Sashe 10
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dasu carrot etc,Salat ta hada Masa daban ta shirya a Tire ta nufi Part dinsa yau anci sa'a tasa Hijab me Hannu Amma shima tsangalallene gaba daya da kadan ya Kai gwiwarta duk kaurinta a waje suke, a palonsa ta iske shi Yana kallon Ball ya rage kut sannan ya kunna kida me Masifar Dadi a speaker dinsa manya. A kwance yake saman 3seater idonsa a lumshe,tunanin Khadija Bacci yayi Bata San yunwa ce ta cikawa Abdallah ciki ba,a hankali ta ajiye tire a gefe tana tafiya Sadaf Sadaf kamar Barauniya,fuskarsa ta leka a hankali tafin Hannunta tasa a fuskarsa yanda bazai tashi ba,taji Shuru a fili tace bacci yake ma,Wakar ce ta Kare wata wakar ta shigo ta Yemi Alade Amma da yaren Igbo tayi wakar,Nan jikin Khadija ya fara rawa,kida ya cika Palon,Kara leka fuskarsa tayi ta tabbatar bacci yake,Bata San duk abinda takeyi Yana jinta Yana kallonta,Hijab dinta ta gyara ta fara rawar Igbo idan tayi kadan sai ta kalleshi taga Bai farka ba sai taci gaba,Motsi yayi tare da gyara Murya da sauri ta tsaya cak ta matsa kusa da abincin kamar gaske ta matsa kusa dashi tunaninta Bai ganta ba,tace ga abinci Yana bude Ido ta fice da sauri. Farin ciki ya lullubeshi Kuma ya Jinjinawa Khadija data iya gane Abinci yake nema,sabo da akan bikinsa Sunyi fada da Maminsa yau sabo da tace yaje zance wurin matar da zai Aura Humaira yaki zuwa. Abincin ya birgeshi ga shegen Dadi yaci ya koshi tare da Hamdala. Washe gari kuwa da yamma 5pm Abdallah Yana da Meeting ya Dace ya halacci meeting din Umarnin Daddy ne,Gashi Mami tace idan baije zance Kano ba wurin Humaira Babu shi ba ita,Wata dabara ce ta Fado Masa sabo da taron da turanci za ayi Gashi Kuma manyan masu kudi ne za ayi meeting din,Gidansu ga Samari nan da yan Mata Amma baka Isa kasa kaninka aiki ba sabo da iyayensu sun tarwatsa gidan,ba a zumunci,Babu ganin girman na gaba sannan kowa Bai Isa da kowa ba,Yan uwa sun tsani Yan uwansu tarbiyan iyayen ce, kishi ya Zama hauka da faccalanci har 'ya'yaye. Karfe hudu zai bi jirgi zuwa Kano Zance wajen Humaira,Khadija tana part dinsu ta dawo Daga schl tayi Shirin Islamiyya Abdallah ya tura Afrah ta Kira Masa ita,Samunsa tayi yasha uban wanka cikin Sea blue shadda azabar kyau dai ba a magana komai designers Khadija sai kallonsa takeyi,Wani kwali me shegen kyau ya Mika Mata,karba tayi sannan yace Gashi ki shirya cikin kayan Nan ki tabbatar kinyi kyau Driver zai kaiki Mountain Hotel za ayi Meeting bance kice komai ba kawai kece Kika wakilceni sannan duk abinda aka fada a taron ki tsaya kiji sosai idan Na dawo kizo ki fada min komai,Idan Zaki manta wani abun ki ruba a jotter,Tsoro ya Kama Khadija cikin manya zata je,Amma baza ta iya Masa musu ba tace Alright Ina zakaje Kai? Zance zanje zanga Amaryata wacce Zan aura nan da 3mnths Murmushi Khadija tayi tace she's lucky girl to have u as her Husband so Nice, Congrats zamuyi rawa wooo ranar Sai na cire Hips Dina a bikinka can't wait. Harara ya watsa Mata Yana daura agogonsa me tsada Diamond. Sallama tayi Masa ta wuce domin shiri,dagewa tayi sosai ta shirya cikin rantsatsiyar black and Golden color daya Bata a kwali harda Takalmi da jaka me Masifar kyau da tsada Golden da siririn mayafi,dake ta waye bata wani Sha wahalar shiri ba,Kwalliyace kawai batayi ba,Powder ta shafa sai lipgloss light pink duk da Haka ba karamin kyau tayi ba abinka da farar fata idan Kaga Khadija ka rantse Yar Gomna ce,ko da ta fito wajen driver ba Wanda yayi zaton itace har ta shiga mota Driver ya fita da ita tunanin kowa bakuwa ce. Har Katafaren Hotel din ya kaita Inda aka samu matsala kawai Bata da waya,Duk da Bata da tsoro taji a wannan lokacin,gabanta na faduwa ta shiga Hole din zagaye yake da masu kudi har da turawa fararen fata, sai da kowa ya taru sannan aka fara gabatar da Kai,Ana Zuwa Kan Khadija tace itace Wakiliyar Abdallah ya danyi tafiya ne,Mutanen wajen ne Suka tambaya ko Matarsa ce?Yes kawai Khadija tace tare da Basu amsa Fiance dinsa ce ita, Taro aka Fara Akan harkar ci gaban Kasuwancinsu da hadin gwiwar da zasu da turawan America,Jotter an ajiye kowa a table nasa Khadija ta dauka tana ta rubuta Abubuwa masu maana Dan kar ta manta,Haka duk abinda akace tana ji kamar zata Ari kunnen wasu,Bayan kowa yayi Magana Khadija ce ta karshe Dan kar ta bawa Abdallah kunya ace ta kasa ko tari,Haka ta daure gabanta na dukan Uku uku ta mike tare da dakewa cikin English Zallar Grammar ta Fara jawabinta itama,Yan Jarida da masu Hotuna suna tayi kamar me,Khadija Bayanai ta kawo masu Amfani sosai Wanda sai da turawan Suka jinjina Mata,ba wani bayani me tsayi tayi ba ta zauna abinta,bayan an Gama aka ci aka Sha sannan taro ya tashi,Driver na mota Yana jiranta ta fito tana Jin Dadi sannan tana jan ajiyar zuciya Bata ji kunya ba,Tana komawa Gida ta cire kayan da taje dasu ta wanke ta shanyasu. Abdallah tunda ya sauka a airport din Kano yake Jin Masifar kunci,Drivern su Humaira da zai aura shi ya daukeshi a Airport zuwa katafaren gidansu dake GRA,gidane na Alfarma Amma Abdallah yasan nasu gidan ya linka nasu Humaira sau dubu,Babban Palo aka kaishi yaji kayan Alatu na more rayuwa,kafin kace me an cika Masa gabansa da kayan ciye ciye,Yana zaune Yana Izza da mulki Maman Humaira ta shigo Palon tana Isa da takama ka rantse matar shugaban kasa ce,Zama tayi tana basarwa Abdallah ya duka har kasa ya gaidata,ta amsa da sakin fuska sannan ta Kira Maminsa tace ga Abdallah ya iso lfy,Mami sai Dadi take ji,Maman Humaira na Fita Abbinsu ya shigo shima Abdallah ya kwashi gaisuwa,Dama Humaira ita kadai Suka Haifa a duniya,suna ji da ita matuka sai abinda take so shi yasa Bata ji kamar Yar Allah bani Haka take sai dai suna da kyau sosai. Karar takalminta yaji kwas kwas ta fito a tsuke cikin Riga da wando sun dameta tsam kamar a jikinta aka haliccesu,Tana zuba kamshi Gashin nan nata me tsayi yasha gyara na azaba ka rantse sa Mata akayi,kyau kam tayi Amma a gidan miji ya Dace tayi shigar. Gefen Abdallah ta zauna kafadarsu tana gugan juna,matsawa yayi kadan,Ido ta kashe Masa sannan tace ya kk? Lfy kawai yace itama shike Nan gaisuwar tana tauna Chewgum tayi wani kas kas a kunnensa sannan tace ga abinci. Kallon ikon Allah Abdallah yake kawai,kiranta akayi a waya ta daga tare da cewa Hlo...Zakk what's up yau zamuje Club din ne? Ok to ka tabbatar kun kawo min shisha ta Kasan dai kalar nawa daban ne Dana siyo a Qatar masu tsada ne,yanzu guda Daya ce a wajena Mama ta siyo min Flavour masu dadi zanzo dasu. Tana ajiye wayar Kira ya sake shigowa ta daga Hajiya Ruky? Dariya tayi sannan tace a wanne Hotel kike? Ok George ya shigo kasar Nan kenan,Oh Sorry Ruky zanzo anjima Ina da bako na fada Miki zanyi aure kwana Nan,ya zanyi su Mama sun dameni,Musamman Abbi Wai nayi aure,Auren nan wahalace fa kawai,daga kaje sai ciki sai Haihuwa mene ciki,11pm zanzo karki damu. Tana kashe waya ta sake daga wani kiran tace da masifa uban me ka kirani ka min Dan iska shege just common dubu dari Uku baza ka bani ba to wlh kwalliyata ka daina gani,bazan Kara maka kwalliya ba,ai ba Kai kake siya min Kayan kwalliyar ba tsaki taja tare da kashe wayar Baki daya sannan ta kalli Abdallah Wanda ya nuna Sam Bai San ma da iskar data kawota ba,Kawai wayarsa yake latsawa Yana Izza,Duk wankan Jan hankalin data yi ko kallo bata isheshi ba,A ranta tace Lallai guy din Nan baida mutunci,Dan Yana da kyau da kudi yake wulakantani haka zanyi maganinsa Bari na aureshi dan uwarsa. Agogon Hannunsa ya kalla gab da Magrib ya mike ko kallonta baiyi ba ya fice abinsa Yana fita Driver ya taso da sauri ya bude Masa mota tare da kaishi airport Bai Bata lokaci ba sai Kd,Sharp sharp ya Isa gida Yana Allah yasa Khadija tayi abinda ya sata a taron Nan,Amma yasan anjima kadan za a haska a gidan tv da Radio zai gani da idonsa,Wanka da Sallah yayi sai ga Mami tana murna tace har ka dawo ashe? Abdallah yace ae Mami,to ya ka ganta tayi ko? Kai kawai Abdallah ya daga Dan baya son ma ko labarin Humaira ya sake ji,Mami tana murna tace ai nasan Dole tayi maka,sabo da kalarka ce,ko Mai me kyau kake so kamar yanda kake,gata big girl ga kudi ba jinin talauci ba Kar tazo ta lalata Mana Zuriya da warin talauci. Mamakin Mami Abdallah yake kawai Amma Bai ce komai ba Dan kar tace yaki zabinta,Mami tana washe Baki tace Bari Afrah ta kawo maka abincinka Allah ya maka Albarka Abdallah,Ameen ya Furta ransa a bace domin Mami Bata taba sawa yaranta albarka sai dai zage zage Amma yau Dan kawai tana son ya auri Yar me kudi shine harda sa Masa Albarka Allah ya shiryi Mami cewar Abdallah. Tv ya kunna Yana kallon News sai ko ga taronsu da Khadija ta halatta Ana nunawa,Khadija tayi shegen kyau ya furta a ransa,Yana Kare Mata kallo kamar wata Balarabiya Haka ta fito,a ransa yace Ashe ta iya gyara kanta yarinyar Nan,ganin an nuna jawabinta a matsayin matar da Abdallah zai aura ta mike Kuma ta kawo shawarwari Bai San sanda ya Kama yake hakora ba Yana Murmushi tana gamawa har da tafa Mata kamar Wanda a gabansu take, tana ta rubutu a Dan paper yasan Shi zata bawa,a fili ya furta Dole nayi Miki kyauta. Kyale tv yayi sannan ya kunna gidan radio ma ya fara saurarar nasu labaran sai gashi kuwa anyi da Jinjinawa Khadija da akayi a matsayinta na Yar yarinya ta kawo shawarwari masu kyau. Abinda Abdallah Bai sani ba Mami dasu Afrah suna Kallon News Suma sai gashi sunga Khadija ta bayyana kanta a matsayin matar da Abdallah zai aura,kafin kace me Yan gidan ma duk sun samu labari,sannan sun gani har frnds na Abdallah da abokan Business nasu,Daddy