Sashe 14
Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rame,baida nutsuwa,ko Abinci Bai fiye ci ba,idan aka Masa Haka zai cutu Daddy,Daddy yayi Murmushi yace Khadija ko dai kina son Abdallan nawa ne? Da sauri ta hangame Baki tace Daddy a'a Frnd Dina ne kawai Yana min kirki shi yasa Kuma har kudin break yake bani,yasa a kaimu schl kamar kowa a gidan Nan,to kaga duk me maka Haka ai Dole ka damu da damuwarsa That's why ma nace Kar ayi Masa,yanzu Daddy ko Murmushi ya daina Yi min,idan na Kai Masa abinci baya ci,part dinmu ma ya daina zuwa,Kuma before Daddy idan kana ganin dariyarsa kullum da yawa da Murmushi,harda Icecream yake siya min,da kaza katoto,yanzu idan Ya Tafi wurin Matarsa shike Nan Kuma baya sonta fa. Daddy yayi Dariya kawai ta manya yace to zanyi tunani Khadija jeki,Tun daga wannan rana kullum da safe ko dare sai taje wurin Daddy taji ko yayi tunanin sai yace baiyi ba,har aka kwashe wata guda biki saura sati Biyu,Yau Khadija tana shiga part din Abdallah sai ta Iske Yana kuka saman Sallaya tunaninta auren Dole yakewa kuka sai itama ta zauna a gefensa ta fashe da kuka,Suka ruguntsume suna ta kuka,Dan shi dayaji Khadija tana kuka sai ta Kara Masa karfin gwaiwar yin nasa sabo da shi gani yake Daddy mutuwa zaiyi shine damuwarsa bana auren ba,Ita Kuma Khadija tsoronta za a Masa auren Dole ta manta ma taji Daddy nada Ciwon zuciya ta auren dolen Abdallah takeyi. Tana kukanta tace kayi hakuri kaji idan ka aureta ka saki shegiya saki uku zaka Mata,ranar da aka kawota gidan nan da Sassafe zanje na Mata shegen duka dashi zatayi breakfast,duk kuncin da Abdallah yake ji Saida Khadija ta bashi dariya,a ranta tace Kinga Yana dariya Ashe Lallai Yana so na Duke ta ya tsaneta sosai,a fili tace ka daina kuka sai na ci Ubanta wlh kaji na rantse sai tasan ta aureka tunda munafuka ce tsinanniyar yarinya,Ni Malam liman ma ubansa naci a kauye. Abdallah sai gashi ya daina hawayen Yana dariya,Mikewa yayi tare da wanko fuskarsa ya wuce wurin Mami,tana ganinsa ta tabe Baki Abdallah ko kashe kanka zakayi Dole sai anyi auren nan kaji na rantse,Murmushi kawai yayi ya gaidata ya fice Bata San meke damunsa ba,Wurin Daddy yaje suka Sha Hira sai ga Khadija tazo tambayar tunanin Daddy Ina ya tsaya,tana gaida Daddy ta zauna kusa da Abdallah tare da furta Daddy kayi tunanin? Daddy zaiyi magana tace Sirrinmu ne fa Daddy karka fada Abdallah yaji,Daddy yace gaskiya ne nayi tunani na yanke hukunci Khadija me kyau kije kiyi Addua kawai. Khadija tayi dariya tace tnx Dad ta kalli Abdallah tace na ceceka yaron Daddy ka Fara murna kawai ta fice da gudu, Ana ta shirye shiryen biki,Khadija kuwa ta mike kafa sai fada takeyi ku Gama gyaran banzarku baza ayi wannan aurenba. Tana part din Mami duk sun baje Kaya sun sata aiki,ta kalli Afrah dake ta iyayi Khadija tace ku Gama wannan aure bazai yuwu ba,baza ayi shi ba,kune Baku sani ba,Mami taji a kunnenta tana Fitowa ta rufe Khadija da duka Dan ubanki mugun fata kike Mana shegiya matsafiyar banza Da kyar Khadija ta kwaci kanta tare da guduwa part dinsu. Duk wani anko da komai Baba yayiwa Su Khadija Suma,Khadija ranta fes nufinta baza ayi biki ba kawai ta dinga gyare gyare ita da Merry kamar Amare Baba ya Basu kudi Suma na gyaran da akeyi,sun Gama shiri Daddy yace baza ayi shagali ko guda ba,za a daura aure kawai suyi Dj a gida a Kai Amarya ba biki,Hakan yayiwa Abdallah Dadi,Amma Mami kamar zatayi ihu sun Gama shirya karyar da zasuyi a bikin Daddy ya rusa sai haushi suke ji bikin farko a gidan an hanasu,kishiyoyin kuwa sai Murna Yan bakin ciki,Hafsatu Sai da ta rangada guda an Hana biki tana murna. Ana gobe Biki Baba da Mama sun Dade a wurin Daddy suna magana,Su Khadija kuwa an tafi saloon da Lalle,Gida ya cika da Yan uwa da abokan arziki tare da kawayen Yan Matan gidan,abokan Ango Dr Hussain ma suna part din Ango an gayyaci frnds da yawa,Khadija ma ta gayyaci Yan schl frnds nasu mutum hudu duk da cewar Bata tunanin za a daura Auren Nan,Abu Kawarta ta kauye da Madam Ngozi sunzo bikin,Khadija tana lalle Bata san Abu tazo ba. Sai wurin 6pm Suka dawo Abdallah ya gaji da nemanta ta samo Masa abinci sai yayi ta aikowa ace Basu dawo ba,Kyan da Khadija tayi ya baci lalle ne na kece raini kamar itace Amaryar,gashi yaci gyara,Ganin Abu yasa suka buga tsallen murna,Abu tace kin ganki kuwa Wallah kamar Yar Shugaban kasa, Kin daina wasan kasa ke ko? Khadija tace ai nan birni ne basa Yi Ina so muyi basa Yi,Abu tace ai nazo zanyi sati guda sai muyi wasanmu ko? Khadija tace har katuwar Teddy gareni da ita zamuyi abinmu. Madam Ngozi tace kunfa girma Amma Kuna wani Wasa yanzu wa yake Haka,Khadija tace wanne girma Ni dai zamuyi Ina so. Abinci sukaci Khadija taja Abu Garden Suka Fara wasansu Khadija tace Ayyiri yiri Anyi aurena,wasansu suke Basu San Su Sagir kannen Abdallah da abokansa sunzo wurin bama suna Hutawa,Suma su Abdallan da frnds nasa duk sun dawo Nan Ana ta Hira,sai lokacin Suka kula dasu Khadija Jin gudar da Khadija ta rangada kamar an kawo Amaryar gaske,hakan shi yaja hankalinsu suke saurarar wasan yaran. Khadija tace to anyi min Aure kece Mama ta sai ta fashe da kukan karya Wai an kaita gidan miji tana kuka,Abu tace to kizo ganin gida wurin Mamanki kina da ciki Kato,Khadija ta cire dankwali tayi ciki dashi ta taho wurin Abu tare da cewa Ina kwana Mum,Abu tace oh Baki gaji ba Khadija wannan katon ciki Haka dashi kike yawo da zauna me za a dafa miki? Khadija ta dafe cikinta ta zauna da kyar tace wash a shagwabe Agwalima nake so kawai,Abu tace kash Ina ma da yaro sai ga Ahmad kanin Khadija sukace zo muyi Wasa Ahmad,Shima yazo wurin Suka Fara wasan tare Abu tace karbi Tanimu ga kudi maza siyowa yayarka agwalima,Ahmad ya karbi ganyen bishiya matsayin kudi sannan yaje bayan bishiya ya tsinto wasu Yayan bishiya kana na ya kawo,Khadija tayi zaman masu ciki tana cin karya,bayan wani lokaci Wai sai ta Kama Nakuda ta haifo Teddy dinta,Abu tace gaskiya Yar Nan da kyau take santali Khadija tace Mama ki kawo a Bata Nono Tasha,sai sata a kirjinta tace yawwa ta koshi, Haka suke ta wasansu Abu shegen wayo gareta kamar Yar tsofaffi,samarin suna jinsu ta baya can suna ta dariya musamman Khadija komai sai ta gwada. Da suka gaji Suka ce Wasa ya watse kowa ya tashi Merry ta fito tace ke Khadija Mama tace tun dazu Yaya Abdallah ke nemanki Zaki Masa aiki. Khadija ta dafe kirji tace wlh na manta Yana Ina? Gashi can a bayanku shi da mutane,Kunya ta rufe Khadija tasan Dole sunji wasansu da sukayi na Haihuwa,Merry Hannun Abu taja da Ahmad suka yi ciki,Dankwalinta ta yafa saman doguwar rigar Tata,Lalle Kam gashi Nan yayi Masifar kyau da gashin Nan daya sakko ta baya,frnds na Abdallah sai yabawa sukeyi kowa Yana so Khadija ta Zama mallakinsa. Hausarta ke Basu dariya da Bata iya ba,nesa kadan dasu ta gaishesu tare da cewa Bro Abdallah Mama tace kana nemana? Sai yanzu Kika ga damar zuwa? Na manta ne I'm sorry lalle naje fa kalla nayi kyau ta durkusa a gabansa tare da nuna Masa hannayenta da kafa,Kallo daya yayi Masa tun dazu suna Wasa ya Gama gani dama, Harara ya zuba Mata tayi Shuru tace na tafi? Jeki yace kawai zata sheka da gudu kenan ya Mata mugun kallon da ba shiri ta nutsu ta fasa gudun ta tafi a hankali,tana tafiya frnds Suka Fara Koda kyawunta wasu ma sunce suna kamu,shi dai Abdallah Bai kulasu ba. Sai da Khadija ta Shiga cikin Yan biki taji Ana cewa lefe akwati ashirin da biyar Mami tasa Abdallah hada,takaici ya Kama Khadija tace Allah yasa wuta ta Kama kayan Amaryar sai da Mami ta duketa. Washe gari kowa yayi Shirin tafiya Kano a jirgi abinka da manya maza an dau wanka da wasu Matan Dangin Ango za aje a sheda,Wai Wai Ango yau kamar yau aka kyankyasheshi yazo duniya sabo da kyan da yayi abin alajabi ne ma,Khadija da wuri taci kwalliya cikin Shadda dakakkiya da Daddy yayi musu dama tunda taga an kawo kalar da Ango zaisa farar shadda itama tace Baba farar shadda zai siya Mata,Su Kuma su Merry nasu daban,Khadija ita kadai tayi anko da Ango ba karamin kyau tayi ba itama gidan kwalliya taje aka Mata har dauri ka rantse itace Amaryar ganin da gaske fa Daddy sai yayiwa Abdallanta Auren Dole shi yasa ta hakura kawai tayi kwalliya yanda baza a barta a baya ba. Kuma dama ta rantse Abdallah ne zai Fara ganin kwalliyarta sai da ta Bari sun fito da Frnds nasa zasu tafi Airport Mami su Afrah da sauran Matan gida duk suna compound Ana kallon Ango Ana Masa pics sai ga Khadija Dan tsokana bul ta fito kusa da Ango ta karaso,Da kyar Abdallah ya ganeta sabo da tsananin kyan datayi ga Daurin dankwalin ya Hadu ka rantse Amaryace sukayi anko da Angon ,Dariya tayi Masa tace munyi anko da Ango,Murmushi ya saki ba shiri,Dr Hussain ya shiga kyastasu a pics, Khadija ganin kowa na kallonta da mamaki ta dafa Ango aka daukesu,ta rike hannunsa shock na taratsatsi a jikinsu Dr Hussain kuwa sai dauka yake Yana Basu style, Daddy da Baba Suka fito Khadija ta jawo su ta hadasu da Ango Dr Yana ta daukansu ba ji ba gani sai Da Baba ya koresu,Khadija tace Ango saura daya gobe fa zaka bar Mana gidan,Hannayenta ya riko biyu suna facing juna Dr ya dauka kyas kyas,Sai ga Mami ta Fado tare da make Khadija Saida ta Fadi a kasa,sannan ta bita da ashariya,ganin Haka yasa angwaye Suka tafi mota Drivers suka jasu,Daddy Yana kallon abinda Mami tayiwa Khadija ta cikin mota,kwafa yaja kawai suka tafi.