← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 59

Sashe 15

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dije na jinsa tayi luf tare da qara gyara kwanciyar kanta a kirjinsa dukansu sai suka tsinci kansu cikin yanayi me wuyar fassarawa dije kam sai sauke ajiyar zuciya takeyi tare da qara shakar daddadan kamshi turaren dake jikinshi har take taji wani bacci na shirin kwasheta

jin shirun da sukayi ne yasa naseer leqowa dan duk su yusra da sajida gayyar tsorone hakan yasa suka kame a waje

yanayin daya gansu ciki duba da yadda yaga habeeb ya wani rufe ido bakinsa saitin kunnen dije gashi kuma ita ta wani lafe a jikinshi

duk radadin da ilahirin jikinshi keyi mishi sai yaji ya dena ji yayin da yaji zuciyarsa tayi masa wani irin zafi dan me zai rungumeta haka to me hakan ke nufi

jin shirun da matan sukayi ne yasa su dan shirin leqowa dan da alama abun ya lafa tunda sunji shiru aikuwa suna leqowa idon su yasauka akan abinda naseer ya kurewa gani

daram dammmmmm gaban sajida yayi dubs da yadda taga mijinta rungume da wata mace bata san lokacin datayi kansu ba tana zuwa tajanye dije daga jikinsa dije najin an jata tayi saurin qara langabewa ta zube a gurin

shi kuwa bude idonsa yayi a hankali ai kuwa ya saukesu cikin na sajida data kafeshi da ido ckin tuhuma waigawa yayi ya kalli inda dije ta sheme kafin ya maida dubansa ga naseer yace sai ku maidata gida tunda kun rama

yana gama fadar haka ya juya ya fice a dole sajida ta bishi itama............

*vote*
*comment*
*with 08066364077*

*Alqalamin khady*✍
[16/12, 11:41] ‪+234 806 493 3819‬: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

TA ME GARI

1⃣5⃣

team dijeee kuna qarawa wutar nan fetur sai dai fa kuma hmmm a dai yi shuru yanzu muci gaba da gashi

ga masu tambayar littafin daga farko masu kirana da masu yimin mgn ta pc pls ku taimaka ku dinga tambaya a group dina in baki ciki kiyi min magana zan tura link kiyi join nasan mutan gidana akwai karrama bako da kin tambaya zasu hau tururuwar tura miki dan akwai su da karamci 👍

ina mugu mugun ji daku member's na khadeeja fans novels😘

******

ita kam yusra ko ta kan dije dake kwance bata qara biba ta lallaba ta shige daki shima naseer din binta yayi inda ba shiri dole ya dauki emergency care box suka nufi part din habeeb yayi musu dressing kafin suka dawo ind take kwance har yanzu tana nan yadda suka barta itako dije bacci ne ma yadauketa a gurin sai sauke ajiyar zuciya takeyi cikin baccin

koda suka shigo suka risketa a hakan naseer ya kalli yusra yace ke jeki tasheta ta tafi gida

wani kallo tayi masa kafin tace kai ka tasheta mana

ah ah naga dai ai ke yafi cancanta daki tasheta tunda ke kika sa aka kawo miki ita

hmm lallai to ai sai kayi duba cikin ni dakai wayafi wani shan jiki kaga kenan wanda yafi wahala shine yafi matsuwa da a barshi ya huta ni zaka danawa tarko inje in tabata tayimin yadda ta yi maka ka ganka kuwa?ta fada tare da sakin dariya

kulewa naseer yayi kafin yace ban ganni ba amma na ganki ki duba gefen bakinki da kuma kumatunki ga dankwalelen cycle nan an zana miki na musamman dan haka ki wuce kije ki tasheta ta bar gidan nan ina zaman zamana ke da mamy kunja an rudamin jiki yanzu ta ina zan doshi zuba ruwa duk yarinya tabi ta yage mutane sai kace kura nk ina zargin ma a garin nan akwai damusoshi alamu sun nuna cikinsu ta girma ga kuma 'ya'yan aljanu nidai wannan yarinyar ba qaramar jaraba baba malam ya jefo mana ba

kaga ni wlh duk ba wannan ba yanzu dai ka samo min maganin da zansha wlh ji nakeyi fuskata duk ta daure

hararar ta yayi kafin yace toh duk azabar da kk ji bata kai ya wadda nake ji ba

suna tsaka da maganar dije tayi juyi tare da yin miqa alamar zata tashi

da gudu suka kwasa suna rige rigen shiga daki wajen shiga dakin ma yusra ta riga shiga inda tana shiga dai dai naseer ya kawo kai danya kutsa ai kuwa ji kk yi bamm tare da wani sauti qummmm goshinsa ya daki qofar ko zafin daya ji baibi ta kai ba ya danna qofar ya qarasa sa key din kafin ya jingina bayansa da kofar suka shiga maida numfashi kamar wadanda suka yi gudu ko wani aikin wahala

jin goshinsa yayi kololo ne yasashi sa hannu ya taba yaji zafi kuwa kallon yusra yayi dake zaune gefen gado tana mayar da numfashi kafin yace kinga maza ki kira mamy ta turo a kwashi yarinyar nan

da sauri ko ta dauki wayarsa ta shiga kiran layin mamy

tana dagawa yusra tace yauwa mamy pls ki turo a dauki yarinyar nsn pls

jin hakan da mamy tayi yasata fadin baku kuka ce a barta tayi kwana biyu ba meye kuma na cewa ta dawo yau ko har kun gama huce fushin naku ne?

ai gara kawai ta tafi din inba haka ba...fizge wayar naseer yayi tare da fadin hello mamy

au kana kusa ashe ya akayi ne naji kunce a turo a dauketa yau ince ko kaci ubanta dai ko

yasan halin mamy inya fada mata abinda ya faru zata iya sasu daukar wani matakin shi kuma a nashi tunanin ya lura duk lokacin da ya yima yarinyar wani abu toh sai yaga shi yafi cutuwa qara maimaita tambayar tayi hakan ya katse mishi tunanin dayake yi ko baka jina?

tun yaushe ma ai ba qaramar lallasata nayi ba i hp dai daddy ma baya nan dan ban son ya ganta a wannan yanayin gashi kuma yusra kinsan ta da rigima tace lallai saita koma yau dan wai kada inyi kisan kai ganin yadda na lugwiguita mata jiki

ah to indai haka ne gara ta dawo din dan daddy'n ku yana nan kada kuma ya ganta yace meya sameta ta fada mishi gaskiya kasan shi fa akan yarinyar nan kamar wanda aka sihirce dan haka inaga kawai ku barta ta qara kwana kafin nan ta dan murmure sai ta dawo bayan ya tafi ni kuma in barje nawa haushin

no mamy ai duk hukuncin daya kamata ayi mata zan gama yi mata kedai barni da ita kawai amma dai ki turo a dauketa din kawai

tunda kun matsa dai to ka kawota mana kaga ma saika san abinda zaka fadima daddy'n naku ka fadi wani laifin tayi ka hukuntata

nikam yadda nake din nan ina zan iya fita ki ganni ya fada a zuciyarsa

ya naji kayi shuru

naga ne zaiyi wuya in samu lokaci dan inada meeting karfe 8 din nan na dare gashi zai daukemu lokaci kuma kinga ni inama zan sami time har inkawo ta kawai dai ki turo din inya so kisan me zaki fadawa daddy inya ganta ko kuma kawai ma ki hana haduwar ta so

ok to hakan yayi bani yusra

mika mata wayar yayi suka qara magana ta kashe wayar

******

shi kuwa habeeb ba qaramin fama yasha ba kafin sajida ta fahimceshi saida yasha aikin rarrashi tare da fada mata kalaman da suka kwantar mata da hankali kafin suka koma normal

****

ita ko dije koda ta farka ganin wai hartayi baccin gaske daga na qarya ganin yadda suka kwasa da gudu dazun duk tana kallonsu jin duk jikinta na ciwo ga kuma fatarta data tashi inda naseer ya daketa tunawa da abinda tayi musu kuma yasata sakin dariya tare da fadi a fili ta furta wlh tunda kuka yimin haka sau kun sani wato ni kuka kawo ga jaka kuyita dimata har kwana biyu hhhhhh bakusan dije bane na gwada muku kalata ta fuskar rahma kunki fahimta yanzu aka fara game din let's see who's d winner between us dakin dake pacing dinta ta nufa koda ta shiga hakan ya nuna mata bedroom din yusra ne dan haka kanta tsaye ta nufi toilet din dakin heater ta kunna har ruwan yayi dumi kafin ta fara yin wanka tanayi tana wash tare da matsar kwalla tana kuma ayyana irin fansar da zata dauka akan su

niko nace dije banda kuma kisan kai 🤣

ta jima sosai kafin ta gama ta dauro alwala tana fitowa ta bude wardrope ta shiga neman kaya sai kace dakinta tasan duk kayan yusra sun mata yawa duk da ba wai sosai ba dan haka ta shiga neman ko doguwar riga ce cikin sa'a ta samu kasancewar rigar nada madauri saitayi mata dai dai bayan tayi sallah ta fito farlon inda ta hango mutan gidan nata zuro kai ta qofa suna leqe

duk tana lura dasu ta share su ta zo parlour ta zauna tare da dora kafa daya kan daya ta shiga tunanin meya kamata tayi musu ne ma

ba ta jima ba ta tsinkayi bugub qofar falon tare da sallama kwarai ta dau murya ta baba habu driver ce amsawa tayi tare da fadin ana zuwa

su kuwa mutan gidan sunaji aka fara takaddama nasir yace yusra ta fita ita tace shi ya fita kowa yaqi fitowa cikin hasala yace wlh dai kinji kunya wai wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar tasa ki kasa fita dan tsoro

mun dai ji kunya ni da kai idan kai ka kirani babba akanta amma akanmu fa nida ita ai kaine kai kuma yakamata ka fita ka sallameta tunda kaine me gidan ni kam bazan je ba dan ko yanzu ban gama jin zafin ciwon jikina ba haka kawai yarinya ta zo ta qaramin wani ciwon kana gani ma dan raini harda samin kaya ni inka fita ma kaja mata kunne ta ciremin kaya wlh ko inzo inci mata uwa

bude qofar gayi tare da fadin zo ki je da kanki ki fada mata zuwa da kai ai yafi sako maza zo ya fada yana me nuna mata hanya

wlh ba inda zani dan ba sunana saratu ba zan iya zuciya in shake yarinya har saita mutu kaga ko maganin kada ayi kar a fara wuce ka sallameta tabar min gida

yaso ya qara magana amma ya qyale yasan halin yusra akwai rai ni gara ya koma mata nasir din kada taga damar sa
Chapter 15 · 0% Book details