← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 59

Sashe 40

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah sarki!! Ai sun tafi neman kudi ita da mijinta yanzu haka suna legas,tun bayan haihuwarta,

Allah sarki!

ashe harta haihu kenan?

eh tasamu diyarta mace ansa mata suna Hadiza.

washe baki Dije tayi cikin nuna farin ciki tace kai amma Allah ya raya,yaushe zasu dawo?

ai basu jima da tafiya ba dan dama da Hansai ya fara tafiya daga baya ya dawo da ita data cika kwanakin ta saiya dauki Hafsy din.

nan Dije ta kara sabin sharhi da sabbin dokoki kafin tayi musu sallama suka ce zasu koma

har kaji madu rai Inna haule tasa aka kama guda biyu d sauran tsarabun kauye ta bawa su Dije a cewarta da ta fada komar 'yan sanda gara tayi kyautar shiga daka kayi kuka.

**************

Yau jumma'a dan haka tun safe maigari ya tattara iyalinsa gaba daya manyan yaransa ya kira ya sanar dasu abinda ke faruwa,tare da kuma bukatar da dan uwansu yazo da ita,dukan su sun amince sun bada goyon baya,

Amma baba Inusa ya dan jimanta abun a ransa amma daya tuna zumunci abu ne mai girma sai kawai yayi addu'a.

Ana idar da sllar juma'a daruruwan mutane suka shaida daurin Auren zuriyar gidan mai gari.

KHADIJA INUSA
DA
HABEEB KHAMIS

ZAINAB KABIRU
DA
NASEER KHAMIS

Tare da mai gayya mai aiki madugu uban tafiya.

ALHAJI KHAMIS (Daddy)

da

Zarkwadediyar amaryarsa,tsohuwar budurwarsa wadda yaso aure tun farko Allah baiyi ba wato

MARYAMA diya ga kanwar maigari amma ita yanxu da sanin ta da amincewar ta dan tun zuwan su Daddy daya ganta tazo gidan mai gari aka sanar masa mijinta ya rasu gashi dama bata taba haihuwa ba,to fa sai tsohuwar soyayya ta motsa nan aka shiga tuna baya sai kuma lamari yazo akan gaba.

*tabbbbbb......Alkur'an ba ruwana dan akwai bom*

*vote*
*comments*
*with*
*Alqalamin khady*
[3/15, 11:27 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*AWESOME WRITER'S ASSO...🇳
(palace of excitation n'd pleasant writer's)

*TAME GARI*

NA
Khadeeja usman

4⃣0⃣

Tuni labari ya iso gari cewar,an daura auren Daddy da kuma yaranshi,abinka da kauye,nan da nan magana ta bazu,masu sa albarka nayi,masu tsegumi nayi.

kasancewar ana idar da sallah kuma cikin masallaci aka daura auren, yasa su Habeeb dake nesa daga waje suke jin kamar kunnensu gizo yayi musu jin kamar an ambaci sunayen su wajen daura auren.

Suna nan tsaye suka hango fitowar su Daddy da maigari anata mika musu hannu tare da yi musu Allah ya sanya alkhairi inda sukaita washe baki,da alamun farkn ciki a fuskar su,suka nhfo inda su Habeeb din suke,wadanda suma ya zuwa yanzu sauran 'yan uwa nata zuwa suna basu hannu,tare da ce musu Allah yasanya alkhairi,lamarin daya kara daure musu kai kenan har su Daddy suka iso inda suna zuwa suka tasa su gaba batare da dogon bayani ba zuwa gida,dukan su ji sukayi jikinsu yayi sanyi toh me yake faruwa? yanzu haka inka bibbiya aure aka daura a gidan Daddy zaisa suyi alheri shine ya kirasu.Da wannan tunanin suka karasa gidan.

Nan ma suna shiga gida yadau guda da fadin ga angwaye nan,inda sauran mata da abokan wasa suka shiga tsokanar su,lamarin daya kara sasu yin yake dan badai murmushi ba.

Jan su baba malam yayi zuwa bangaren shi,inda suna zuwa suka samu guri suka zube yarab dan ba wani mai kwari cikinsu,duk da basu tabbatar da abinda suke zargi ba.

Bayan baba malam gayi gyaran murya nan ya shig rattabo musu bayanin komai game da abinda suka ji kuma suka gani yanzu,inda ya dinga musu sharhin da sam bama sa fahimtar shi har ya kare batunsa Daddy ya shigo ya karbe,nan din shima ya fada musu dalilinsa nayin hakan,ganin kowannensu baice komai ba yasa Daddy yakalle su yace,

"Naji kunyi shuru", ko baku karbi hukuncin danayi yanke muku ba? ko baku yadda da zabin nawa ba?

Nan ma shurun sukayi har saida ya kara magana.

Mun Amince Daddy Allah yasa haka shine mafi alkhairi!

Ameen!! Allah yayi muku albarka ya albarkaci zuriyarku baki daya,yasa kuyi alfahari da wannan auren ko bayan ba mu.

kai kayi alfahari da Auren Khadija,kai ma kayi da taka matar zainabu!

Ameen suka amsa

nan maigari da Daddy suka fice suka barsu zaune an rasa ma me cewa kanzil kowanne zuciyarsa cike da tunani barkatai.

wani abu suka tuna lokaci daya ksmar kowa yasan abinda ke zuciyar kowa kawai sai suka saki dariya inda suka kalli juna suka kuma hade rai.

Wallahi ni dai an cuce ni,dan ni a tsarin rayuwata ban shirya qara aure yanzu ba,cewar Naseer.

Wai kai aka cuta ko ni? ni da a tsarina ba auren mace fiye da daya,ai gara kai kana da niyyar karawa wata rana ni kuwa fa?kai ni duk bama wannan ba a ma rasa wadda za'a hadani da ita sai Khadija kawai dan tsabar ci baya,yarin yar da bata cikakken bacci kullum Aljanu na bisa kanta,so akeyi nima tazo gidana ta haifamin irinta masu fitinar tsiya,to wa ma zan nunawa wannan tatsitsiyar yarinyar ince wai mata ta ce! ni wannan ma ba shine abin ji ba shiyas kaga nayi dariya dazu,yadda gidanmu zai kama da wuta,idan su mamy suka sami labarin abinda ya faru,ni wallahi da za'aimun gata da sakin yarinyar nan zanyi salin alin batare da ankai ruwa rana ba.

Kana sakinta ni kuma sai ince a bani ita a bar Zainab din,dan wallahi gara khadija sau dubu akan Zainab,kai ba fa kaga kafafunta ba wallahi sunyi nawa,gata baka,kai ni wallahi ni aka fi cuta,khadija kuwa nasanta nasan halinta sai in lallaba ta muyi zamanmu hankali kwance wallahi magani ma zan nemar mata.

Ji yayi ransa ya baci da kalaman Naseer,dan haka cikin dan zafi yace,

kai wane irin mahaukaci ne? matar tawa kake fadin wadan nan maganganun akanta?

ah to ya kake son ince?

kai tunda baka so ba sai ayi furfure ba,Wallahi ni da gudu zan amshe ta,kai ni fa da ni aka bawa ita bazanyi wani bakin ciki sosai ba duk da ban shirya ba,amma ya zanyi ance kaddara ta riga fata,ya karasa maganar kamar zai fashe da kuka.

Hmmm!!!! lallai Naseer kayi nisa ya fada yana me mikewa ya cire rigarshi ya fada saman gadon yayi rufda ciki,tare da lumshe idonsa,ya rasa dalili sam baya jin bakin cikin yin auren da akayi mishi,amma kuma baya farin ciki,tunanin khadija ya fara yi zamansu da duk wata dramar da aka dinga kwasa a zuciyarsa ya furta,ashe ba'ayi komai ba tukun dramar na nan gaba.

Shiko Naseer tunanin kafafun Zajnab kawai yakeyi,wai ya zaiyi inya tashi sai mata takalmi.?

🤔

*Ni ko nake lallai kowa da abinda ya dame shi*

*ga wannan ku dan taba dan naji dadin comments dinku akan page din jiya,ku dai tanaji ruwan kashe wuta dan har yanzu fa Dije bata da labari ,bare kuma uwayen gayya 'yan birni,masu brush da kwandala*

*vote*
*comments*
*with*
*Alqalamin khady* ✍[3/18, 8:02 AM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*AWESOME WRITER'S ASS..* 🇳
(palace of excitation n'd pleasant writer's)

*TAME GARI*

4⃣1⃣

Da gudunta ta shigo dakin,inda ta iske Dije kwance rashe-rashe saman gadon Innah,tana waya da Ishaq.

Ganin yadda ta shigo din yasa Dijen dagowa ta kalleta,batare data kashe wayar ba tace,

ke kuma lfy malam kika shigowa mutane a haukace haka ? ina tsaka da soyayya ta zaki katsemun jin dadinta!!!

Au kice zani ce ta tadda muje bari kawai inyi shuru da bakina tunda abin nema ne duka ya samu,kin san da jikon da akayi tun da can kenan!

ban fahimci abunda kike magana akai ba? wata ce ta zageni ko tayi gulmata inje in kaddamar mata maxa fadamun da sauri kar hawan ruwana ya tashi",

Sha kuruminki ni nadauka ma kin samu labari amma naga alamar baki san da zancen ba,to albishirinki!!

Goro fari kal!

meye tukwicin?

"nabaki dan mutum da uwarsa"

masha Allah

to karkarde kunnuwanki kisha labari.

ke ni in zaki fadamun abu ki fadamun in bazaki fadamun ba ki kara gaba ki barni insha luv dina da rabin raina.

gyara zama tayi,kafin tace,

.Allah yayiwa maigari albarka Allah ya ja da kwana.

Ameen Dije ta amsa dan ta matsu taji meya ke faruwa.

kin san tun ranar dana fara ganin su yaya Naseer naji duk duniya ba namijin danake so saishi,amma saboda nasan ya wuce ajina dan ba abinda zaiyi da 'yar kauye da kuma hango halin mamansa da nayi yasa na cirewa raina wannan banzan tunanin,ban san ma ina sonsa ba har yanzu saida naji yayi aure kuma naga matarsa yanzu ,har ga Allah naji kishinta matuka,amma ganin wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa yasa nacire abun a raina.

to cikin ikon Allah da kuma yardar sa yau gashi Allah ya amshi rokona ya cika min burina,tsoho mai ran karfe yayi abinda zan ta yimasa addu'a har karshen rayuwata.

Ke ni fadamin meya faru ne nagaji dajin soki burutsun ki.

kafin ta bata amsa suka tsinkayi muryar Inna tana magana cikin kuka tana fadin,

Wallahi bazai yiyu ba malam,sai dai ince kayi hakuri wannan lokacin,nasan ban taba sabawa umarninka ba amma wannan lokacin dole inyi magana,ta yaya ma hakan zai yiyu! duk da yarinyar nan bata fito ta fada mana irin zaman datayi a birni ba,amma ai munada hankali,kuma zuwan su ya nuna ya kuma tabbatar da batayi zaman wani jin dadi a can ba,nasan halin Dije da shegen kafiya da taurin kai,shiyasa ta zauna,duk a bar majjjjjjjjjj ta wannan ta yaya kake tunanin Dije zata iya zaman kishi da wannan matar wadda ko ni uwar ta ban isa ba,yakamata a dinga mun adalci,Dije ita kadai Allah ya bani duk wani hukunci da kuke yankewa a kanta ban taba magana akai ba,amma wannan lokacin ina ganin anyi abinda bai dace ba gaskiya,dan dalilinku bai kai dalilin da zaku hada su aure ba alhalin kun san ba son junansu sukeyijjjj ba,kai yau ko Dije tacemun tana son yaron nan wallahi bazan bari ta aure shi ba dan bata isa yin kishi da wannan guzumar matar ba,indai ba so kuke a kawomin gawar ta ba wata rana..ta karasa magabar tana me sharbejjj majina.
Chapter 40 · 0% Book details