← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 59

Sashe 57

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda Dije taji ya Fadi haka ta ramfo shi,wato irin malaman Nan ne masu fakewa da rukiya suna cutar da yaran mutane,to ko yau zakasan ka kawo kanka,Dan lamarin a kanka zai Kare,ta fada cikin zuciyarta.Shikuwa malam buba,tuni ya juya ga jakarshi ya hau lalubo hankachif din dazai Shaka Mata,daukoshi yayi tare da sakin murmushi sannan ya dauko wani ruwa a 'yar Karamar kwalba,Wanda zai Shaka Mata ta farfado bayan ya Gama biyan bukatarshi....sai dai me?Yana juyowa yaga Dije tsaye rike da kugu tanata rarraba ido,yadda yaga tana zare idon yadan tsorata,Amma yasan duk wannan abinda takeyi Daya samu nasarar Shaka Mata,to batada katabus,nufota yafara yi,amma saiyaga itama tana matsoshi,hakan yasa yaja ya tsaya zuciyarshi na bugawa kadan kadan,Amma ya dake,gani yayi gadan-gadan take tunkaroshi tana yake hakora tare da dariya kyal-kyal-kyal,jikinsa ne yadan Fara rawa kadan,itako Dije abinda take so kenan,aikuwa saita birkice tana biyoshi shikuwa ya shiga ja baya,aikuwa sai gani yayi Dije ta kwasa da gudu ta Fara zagaya falon,inda tayiwa inda ta ajiye makaman yakinta tsinke,muciya ta dauko tare da wannan wukar,ganin ta nufo shi da gaske,yasashi wage baki ya shiga karanta ayatul kursiyyu da karfi,ji yayi tayi çaraf ta cafke taci gaba da karantawa,aikuwa guri ya Kara kacamewa,sosai jikinsa yahau Bari,itako Dije Kara lankwashe baki tayi tare da fadin,"bakai malami Mai fitar da aljanu ba! To yau kaina zan fitar maka da naka,wato ka fake da Allah kana zaluntar iyaye kana lalata musu yara ko?,to daga yau bazaka Kuma ba,Dan billen danayi niyar yi musu Kai zanyiwa shi.
Zubewa yayi a kasa bisa gwiwoyinsa,Yana fadin,"Dan girman Allah kiyi hakuri,wallahi ban San cewa ku gawurtattu bane ba da ko kusa bazan Fara zuwa ba".

"Karya kakeyi ka sani,tunda har kasan cewa mu 'yan daba ne,to kawai gara na farde cikinka yau musha jini,sannan muyi soye da namanka".

"Dan girman Allah kiyi hakuri, wallahi ba laifina bane Hajiya ce ta kirani".

"Ai nasan ita ta kiraka,Amma meyasa data kirakan bakace bazaka zoba,to ka sani,yau din Nan basai gobe ba zan kaddamar maka,Dan saina rabaka da duk wata gaba ta jikinka".

Ba Kuka yake ba,amma yanayin dayake ciki garama ace kukan yakeyi,Dan haka ya shiga rokon Dije,magiya sosai ya shiga yi Mata ita kuwa tana Kara fada Masa nau'ikan azabar da zatayi Masa,Saida taga ya Fara fitar da kwalla,sannan ta bashi umarnin ya mike tsaye,Yana mikewa tace yayi rawa,tsayawa yayi Yana tunanin ta yadda zai Fara,Dan marabinshi da yin rawa tun Yana yaro,Dan haka yanzu baiko San ta Ina zai Fara ba, kasancewar ya jima Yana rokonta harya hada zufa,shiyasa ya cire hularshi ya ajiye gefe,aikuwa Dije tayi ido hudu da rantal din kansa,take muguntar ta Kara motsawa,Yana tsaka da tunanin taya zai Fara rawa,gara kawai ya saita hanya ya fece,aikuwa sai ji yayi kwallllll akansa,Dije ta kwala Masa muciya akansa,ji yayi dukan ya ratsa dukkan jikinshi Dan ji yayi kanshi ma kamar ba'a jikinshi yake ba,Yana so yayi ihu ba halin yi,saboda Kar a jiyo malam na kuka.

"Zakayi rawar ko bazaka yiba"?

"Zanyi wallahi,zanyi" ya fada Yana me gyara babbar rigarshi,Nan ya shiga rawa babu kida,haka yaita tikar tawa abin ba fasali,itako Dije Dan dariya harda faduwa kasa.

********
Jin shuru yasa kowa tunanin ko lfy?, Shikuwa Habeeb Sam hankalinshi ya kasa kwanciya,Dan shi bai yadda ace malami ya nemi a barshi ya kebance da Mara lfy shi kadai ba,Dan haka kawai ya nufi kofar,yanaji mamy na kiranshi Amma yayi shuru har Saida ya bude kofar,dai dai malam yayi wata irin malkwada da Dije tasashi yayi,Wai a cewarta rawar 'yan Indiya ce,a indiyan ma 'yan Tamil Nadu keyi irinta......

*Alkalamin khady* ✍*AWESOME WRITER'S ASSO..*
(palace of excitation n'd pleasant writer's)

*TAME GARI*

NA
KHADEEJA USMAN

6⃣6⃣

Sakin baki yayi ya tsaya Yana kallon ikon Allah,yayin da Da malam ya takarkare Yana tikar rawa Yana wani lankwashewa,Sam yama Manta da wata Dije agun ya shagala da kallonsa yanata malkwaya gashi Kuma Yana kuka,yana tsaka da yin rawar kawai yaga ya zube tare da fashewa da kuka,sannan ya kalli Dije yace,"wallahi sai dai in kasheni zakuyi ku kasheni Dan na gaji,Ni ba Dan oroso ba,Amma an maidani Dan cashiya,wallahi na gaji,Dan girman Allah kiyi hakuri wallahi na tuba,ban San cewa ku hatsabibai bane,da ba abinda zai sa da aka aikamin goron gayyata inzo",ya karasa maganar Yana fyaçe majina da gefen rigarshi.

Wani juyi Dije tayi,ta dira gaban malam,Wanda yasa Habeeb antayawa a 360 ya Isa gareta ya rikota,fadawa tayi jikinsa,inda ta rufe idonta da suketa faman Marmar,Wanda badan Habeeb a rude yake ba,daya fuskanci halin da take ciki na likimo,Amma shi kanshi a tsorace yake,Dan jikinshi Banda rawa ba abinda yakeyi,Dan In ba Dan Kar ace yayi karya ba, da Saiya ce wani irin nauyi yaji ta Kara,(Niko nace Kai Habeeb Banda zuki ta malle😂),yasan hakan Bai rasa nasaba da aljanun dake kanta a yanzu.

Shikuwa malam ganin Dije ta zube,aikuwa ya suri jakarsa ya antaya a guje,su mamy dake labe bakin kofa suna son shiga suna Jin tsoro,sai ji sukayi rakacam,malam yayi ciki dasu,kafin suyi wani yunkuri suka tsinkayi muryar malam Yana cewa,"kada kuga laifina wallahi aljanun 'yan daba ne,da 'yan rawar solo,kudai kuyi ta kanku,nikam nayi Nan.mamy ce tayi kokarin mikewa,tare da shafa gefen bakinta inda taji Yana Dan Mata zafi,jini ta lakato aikuwa ta maida kallonta ga Sauran,ganin goshin yusra tayi alamar hakora gashi shima ya dan fashe,cikin hasala tace"ke Kuma waya cijeki?

"Mamy ba kece Kika kafamin hakora ba".

Dafe kirji tayi tare da fadin,"Ni Kuma Yusrah?kada kimin sharri,kinaji malam yace aljanun 'yan daba ne,waya sani ko su suka Miki aik.....Bata karasa ba,ta hangi Sajida da Laila ana kiciniyar tashi,Dan Suma ragas sukayi,suka Fadi,cikin rashin sa'a Sajida ta fada kan Laila,gashi su Sajida Abu ba kadan ba🙊,ita Laila dukta kuje,itako Sajida tana kyautata zaton tayi targade a yatsanta na kafa,Dan taji lokacin da yayi Kara,hakan yasa ta gagara tashi daga kan Laila,wadda nauyi ya isheta take ta kokarin tunkudeta,ganin hakan dasu mamy sukayi,yasa su karasawa suka hadu ita da yusrah suka janye Sajida da kyar,itako Zainab da Naseer suna gefe,Banda dariya ba abinda sukeyi,ganin su mamy sunja gefe sun tsaya sunata haki,cikin hasala mamy ta juyo tace," ku Kuma uwar me kukeyiwa Dariya?

Naseer ne cikin Kara guntse dariyarsa yace,"babu komai mamy kawai dai dariyar ce tazo Mana lokaci daya".

"Eh lallai nagani ai,Kuma Naga rashin mutunci irin na riqaqqun aljanu,wato abinma harda Nuna bambamci,da sanayya,Kai da suka San kana auren irin godiyar tasu,wato sai suka rabu da Kai da matarka,da Suka rarako malam shine mu suka hada damu,to wallahi ko zasu daddatsani Allah ya isanmu bamu yafe ba"..... zata Kara magana yusra ta toshe Mata baki,tana fadin,"Bari mamy,kada ki Kara jawo Mana jaraba,bamu fita daga wata ba mu afka wata,Nidai ki cireni a Allah ya isan Dan na Dade da yafewa".

Ganin tsayiwar bazata fisshesu ba yasasu Kara sadadawa,suka Dan tura kofar,Dan suga meke wakana a ciki,suna lekawa suka hango Dije kwance,shame-shame a jikin Habeeb,yanata tofa mata addu'a,ganin alamun kamar aljanun sun sauka yasa suka Dan Fara shiga a layi kamar masu neman aiki🙉.

Ganin barnar da Dije tayi yasa mamy fadin,"kan ubancan,ai wallahi wadannan sunci uwar 'yan daba, directly a kirasu da 'yan ta'adda wannan barna haka? Sai kace dangin bera lallai dole mu dauki matakan tsaro a gidan Nan Dan abin Naga ba sauki.Duk abinda sukeyi Dije na jinsu,Jin addu'ar ta Gama ratsata a cewarta,yasa tayin wata katuwar Mika da doguwar hamma,[8/24, 11:21 AM] +234 814 016 5919: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*AWESOME WRITER'S ASSO...*
(Palace of excitation n'd pleasant writer's)

*TAME GARI*

Na
Khadeeja Usman

6⃣7⃣

Dukansu zabura sukayi tare da Kara ja baya,ganin tana kokarin mikewa, harta mike tare da bin falon da kallo ita a zuwan Bata San meya faru ba.ganin tana ta raba idanu yasa Habeeb fadin,"sannu kinji lovely sis".

Can kasan makoshi ta furta yauwa,sannan ta shiga tambayar meya faru? Bawanda ya Bata amsa illah wani kallon tsoro data ga suna Binta dashi,hakan yasa a zuciyarta ta furta,lallaia yau da malamin gaske aka kawomin da karyata ta Kare,duk da Banga wannan tsoron a idanunsu ba,yanzu kuwa ji yadda suke want girmama Ni,kamar cikinsu duk nice babba!tana tsaka da tunanin taji ya riko hannunta,tare da fadin,"zo muje kiyi wanka ki gasa jikinki,fatan dai ba inda Kika ji rauni ko?.

Gyada mishi Kai tayi tare da kwabe fuska,cikin salon shagwaba tace,"banji ciwo ba my lovely bro sai dai jikina dakemin ciwo,sannan kaina ma musamman keyata da Kuma goshi na"ta karasa maganar tana matsar ido,duk a salonta nason matso hawaye sai dai sunki zuwa.

"Ya Salam! Ya furta tare da cewa"to yanzu ya za'ayi kenan? Asibiti zamu wuce in dubaki?

"Ah ah,Nidai ka daukeni ta fada tana Kara narkewa.

Hakan kuwa akayi,ya shiga nannade hannun rigarshi kamar zaiyi dambe da kato ya sunkuceta,yayin da yabar mutanen Falon da kallon juna.Naseer na ganin hakan yasa Kai ya fice Zainab ta Mara Mai baya,ganin hakan yasa itama yusrah tabi mijinta Nan akabar mamy tsaye dasu Sajida,tsaki mamy tayi itama tasa Kai ta fice Dan tsananin takaicin data Shaka inta tsaya tace zatayi magana,to fa kuka zatayi.Tana fita Laila ta kalli sajida da kunajjen goshi tace,

"Gaskiya kawata bazan Kara zuwa gidanki ba,Dan na fuskanci ajali ke kirana Inna sake na amsa Kira na uku, wannan wace irin jarababbiyar yarinya ce,ko ince hatsabibiya,Nidai shawarar da zan baki,kawai ki rungumi kaddara,ki zauna da mijinki da ita kanta kishiya ki lfy,kowa ya iya biya allonsa ai Saiya wanke,Nidai Kinga tafiya ta Dan wlh ban sayu ba baza'a nakasa Ni a banza ba,asa na Kara yin kwantai,ko kafin Sajida ta ankare har takai bakin kofa,hakan yasa tayi saurin Binta danta cimmata,Amma ko kafin takai ga cimmata harta fice,hakan yasata dafe kanta,tare da laluben gurin zama ta zauna tare da kallon dakin taga yadda Dije ta haukata Mata shi, sannan ga muguwar barnar da tayi Mata,tabbas dole ta nemawa kanta mafita,dolene taje gida gun mummy ta Bata shawara.

Ita kuwa Dije suna shiga,Bai zame ko Ina da ita ba sai toilet,ruwan dumi ya hada Mata sannan yace tayi wankan Yana zuwa,ba musu kuwa tace dashi to,Dan gara Daya fita din,saboda duk sanda yace suyi wanka tare,wata kunyarshi takeji.
Chapter 57 · 0% Book details