← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 59

Sashe 11

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ah ah khadeeja rufa mana asiri wlh ba haka bane kada kija mana wani bala'in

to tsayuwar me mukeyi ku wuce mu tafi mana

jiki ba kwari suka ja motar suka nufi gida a hanya dije tace kunga ku wuce dani gidanku kawai mukwana can dan ni gobe ma kauye nayi😃

bikin fa?

wanne biki ai inba so nakeyi a hada da jana'izar gawata ba gara in gudu qauye harsai jarababbun nan sun bar gidan daga baya in dawo dan in suka san gaskiyar abinda yafaru inaga naman jikina zasuyita yanka har sai sunga nakai takarda😋

dariya suka sa tare da fadin ashe khadija tanada tsoro

hmm ai tsoro halak ne haka kawai a taba lfy ta a jawa me sona asara mijin dazan aura duk yaga tabo a jikina me yafi raina?gara in san nayi koba komai tsawon shekara uku danayi banga innata ba zan fanshe

a haka har suka qaraso gidan su rufaida suna shiga sukayi wanka sukayi sallah tare da cin abinci suka kwanta bacci

*****

gida fa ya kacame inda mamy ta kira naseer cikin bacin rai tace tana son ganinshi

bai wani jima ba yazo yana shiga dakinta ya iske yusrah kamar mahaukaciya fuskar nan ta hade da majina da hawaye idanunta duk sun kumbura alamar tasha kuka

cikin ladabi ya gaisheda mamy ko amsawa batayi ba ta shiga tambayarsa dalilin daya sa ya aikata abinda ya aikata

bayani ya shiga yi mata inda nan take yusrah ta karyata tare da fadin wlh qarya ne mamy kinga text din fa dayamin

karba mamy tayi ta karanta tare da fadin ubanwa to ya tura wannan saqon ?

karba yayi ya duba yakaranta yaga number sa ce kuwa

cike da mamaki ya kalli mamy yace na rantse da Allah wlh wlh bani na tura sakon nan ba tabbas number ta ce amma banida masaniya akanshi amma mamy ai itama ta turamin wata cousin sister dinta tace wai dreesing dina beyi ba saina dawo na sake wani

caraf ta amshe da fadin wlh qarya ne ni babu wanda na aika nan aka shiga musu

ganin haka yasa mamy daka musu tsawa tare da fadin kai ban son iskanci

ya akayi ka hadu da dije a gurin to

be boye komai ba ya fadawa mamy

nisawa tayi kafin tace amma wannan anyi shegiyar muguwar yarinya yanzu nagane bakin zaren cikinku akwai wanda yayi mata wani abun tayi maku ramuwar gayya kenan

nan kowa ya shiga fadin abinda yafadawa dije akan zuwa gun dinner din

koda naji yanzu naji batu amma ko wannan uwarta ta haifi fitina da kanta zako tasan tayimin haka wlh saita gane batada wayo nan ta gama fadin duk abinda zata fada suma kowannensu a zuciyarsa ya gama kiyasta hukunci. dazai yima dije niko nace to ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta🙊

*******
washe garin ranar asabar aka daura auren habeeb khamis da sajida A lawan tare da na yusrah Abubakar da angonta naseer khamis duk akan sadaki dubu dari dari inda dinbin jama'a suka shaida duk dangin kauye maza sunzo harda ko mahaifin dije da megari

ansha yinin biki inda karfe takwas aka dauki amare zuwa gidajensu dake wuse zone 2 gidan yayi matukar kyau tare suka gina shi gate daya ne amma kowacce part dinta daban babu kuma abinda aka banbanta wajen ginin konai iri dayane

har aka gama shagalin biki ba wanda yaga idon dije duk masu son ganinta kuwa sai washe garin ranar ta dira a gidan koda ta iso 'yan garinsu nata shirye shiryen komawa kauye dan haka itama ta hada kayanta suna can falon baki ta iske su bakaramin dadin ganin mahaifinta tayi ba inda shima yaji dadin ganin tilon 'yar tasa ganin yadda ta canza tayi kyau ga kuma nutsuwa

shima a bangaren me gari dadin yaji inda ya shiga sa musu albarka

koda tace zata bisu bawanda yayi hanzarin hanata dan ta yi kokari dan haka koda aka tashi tafiya da ita aka shiga mota sai bayan ta shiga ne mami ta ganta inda ta ciji yatsa takira daddy akan meyasa za'a tafi da dije yace zata ganin gida ne duk yadda taso ya hana bata samu shiga ba a ranta tace zaki daw ki sameni

su dije an dau hanya yayin da zumudi da farin cikin dokin ganin innarta yasa take gani. kamar motar bata gudu tayi bacci ta tashi yafi sau nawa kafin a isa sai kusan yamma suka iso gida zo kuga murna gurin dije

*WELCOME BACK TO VILLAGE DIJE*

*vote*
*comments*

*with 08066364077*

insha Allah indai nasami lokaci zaku jini zuwa dare
[16/12, 11:41] ‪+234 806 493 3819‬: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TA ME GARI*

NA
khadija usman

1⃣3⃣

*rawa da girgiza zanyi gabanku in jujjuya💃💃💃 zanyi muku albishir comments dinku na burgeni💃💃💃*

*gaskiya naga soyayya a zahiri da badini jinjina gareku masoyana nasan soyayyar tame gari ce ta shafeni ina matuqar godiya gareku Allah yabar qauna*

*sadnaf ina tayaki murnar samun lfy Allah ya qaremu da lfy da duk musulmin Allah baki daya,Aunty safiyya huguma kema ina miki fatan samun lfy me dorewa Allah yasa anyi aikin a sa'a*

****

kallonsu dije tayi taga yadda jikinsu ke makyarkyata ita abunma sai ya bata dariya dole saida ta dan murmusa kafin ta maida kallon ta garesu tace na kira waya azo a tafi daku sbd haka ku tashi mu tafi dan bana son jira

magiya suka shiga yi kuka wi wi dan inna mairo harda fyace majina suna wlh ba laifinta bane hansai ce shima din hamidan duk akan hansai suka dora laifin ganin da tayu duk suna son zamewa su barta ciki yasata sakin kuka tare da fadin munafiki wlh qarya ne duk da laifinsu suma kuma ni yauhe ma nasa ku quntatawa 'yar mutane bakai ka gani ka auro ta ba ko nice inna da dole innace kayi abu se kayi ?

ah ah hansai kiji tsoron Allah ki fadi gaskiya wlh 'yan sanda basuda imani ko kadan kikkilemu zasuyi ko digon jininmu baza'a samu ba sbd haka ki karbi laifinki kawai a tafi dake ni a barni da dana se 'yata hafsy ta qarasa maganar tana miqa hannu da dafa kan hafsy data maqure guri guda tana kallon ikon Allah

kunga duk nagaji da surutu sbd haka kutashi mu tafi kawai ta fada tana me qoqarin mikewa

hansai ce ta miqe da kyar ta kalli dije kafin ta kaikaice ta ce ke dayalla gafara can dan kinga ma ana lallabaki wlh dukanku ina iya hadawa inci uwarku ba inda zani hukumar hegiya dan haka kin dade baki ce su shigo din su tafi dani ba

ganin yadda taketa bala'i da kumfar baki yasa fa zuciyar dije bugawa daram dararam dam dan ita kanta tasan idan ta bari wannan me kama sa jinsin ordisay din ta damketa to fa wlh saita ci kut......🙊
gara ta lallaba ta zame dan taga alamar wannan kaddarar hafsy ce koba kamai ta tayata da addu'a kawai 🤣

ganin da hansai tayi kamar dije ta tsorata da ita yasata qara sakin sababi duk da itama qarfin halin ne dan wlh da za'a tsaga kirjinta tsab zuciyarta zata fado ta fito

kallon tsaf dije tayi mata ta lura da sababin da takeyi na iya baki ne a ranta tace kin gama yawo yarinya amma a fili saita ce

keeeeeee!!!!!

shutup your magout maout ina magana kinayi kin san wacece hukuma kuwa ?kinyi lafuffuka da dama kuma masu girma ciki harda na zagin hukuma dan haka dole ki karbi hukuncinki tare da masu mara miki baya dan haka kuna batamin lokaci pls ku wuce muje

hamidan ne yace yanzu dai ranki ya dade laifin waye ya shafeni ni?

oho dai koma laifin waye ai kai ka sani ni ba ruwana danme zaka auro yarinya ka maidata baiwa suma iyayenta saina sa an tafi dasu tunda basu kula da yarinyarsu suka dauka duka bata

kinga ranki ya dade wlh wlh laifin duk na hansai ne ko inna?

eh wlh itace da anyi abu saita ce zata zane mutum kota zaune shi sbd haka muke yi mata biyayya duba da yanayin hallitar da Allah yayi mata

oh yanzu nagano bakin zaren kana namiji matarka kw juyaka kenan to waye mijin cikinku?

nine wlh amma a suna

toh yanzu ka zabi daya shin zaka barta matsayin mijin ko kuma zaka dawo mikin in yaso a dai daita?

wlh zan koma cikakken namiji ma

toh masha Allah wane mataki zaka dauka yanzu?

sakinta zanyi dama ta isheni wlh

nisawa tayi taga dai ba kyau raba sunnar ma'aiki kuma ta lura da yadda hansai jikinta yayi sanyi daga jin an ambaci kalmar saki saita bata tausayi tace to yanzu zanyi muku wani adalci guda daya zan rufa muku asiri kowa yazauna muyi magana zama sukayi duka inda su kansu suke mamakin yadda suke bin maganar yarinyar kodan fa hukuma ba sauki

ganin su nutsu yasata zame gilashin idonta abin mamaki ji nayi su dije an afka wa'azi gadan gadan ta shiga yi musu nasiha da taushin murya

Allah kenan duk cikinsu nutsuwa sukayi sunaji inda duk jikinsu yayi sanyi saida ta gama kafin tabi kowa tanaa fada masa laifinsa tare da sanar dasu inta kaisu abuja irin hukuncin da za'a musu amma yanzu in sunji nasiha zata san yadda zatayi a kyalesu amma fa daga wannan lokacin zasu yawaita kawo ziyara qauyen kuma kowannw lokaci suna iya zuwa

da sauri suka amsa sun yadda inda daga baya dije tace ta sallamesu su tashi su fita wai zata yiwa hafsy gwajin cutar caskalaxation 🤣

duk suka miqe suka fita jiki ba kwari

sun jima da hafsy tana yimata nasiha akan rayuwa kafin ta bata abinda tazo mata dashi tace zata tafi amma kafin ta koma abuja zata dawo sai dai kada ta bari su rainata itama kuma kada ta raina kowanne cikinsu a haka sukayi sallama hafsy harda kuka tanama dije godiya

sai yamma ta dawo gida babu wanda ta fadawa abinda tayi washe garin ranar tasamu zuwa gidan su shatu ita kam ba laifi da sauki abin in akayi la'akari da auren kauye dama an san dole sai anyi wannan bautar

********
Chapter 11 · 0% Book details