← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 59

Sashe 26

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana tsaka da cin abinci su habeeb suka shigo su dua ukun habeeb,naseer,sai doctor yusif suna shigowa suka zauna naseer ya cire waya ya kira yusrah ba jimawa kuwa saigata tazo nan fa aka shiga hirar yaushe gamo itakam dije saida ta tabbatar ta koshi kafin ta qaraso falon ta shiga gaishesu dukansu suka amsa cikin sakin fuska

juyawa tayi taja yaran sukayi cikin dakinta ta shiga yi musu wasa

sai da akayi sallar la'asar kafin su yusuf suka fara shirin tafiya suna harrakawa dije ta gito da yaran

kallonta doctor yusif yayi kafin yace Auntyn yara kun gaji da wasan kenan da har muna shirin bar miki su

murmushi tayi kafin tace to ai ni koda an barmin ina so wlh

to tunda kina so ki bisu gidansu kiyi kwana biyu cewar sajida aikuwa Amina tayi caraf tace wlh kuwa da naji dadi dan dama in Abban Anwar ya fita rasa 'yan hira nakeyi kinga sai kiyi mana weekend ko sister

me zai hana ai ko cewa kk yi ta dinga zuwa duk week tana muku weekend bakuda matsala dan haka ke jeki shirya ki zo ku tafi cewar habeeb

mamaki ne ya cika zuciyar dije ganin yadda ake ta tallarta dan haka saita maxe tayi kamar bata ji su ba

naseer ne me fadin ai khadija batada matsala akwai dadin zama dan haka Allah ya taimaka

haka sukaita tunzura har saida Amina ta dameta ta dauko kayanta kala biyu ita kam taga ikon Allah yau

koda suka zo shiga mota har rige rigen bude mata mazan da matan keyi koda ta shiga ta zauna da sauri suka rufe ji kk yi bammmm ita abin nasu ma dariya ya fara bata

dan haka saita bude motar da niyyar fitowa

cikin hada baki suka tambaye ta

ina zaki kuma?

kallonsu tayi daya bayan daya kafin tace mantuwa nayi zan koma in dauko

da sauri habeeb yace wa sajida matso ta fada miki abinda zaki dauko mata basaita fito ba idanma yana nesa ne to ki fada mata sai ta dauko akwatin in kin dauka saita mayar kada ki samu damuwa 'yar qanwarmu..........

*Allah ya raka taki gona dije* 😂😂🤣🤣

*Alkalamin khady* ✍
[3/15, 6:30 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TA ME GARI*

NA
khadija usman

2⃣5⃣

ita dije abinma dariya yabata ganin da gaske sukeyi yasata fadin

ah ah a barshi ma nafasa daukar

yauwa 'yar albarka kuje kawai yusuf Allah ya kiyaye sai munyi waya cewar habeeb

shikam yusuf dariya yaketa yi ciki ciki dan yasan wannan tunkuda dijen da sukeyi wlh ba banza ba

haka yaja motar sa suka fita mutan gidan nata daga musu hannu kamar dangi sunzo rakiyar mutum zashi saudiya🤣

suna ganin sun fice a gidan duka suka ce Alhmdllh Allah ya raka taki gona

ameen inji matan nan kowa yayi nasa wuri da matarsa

******

saida ya biya ya dan yi musu siyayya kafin suka wuce gidan

ba karamin mamaki dije tayi ba ganin haduwa da tsari irin na gidan doctor yusuf lamarin bai qara rikitata ba saida suka shiga palon gidan gaskiya masha Allah ya hadu iya haduwa

suna shiga ita da yaran suka qarasa saman kujerar suna tsalle ita kuma ta qarasa a hanki ta zame qasa dan ta zauna yayin da taga doctor yusuf yayi wuf ya shige daki tare da ledar daya yo musu siyayyar da ita yana shigewa kuwa ta tsinkayi muryar wata dattijuwa na fadin

to to andawo jaraba ta dawo da yau bakina shuru gidan tsit na yi bacci na cike da annushuwa da mafarki me dadi amma yanzu daga dawowarku har kun ajiye shaida ina shi yusuf din yake naga duk na ganku amma shi ban ganshi ba ince dai ba wani abun ya siyo kuka munafunce ni aka shige dashi ciki ba ko?

ikon Allah cewar dije data tsaya tana kallon sababi

jin dije tace ikon Allah yasata juyawa gurin sai yanzu ta lura da ita

to ita kuma wannan sadakan yallan daga ina iyayen kwashe kwashe?

yusuf ne ya fito cikin fara'a yace qanwar su habeeb ce ta zo mana weekend

washe baki tayi tare da fadin ah ah Allah sarki nako ga kama kamar an tsaga kara kice ke 'yar gida ce ai na dauka kina daya daga cikin irin kare arzikinka ta fada tana me wurgawa Amina harara

Amina wadda idan da sabo ya zuwa yanzu ta saba da halin hajiya hauwa dan haka ta qara dukar dakai sbd bata son tayi wani motsin kirki yanzu a qarewa iyayenta sababben zagin yau da kullum tun da ta auri yusuf take cikin wannan halin da hajiya hauwa wadda mahaifiya ce ga yusuf din a cewarta bata so ya auri 'yar talaka ba wadda zasu qarar da arzikinsa gara ya auri 'yar masu kudi to da yake da rabo gashi harda yara biyu

haka kawai ta tattara kayanta ta dawo gidan da zama kullum bata bacci har sai taga shigowar yusuf kuma ta tabbatar be shigo da komai ba da kanta take kulle qofar falon ta rike key din a gurinta da asuba ta zo ta bude wai duk dan kar aje ko ya boye abinda ya siyo a mota saita yi bacci ya dauko

iya kyautatawa yusuf nayi mata duk wani jin dadi ya dauke mata shi amma sam bata gani taki barinshi ya sarara

su biyu ne yaranta daga shi sai qanwarsa farida wadda yanzu haka tana aure a kd ne bata fiya zuwa ba sbd batajin dadin yadda mahaifiyarsu keyi gashi amina nada kirki sosai

to ku haka ake bakuwa kusata ta zauna qasa ta fada tana me karasawa inda dije take zaune

tashi kinji ai daga ganinki ke jinin arxiki ce kin saba da hutu ji fatarki ina ke ina zama a kasa tashi ki zauna kinji duk inda yayi miki ki zauna ki mike kafa ai tunda jinin su habibu ce ke bakida matsala dan yaran kirki ne sun san mutunci

ita dai dije ta kasa magana haka hajiya ta dinga tantadinta harta gaji aka kira sallar magrib kowa ya kama gabansa Amina ta kai dije dakin da zata zauna

bayan tayi sallah ne tana zaune kan dadduma Amina ta shigo dakin da sallamarta dauke da faranti a hannunta

amsawa tayi tare da qara gaisheta ta amsa cike da fara'a kafin ta ajiye ta nemi guri ta zauna tace ya bakunta

.sunkuyar da kai dije tayi kafin tace Alhmdllh nan da can ai duk dayane

to Allah yasa haka kika dauka harga zuciyarki

wlh dagaske nake Aunty

ina yaran ne?

kin san suyi jaganiya yauban gaji ina musu wanka har sunyi bacci

toh da wuri haka ?

wlh kuwa ga abinci nan kici sai dai kiyi haquri da abinda kk gani ban sani ba ko baki saba da cin irinshi ba kiyi haquri tun safe kafin mu fita hajiya tasa aka dafa amma dayake kin zo da kafar dama nasan gobe za'a canza insha Allah

yauwa Aunty dama abinda ya dan dameni nake tunanisa yanzu kenan

meyasa kika zauna tana ci miki mutunci haka duk da ban sanki ba ban san halinki ba amma na yaba miki Allah inda nice ko hmmm da tuni an wuce gurin

kallonta Amina tayi tare da yin 'dan murmushi kafin tace kuruciya kenan ai ko kece khadija ba abinda zakiyi illah hakuri ko dan albarkacin kina auren danta sannan ko ba komai nasan wata rana sai labari tayi duk yadda take so nasan wata rana in ance tayimin ba bazatayi ba

tabdijam wlh Aunty baki sani ba ne irin wadannan tsoffin zeyi wuya subar mutum ya sarara gasu da shegen tsawon rai yanzu wannan saita iya qara hamsin ko ma fiye nan gaba

dariya Amina tayi tace kai khadija to ya za'a gansu kuwa lokacin

ai qanqancewa sukeyi kiga sunata komawa kamar masu cutar tamowa qarshe sai dai kiga ana sasu a baro in kuma sunada gata ne zakiga ana turasu a keken nan na jarirai da suke koyon zama

kai khadija😂

Allah kuwa Aunty halan baki taba gani ba?

ah ah Allah bai taba gwadamin ba

to kuwa kiyi addu'a sosai dan ga alama nan a gidanki

dariya Amina tayi tana qoqarin mikewa tace ni dai ci abincin kafin in dawo musha hira

to tana dai bari ayi hirar ko?

ai na fada miki ke da sa'a kika zo gidan tunda har fada tayi wai laifinmu ne da bamu kirata munce zamu taho dake ba gashi yanzu munja mikk cin tazarce dan haka kada ki damu ke din da hajiya kun jone

murmushi dije tayi a ranta tana kissima yadda zata saita hajiya

Amina na fita dije ta jawo farantin gabanta din ta bude

wake da shinkafa ne mai da yaji ai kuwa dije dadi taji maimakon taji haushi dan ta dade marabinta da ci a ranta tace inba ma dai abin da izgili ba ai wake da shinkafa abin marmari ne dan dai kawai anyi hakan ne da mugunta

sai da taci ta koshi sannan tayi sallar isha'i tana tsaka da sallar taji an turo kofar dakin

au to ana nan ana gaida ubangiji kenan to Allah ya amsa ta nemi guri tazauna

saida dije ta gama addu'ointa kafin ta juyo tayi mamaki ganin hajiya zaune amma saita maze ta shiga gaisheta

cike da fara'a ta shiga amsawa kafin daga baya ta fara zubawa dije surutu ganin da dije tayi tasamu abokiyar yi yau yasata cire hijabin datayi sallah ta gyara zama

kallonta hajiya tayi kafin tace Allah me halitta kenan

yanzu ke wannan farin nske baya damunki ji beki fa waima da dare kenan ina ga rana

au dama fari yana damun mutum sai kace na Allah ya isa

eh mana kin ganki kuwa nifa inba idona ne yakemin gizo bahar wani yellow yellow naga kinayi ko ma dai harda shawara farin nan naki

ah ah ba shawara bace ai da kin lura da kyau da zakiga kwayayen lantarkin da aka jona min suna kawo wuta😠

rike baki tayi tare da nuna al'ajabi tace wuta kuma a jikin mutum yarinya?

eh mana ai zamani ne yazo da hakan ke kanki nasan da'a zamaninku akwai wannan fasahar to wlh da ke za'a fara gwadawa a kanki
Chapter 26 · 0% Book details