← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 59

Sashe 16

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin hade rai ya fito tare da nufo inda dije ke zaune

ko kallonta beyi ba ya wuceta ya nufi qofar falon bayan ya bude suka gaisa da baba habu kafin yace bari ya kira dijen ta fito su tafi

yana shirin shiga sukayi kacibis da ita

ke maza inda abinda zaki dauka dauko ki wuce gida

to tace tare da rabashi ta wuce

a ranshi yace wannan duk wanda ya aureki ya aurarwa kansa masifa da kudinsa

bakin mota ta nufa shi kuma yana ganin haka ya koma ciki

tana qarasawa bakin motar ta dubi baba habu tace

baba dan Allah inda hali aromin wayarka in kira daddy

mika mata yayi yana washe baki bayan ya matso number Alhajin

flashing tayi inda daddy na zaune yana cin abinci yaga shigowar kiran habu driver kuma yasan ya tafi dauko khadija hajiya ta fada masa dan haka yssan ba mamaki akwai magana shiyasa ya yi dialling number

muryar dije yaji dan haka cikin sauri yace lfy diyata?

lfy qalau daddy dama naga baba ne yazo daukata kuma ni gaskiya daman um....dama...kinga fadi kawai kanki tsaye khadija me kk bukata

dama cewa zanyi munyi magana ne da Aunty yusra da ita matar yaya habeeb shine suka ce in dawo nan da zama toh shine nace su fada maka wai bazasu iya ba shine nace ni bari na fada maka

dadi daddy yaji dan haka cikin sakin fuska yace kaji su to ai wannan ba matsala bane duk dayane ai naji dadi kwarai

to nagode daddy gobe abawa baba habu yakawomin unifoam dina zan wuce school in mun taso sai in biyo in dauki kayana

toh badamuwa Allah yayi muku albarka

ameen daddy ta kashe wayar tare da miqawa baba habu tace ya tafi kawai

ita ko ta juya ta koma cikin gidan

tana shiga falon ta tarar da su zaune jin bude kofar suka jiyo suna ganin dije kusan a tare suka furta lfy?me kika dawo yi kuma

bata tamka musu ba saita fara kokarin zama saida ta zauna kafin tace naji kunce kuna son nayi muku kwana biyu ne shine nace bari in zauna din yafi kada in tafi kuga rashin kyautawata ko mamy tayi fada

mun shiga uku🙆‍♀

🤣🤣

*vote*
*comments*
*with 08066364077*

*Alqalamin khady✍*
🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*TA ME GARI*

1⃣6⃣

*ina neman afuwan mutane pls dan Allah ku dinga min adalci nasan masoya basa yawa kuma daukaka daga Allah take ina iyakar kokarina wajen ganin na faranta ran kowacce a cikin masoya na idan kun tambayeni littafin daga farko ko wani page din ban tura muku ba kuyi min uzuri kun san jiki da jini kuma inada abin yi amma nake sadaukar da lokacina dan nishadin ku duk wadda take son littafin tayi magana group nasan zata samu pls afuwan dan Allah na kuma gode da soyayyarku gareni Allah ya bar kauna ya qara zumunci*

***

kut......in kin isa Allah ya tsinen ai wlh bazan zauna da 'yar jagaliya a gidana ba cewar yusra ta fada tana huci

shima nasir cikin hade rai yace ke ina wasa dake ne ?wlh tun muna mu kadai ki tashi ki tafi gida waye zai yadda ibola ta zauna masa a gida har kwana biyu ko ki tashi wlh ko in babbala ki a kwasheki a kaiki

gani sukayi ta miqe yusra da dama tun tuni ta miqe tsaye ta riqe kugu ganin dije tayo kanta yasata kwasa da gudu tayi bayan naseer wanda shima ganin dijen ta miqe ya danji wani abu a zuciyarsa amma fa gara ya nuna mata shima namiji ne dan haka saiya dake ya tsaya yana fadin ke yusra meye haka ban son iskanci

saida ta qaraso gabansa kafin ta kalleshi ido cikin ido shiko kawar da kai yayi domin shi in yana kallon idonta sai yaga kamar idon mage bare yanzu daya qara tabbatarwa kansa yarinyar nan ruwa biyu ce wato mutum aljan😂dan haka be son hada ido da ita kada yaje ko maguzawan ne akanta arnan farko su nuna masa basu san hasken addini ba

tsinkayar muryarta yayi tana fadin

haba yayana yanzu kawai dan nace zan kwana biyu gidan ka kk korata bayan kuma tun farko ku kuka nemi da in zo inyi kwana biyu a wajenku ai ko ba komai nayi muku haka dan zumunci amma tunda bakwaso shikenan

jin kalaman datayi yasashi sauke a jiyar zuciya domin yasan yanzu zata ce zata tafi amma me ?

sai ji yayi tace tunda na fuskanci baka son in zauna gidanku hakan na nufin tun yanzu zumuncinmu zai samu rauni kuma nasan megari bazaiji dadi ba bare iyayenmu dan haka na yanke shawarar zamana a gidan nan har sai ranar da nayi aure

😳

me?

la'ilahaillah anta subahanaka inni kuntu minazalimin

a'uzubillahi minasshaidanir rajim

ka manta baka hada da ayatul kursiyyu ba

cewar yusra dake bayan naseer wanda keta kwarara addu'o'i kawai dan dije tace zata zauna a gidansu

itako dije dariya ma abin yabata cikin zuciyarta tace ikon Allah sai kallo

ganin yaki yin shuru banda ruwan dala'ilai ba abinda yakeyi hakan yasa dije fadin haba ya naseer meye naga kanata addu'a ko wani abun ne yafaru ?

kinga khadija dan girman Allah da ma'aikinsa na rokeki ki taimaka ki koma gida kinji

to wai sbd me?

ta tamvaya

yasan sha'anin jinni be zama lallai yarinyar tasan meta aikata musu ba kuma baya son tasani dindan haka saiya waske yace kawai kinga mamy nada hawan jini ga shi ma yau mura take fama da ita matsananciya ina ma zargin limoniya gareta kinga gara kije ki zauna kusa da ita nasan zaki taimaka mata da wasu abubuwan

hakane kam yakamata in koma

yauwa qanwata ya fada a dan raunane

yusrah ma harda gyada kai tare da fadin wlh kam gara kije dan tayi kewarki

toh shikenan ta fada tare da fadin

ni zan wuce toh saida safe

Allah ya tsare ya kiyaye a sauka lfy

qofar falon ta nufa har ta isa sai kuma ta tsaya ta juyo yake sukayi mata tare da wiving din hannu ita wlh dariya ma suka bata dan haka saida ta dara tare da fadin

lah ya naseer meya sameku ne a fuska kaida aunty yusra naga duk kunji ciwo

saurin kallon juna sukayi kafin daga baya suka hada baki wajen fadin Accident

subahanallah accident kuma?da kura ko kuma da kare dan wannan ai naga ciwon kamar bada mota ko wani qarfe akayi shi ba ko

da biri mukayi fada naseer ya fada yana yashe baki

.biri kuma a ina?

ai da yake akwai shi a nan gidan toh shine ina masa wasa ya yakusheni yusra ma haka

.wow gaskiya wlh har kunsa nafasa tafiya sbd wlh ina son biri dama

.wayyyoooo 🤣

dan girman Allah ki tafi kawai gobe zan kawo miki shi

ah ah nidai ina son ganinshi wlh

ai nasa an kasheshi

what ?

kisa fa?

akan me?

.sabd yaji mana ciwo har haka saina lura gaba gaba zai iya daukar rai ma

amma ko wannan biri sai kace ba dan nigeria ba

ah ah dan boko haram ne

au dama dabbobi ma suna zama 'yan ta'adda

ai.....kaga dan Allah ka barta ta tafi dare yanayi kuma gashi taxi zata shiga Allah ya kaiki lfy sister cewar yusrah dake tahowa danta dan tura dije

au ni kinga ma fa na manta wlh aunty ashe fa baba habu ya tafi ko yanzu ya zanyi to ni dije ta fada tare da rike haba

.akwai abinyi kawai kinga bari nadauko miki kudi kishiga taxi tunda baki da su ko

ah ah barsu kawai inaga inada su a jakata zasu isheni zuwa gida

to a gaida su daddy zasu ji tace tana qoqarin fita

tana ficewa kuwa yusra ta rufe qofar tare da sauke ajiyar zuciya haka shima naseer din

bakin gate ta nufa gurin me gadin gidan inda ta samu guri tazauna suka shiga hira kamar sun san juna tun da can gumi fa ta hadu da anka nan kayan zance ya hadu sukaita zubawa kuwa kafin daga baya taji qarar mota a waje koda suka leqa baba habu ta gani da kayanta a akwati kin kim kim musa me gadi ne ya karbi kayan tace ya tafi kawai nan ya juya ya musu saida safe

ganin dare nayi ne yasata miqewa tare da fadin toh baba musa zan shiga ciki saida safe ko

toh hajiya mu kwana lfy

Allah yasa ta fada tare da jan trolly dinta

harta nufi part din su yusrah kuma saita fasa ta tsaya ta danyi jimm kafin ta juya akalarta zuwa part din su habeeb tana zuwa ta shiga knoking a hankali a daidai wannan lokacin suna zaune suna hira tare da dan taba kallo jin ana buga kofar yasa shi fadin waye a hankali

shiru tayi sai da ya qara maimaitawa kafin tace nice

jin muryar mace yasa sajida saurin miqewa ta nufi kofar tana fadin kece wa?

khadija!!

bude qofar tayi sukayi ido hudu da dije inda gaban sajida ya yanke yafadi ganinta da tayi da jaka dirkekiya

lfy ?

ta tambayeta cikin dan hade rai

kallonta dije tayi ganin yadda tayi mata tambayar yasata itama hade nata ran kafin tace lfy lau mana ta karasa maganar tana me kutsa kai palon

sai yanzu ya dago ya dubesu shima ganin dije da jaka yasashi mamaki tare da fadin ke lfy naganki da jaka haka kamar me shirin barin gari

guri ta samu ta zauna tare da fadin lfy lau wlh nadauka daddy ya kiraka yayi maka bayani ai shine yace in zauna inyi kwana biyu anan nama shirya zan tafi sai gashi yasa an aikomin da kaya na toh da zanje part din ya naseer sai naga kaine babba kada kaga ban kyauta ba gara in zauna anan ko

hmmm haka

tunda yace haka be qara fadin komai ba illa juyawa da yayi ya kalli sajida dake tsaye kikam ta zuba musu ido maida kallonsa yayi ga tv din itama sajida ganin haka yasata samun guri tazauna dan nesa dashi

sun jima a haka banda karar tv babu abinda kk ji a falon itako dije duk jikinta ciwo yake mata gashi tana jin yunwa ga bacci data fara ji

gyaran murya tayi kafin tace am yaya nace ba
Chapter 16 · 0% Book details