← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 59

Sashe 32

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ai bata karasa ba taji saukar wani shu'umin marin data rasa daga ina yazo bata gama tantancewa ba ta fulanin ta motsa jin ana neman sata jinyar dole aikuwa tayi kan mimi a sukwane cikin sa'a kuwa ta dami gashin kanta dayake kalba ce akayi mata da Attact iya qarfinta ta rike tare da cizgawa

wata kara mimi ta saki wadda tasa su kausar nufo dije da dukkan karfinta ta tunkuda mimi da kanta ya daki karamin center table din dake gurin aikuwa take kai ya fashe ganin jini yasa ta sakin wata karar a karo na biyu

kausar na ganin hakan tayo cikin dije yayin da humaira tayi gurin mimi data bare baki tana kuka tare da shafo jinin a hannunta wanda wannan shine karo na farko a rayuwarta data taba jin ciwo da jini haka

tattaro dukkan karfinta tayi itama suka kacame aikuwa nan dije ta nuna ita rainon kauye ce dan kuwa tuni ta samu lagon kausar kasancewar ita basu saba da irin wadan nan wahalhalunba da iyakar karfinta dije ta kama nonon kausar ta murde itama karar tayi nan ta shiga neman hanyar kwatar kai amma ina dije dan mugunta harda cije lebe takeyi jin da kausar tayi dije na shirin kasheta kuma ba mafita yasata gartsawa dije cizo a hannu ai kuwa jin zafin cizon yasa dije qara himma bata san lokacin data gwara kan kausar da plasman dake manne jikin t.v stand ba ji kakeyi kwararats ta sheqo kasa ta tsage

nan fa ihu ya hadu biyu ita kanta dijen daba damar kukan ne da tayi dan ta dan sha jiki su kuwa duk sun bude baki suna ihu humaira dataga abinda ya faru da wadanda suka fita tsageranci ai take jikinta ya hau bari dan dama duk burga ce sun fita kwaliti

sai yanzu hankalinta yakai ga bugun kofar da akeyi haggu da dama ma'ana dakin sajida da kuma kofar falon

duk ta rude ta rasa inda zata nufa ga ihun wadan nan na kwancen ita kuma dije tayi mata zuru masifa na cinta jira takeyi tasamu nama kawai

yanayinta ya kara tsorata humaira duk da tabi ta rude aikuwa nan ta fara kokarin guduwa dije ta rufa mata baya
tana fadin ai ba inda zaki dan uwarki yau ko ni ko ku badai kunce sai anyi yakin badar yau a gidan nan ba to sai munga karshen shi muga wakeda nasara nan ta yi cikinta da himma ganin hakan yasa humaira daukar duk wani abu data gani ta jefawa dije ita kuma tana gocewa wani yaje yasamu frame din dake manne a falon sai dai kaji rassss sun sheqo kasa

au to ai sai ki fadamin zakka kk son ku fitar shiyasa zakuyi mana barna a gidan duk da ban san nawa kk fasawa ba yayana ya siya ko ku kuka kawo 'yar uwarku dashi to bari na tayaki nan fa ta nufi dinning duk coolers din dake kai sai da ta dinga saita humaira dasu tana jifanta aikuwa kan kace me falo ya kacame da yayi kaca kaca

cikin zafi humaira tayo cikin dije bisa ga shawarar zuciyarta data bata akan cewa ta ci uban dije kawai yadda take lange langen nan suma su kausar rashin zuciyane yasa haka aikuwa tana zuwa dije tayi mata na 'yan wristelling ta kai mata wani wawan naushi amma fa bada hannunta ba da ludayin miyar da ita kanta humaira bata lura dashi ba ba shiri baki yayi tsartuwa aikuwa nan dije bata bata wata damar kuka ba sbd mugunta duk inda tasan saitin kashi ne saita buga harda goshi duk inda ta buga sai dai kaji yace kwalll ai kuwa saita saki dariya sbd zalunci gwiwar ta saita ta bada kwalll ai kuwa humaira ta bude dukkan muryarta tana ihu tana kiran wayyooo Aunty ki zo ki taimakemu wai bakuda imani ne bamai taimakon mu a hannun kinfi 'yan boko haram rashin imani ta fada tana me qara rushewa da kuka itako dije dariya ta shiga tana fadin muje zuwa mana ai yanzu aka fara ni yaseen ko rabin gajiya ban tashi yiba kawai muci gaba da kaftawa yau nayi muku alqawarin sai kunga kalar mazgar da baku taba gani ba

sajida da hankalinta ke mugun tashe ta kira habeeb yace mata yana kan hanya amma shuru gashi sai ihun 'yan uwanta take jiyowa wanda take addu'ar Allah yasa yarinyar bada mutanenta ta hada su ba suke caskala su dan tasan ita da an tabata sai sun kawo ziyara ita fargabarta ma abin ya tsaya iya wadanda suka jawo kar su ce a gidan zasu kwana yau an taba musu hantar su layin habeeb ta kuma kira nan ya shaida mata gashi nan shida naseer sun kusa zuwa tunawa tayi da spare keys din dake cikin lokarta nan ta shiga dubawa ta dauko na dakinta ta bude amma sai me ? sam takasa fitowa illah ziro kai datayi kadan batare da sun lura ba nan ta hango su kwance sunata wai wai tare da reto da jiki kamar suna takaraa makarantar allo ga dije nan kamar uwarsu tasa sun kama bakinsu da hannunsu amma fuskar nan tasu a kwabe sunata digar hawayen azaba

jin ana buga kofar ne sosai yasa sajida fitowa da kyar ta nufi kofar kamar ta tashi sama dan karma dije ta ankare da ita dan ita masifar yarinyar tsoro yake bata

dije ko tana lura da ita ta shareta dan ita kanta ta matsu a zo a rabata da wadannan kartin banzan a cewarta da bataga amfaninsu ba inda itace kamarsu ai aikin soja zata shiga dan jikinsu kalar wannan aikin ne amma sai gashi taga alama ko aikin office ma ba alamunsa anan

koda ta qarasa ta bude kofar taga ba key jiki dole ba yadda zatayi ta juyo falon kamar tasan yadda akayi nan ta shiga duba kan kujera ko kala batace ba kamar munafuka sim sim ta ganshi ta dauka ta bude kofar su ukune tsaye habeeb naseer da yusrah sai musa dake tsaye daga can bayansu wanda da za'ace arrrr yanzu zai sheka dan ya kudirarwa ransa baxai kuma shiga gidan nan ba matukar yaji ana sautin neman taimako

da sauri suka shigo inda sukayi cirko cirko ganin su mimi zaune suna reto da kawuna ga ciwuka ga falo daya hadu ya hade wadda ita kanta sajida sai yanzu ta lura da barnar da akayi

ya Allah habeeb ya fada kafin ya kalle su cikin bacin rai yace kaii uban mu ya faru haka naganku kamar kunyi Accident dubi yadda kuka mayarmin gida tamkar na mahaukata anya kunada hankali kuwa?

sai yanzu suka farga da shigowar su aikuwa da sauri suka rarrafa suka bude baki cikin kuka kausar tace wlh yaya ku gaggauta fita da wannan yarinyar a gidan nan dan wlh batada hankali wlh bakaken aljanu gareta da alama sannan suna sata hauka wlh yaya zata iya kashe ku wata rana

cikin rawar murya yusra tace to ku wane tsautsayi yakaiku fada da ita kuma ke Aunty sajida ai laifinki ne meyasa baki sanar dasu fada da aljani ba dadi

cikin bacin rai tace su basuda hankali ai daka fara fada ka kalli fuskar wanda kk yi dashi kasani in mutum ne in ma aljani ne kuma nace musu baruwana suka ki ji gashi ban sunjawa kansu ai an zuqe musu jini dan da ganin yadda suke yanzu sai an musu karin jini

to ku meya kaiku taba da transfomer ana ruwan sama ?cewar naseer

wlh kaddara kasan ance me rabon shan duka bayajin kwaba ni babban takai cina na ji yadda aka sauyanin halitta duk da ban kalli madubi ba amma dana shafa goshina wlh naji kamar ma ba fuskata ba dan sai naji kamar ta Dila

wlh in kince dila kinyiwa kanki zabe me kyau bakiga yadda kika koma ba sai kace fukar bahaguwar bakar rakuma cewar naseer daya fada yana kunshe dariyarsa

wayyo ni na shiga uku wayyo Allah yanzu ni dan banida gata babu wanda ya duba yadda nake ba wanda ya saurareni sai 'yan uwanku kuke ta tasu cewar dije data dora hannu aka ta baje baki tana ihu

wadda ihunta yayi dai dai da shigowar mamy wadda tashigo a sukwane jin ihun sakamakon kiranta da yusrah tayi a waya cikin tashin hankali lokacin da basu san abinda ke faruwa ba sai ihu da sukaji..........

*vote*
*comments*
*Alqalamin khady* ✍
[3/15, 11:07 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TAME GARI*

NA
khadija usman

3⃣1⃣

Ah ah wlh basai kin fasa ba ki tafi kawai duk lokacin da muka so ganinki ma zo ko? suka tambayi matan

eh wlh Allah ya tsare ya kiyaye hanya

Ameen ta fada jiki a sanyaye kamar wadda kwai ya fashewa taja qafa tana tafe tana waiwayensu mamy kuwa nata raka su da harara saitayi tafiya kadan sai ta tsaya su kuma sai kaji sunce ya akayi ?

saita ce kewar ku ce wlh ji nakeyi kamar in fasa tafiyar san ba yadda zanyi ne

aikuwa dole ki tafi tunda mamy ta bukaci hakan dan ba yadda za'ayi ta yanke hukunci ki ketare cewar habeeb

to banda abinka yaya ai bafa cewa nayi bazan je ba cewa fa nayi ina jin kewarku kamar in fasa tafiya

ke ni dayalla wuce muje kun tsayamin surutun banza cewar mamy dije na ji tana gani aka nausa mota aka nufi gidan daddy

*welcome back home dijeee*

*******

ba karamin jin dadi basira tayi na ganin dije ba aikuwa nan aka shiga hirar yaushe gamo danma jikin dije yayi tsami tana bukatar hutu dan haka bakin a mace yake

tun asubar fari mamy ta iso dakin dasu dije suke tace dije ta fito ita zatayi aikin gidan nan yanzu

ga mamakin mamy sai gani tayi dije tayi tsalle tare da fadin Allahu akhbar

kallonta tayi ta dan ja baya tare da fadin ke dan ubanki meye na jamin farkon kalmar kiran sallah ?

wallahi farin ciki ne mamy kai kedai Allah ya biyaki yayi miki duk abinda kk da niyyar yimin

ba amin ba dan ubanki kajimin shegiyar yarinya da muguwar addu'a ke kin san me nake shirin yi miki ne?
Chapter 32 · 0% Book details