← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 59

Sashe 59

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ganin da mama mariya tayi Dije nata bazgo zance harda cewa gwanda da ita Bata haihu ba yasata,karasawa gabanta,tana fadin"haba manyan mata, haihuwar kike yiwa wannan Abu Dan sakarcin banza! Yanzu fa Kika fara.....

"Na Fara me? Ciwon ko me? Ai kuwa indai abinda nakeji yanzu na Fara ji ma toko wlh mutuwa zanyi kawai Dan Allah ki kiramin innata".Ta karasa da kyar tana Kara rushewa da kuka.

"Ni ba nakudar nake nufin yanzu Kika Fara ba,haihuwar nake nufi Wanda zaiyi dozin biyu ne daga Daya Yana ihu inaga sauran Kuma!,Dan Allah kiyi shuru ki dinga addu'a kinji yi dauriya,ba'ason mace da raki".

"Naji,zanyi dauriyar, amma Ni bazan Kuma haihuwa ba,wallahi Kuma idan na samu na haye,duk shegen Daya Dakar mun da sai munyi shari'a dashi,ashe dama haka akeji,wayyo Allah Bari dai in karasa saukar Nan kawai,bude murya tayi tahau karanta ayar da duk tazo bakinta,harda su hadisin da annabi sallallahu alaihi wasallam yace abi uwa sau uku kafin yace abi uba sau daya,.

Juya fuskarta tayi ga Habeeb,inda ta ganshi tsaye Yana kokarin daura Mata wani ruwan,Sam bazaka iya bambamce halin dayake ciki ba,tabbas duk Dan da baibi uwarsa ba sai dai muyi Masa fatan shiriya.

Muryarta ya tsinkaya tana fadin,"lallai manzo yayi gaskiya,Daya ce a fifita uwa akan uba,Yaya kana Jin abinda nake ji kuwa? Tabbas na amince ka Kara aure Dan Ni nabarwa kowacce mace Kai,tazo taita haihuwa Ni na yafe,kawo kunnenka kaji Yaya in bar maka wasiy.....maganar ce ta makale sakamakon wani nishi Daya taso Masa,wata katuwar kabbara tayi tare da nishi Mai karfi,saiga baby ya fado take ya tsanyare da kuka,Wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da fadin Alhamdillah!

Kasancewar daga shi sai mama mariya a dakin,Dan yace shi zai karbi haihuwar matarshi,mamy da Daddy na can reception suna jiran tsammani,shiya duba baby'n yaga baby girl kyakkyawa da ita,Dan a take ya hango tsantsar kamarta da mahaifiyarta,ji yayi soyayyar yarinyar data mahaifiyarta na ratsa dukkan sassan jikinsa,kayan asibitin da suke bayarwa aka sawa jaririyar sannan aka gyara Dije wadda ya zuwa yanzu ba baka sai kunne,Banda haushin Habeeb ba abinda takeji,shi kuwa murnar ganin ta sauka lfy ya duba yaga Kuma batada matsala yasa yayi Mata 'yan allurai danta huta,ya makale baby babu ko kunya,Saida mama mariya tace yakaiwa su mamy ita,ita Kuma Bari taje gida tayi duk abinda ya kamata ta kawo.

Cewa yayi ta barshi kawai Dan Nan da awa Daya zata farka saisu tafi gida.

Haka dai ta sanar dashi dole ta koma gidan ta hada mata abunda zata bukata sa sameta acan,

Sosai mamy ta Nuna farin cikin haihuwar Wanda har Saida kowa yayi mamaki,ta rike yarinya Kam da kyar tabawa Daddy ya ganta yayi Mata addu,a.

Kamar yadda yace ko ba'afi awa dayan ba ta farka,tea ya hada mata Mai kauri ya Mika Mata,Wanda badan tanajin yunwa ba acewarta bazata karba ba Dan gani takeyi duk shi yaja Mata ta wahala,shi kuwa Yana sane da take takenta ya kyaleta,Saida ya tabbatar ta shanye sannan ya hau shirye-shiryen tafiyarsu gida.

Koda suka iso gida kulawa sosai aka bawa Dije,yayin da mama mariya tace ta dawo bangarenta,tako ji dadin hakan,bayan sun Isa ko wanka sosai na gargajiya akayiwa Dije,yayin da Habeeb ke fadan Wai meyasa aka Mata wanka,fada mamy tahau yi masa tana cewa su meya samesu da aka musu,ganin anfi karfinshi yasa shi yin shuru,dama ga haushin an maidata bangaren mama mariya

Suna zaune da dare tana cin tuwon dawa miyar kuka da taji naman rago da manshanu,ga yajin daddawa,gefe Kuma katon mug ne cike da kunun gyada,ga farfesun Naman Kai an Sata a gaba Wai dole Sata cinye duka,tana Jin dadin tuwon sosai,suka ji sallamar ta,cikin sanyi ta shigo ta nemi wuri ta zauna,amsa Mata sukayi suma,Nan ta shiga yiwa Dije sannu da jiki da Kuma barka,itama amsawa tayi,baby'n Zainab ta Miko Mata,ga mamakinta sai gani sukayi tana kallon baby'n tana share Karamar kwalla,ta jima anan kafin ta tashi ta tafi,duka suka bita da kallo kowa da abinda yake sakawa a ransa.

Tana shiga bangarenta dirent dakinta ta wuce ta fada kan gado,kuka ta fashe dashi tare da mugun tausayin kanta,taso ace itace ta haihu da Habeeb ko Dan soyayyar datake tsakaninsu,me yasa ta biyewa rudin shaidan da zuciya,ta tabbata da yanzu itace ta haifi wannan cikin da ita da kanta tayi sanadiyar barewarsa,to waima a zamanta da khadeeja da kishin data Nuna Mai ta tsinta? Haka taita kuka har Habeeb ya dawo ya risketa,sosai ta bashi tausayi,Dan rashin haihuwa babbar jarabta ce,rarrashin ta ya hau yi,Saida ya tabbatar ta samu nutsuwa,sannan ya shiga yayi wanka itama tayi suka kwanta.

*****

Ana gobe suna duk 'yan garinsu Dije suka zo,dama Bata San ran zuwan innarta ba,Amma harda matan Mai gari.

Ranar suna yarinya taci sunan Inna wato (saudat) Amma sun Mata lakabi da( Sukaina).

Sosai akayi shagali sai dai muci Allah yakaimu na 'yan baya wato su Zainab.

Kwana biyu da suna akace za'a tafi da Dije gida,aikuwa fur Habeeb yaki amincewa,saima yabar gidan,ana fadawa Daddy yace a tafi da ita Bai dawo ba sai dare,yasan dai dole 'yan tafiyar sun tafi yanzu,Amma Yana zuwa Daddy yayi Masa albishir din an tafi da Dije. Da izininsa,sosai ransa ya baci har yayi fushi.

Ganin fushin ba inda zai kaishi yasa dole ya sakko Kodan kada ya shiga hakkin Sajida wadda a yanzu take bashi tausayi,Dan duk tayi laushi lubus.

******

Cikin kwanciyar hankali take wankanka inda take shan gyara tako Ina take Shan gyara,Saida tayi wata uku sannan ta dawo,kafin ko ta dawo Habeeb duk sati sau biyu yake zuwa.

Tabbas zaman su yanzu ya sauya domin Zama sukeyi na mutunta juna Dan yanzu duk wani shiririta dukansu sun watsar,yayin da Sukaina tayi wayo matuka,kusan ma Rabin kulawarta Yana gurin Sajida ne,Habeeb na kokarin kwatanta adalci sosai a tsakaninsu,Dan ko wacce yanzu da nata matsayin a zuciyarsa.

*5 years letter*

*******

Zaune suke a falo gaba dayansu yayin da Suke Hira cikin Jin Dadi, kasancewar yanzu Habeeb yayi musu babban gida shima Naseer yayi nasa da matansa Kuma duka Alhamdillah kowanne bangare ana samun zaman lfy.

Duk sun maida hankalinsu ga kallo,yayin da Dije ke zaune a kasan capet tana bawa Nihal wato jaririn data Kara Haifa nono suka jiyo karar fashewar Abu daga kicin,dukan su mikewa sukayi suka nufi kicin din,suna zuwa suka ga Sukaina ce ta baro da kofuna daga saman cabinet bayan ta taka kujera kome zata dauko,oho? Ganin fuskar Dije da tayi yasata firgita dan tasan ummin nata Bata Mata da sauki kawai saita kakkafe ido tare da karkace baki ta langabe Kai,ganin hakan cikin tashin hankali habeeb ya Isa gareta da sauri ya rungumeta,ya shiga Kiran sunanta,itako sai fa far take da ido,dakinta ya nufa da ita,inda yana shiga ya sauketa saman gadonta cikin rudewa da rashin sanin abinyi,ji yayi ta kyalkyale da dariya,tare da kashe Masa ido Daya,

"Sorry Daddy! I do all this because of ummi she didn't beat me yap" ta Kara kashe Masa ido,Dije da shigowarsu kenan cikin kidima ai sai suka tsaya Jin abinda yarinyar tace,a fili Dije ta furta tabbas tarihi zai maimaita kansa.......

*TAMMAT BIHAMDULLAH*

Anan na kawo karshen wannan littafin na *TAME GARI* Ina rokon Allah yagafartamin kuskuren da nayi a ciki,abinda nayi dai dai Allah ya bani ladansa.

Ina Matukar Mika godiyata ga masoyana na nesa dana kusa ina farin cikin kasancewar kaunarku gareni,insha Allah Nan bada dadewa ba inhar Allah ya sauke Ni lfy zaku jini a sabon littafina Mai dauke da nishadantarwa fiye ma data me gari,na barku lfy.

*Alkalamin khady* ✍
Chapter 59 · 0% Book details