yafe Ni Khadija tace ai tuni an wuce wajen Mami an yafi juna Baki daya Allah ya Baki lafiya kowa yace Ameen. Abdallah yace kowa ya yafewa kowa an daina fada ko wani kyashi da Hassada,Mama tace komi ya wuce Merry sukace Inshallah itama Hafsatu Allah ya Bata lafiya ta dawo gida a rufawa juna asiri yaran Hafsatu suna Hawaye Suka ce Ameen,Baba yace a'a ko ta warke na Riga na saketa saki daya ku shaida bazan Kara rayuwa da ita ba zuciyarta Babu Imani,kowa baiji dadin sakin ba sai Khadija kadai Wai akan ta sawa mijinta cuta sai tace Weldone Baba. An Gama taro Abdallah yace shi Abuja zai zauna da Matarsa Amma sai Nan gaba zasu koma ba yanzu ba sabo da aiki ma na Business dinsa can zai koma,Addua akayi kowa ya watse,Abdallah da Mami suna part din Mama dakin da aka bawa Mami suna Hira ta uwa da danta,Abdallah yace Mami wannan ciwonfa Haka ya kamata ayi Addua ayi na asibiti,Hmm Haka Babanku yace Bari dai mu gani,Ya matar taka? Na dauka Zan ganta da jikana ko ciki? Dariya Abdallah Yayi lokacin Afrah da Meenal sun shigo room din yace Sisters How far? Dariya sukayi suna Murna Yaya Wlh baka gani ba kayi kyau sosai matarka kamar wata Baturiya kunfi da kyau Yaya ku ci gaba kukayi, jikinsa Suka koma Suka makaleshi Meenal tace Mami Kinga Yaya yanda yake dariya ya daina wannan kuncin da fushi kullum,Mami tayi dariya Surukata ta gyara Masa Zama ya Zama Babba,dariya sukayi Baki daya,Afrah tana Yaya Bata da ciki Dan Allah? Rankwashi ya zuba Mata Ni sa'anki ne...Kara ta saki,Mami tace ya zaka Dakar min yarinya Dan ta tambayi gaskiya nima ai baka bani amsa ba,Mami Bata da ciki fa ya Furta a shagwabe,Dr Hussain ne yazo yaga abokinsa Nan fa murnar ganin juna Yana Gama duba Mami Suka koma part din Baba suna ta hira baji ba gani daga Nan ya bashi labarin soyayyarsu da Merry an kusa sa Rana tare za a hada dasu Usman,firdausi etc. Abdallah ya tayasu Murna shima harda bashi labarin yanda yake son Matarsa Khadija da kyawawan Halayenta,Dr sai tsokanarsa yakeyi Wai a dawo da Humaira Abdallah yace soon zan kamata wlh sai tayi prison dariya sukeyi sannan Suka tattauna Kan rashin lafiyar Mami da Kuma Me maganin Musulunci me Addua zai Fara zuwa gobe,sosai Abdallah yaji Dadi, bayan Dr ya bar gidan Baba ya sanar Masa Dukiyarsa tana Nan a hannunsa idan Mami taji sauki zai koma Office zai damka Masa,Abdallah harda Hawaye sabo da tunawa da Mahaifinsa Ashe har tanadi yayi Masa sabo da yana son Abdallah. 5pm kowa ya nutsu Abdallah ya dau wankan sugar cikin wata arniyar shadda Milk color kyan da yayi ba a magana kowa ya kalleshi sai ya Kara,Su Usman dasu Omar duk suna gidan Baba Ana harka Babu banbanci,Abdallah yazo cikinsu yace Usman wace Amaryar taka ne? Dariya yayi yace kaganni dai duk kyan Nan nawa na kasa samun ta aure wlh ko wacce shegiya naje sai tace tana da Mijin aure,wata Kuma ta yaudareni ta lashe min kudade na, Ni Kuma gani Allah ya yoni da kyauta, dariya sukayi Omar yace mu kuwa duk mun samu Banda shi Allah sarki ga kyau matashin tuzuru,Abdallah ya kalleshi Yana dariya shima sabo da Usman ba karya shima akwai kyau ga iya daukan wanka to ai Kaine ka Dade kana yaudarar Mata Dole ta aure ta garareka,to Dan iska Yi min Baki cewar Usman Yana zagin Abdallah,Abdallah yace to yanzu Ni nayi maka Mata in kana so ga Abu zainab kawar Khad Dita ka aureta wlh tana da halin kirki sannan Wife Dina zata ji Dadi Zan sata a farin ciki gata ga Kawarta. Usman ya tafi tunani yace wannan yarinyar me shegen iya magana wata Yar Fara Haka doguwa ko? Abdallah yace ita fa kasan tana da kyau Kuma da a birni suke Suka koma kauye ta waye in kana so Allah I'm seriouse a baka number ta ka nemi soyayyarta kwanan Nan Zata zo ma wurin Khad,Usman yace wannan yarinyar mitsila me Zan ji a jikinta, Allah yasa ma tana da kyau da Yar sura, Kai yaro ka kiyayi yaran Matan Nan wasu sunfi manyan Don na kiyayesu hhhhhh suka kwashe da dariya suna tafawa,Omar yace to fa mutumin Shi yaji me yaji kai Usman ka yarda kawai Allah baka Jin tunda Abdallah ya zauna zancen Khad Dita Khad Dita yake Mana,Abdallah yace Dalla tawa dai Mene wani Khad dinka, Usman yace Iyye na yarda kawai a bani number naji ya zamu Kare. Abu dama tana kiran Abdallah watarana ta gaisheshi ko tace ya hadata da kawarta Yana da number dinta sai ya bawa Usman sannan ya Kira Abu yace ga Dan uwansa Yana sonta su Fara magana zuwa Nan gaba idan Halinsa yayi Mata to shike Nan sai ta aureshi,Abu murna harda rawa a gidansu tana cashewa ta samu miji ai tunda Abdallah ne ya hada ta da mutumin tasan ya Hadu kawai zata aura sai rawa. Khadija kuwa tana can dasu Mama tare da kannenta suna ta zuba Hira sai da su Merry suka shiga kitchen sannan Khadija ta kebe daga ita sai Mama,Khadija tace Mama yanzu Haihuwa zakiyi? Ban gane ba Khadija a'a Kar na haihu? Karki Bata min Rai Khadija ke Har yau naga fa Alama kishin ubanku kike, a'a haba Mama ya zakice Haka? ok Mama I'm sorry,Mama Khadija ta kirata,Mama tace Yes Mene ne? Uhmm...ahm...ah...Mama Down Dina akwai ciwo Mama zafi me zanyi? Mama ta bude Baki tace bana koya Miki ba tun ranar da za a kaiki dakin Miji? Duk dadewar Nan sai yanzu kikayi first Night?Su Mama ba ruwansu su Zaman South yasa basu fiye kunyar juna ba, Khadija da kunya tace ae,ok Zaki warke ai