← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 59

Sashe 36

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wlh sajida kina bani mamaki wani lokacin wai duk ina basirarki take tafiya ne?duk ina kissa da kisisinar dana sanki dasu nasan ke ba boka ba malam amma Allah yayi miki baiwar sanin hanyoyin sarrafa d'a namiji shin shi dan wannan matalar ne zata gagareki magance ta

hmmm laila kenan baxaki fahimta ba wannan karon habeeb bakiga yadda ya nunamin ba ina shawo kanshi akan.komai cikin sauki amma wannan karon abin yaki

to ai wannan.me sauki ne ki nuna masa kawai kin amince ku daina tsarin iyalin amma ai yasan Allah ke bayarwa kuma lokacin daya so inyaga baki samu ba sai ki nuna masa illar maganin ne yasa haka

ummmm hakane amma ko kin manta habeeb likita ne likitan ma na mata ina gudun kada yayi bincike ya gano karshe abin ya kwabe ..

to ke tsayawa zakiyi harya gani din ko kinaji kina gani zaki tsaya yayi miki gwajin ai family doctor dinku zaki tasamma ya baki bake result ki nuna masa inya so yayita baki magani kina banka

ina gudun ranar da zai san bana haihuwa yayimun kishiya wannan abar ita nake tsoro

ke dan Allah ma kibar wannan zancen ai kishiya keda ita sai a lahira kawai dai kibi shawarar dana baki inaga ita ce mafita

hakanr to Allah yasa mu dace

Ameen ta fada tana me qoqarin mikewa

bari nakawo miki ruwa mun tsaya zance ban.baki abinci ba

*****

yawan nacin sa da kiran dayake mata yasa ta fara saurar sa ishaq mutum.ne mai sauqin kai da kuma barkwanci wasa da dariya itako dije ga son zance da haka ya siyeta ta fara biye masa a waya suna shan hirar su kullum sai sun raba dare duk yadda ya so tabashi dama yazo gidan su ki tayi hakan yasa nan.ma kullum yake mata magiya amma sam taki yarda

itako mamy tarasa hanyar dazatabi dan ta kuntatawa dije tabar gidan ta tsani ganinta amma taga alamar yarinyar tazo kenan koda yadda Alhaji ke nunawa sai dai aure ai kuwa in kin san wata baki san wata ba ta fada a zuciyarta wani tunani tayi nan ta saki murmushi kafin tace a fili

ta yaro kyau take bata karko daga ke har fasinjojin naki nasan inda zan jefa ku sai abi wani sarkin kuma muma mu huta mun yadda kwallon mangwaro

*muje zuwa kudai reader's dramer yanzu aka fara fatana ku kara hakuri*

*Alqalamin khady* ✍
[3/15, 11:19 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

TAME GARI

NA
khadija usman

3⃣5⃣

Alhamdulillah,naga sakon ku masoya tame gari,masu kirana ma duk ina godiya Allah ya kara kauna ya barmu tare Ameen

yau tun safe mamy tasa ake gyaran gidan, hakan ya tabbatarwa da dije daddy na nan shigowa gari kenan,dan haka itama ta shiga nata shirin,dan tana son sanar dashi batun zuwanta gida dan ya zuwa yanzu yakamata ace taje taga iyayenta dan tayi kewarsu.

Shigowar dare daddy yayi,dan haka basu samu damar haduwa da dije ba sai da safe wajen yin break fast,wanda yau mamy da kanta takira dijen sai wani nan-nan takeyi da dije da wata fara'a inda abin ya dinga bawa dijen mamaki,shi kuwa daddy dadi yadinga ji, ganin yadda mamy yanzu take nuna tsantsar kulawarta akan danginsa,sabanin da datake nuna tsanarsu k'arara da kyama,hakan gasa dayaga yadda take yiwa dije da kuma sanar dashi datayi wancan lokacin zataje kauye sai ya ji ya k'ara sonta,tare da k'ara bata wani matsayi a zuciyarsa.Cikin fara'a ya amsa gaisuwar da dije ke yi masa, haka ma mamy,yayin da dijen ta fara aikawa cikinta d'a'amin ba kama hannun yaro,dan dama dije fannin girki ba wasa.

ko da suka gama daddy ya koma falo shi da mamy suka zauna,itama dije na karewa ta taso ta iso falon ta zauna kasa daga gefen daddy ta shiga sanar dashi batun zuwanta kauye,cikin fara'a da jin dadin maganar tata yace

"kai beautifull daughter amma naji dad'i wlh" dan nima kin tunamin da zumunci ai tafiyar dani za'a yita,dan haka ki fara shiri zuwa next week saimu tafi gaba d'aya, zanyiwa yayyenki magana sai su shirya har matansu a tafi gaba d'aya.

cikin farin ciki dije ta amsa da to daddy nagode Allah ya kara girma.

Ameen daughter,sai a fara shirin zuwa ganin maigari ko?

mamy da tunda suka fara maganar taji yace dukansu zasu kauye taji ranta ya baci ta dago kaitare da fadin"haba Alhaji ! ya zaka ce a tafi gaba d'aya bayan na fada maka lalurar da yaran can ke fama da ita,kasan kuma bai kamata ace suyi doguwar tafiya ba yanzu.

Au hakane fa kema kin kawo uzuri,wannan ai bawata matsala bace, su mazan sai a tafi dasu, tunda dama su zuwan yake kamar wajibi a gurinsu dama dai dan matan nasu suje suga tushen mu ne.

To wai zuwan yazama dole ne ?naga ita khadija yazamarwa dole tunda ita ce tushenta can kowa nata nacan,banda ma dai son zuciya da kwadayi irin na mutanen kauye,ta yaya zan haifi 'ya kwaya daya tal a duniya sannan in bari tayi nesa dani,to amma mutanenmu musamman na kauye sun baci da shegen son abin duniya da mutumin kauye da noma da kiwo a ka sansu, amma yanzu sun sawa ransu wai suma sai sunyi boko,to bokon da suk........ya isheki karima!! cewar daddy cikin daga murya,wallahil azeem ki kiyayeni cin mutuncin naki ya isheni,da na dauka kin shiryu kin daina ashe tuban muzuru kikayi,ni banma yadda da zuwanki da kikayi garin ba kwanan baya ,nasan akwai abinda ya kaiki,ina so ki shiga hankalinkk ko da na barki a baya kina abinda kika ga dama to ba tsoronki nakeji ba,kyaleki nakeyi kawai dan a zauna lafiya,amma ke na lura kinki ki fahimci hakan to wallahi ki kiyayeni kinji na fada miki.Fada sosai daddy ya shiga yi inda yake shiga bata nan yake fita ba,da farko Dije taji haushin maganganun mamy amma daga baya dataji yadda daddy ya fara sababi saita dan ji sanyi.

Mamy kuwa lakwas tayi dan batayi tunanin daddy zaiyi mata magana haka ba,kallonta ta mayar ga Dije suna ko hada ido Dije ta zaro mata su tare da dan wurkila su,sai mamy taga kamar abubuwan ne,ji tayi gabanta ya fadi dan haka tayi saurin kawar da kanta tare da fadin nashiga uku a zuciyarta,tsam ta mike ta nufi part dinta,daddy ma kwafa yayi ya nufi part dinsa shima aka bar Dije na muzurai ganin haka yasa itama ta mike tayi nata gurin ranta fari kal sbd batun tafiyarta kauye.

*****************

Tun ranar data furta masa ta amince ta daina shan duk wasu kwayoyin haihuwa ya saki ranshi, inda ya dad'a dagewa tare da bata kulawa sosai ko yaushe yana manne da ita wai duk dan ta samu ciki,ita kuwa sai ta kara narke masa,soyayya sosai suke sha abinsu.

Sosai Naseer ke bawa yusra kulawa, dan har aiyukan gida shike tayata, tunda tun farko sun hada baki da sajida sunce basa son masu aiki.

****

Ko da daddy ya kirasu ya sanar dasu batun tafiya kauye duk ransu bai so ba,amma dole suka amsa masa,dukan su kamar abin hadin baki da suka fadawa matan cewa sukayi sai sun bisu,shi Habeeb bai wani damu ba da sajida tace zata bishi,amma shi Naseer lallaba yusra ya shiga yi inda fafur taki amincewa tace ita saita je tunda ba laulalayi takeyi ba dole tasa ya hakura aka shirya tafiyar da ita.

******

Gobe Alhamis ranar ta kama ranar tafiyarsu dan haka, daddy yace su shirya da wuri,ko da dare yayi dije kasa bacci tayi dan murna inda Ishaq ya kirata a waya,koda ta fada mishi batun tafiyar da zatayi gobe,sosai ya nuna mata rashin jin dadin sanar dashi da wuri da batayi ba inda ya dinga rokonta akan ta amince ya zo da safe suyi sallama amma taki amincewa dole ya hakura.

Washe gari da sassafe kuwa sai ga su Habeeb dukansu,ko da daddy ya gansu da matansu bai tambayi dalilin su na tafiya dasu ba.

Zuciyar mamy cunkushe take fa tsantsar bakin ciki daka kalleta zaka san tana cikin zunzurutun bacin rai dan ba yadda zatayi ne kawai ta hakura dan yanzu lamarin daddy yafi karfinta da alama sakin hannu ya kamata.

*(niko nace dama ana sakin hannu ne a bangaren asiri,haba mamy)*
😂😂😂😂😂😂

kowa ya shirya dan haka suka fito gaba daya dan shiga motoci.

Daddy ne ya kalli Habeeb yace,

amma dai kun san ba zaku debi motoci haka mu tafi dasu ba kamar zamu taron siyasa.Dan haka ku da matanku ku shiga mota daya muma saimu shiga daya.

to daddy suka amsa cike da ladabi.

yadda yace din hakan sukayi dan haka suka shiga suka saita hanya sai garin jigawa kauyen gawo.

*A sauka lfy*

*vote*
*comments*
*with*

*Alqalamin khady*
[3/15, 11:20 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

TAME GARI

NA
khadija usman

3⃣6⃣

*Alhamdillah gaskiya ban san da bakin da zan godewa masoyana ba,hakika naga ainihin sahihiyar soyayya naga zallar so fiye da yadda dije ke son mazga ina alfahari daku da godiya gareku tare da addu'ar Allah yabar kauna ya kara zumunci ya sa zumuncin da soyayyar su dore har abada ameen*

sai kusan la'asar suka shigo garin,inda gida ya kacame da murnar zuwansu,mai gari kuwa abin ba'a magana,ba karamin farin ciki yayi ba na ganin daddy gaba daya da iyalansa,nan da nan aka shiga hidima dasu.

itako Dije ko da aka iso babu wanda ya lura da sulalewarta sai gida,sai da mai gari yace wai ina tawaje na ne?sannan suka lura da bata nan,dariya yayi dan ya tabbatar ta tafi gidane.

da gudunta ta shiga gidan tana kwalawa inna kira,wadda tun isowar su labari ya isko ta cewar gasu Dije nan aikuwa tsantsar farin cikinta ya kasa boyuwa dan tayi kewar 'yar ta sosai.

tana zuwa ta fada jikin Inna, inda ita kanta Innar ta debe kunya ta rungumeta,sosai Dije ke kukan farin cikin jin dumin mahaifiyar ta, suna tsaka da haka baba Inusa ya shigo dan ya samu labarin isowar su yanzu ma daga gidan mai gari yake yayi wa su daddy sannu da zuwa,ya nufo gida dan jin cewa diyarsa tana can domin shima yayi kewar ganin tilon 'yar sa,ba karamin farin cikin ganin Dije yayi ba domin gani yayi ta canza masa tayi masa girma a ido,tabbas ya yaba da kokarin yayan nasa wajen rikon diyar tasa.
Chapter 36 · 0% Book details