← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 59

Sashe 27

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ah ah wallahi daina jamin jafa'i tunda Allah ya tseratar dani oh ni hauwa'u yanzu har takai ga bature yayo wayar da za'a jona jikin mutum to meye amfaninta

ga amfaninta nan kin gani irinku masu gani suki kyalewa yake haskawa hanya yanzu ba gashi har kinga yadda fatata take haske ba

uhmmm lallai lamarin babba ne ta fada tana me rike haba

itako dije kuluwa tayi cewar da tayi farinta da kuma shawara ke damunta shiyasa ta matsu ta tashi ta tafi ganin taki tafiya saima qara malkwado wani zancen takeyi yasa dije miqewa ta shiga toilet batare datace da ita ko kala ba

wanka tayo ta fito daure da towel a jikinta

aikuwa caraf sai ji tayi tace oh ni 'yasu ke ko wannan yarinyar kina cin abinci kuwa ? ji kashin wuya kamar a zuba tiyar hatsi

ai in kinji ci daya ma kenan ni ko ke cin abinci wannan kashin wuyan nawa da kika gani wani sirri ne bari ma in fada miki daya a ciki ko wanka da kikaga nayi yanzu bada sabulu nayi ba dan ni sabulu na najikina

😳 jikinki kamar ya?

ai sbd ramar tawa da tayi yawa wata rana ina wanka lokacin an siyo mana wani sabulun wanka girmansa yakai kwanan sha to shine fa ina cikin wanka dashi na nemeshi na rasa nayita nema ban gani ba hae na haqura nace bari nayi da ruwa kawai ina zuba ruwan naga kumfa na tashi shine fa na fara lalube koda na duba sai naga ashe lokacin da nake murzawa ya subuce ya fada cikin kashin wutan nan nawa da kika magantu akan shi to da nayi niyyar in dauko shi kawai sai nace bari in barshi na huta idan na tashi yin wanka ba saina sha wahalar murza sabulu ba

qarya kikeyi dan uwarki 🤣🤣🤣

taji hajiya ta fada

😂😂😂

*managed pls*

*Alqalamin khady* ✍
[3/15, 6:31 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TA ME GARI*

NA
khadija usman

2⃣6⃣

*ina jinjina gareku khadija fans novels 1,2,da kuma 3 tare da tame gari fans da kuma hausa novel 1,2,3 da zama na amana 2 Facebook gaskiya na yaba sosai da comments dinku ina kuma godiya da addu'arku gareni kamar yadda kukemin kuma Allah ya biya muku bukatunku*

*bazan manta daku ba kuna raina kuma ina ganin comments dinku gaskiya ina godiya Allah yabar kauna*

*jattako novels fns*
*sadnaf novels fns*
*zauren mai dambu group*
*Hikayar marubuta*
*online writters groups*
*Arewa novels fans*
*da duk wadanda ban fade su ba suna raina wlh ina kuma mugu mugun ji da ku*

ah abin harda zagi kuma hajiya babba

ai dole in zage ki ke yanzu inba kin rainan wayo ba ta yaya zaki cemin wai sabulu ya bace a jikinki ko da dan mitsili ne bare kuma girman kwanon sha anya ma kuwa kinsan kwanon sha kuwa?

a haifeni a kauye kice ban san kwanon sha ba hajiya ni ko na sanshi kawai ki yadda da maganar da na fada miki

na rantse da Allah bazan yadda ba dan ko'a tarihi ban taba jin makamancin abinda kk fadamin ba sai kace sabulun aljanu

*yauwa anzo wurin dije ta fada a zuciyarta*

au to wai da ke kin dauka sabulun na mutane ne?

to amma ai ke kikace wanda ake siyo muku na kuwa san babanki ne ke siyowa ko kuma ai mutum ne shi ko kuwa kina son kicemin yasan dandalin aljanu acan ya siyo muku

to da nace miki ana siyo mana ai bakiji nace miki ga wanda ya siyo ba ko?

eh kuma fa hakane amma ke inba karyar jaraba ba a ina kikaga aljanun da har zasu siya miki sabulu

murmushi dije tayi kafin ta nufi kofa ta murza mata key ta dawo ta rufo toilet ma sannan ta fara leqe leqe kamar munafuka

hajiya ta bita da kallo kafin tace ke wai uwar me kk leqawa haka sai zagaya ni kk yi kamar kin kama akuyar mayu

shiiiiii dije ta dora hannunta a saman bakinta ina zuwa kedai

saida ta gama 'yan dube dubenta kafin ta kalli hajiya tace wani sirri zan fada miki bana son kowa yaji shiyasa

sirri kuma?

wane irin sirri duk ke 'yar nan duk duniya ki rasa abokin da zakiyi sirri dashi sai ni anya ba yankani kike shirin yi ba kuwa dan ni wlh inda abinda nake tsoro yanzu bai wuce mutuwa ba in kin san abinda zaki aikata min kenan gara ki sanar dani dan manzo

kai hajiya wlh kin fiya tsoro to dama maganar da kk takalo ce ta Aljanu kin ganni nan to inada su sunkai miliyan daya a kaina

innalillahi wa'innailaihir raji'un miliyan daya fa kika ce ?to ni dai ko a mazahabar jama'u ban taba jin kan mutum ya dau Aljani fiye da dari ba daya ba shima cikon na darin danna mutuwa ne shiyasa amma ke kice har miliyan daya sai dai in kece aljanar da kanta

to Alhmdllh tunda kin fahimta shikenan

na fahimci me ?ba dai da gaske ke din aljanar bace?

eh ah'ah

rabi mutum rabi aljan nake

😳ke 'yar nan fadamin gaskiya in san abinyi tun wuri

ai gaskiyar kenan abinda yasa ma kikaga na tsaya haka sbd naga yadda kika karbeni ni shiyasa ni bana cutarwa da kike ganina ina rayuwata ne cikin bil'adama amma ina azabtar da duk wanda yake kuntatawa jama'a su kuwa masu shiga tsakanin masoya ko ma'aurata kashe su nakeyi gaba daya masu gani ba kyalewa kuwa kamar masu tanka halittata su kam bakin nake murgudewa in tsiyayar da idanunsu ta yadda bazasu moru ba sannan in.........

wayooo na shiga uku hajiya ta fada da karfi

yusuf da Amina da tun dazu suka zo da niyyar susha hira da dije suna dab da shiga suka tsinkayi hirar hajiya da dije akan sabulu suka tsaya suji yadda zata kaya ai tunda sukaji dije tacewa hajiya ita aljana mutum.ce yusuf ya tuna da yadda naseer ya basu labari dije tayi musu aikuwa nan ya kama dariya Amina ta kalleshi kasa kasa take tambayarsa

janta falo yayi ya fara bata labari kafin yace nasan ta fuskanci halin da muke ciki shiyasa ta bullo mata ta wannan hanyar

marairaice fuska Amina tayi kamar zatayi kuka tace haba Abban Anwar baka tunanin hakan ya cutar da ita kaga fa tsohuwa ce in jininta ya hau fa?

hakanma bazai faru ba nidai kawai fatana Allah yasa wannan yarinyar ta zama silar shiryuwar hajiya ta barmu mu zauna lfy kinga ni tashi mu zaga ta bayan window musha kallo kinji my choice

jiki ba kwari ta mike ya kalleta yace haba mana ki saki jikinki pls kin san dai hajiya mahaifiyata ce bazan so abinda zai cutar da ita ba ko nasan halin yarinyar a sai dai ta firgitata kamar yadda ta firgita wadancan kartin tunawa tayi da labarin daya bata aikuwa ta kama dariya suna tsaka da haka suka jiyo ihun hajiya da gudu suka fita suka zaga ta window suka danyi slide dinsa kadan suka kama kallo

ni fa ki daina min ihu me nayi miki ?

kinga dan Allah yake muminar aljana kiyi haquri daga ganinki hwlh anga me afuwa wlh ban aikata ba duk abinda kika ga inayi ciwon sanyi ne yake tabani badan ma kar ince ki tambayi yusuf ba nasan bai sani ba da nace ki tambayeshi to tun ina budurwa na hadu da matsalar sanyin kwakwalwa inya bugani sai inta abu irin na marasa hankali ni dama tunda na ganki nasanke ba mutum bace amma da naga kuna yanayi da su habibu saina yadda ashe ke mutum aljan ce nasan suma basu sani ba amma ina rokonki da kada ki kasheni inada marayu kinga ni ke kula dasu gashi......

to wai laifin me kikayine da zan kashe ki?

nasan nayi kuma kema nasan kin sani kawai kina son kiyimin kisan rashin imani ne bayan kin murgudemin baki kin tsiyayarmin da idanu ki tausayamin ki duba tsufacda furfurata ki duba qananun yarana

au har yanzu kina haihuwa dama?

ah ah yusufa da farida mana in an hada da irin shekarunki ai kinga su jarirai ne ko?

hakane ina zuwa

kaya ta ciro tasa dan sanyi takeji kafin ta dawo ta zauna akan bedside drower ta dora data kan daya

kafin tace hajiya

cike da rawar baki ta amsa ya zuwa yanzu tayi zaman dirshan bisa tiles

na'am ranki ya dade me haskrn sallah dan naga ke din musulma ce ko a cikin aljanun kinada imani bakya wasa da ibada

duk naji yanzu dai ki fadamin dalilinki na hana yaranki sakewa da iyalansa kika zo kika takura musu kika......

kinga duk basai kin fada ba nasan kin sansu wlh sharrin ciwon sanhi ne kamar yadda na fada miki amma ina nan ina neman magani

oh kenan shi kesa kike aikata abinda kikeyi ?

sosaima kuwa ni tsorona ma kada yasa in aikata kisan kai gara in nemi magani tunda wuri

ai indai magani ne kin gama samu dan ni har maganin dayafi nashi ma ina bayarwa

cikin hajiya ne yace quuuuuuu cikin sauri ta yamutsa fuska tace ah ah bama sai kin bayar ba dayake na karbi wani ina kan aiki dashi yau ma wa'adin zai cika nasan gobe na warke

to shikenan naji amma yanzu dole ki karbi hukuncinki na yin katsalan dan da tanka halittar Allah da kuma shiga shirgin daba naki ba

haba yallabiya kiyi haquri sharrin shaidan ne da kuma....

ganin da dije tayi duk hajiya ta hada zufa duk da sanyin A.C dake dakin ga kuma fanka saita bata tausayi dan haka ta rage abinda tayi niyyar yimata sbd gudun kada taje jinin tsohuwa ya hau ta shiga uku garin gyara ayi barna

shikenannaji tunda kin bada haquri kuma kin smu maganin cutar dake damunki ba matsala zan kyaleki amma daga yau kullum da dare zan dinga kwana gidan nan sannan da rana zan ding zuwa zagaye batare da kowa yasani ba inga halin da ake ciki idan naga baki warke ba sai in dora da nawa maganin

wlh nama sn zan warke

sannan kada ki sake inji in fadawa kowa ni ba cikakkiyar mutum bace dan ba wanda yasani
Chapter 27 · 0% Book details