← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 59

Sashe 8

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*vote*
*comments*

*with* 08066364077
[16/12, 11:41] ‪+234 806 493 3819‬: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

TA ME GARI

NA
KHADIJA USMAN

9⃣

narasa bakin da zan godewa masoya wannan littafin sai dai ince Allahu yabar qauna yaqara bani kwarin gwiwar faranta muku ko yaushe 😘

******

ko gama parkin habeeb beyi ba naseer ya balle murfin motar ya nufi gurin su da sauri yana tambayar lfy meya faru meya sameku naga duk kun shanya baki a iska?

yusra da bakinta ya kacame da daci ne ko bauri ji takeyi bakin duk ya dade itace tayi qarfin halin ce mishi abinci mukaci me yajin bala'i

kallonta yayi duba na rainin hankali kafin yace wannan wane irin rashin sanin ciwon kai ne ta yaya zaku je kuci abunda kuka san zai yi muku illah yanzu dan Allah dube ku kunyi wani zugwi zugwi daku kamar mayunwatan 'yan boko haram dayalla ku tashi ku shiga ciki

kada kai su maryam suka shiga yi tare da fadin ah ah mudai basai mun shiga ba dan Allah dai ka taimaka ka bamu maganin wankin ciki pls

habeeb ne ya qaraso gurin yana tambayar sa lfy ? nan ya sanar dashi wai yaji suka sha fada yayi musu sosai akan illar da yaji keyi kafin yace su shiga ciki kafin yakawo musu magani dan kar yajin da suka sha yayi effected dinsu dan yaga sunsha da yawa shiko naseer fada yayita yiwa yusrah duk yadda yaso su khaleesart su shiga parlor ki sukayi har sai da habeeb yakawo musu maganin suka tafi ita ko yusrah da sanda ta shiga ta wuce dakinta inda ta fada toilet tanata brush kamar zata qarar da kamfanin makilin sai yunkurin amai takeyi dan ji takeyi gaba daya makogoronta kamar ya qone 🤣

******

tun daga wannan rana wani kallon rashin mutunci ko na raini be qara shiga tsakanin dije da yusrah ba har saida mamy ta dawo zuwa lokacin daddy na nan domin shirye shiryen biki kudi sosai dije ta karba gurin daddy dan yin siyayyar nata kayan bikin a cewarta tunda ba'asa da ita a anko ba baruwanta nata zatayi rufaida da husna qawayenta sune suka tafi siyayyar tare kudi sosai suka kashe dan har ciko sukayi mata tare da qara mata wata siyayyar direct shagon wani me yi musu dinki rufaida ta kaisu suka kai kafin suka wuce gida duk sun gaji

suna sauketa suka wuce ita kuma ta nufo gate din gidan ta qaramar kofa ta shiga inda tana shiga ta iske su yusrah da qawayenta tare da naseer sai abokansa da alama suna tattauna harkar bikin ne

ta so ta wuce su amma ganin yadda yusra ke binta da harara yasata yin kwana ta nufi gurin da suke cike da takunta na 'yammatan zamani wadan da inuwar budurcin bata dade da sauka bisa kansu ba riga da siket ne na wani blue din material a jikinta wanda aka yiwa ado da kyalkyali na yellow din flowers dan haka tasa takalmin me matsakaicin tsini tare da siririn mayafinta yello kanta babu dankwali hakan ne ya qara bayyanar da yalwataccen gashin kanta dayasha gyara yanata walqiya da dan murmushi akan fuskarta ta nufo gurin su inda hankalin Amir abokin naseer ke kanta

wow so beautifull bros ya dan daki kafadar naseer do u look what i see?

dagowa naseer yayi domin ganin me Amir ke kodawa haka ganin wadda ke nufo su ne yasashi sakin sirirn tsaki tare da juyawa yaci gaba da maganarsa dasu maryam

duk abinda yayi dije ta lura dan haka ta qara fadada murmushinta ita ko yusrah baqaramin dadi taji ba da yadda naseer din yayi

cikin siririyar muryarta tayi musu sallama da sauri qawayen yusra suka amsa tare da wage baki kamar ze yage dan fara'ar da suketa yimata hakama abokan ango dukansu kamar masu tallar makilin a ranta tace ikon Allah sukuma wadan nan haka Allah ya hallice su babu aji bare aje maganar jansa

cikin salon karya harshe tace barkanku da hutawa Aunti's dina

har rige rigen amsawa sukeyi cikin sakin fuska

ykk qanwar mu ya kuma shirye shiryen biki?

all is fine so ya gajiya da yawace yawace ?

duk alhmdllh

toh fatan dai yayana be barku kunata dibar kura a bakin zannuwa ba

cike da rashin fahimtar maganar ta suka juya suka kalleta

nup kada ku damu bawai ina nufin wani abu bane naga kun zubamin ido kamar zaku hadiyeni ina nufin fatan dai yana cika muku jaka da tsaba ko dan nasan halin yaya naseer badai mammako ba

sai yanzu yadago ido ya dubeta tare da sakar mata harara amma sai yaga ta waske tare da fadin

sannunku abokan ango ykk?

lfy beauty cewar Amir dayafi kowa zakewa

yayi kyau tafada kafin taci gaba fatan dai kuna cikawa 'yammatan jakunkunansu ko dan nasan halin samarin yanzu duk 'yan kamus ne

dariya Amir yayi tare da gyara tsayuwarsa danya qara burgeta yace ah ah qanwarmu ai mu ba irin wadanda kk sani bane mun bude bakin aljihu basu da matsalar komai

hmm au hakane ?

ta tambaya tare da yatsina fuska

sosai ma kuwa ai gasu nan indai ba butulci zasuyi mana ba sun san mun bude bakin aljihu sunata kwasa

hakan yayi kyau abokin ango dan wahalar banza😂ta fada tare da qoqarin barin gurin

yake kawai Ameer yakeyi bakin ma yaki rufuwa dariya ce ko kuma murmushi duk ya rasa tayi itako ta sa kai da nufin barin gurin sai kuma ta dawo ganin yadda yusra ke yi mata wani kallon raini tare da naseer dake harararta

gaban naseer taje ta dan rusuna tare da fadin gani yaya?

ubanwa ya kiraki ?

ubana mana

ta fada tare da qifqifta ido kasan ance babban wa magajin uba kaga ko ai kai ubana ne ko?

rasa me zaice mata yayi sai yusrah datayi qarfin halin fadin ke wai wannan wane irin iskanci ne haka anan kinga sa'anninki ne

miqewa tayi tare da fadin ah ah wlh ko daya daga sa'annin baffana sai yayyena sai kuma wadanda ban sanma a wanne mataki zan ajiye su ba dan nasan da sunyi aure da wuri da ko a haihuwar raquma nice auta cikin 'ya'yansu tana gama fadar haka ta qara gaba tabar kowa shaye da mamakinta

kwafa yusra tayi tana jinjina rashin mutuncin dazata yiwa yarinyar danta lura tashen balaga takeji

******

tun daga wannan lokacin babu wanda ta kuma haduwa dashi kowa yana cikin hidimar biki inda suketa shirye shirye

****

rana bata karya yau saura kwana biyu daurin aure yayin da mutanen qauyen gawo suka iso dije ce ta sama musu masauki danta lura indai ta hajiya mamy ne sai dai su wulaqanta dije tasa ran zuwan innarta amma sai taga ba'a zo da ita ba har kuka sai da tayi nan aka shiga rarrashinta ita da basira suka shiga dawainiya da mutanen inda daga baya ta bar baseera ta tafi dansu rufaida nata jiranta dan suje qunshi tunda batada waya da sauri ta fita ta bar gidan tana zuwa kuwa ta tarar suna jiranta nan suka shiga mota suka tafi sunata mata mita dan rufaida akwai son biki kai kace bikin yayanta za'ayi

anyi musu qunshi ja da baki tare da gyaran jiki barakallah masha Allah sunyi kyau sosai matuqa sai dare suka dawo gidan duk wanda yaga dije a cikin mutanen kauye saida ya yabata masu taya iyayenta murna nayi masu hassada a zuciya nayi

ranar akayi kamun yusrah inda aka gabatar da komai cikin wadata

****

yau ake dinner dan haka kowa yake burin qure wanka

sauri takeyi ta qarasa part din da 'yan garinsu suka sauka dan zasu je gurin makeup da sukayi booking sam bata lura da shi ba hakan yasa ta dan bugeshi kadan

wata irin angaza yayi mata kafin tayi wani yunkuri yakai hannu da niyyar marinta cikin sauri ta kauce

a hasale yafara magana ke wace irin mahaukaciya ce iye dan ubanki bakya ganin gabanki in kina tafiya kamar budurwar qauye au ashe fa banyi kuren harshe ba itace wato ke kin girma ko shine rannan harda yiwa mutane rashin kunya ke ga 'yar birni wai tsaya ma duk wannan saurin da rawar jikin da kikeyi duk na menene?

idan ma na zuwa gun dinner ne wlh kiyi saurin fasawa dan wlh naga qafarki a gurin saina ci ubanki saina babbala ki gurin manyan mata ne wato classic lady ba irinku wadanda ko dadewa da yayeku ba,ayi ba wuce ki bani guri shegiya me siffar aljanu

kalamansa sunyi mata zafi matuka ta so yin kuka amma saita ga meye nata nayin kuka a wanne dalili hmmmmm kawai tace tare da qarawa gaba taje tayi abinda zatayi ta fito tana fita still ta hadu da yusrh daqawayenta suma da alama fita zasuyi dan su shirya tagansu da akwati

yauwa ke zonan dan uwarki

kin kula su tayi tasa kai da niyyar ficewa

wani sauri yusrah tayi tare da fadin ke ina miki magana kina jina nasan duk wannan rawar kan da rawar kafar da kikeyi danki fita bazai wuce dan kije gun dinner bane to wlh kk sake naga kafarki a gurin nan sai kinci kut........dan gurin manyan guys ne da big girls ba cakuri cici irinki indai ba tsintar bottle din da akasha drinks zaki tsinta ba

wucewarta tayi batare data tsaya qara jin me yusran zata ce ba tana fita ta shiga tunanin maganganun su duka biyun wato suna nufin ita batakai wadda zata je bikinsu ba?suna nufin ajinta yayi low dayawa da har zesa takasa taka gurin?juya maganar ta shigayi cikin ranta ta jima tana saqa da warwara kafin daga baya tasami mafita murmushi tai tare da yin kwafa a fili ta furta

big guys
classic lady's

a kafta😜

******

shiri sosai kowanne bangare keyi musamman bangaren amaren dan ko wacce so takeyi taga ta burge ta bada kala cikin taron dan haka kowacce ke babban shiri

dije ce ta shigo gidan direct part din mamy ta nufa dake upstairs tasan su yusra na can na shiryawa a zaune ta same su ana shirin fara yiwa yusrah kwalliya da sallamarta tashiga dakin wasu sun amsa wasu kuwa suna sabgar gabansu da qarasawa tayi inda yusrah ke zaune tanata hura hanci tace sannu Anty

meye kuma ?

ta fada tare da hararart
Chapter 8 · 0% Book details