← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 59

Sashe 39

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana jin kira na shigowa yasan itace ke kiransa dan taga missed calls dinsa,sai da kiran ya katse wani ya kara shigowa kafin ya mika hannu ya dauka amma saiya ga kiran mamy ne,dan haka da sauri yayi picking tare da sallama .

ko amsawa batayi ba ta fada mishi Sajida ba lafiya,

tambayarta yayi mike damunta tace mishi zazzabi ne me zafi yanzu yanzu ya kamata.

cewa yayi yana zuwa,dan haka ya mike ya fice ya shiga neman Haruna danya rakashi cikin gari yasamo mata magani.

Shi kanshi yayi mamakin ganin yanayin datake ciki,to kodai ciki gareta ya fada a zuciyarshi,daga wannan tunanin ya tsinci kanshi da tsantsar farin ciki wadda ya kasa boyewa har saida ya murmusa tare da shafo sumar kanshi,nan ya tasheta yasa tasha magani,bashi yabar gidan ba sai da yaga tasamu bacci,inda lura da yanayin sa yasa mamy ta fahimci ciwon dadi ne kenan dan haka ita ma ta kwantar da nata hankalin ta kwanta abinta duk suka fasa wankan.

**************

Washe gari ma da zazzabin ta tashi inda koda Dije tazo ta gaishesu duk kin amsawa sukayi, duk yana cikin plan din mamy wadda take ganin in suka nunawa dije haka a gaban iyayenta zasu fahimci komai su hanata komawa su yadda kwallon mangwaro su huta da kuda.

Itako Dije nunawa tayiabin bai dameta ba ta dinga dan waskewa,da dama ita ko basuyi haka ba batada niyyar komawa yanzu dan haka ta barsu subata harbin iska,

******

kwanansu biyu a garin mamy ta ballo da ruwa inda sunje gidan maigari gaba dayansu ta tasa daddy a gaba tace sai sun koma gida ita bazata iya ci gaba da zama a wanban kauyen nasu ba,babu abinda ya kara bawa daddy mamaki da haushi illa tattaro sajida da yusra da mamy tayi kuma babu kunya suka nuna masa suma. sun gajiba zasu iya zama a kauyen ba har kwanakin da sukayi niyya su cika ba.

sawa yayi aka kira masa su Habeeb inda a gabansu yace matan su maimaita abinda suka ce,ai kuwa ba kunya sajida ta zage ta dinga rattaba bayanin cin fuska harda cewa wai mayu sun kamata daga zuwa,ganin da Habeeb yayi ta zake dayawa tana ta cin mutuncin asalinshi yasa ya daka mata tsawa ransa matukar bace.

Daddy ne ya daga masa hannu alamun ya kyaleta,aikuwa taci gaba,har saida takai inda take son tsayawa kafin ta tsaya.

Tana idarwa mamy ta amshe nan itama tayi me isarta bawanda ya tamka,harta gaji tayi shuru.

Itako yusra ta kanta takeyi dan laulayin da takeyi shiyasa tayi shuru bata ce komai ba ta tsaya tan sauraren su itadai kawai ta masu ta ganta a gida.

murmushin takaici Daddy yayi kafin ya kalli mamy yace,

"yanzu Karima duk wannan cin mutuncin da kikeyi saboda kawai kinzo kauye ne?

ai bawai batun nazo kauye bane,ni fa a rayuwata natsani kauye kai ni bama kauye ba duk wani jinin talaka wallahi,saboda shi talaka kullum burinshi yaga mai kudi ya wulakanta saboda tsananin hassada da......

ya isa haka!! daddy ya dakatae da ita

Amma ai kin san ko ni wanene kika aureni kuma kin san asalin inda dangina suke ko?

Ai kai ka daina danganta kanka da wadan nan mutanen dan kai Allah yayi maka sutura,inba ma basu barka haka ba waye zai samu ya kubuta daga wannan masifar ta zaman kauye ta dawo kuma wai ko da sunan ziyara.

Hmmmm!!! hakane naji nakuma gode sosai,amma kisani wallahi ban yadda ki koma gidaba dukanku har sai kwanakin dana dibar mana ya cika.

Gangan ma kenan!! ai wallahi bazan kara yadda na kwana da 'ya'yan mutane ba su macemun anan in shiga uku,tafiya kam kamar da kasa,kai da aka binne cibiyarka anan ka zauna har kwanakin su cika saika dawo,Dan haka ku tashi mu tafi tun kafin rana tayi mana.

Mikewa sukayi duka suka nufi kofar fita Daddy baiko ce musu kala ba.

Har sun kai bakin kofa suka Tsinkayi muryar Habeeb ya kira sunan Sajida yace,

Indai nine mijinki ban yadda kibar garin nan batare da izinina ba kuma sai kwanakin da mukayi niyya sun cika.

shima Naseer haka ya fadawa yusrah.

To ni a matsayina na uwarku na basu izinin su wuce mu tafi in kuma ban isa ba sai inji labari,kafin fa juya ta kalli su sajida tace,

In kuma a cikinku akwai mai zama banyiwa kowa dole ba kuna iya zamanku.

Ai wallahi mamh in kin ganni a lahira kaini akayi cewar Sajida,dan ni da kara zuwa wannan kauyen har abada dan haka muje kawai mamy karsu karasa kasheni.

suna gab da fita daddy yace,kin kyauta Karima amma wannan lokackn zan nuna miki ko ni waye kuje Allah ya kiyaye hanya amma wallahi zan shayar dake mamakin da baki taba tsammani ba........

*vote*
*comments*
*with*
*Alkalamin khady*
[3/15, 11:26 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*AWESOME WRITER'S ASSO..*🇳
(palace of excitation n'd pleasant writer's)

*TAME GARI*

NA
khadeeja usman

3⃣9⃣

Zaune yake gaban baba maigari yana yi masa bayani,inda baba malam din ya tattara nutsuwarsa gaba daya ga zancen dan nasa,tare da tunani mai zurfi akan abinda yake shirin aikatawa,dan haka yayi shuru yana saurarensa har saida yakai aya,kafin ya sauke goron numfashi yayi jim kadan yana nazari.

Tabbas maganar dansa gaskiya ce,gaba ake ji ba baya ba,domin karima tana so matuka ta tarwatsa musu zumunci yaransu masu tasowa,gashi maganganun ta sunyi tsauri,bata jin kunyar nuna kyamar ko waye indai dan kauye ne ko talaka,yayi tunanin abin zai tsaya iya kanta ne sai gashi tasa harda surukanta wanda suma sun dauki wannan mummunar akidar ta kin mutanen kauye da kyamar talaka,tabbas inya barta wannan abin yayi tasiri,"toh fa tabarbarewar zumunci za'a samu a zuriyarsa",wadda baya fatan hakan.

maganar daddy ce ta fargar dashi ga tunanin daya tafi,inda daddy ke cewa,inka amince baba ina son ayi abinda na fada abi shawarata dan wannan lokacin nayi rantsuwa wallahi saina nuna mata kalata da bata taba gani ba.

Ka kara hakuri khamis, dan dukka rayuwar hakuri akeyi musamman sha'anin mata,sai dai ni kaina wannan lokacin abinda tayi ya taba zuciyata,amma hukuncin daka yanke kana ganin baiyi tsauri ba akan su?

Baba ai wannan hukuncin shine dai- dai dasu,shine zai sa su shiga taitayinsu.

To kayi shawara da yaran naka ko?

Banyi ba baba!

Amma nasan babu wanda zaiyi mun musu a cikinsu.

To shikenan!!

mu bari zuwa anjima mu tattauna da sauran 'yan uwanka sai muji yadda za'ayi ko?

Toh baba!! Allah yasaka da alkhairi.

Ameen! Allah yayi muku albarka baki daya.

Ameen

nan yayi masa sallama ya fice dan gaisawa da jama'ar dake jiransa a waje.

su kuwa su mamy,ba wanda suka wa sallama ko kallon arziki haka suka hada kayansu suka tafi bayan sun gama cin mutunci da yadda maganganu wai an kama su za'a cinye su an kawo su garken mayu.
_____*********______

Zaune take gefen gadon Innah suna hira ita da Zainab diyar wajen baba bala kanin mahaifin ta,inda zainab din keta yaba kyan da Dije tayi tare da sanar da ita irin surutun datake sha a kauyen na wai taki aure ta tsaya karatun boko.

Dagowa Dije tayi ta kalleta kafin tace,

"kin san Allah ne yaso mutanen garin nan ban karasa wayo na anan ba", da wallahi duk saina sa su ciwon baki,dan kut.....nafasa,

Ah ah!! da kin karasa ai.

Ai na auna na auno na kuma hango ba amfanin karasawar ne,amma inba gulma da shegen tsegumi irin na mutanen kauye ba,meye laifin karatun boko,kuma ma duka nawa muke da har za'a damu dan bamuyi aure ba,su je su ga inda uwayen mata suke,wadana suke cikin jin dadi ga nera ta zauna,gasu bul-bul dasu kamar kajin gidan gona,amma ba mashin shini,sun gama cika har sun fashe.

kamar dai matar yaya Habeebu kenan ko?

dan ni nayi mamakin da aka ce wai itace amaryar sa.

Dariya Dije tayi kafin tace,

To me kika gani game da wannan,badan kar kice nayi miki karya ba wallahi da sai ince miki akwai iyayenta a kasa.

kinga basai kin karasa ba dan wallahi nasan halinki Dije da karyar masifa,duk uwar data haifi kamar wannan.matar ai ta kusa cizon kasa.

kinga fa abinda ke hadani dake da can kenan shiyasa nake kilarki,dan karyata ni da kikeyi,sai ki bari kije ki ganewa idonki wata rana.

Ah ah ni wallahi bada ni ba,kina kallon cin mutuncin da shegun nan sukayi mana,ai naga kokarin zamanki tare dasu da banga alamun targade ko karaya a tare dake ba,saima wani fresh da kikayi.

hmmmm!! kedai abar kaza cikin gashinta,kin san dai halin Dije kowa yayi mata saita rama,to hakan ce ta dinga faruwa shiyasa nasami sa'ida,amma wallahi da in kun ganni sai kun dauka a jejin sambisa nayi rayuwa.

Shegiya!! kice kinji abar,

hmm kedai kawai mubar maganar,bari intashi mu wuce kawai kar rana tayi.

A tsakar gida suka iske Innah tana gyaran shinkafa,inda sukayi mata sallama suka fice ta bisu da Addu'ar Allah ya tsare a kuma gaishe mata ita.

****

wannan karon ma kamar wancan lokacin yara baibaye su sukayi har suka sallami mai mashin suka nufi kofar gidan,

da sallama suka shiga inda suka iske Hansai jingim zaune tana bakacen geron da daalama surfawa tayi.

har wani murgudewa tayi garin amsa sallamar da kuma ido biyu da tayi da jami'ar tsaronsu wato Dije.

cikin sauri bakinta har yana hardewa ta shiga kwadawa Inna Haule kira,aikuwa sai gata nan itama a sukwane jin kiran da Hansai ke mata,tana zazzaga masifa da ya zuwa yanzu ita ke mulkin dan haka ta taho tana fadin,"ke wai lafiya kike ta kwalamin kira kamar naci bashi",

Turus tayi ganin jami'ar tsaron su tsaye ta harde hannuwa.

washe baki ta shiga yi inda ta fara fadin,

marhaban lale! yau kice kun kewayo sannunku da zuwa,ai ko yaushe munata tsimayi da sa idon yaushe zaku bullo ashe zuwan bazata kukeyi,kai amma munji dadin ziyarar nan wallahi,ke Hansai maza tashi ki dauko musu tabarma mana da ruwan sha,

Ganin yadda ta yunkura da kyar dan ta mike,Dije a ranta ta furta Astagafirullah!!! Allah mai halittar bawa yanda ya so yanzu kalli ko hannun ta kawai yayi ni gaba daya,ganin kafin ta mike din ma wani sabon jidalin ne yasa Dije fadin,

Ina ita Dayar abokiya zaman tata take?
Chapter 39 · 0% Book details