← Book details Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 53

Sashe 2

Tubabbiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wlh ke da aure sai dai kiga anayi sai kin tsufa a gida,sai kinyi Shekara Arbain Baki auru ba Zaki san Ni Kika zaga,Ina liman guda me daraja a kasar Nan har ki iya dura min Ashariya Haka tunda nake ko kallon banza ba'a taba yi min ba sai ke. Sai kinyi bakin jini wurin Mata da maza,Babu inda za a so ki,sannan gaba daya zuriarku kun dinga shiga matsala kenan har abada,Khadija tace Kaine Allah? Baka Isa ba Malam tuni zanyi aurena kana Nan kauye,Kuma Wanda Zan aura sai kayi mamaki,sannan sai na kawo ma Mijin har Nan kauyen,Kuma kudi zamuyishi Animal fool an daina zuwa makarantar taka local man kawai,Malam yace ko kunzo ma bazan koya muku ba me kuka sani Yan iska masu yawo da tsangalallun kaya Kika sake cancer ce ajalinki shegiya me Jan kunne,Nasara bayahudiyar banza,Khadija tace gwara Ni kaifa kazami...kazami,see your face like Gost,kuma kasan in this whole village Babu me kyawunmu har city birni sai an duba anyi waca waca (sai an tona take nufi) za a samu kamata,kalleni like oyubo obodo kamar Baturiya Amma matanka fa Nono nasu Haka like slifas me kake tabawa,Babu Hips ko kadan Babu kalla nawa Katuna katuna Khairat ta juyawa Liman mazaunanta maka maka dasu,Liman ya hadiyi yawu,tace ka daina Hadiye saliver naka ba samun kamata zakayi ba. Liman yace Zaki gani jeki,Khadija ta juyo tace sai na tona ma asiri kana Tara mataye a dakin can kana iskanci dasu kana Basu magani,wallayi (wlh)idan banyi aure ba sai na kawo police sun kamaka trust me stupid Khadija ta tafi gida da tsangalalliyar rigarta,Khadija sun koyi halayen yaren kudu na rashin Jin nauyin fadan ko wacce magana,sannan ga ba rufin Asiri,magana Kuma da karfi sukeyi musamman Khadija da Bata ji,gaba daya aladunsu na Yan kudu ne,Sam in ka gansu zaka ce ba musulmai bane sai dai shegen kyau kamar dama sun hada jini da labarawa domin Mama kwarori ne,Babansu Kuma Asalin bafulatani ne. Liman kuwa wajen me gari ya wuce tare da fashewa da Kuka ya sanarwa me Gari abinda Khadija tayi Masa,Me Gari dake liman Yana Masa asiri iri iri sai yace Kar ka damu Liman dama Dangin nasu Mutum biyu ne fa ka manta ambaliyar ruwa duk ta Karar da danginsu kaf,korarsu a garin Nan ba komai bane kaje karka damu dama sun ishemu suna gurba ta Mana rayuwar yaran Gari da shigar banza Tubabbun banza wani musulunci sukeyi na kirki,ai indai akace maka ba bahaushe bane to ba wani musulunci sauran mutanen ke yi cewar Liman. Khadija kuwa tana zuwa gida ta kwashe labari ta fadawa Mama abinda ya faru,Mama tace Allah ya fisu kyalesu,Washe gari Mama taje ta Saro manjan da take siyarwa,ita Kuma Khadija tana can cikin mazan data Tara duk zasu Kai 20 to 19yrs suka tafi gona tare tana inuwa su Kuma mazan suna cikin gonar suna noma Wanda Khadija ce ta Nemo aikin a hannun wani kansila na kauyen sannan kudin da za a biyasu ma Khadija ce ta fada. Sai Magrib suka Gama aikin yayi Masifar kyau Khadija tana zaune a inuwa sabo da ita burinta komai ace itace shugaba,kudin aikinsu Kansila ya Bata, ta cire ba cuta ba cutarwa suka raba da samarin Nan Amma nasu duk yafi nata yawa sabo da su sukayi aikin,itace dai tayi kurda kurda ta samo aikin. Tana dawowa Mama ta ganta futu futu duk farar fatarta tayi furu furu,Zama tayi tare da mikawa Mama dubu biyu ta Bata labarin aikin,Mama tace ewooooo ashe dai Kwangilar Nan da gaske ake yinta ga harka ta Fara budewa,Af Danma ba a birni muke ba na fada Miki,Ina da Yara Kwangila kawai Zan na karba Ina wurin ayi aiki a biyani,Duk wani aiki Zan iya Mama matukar Zan faranta muku ke da kannai na. Mama tace well-done my Daughter Allah Kara budawa,May God Continue to bless u my Daughter, Khadija tace Ameen Mama, Mama taci gaba Allah ya kawo min Miji na Gari na aura Wanda zai dauki nauyinmu Baki daya,Nan take annurin Khadija ya gushe cike da Shagwaba tace wlh baza kiyi aure ba,Dan Daddynmu ya rasu shine Zaki auri wani Dan Iskan,Allah idan Naga wani yazo zance to sai na zuba Masa ruwan zafi,Baki bude Mama take kallon Khadija,ta samu Miji da dama Amma Khadija ce ke hana auren,sai ta San yanda tayi ta Kori bazawarin,Mama tace wlh Bari kiji Khadija Ina samun miji aure zanyi ko mutuwa zakiyi,Baki Khadija ta turo gaba ta shige Bedroom tana kunkuni,Suma su Merry bayan Khadija suka bi suna kishin ubansu. Gidane katafaren gaske estate gudane,Unguwa guda ne gidan part part ne Babu adadi a gidan,part din kowanne ya Hadu karshe yaji kayan Alatu,Babu abinda Babu a gidan irin na more rayuwa,gidan kamshi da kyalli kawai keyi maaikata na sintiri ta ko Ina,kowa da irin aikinsa,ga securities ko Ina Ana tsaro,garden da sweeming pool bangarensu daban a gidan. Mami Pls kuyi sauri mu Isa Airport jirgin Ya ABDALLAH remain 5mnt yayi Landing Kuma kin San Ya Abdullah Bai son jira yau duk sai munci ubanmu a gidan Nan idan ya jira a Airport ba a zo daukansa ba,Mami tace ke karki yiwa Dana Sharri tuni securities sun Isa Airport Daddy ma Yana can tare dasu. Cikin shiga ta Alfarma Dattijuwar daga ka ganta kaga marar mutunci tun a fuska tare da yaranta Afrah da Islam suka fito suna zuba kamshi,parking space suka Karasa inda iya kallonka motocine masu tsadar gaske iri iri ta ko Ina,Wasu Yan Mata ne da samari wasu suna shiga mota da Alamar fita zasuyi wasu Kuma sun dawo,wasu Kuma gasu Nan kowa da abinda yake, ganin su Afrah da Maminsu yasa aka fara gulmace gulmace Ana musu Habaici Ana Harare Harare,itama Mami da yaranta Basu fasa ramawa ba suna Maida martani da gani kasan ba a shiri da juna,itama Mamin da take Babba cewa tayi ki sharesu shegu yaran matsiyata,Alhaji shi ya jawo Daya kwaso iyayensu ya auresu,gida kamar kasuwa tsaki taja cike da Izza suka shige katafariyar mota Yar yayi Driver yaja su suka wuce airport. Mami kyakyawar gaske ce ka rantse balarabiya ce Haka ma yaranta suke wannan na wane wannan a kyau sai Rashi kyan hali. Suna karasawa Airport wani azababben Guy ya sakko daga steps din jirgi Yana janye da karamar Trolley dinsa ta Yan gayun gaske,Sanye yake cikin wata tsadajjiyar t-shirt silver color,da wando jean fari Kal pencil, rigar ta wuce Masa zuwa cinya ta Dan Zobe daga baya kalar ta mawakan turawa,hannunsa wani zoben azurfa me azabar tsada,ga agogonsa Gucci,Haka takalminsa ma fari Kal kamar canvas me shegen tsada Haka yake sai dai an budeshi ba a daure zaren ba ya wani bude kamar wani Justin Bieber zaiyi Waka,Sumarsa irin ta Larabawa baka wuluk Tasha wani aski na iban albarka,an kwashe gefe gefe kadan tsakiya daga gaba an tarata da yawa sannan an yarfota saman goshi tayi wani gaba kamar zata rufe Masa Ido,kowa kallonsa akeyi Dan ka rantse wani mawakine daga kasar London ya sauka a kasar,Amma fa ya Hadu karshe ta ko Ina Babu Wanda ya Isa ya kalleshi Bai Kara ba sabo da Masifar kyansa,gashi fari wani jajir dashi,da Dan sajensa kadan da gemu kuyas, fuskarsa ba me Fadi ba, ba ku ma me tsayi ba,Hancinsa Wai zarkadi kyan hancinsa ya baci,idanuwansa madaidaita lumsassu farare Kar Kar,girarsa me yawa,Haka gashin idonsa,komai nasa me kyau ne,shi ba me tsayi ba ba Kuma gajere ba,ga jikinsa dai dai babu kiba ba Kuma ramamme ba. Wani taku yake na zaratan matasa Yan gayu,lips din Nan nasa masu kyau jajir dasu yake wani tsotsa Yana tauna Chewgum a hankali idan ba kula kayi ba baza kace tauna yake ba. Wani Masifar gadara da yake abin ba acewa komai ga bala'in iyayi da jiji da Kai da yakeyi abin sai Wanda ya gani,Afrah da gudu taje tare da fadawa jikinsa,kamshinsa ya cika wajen. Da sauri ya janyeta a jikinsa Yana hararata Yana Dan Murmushi kamar Dole yace Ke Zaki Samin Dirty,Baki bude suke kallonsa har Mami Amma sun San halin kayansu zai aikata me Hali baya fasawa. Mami ya mikawa hannu tare da rike Hannunta sai Kuma ya rungumeta Yana Dan Murmushinsa da Bai Kai cikin cokali ba a hankali yace Ina wuni Mami,ya gida? Lfy tace Son wannan wanka Haka wlh ban ganeka ba,Haka ka koma ka girma,ka ganka kuwa Abdallah, dariya kawai yayi Wanda mutane da dama maza da Mata sai da suka lalace wajen kallon wannan hadadden bawan Allah yafi uban kowa kyau duk gidansu albarka,ko a turai sai an tona samun kamarsa. Islam wacce Bata Fi 10yrs ba ya dauka tare da dagata sama suna dariya yace cutie How u? I'm Good Bro,wurin Daddy ya nufa har kasa ya rusuna tare da gaidashi suna farin ciki gaba daya suka rankaya zuwa katafaren gidansu. Tunda motoci suka tsaya a gidan Mutanen gidan bataliya guda kowa ya fito ganin gulma da tsegumi,har ta saman bene kowanne part Matan Yara da manyan tare da iyayensu Ana ta leke Ana tsegumin Abdallah. Bayan Abdallah yaci abinci ya huta wanka yayi tare da fita ya shiga part part dake gidan Yana gaida matayen Babansa da yaransu suna amsawa,Yana fita za a fara gulma,Suma Su Mamin hakan take da yaranta Mata sai cewa suke wlh Dan Abdallah ne marar zuciya da mune ko part dinsu bazan kalla ba,Mami tace kyalesu Afrah a Haka zasu Kare na gaba yayi gaba,Can Kuma sauran suna cewa har ya fada Mana turai,muma yaranmu duk sunje can sukayi karatu me za a nuna Mana,ga yaron ma ya dawo a Dan iskansa,jibi askinsa wasu suce Wai su masu kyau shuwa Arab su fa Basu yarda ba Larabawa ne. Mami Kuma da Afrah cewa suke yo mu da muke jinin arziki su kuwa duk matsiyata Daddy ya aurosu,ai wlh tukunnama sai sun ga matar da Abdallah zai aura,Ummi tace wlh kuwa Yar attajiri jinin sarauta Yar sarkin Ethiopia ga kyau ga Naira,Ai Mamanta ma ta Matsu ya Gama Masters Azo a Fara Maganar aure kwarya tabi kwarya,Dan Ma Abdallah banza ne Wai Humaira dince baya so to wlh sai ya aureta ko Zan tafi tsirara,Allah ya kawo Mana Dangin arziki zai watsa min kasa a Ido,Afrah tace karki yadda Mami Dole ya aureta,Mami tace kwarai ma kuwa yanzu ai
Chapter 2 · 0% Book details