← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 59

Sashe 58

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda ta Gama wankan ta fito zaune ta sameshi kan sofa rike da cup a hannunsa ga magani Kuma a gefe,tuni annurin fuskarta ya kauce ganin maganin datayi,Yana lura da ita Amma ya hade Rai,Dan yasan idan ya sakar Mata fuska,to fa zata kawo Masa wargi,itama hakan data gani yasa ta mayar da takkuban musun datayi niyya,tana yamutsa fuska ta karbi maganin Tasha,bayan ta Gama Sha din baice da ita komai ba,ya Nuna Mata alamar ta kwanta ta huta, hakan kuwa akayi ba musu ta kwanta Dan dama duk ta gaji wallahi.

*******

Yau kusan sati da faruwar abun,wato tashin aljanun Dije,sai Kuma yau Sajida tasamu zuwa gida.Da sallamar ta ta shiga falon,ga mamakin ta saita iske duk ahlin nata zaune,hakan yasata karasawa tare da kafe wadda tagani zaune kusa da Daddy'n ta da ido,bayan ta karasa ta zauna ta shiga gaida iyayenta,Nan yake gabatar Mata da sabuwar amaryarsa,Sam bataji komai dangane da hakan ba,illah ma fatan alkhairi datayi musu,Wanda hakan datayi ya mugun bakanta ran mahaifiyar ta,sai Aiko Mata da kantin harara takeyi.

Sai kusan azahar suka Sami kebewa da mahaifiyarta inda suna shiga dakin ta zayyana Mata duk abinda ke faruwa.kallonta tayi shekeke,tare da fadin to yanzu da Kika kwaso jiki Kika taho uwar me zanyi miki?,yanzu ke Dan bakida hankali na fada Miki halin da nake ciki shine Kika kwaso jiki rabe-rabe Kika zo mu jera nida ke,ace wace uwar su waye 'ya'yan,yanzu dubi kannenki su uku muna Nan zaune dasu kullum daga Mai karya yazo sai Mai karairayi,shin ke ko hakan bazai sa ki maida hankali da kwatar 'yancinki gidan mijinki? To Nidai yanzu ba abinda zanyi Miki Dan dama ance gaba da gabanta,Dan wannan da ubanki ya auro nata salon na karuwan Tasha ne,Dan haka kiyi ta kanki inyi ta tawa,kowa tasa ta fissheshi,tunda ke har yanzu kin tsaya yarinya karama tana wasa da hankalinku,haka mummy tayita zazzaga abinda ke ranta Dan haka Sajida Bata wani Sami wata mafita ba,tayi musu sallama tabar gidan.

*******

Zama fa yanzu ya canza salo,domin duk wata hanya da Sajida tabi Akan Dije tofa Bata bullewa,hakan yasa tabi duk ta rame ta Kara baki,domin taki kwantar da hankalinta ta fahimci ainihin zaman kishi na islama,itako Dije hankali kwance take rainon cikinta yayin da take samun kulawa tako wanna bangaren,Dan mamy ma tana Dan kula da ita duk da tace ita badan ita takeyi ba,Dan jikanta takeyi,itakam Dije ko'a jikinta.

Yau tana zaune a dakinta taji zaman ya isheta,Dan haka ta mike ta nufi compound danta Dan taka,Sajida ta hango ta.......

*Alkalamin khady* ✍
[8/24, 11:22 AM] +234 814 016 5919: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TAME GARI*

NA
Khadeeja Usman

6⃣8⃣

*Alhamdulillah barka da sallah ga dukkan daukakin musulmi,farin cikin riskar wannan Rana cikin koshin lafiya yasani yi muku typing,har abada bazan taba manatawa da ku ba masoya tame gari sakamakon addu'oinku gareni,Ina matukar godiya da farin cikin sadaukar da wannan page din gareku masoyana,BARKA DA SALLAH*

SAJIDA ta hango zaune ta zuba uban tagumi,da sauri ta karasa inda take har tana hardewa,(Niko nace Dije tafi a hankali meye na gaggawa),harta Isa gurin Sajidar Bata San ta Isa ba da alama tayi nisa cikin tunani.Dan tafi tayi Wanda yasa Sajida Dan firgita,ganin Dije a tsaye a kanta ga katon ciki yasata sakin tsaki,itako Dije yi tayi kamar Bata ji me tayi ba,Dan haka taja Daya kujerar dake fuskantar Sajida, kasancewar da alama gurin anyi shi ne da alama Dan hutawar masu gidan,ganin ta zauna yasa ta kallon Sajida tare da fadin,

"Aunty waye ya rasu"?

Kallonta tayi da mamaki bayyane a fuskarta itama ta jefo Mata Tata tambayar,

"Waye yace Miki anyi mutuwa"?

"Ah ah ba Wanda ya fadamin,kawai Naga kin zuba tagumi ne,Kuma sai fuskarki ta Nuna alamun kamar an Aiko Miki da sakon mutuwar ne".

Wani tsakin Sajida ta Kara ja,Dan takaici ko amsa Bata bawa Dije ba ta mike tabar ta a gurin.

Itako Dije saman kujerar da Sajida ta tashi ta mike kafarta,tare da taba baki ta furta a fili ke Kika sani.

Ta jima a gurin taji zaman ya gundureta ta mike tayi bangaren mama mariya,can ta karasa yininta kasancewar yau ba itace da girki ba yasa ta share guri tayi zamanta.

Itako Sajida tana shiga bangarenta ta dinga Kai kawo tana nemarwa kanta mafita,Dan harga Allah baxata iya jurar zafin da take ji a zuciyarta ba,zuwa can ta samo maganin damuwarta tare da yin murmushi a fili ta furta,yarinya kin Gama yawo.

*******

Tunda Sajida ta karbi girki zata Iya cewa Bata sashi a idonta ba,duk da dokar Daya kafa ta haduwa a ci abinci gaba Daya,Amma ganin cewa yanzu Bata damu da cin abinci ba tafi ga kayan marmari dana kwadayi yasa baya takura Mata taci din sai dai yayi ta siyo duk abinda take so din,amma yau tsawon kwana biyu Sam Bata ganshi ba,Bai shigo dubata ba,Kuma ta tabbatar lafiya yake Dan tana hango fitarshi da dawowar shi.

Tana tsaka da tunanin meye matsalar taji ya turo kofar ya shigo.Dago Kai tayi ta kalleshi tare da kokarin mikewa Dan zuwa Yi mishi sannu kamar yadda ta Saba,Amma sai gani tayi ya wuceta yanemi guri ya zauna,sororo tayi ta bishi da kallo Amma sai taga ya basar da ita,karasawa tayi inda yake ta zauna kusa dashi sosai,Bai Nuna kulawar komai ba,hakan yasa cikin sanyi ta furta,

"Ina kwana!

Lafiya ya amsa a takaice.

Ganin shurun yayi yawa ita Kuma Bata Saba da hakan ba,Dan ita in ana zaune mutum biyu Bata son taji anyi shuru batare da ana motsa baki ba,Dan haka ta katse shirun tare da fadin,

"Wai lafiya kake my lovely bros,Naganka ba yanayin da na Saba ganinka ba, Allah yasa bani na Bata maka Rai ba?

Hmmm kawai yace tare da kokarin mikewa ya kalleta ido cikin ido,sannan yakai hannunsa ya tadata tsaye ya tsugunna ya sumbaci cikinta,sannan ya juya ya nufi hanyar fita,har yaje bakin kofa sannan ya tsaya baiko juyo ba yace ki sameni a bangaren Sajida yanzun Nan bana son Bata lokaci,Yana Gama fadar hakan ya juya ya fice.

Itako tsaye tayi cike da mamakin sa,da kamar baxata ba sai Kuma kawai tashiga daki,hijabi ta dauko ta fito ta nufi part din Sajida.

Koda ta kafin ta shiga ta tsaya tayi knoking daga can suka Bata izinin shiga batare da sun tambayi waye ba, zaune ta iske su a falo manne da juna,yanayin data gansu taji wani Abu a ranta,Amma saita danne ta zauna a daya daga cikin kujerun falon,tana Zama ta shiga gaishesu,Sajida ta amsa Mata da kyar tana ci gaba da shafo sajen dake kwance gefen fuskar Habeeb.

Shuru ne ya biyo baya na Dan lokaci,Banda karar TV ba abinda ke tashi.

Muryar Habeeb ta tsinkaya ya Kira sunanta,

Khadeeja!

Daga yanayin Daya kirata ta Dan fuskanci kamar ransa a bace yake,Dan haka ta amsa Masa da na'am,tare da Kara tattara nutsuwarta.

Magana yaci gaba dayi Yana kallonta,tunda na aureki na taba ce Miki bana son matata?

Cike da mamakin maganar sa wadda tazo Mata a bazata ta tsareshi da ido.

"Ba kallona Zaki tsaya yiba,amsa nake bukata.

Cikin sanyi ta amsa masa da ah ah!

"Na taba fada Miki wani sirrin kwanciyar dake tsakanin mu da ita?"

Ah ah!

"Koda tsautsayi ya faru a baya na taba ce Miki bana sonta?

Nanma da ah ah ta amsa mishi,sbd tafara Jin zuciyarta nayi Mata nauyi da kalaman sa dayake jifanta dasu.

"To meyasa Kika goranta Mata,tare da ce Mata Ni na sanar dake ba sonta nake ba auramin ita akayi dole,sannan banajin dadin mu,amular aure da ita,sannan kikayi Mata gorin haihuwa?

Kalamansa taji tamkar saukar guduma,Dan haka ta rutse ido tare da budesu tar Akan Sajida,wadda ta watso Mata wani kallo tare da murmushin mugunta,Wanda Nan take Dije ta baro jirgin,Dan haka tayi kokarin danne zuciyarta tare da mayar da kallonta gareshi.murmushin karfin Hali tayi tare da Kara kallon Sajida ta kashe Mata ido Daya,Wanda yasa ta rasa ma'anar wannan kallon,cikin dakiya ta da kwarin gwiwa ta silalo kasa tare da zubewa saman gwiwoyinta ta Fara magana cikin rawar murya irin ta me son yin kuka tace,

"Allah ya huci zuciyar saraki,ranka ya Dade banyi hakan da nufin Bata maka raiba,illah mun Sami misunderstanding ne ranar,sai tace min ai ka sanar da ita duk yadda akayi aurenmu,matsama akayi ka aureni,sannan Kai baka sameni a budurwa ba,kadaiyi hakuri ne ka rufamin asiri Wai Dan Ina matsayin 'yar uwarka,sannan Kai cikin Nan ma kaddara tasa aka sameshi,Amma da da yadda zakayi da tuni an barar dashi,kawai Dan baka farga da wuri bane Saida ya girma,hakan data fadamin ne yasa naji zafi shine nima na fada Mata,nace duk abinda ka fada akaina,to duk ka fadesu a kanta,Amma Dan Allah kayi hakuri ka yafemin,bawai na fada ne Dan in Bata maka Rai ba,na fada ne saboda Jin zafin maganganun da akace sun fito daga bakin Wanda nake ganin girma da mutuncinshi fiye da kowa a duniya.

Bata tsaya lura da yanayin da suke ciki ba ta juya ga Sajida,tare da fadin,

"Ke Kuma Aunty na dauka kin hakura tun a ranar ai,Ashe baki hakura ba,da nasan Zaki fadawa Yaya dana Kara baki hakuri,Amma yanzu Ina me Kara baki hakuri,mu zauna lfy,mu rufawa kanmu asiri da mijinmu,Kinga shi ya fita nemowa,kamata yayi mu da muke gida mu daina shirme,mu bishi da addu'ar Allah ya bashi abinda ya fita nema,ya Kuma tsare Mana shi,Dan Haka Ina dada rokonki gafara akan abinda na fada miki,tana kaiwa Nan ta mike tsaye tare da kallonsu tace nabarku lfy,fatan za'a yafi juna,ta juya ta fice tana dariya ita kadai,Dan ta fuskanci Sajida bom ta hada mata,amma tayi maganinta gobe ta Kuma,shi Kuma zaizo ya sameni ne.

Shikuwa Habeeb tun farkon da Dije ta tsugunna bada hakuri,yaga hankalinta,ransa ne ya baci Jin Wai Ashe ma Sajidar ce ta Fara Mata Gori,Kuma ma ta Bata hakuri Ashe,Amma tasa shi yake shrin CI mata mutunci,gaskiya Allah yasoshi,ji yarinya Mai hankali,har tasan ta roki a yafe Mata sannan a zauna lfy.

Cikin bacin Rai ya Juyo ya kalli inda Sajida take zaune,wadda tayi mutuwar zaune,domin kuwa ta kurawa inda Dije ta tashi ido bako kiftawa.....

*Dominku masoya tame gari,ku Kara hakuri,komai nisan jifa*

*Alkalamin khady*✍
[8/24, 11:23 AM] +234 814 016 5919: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*TAME GARI*

NA
Khadeeja Usman

7⃣0⃣

*_To ai hikenan_*
Chapter 58 · 0% Book details