← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 59

Sashe 17

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallonta ya juyi yayi jin yadda take son yin magana dashi lallai ma yarinyar nan yafada a ranshi

itako ko'a jikinta tace wai azumi kukeyi ne a gidan nan?

cikin rashin fahimtar magsnarta yace kamar ya ban gane ba kina nufin na nafila ko me?

ah ah na dare nake nufi naga ne ko ruwa ba'a bani ba ga yunwa da nakeji kamar hanjina zai tsinke toh naga kada inyi nauyin baki tunda ni bana azumin gara a in magantu kada in cuci kaina

binta yayi da kallo wanda tarasa na meye shi kanshi ya kasa tantancewa ko kala be ceba taga ya miqe tare da daukar wayarsa ya nufi dakinsa

ganin hakan datayi yasata fadin to ko masauki a tausaya a bani ai ko tunda abincin bazai samu ba nazo gidan economic masu auna ci da ciyar da wani

rasa me zai ce yayi kaji yarinya sai kace irin kurege shi sam be son yawan magana bare wasa dan haka cikin dan hade rai yace ki tambayi matar gidan mana ai itace da gidan yana gama fadar hakan ya shige daki

sajida data tsaya kallon ikon Allah tare da nazari inda daga karshe taji dadin yadda habeeb din yai sannan tasaki ranta tare da fadin oh khadija baki abin magana ga gajen haquri tashi muje in nuna miki inda zaki sauka

ok ta fada tare da mikewa dakinta dayan takaita inda tace ta zauna a kawo mata abinci

ah ah ni ai a gidan nan nafi qarfin a kawomin kice dai in tashi in dibarwa kaina kawai in hidimtawa kaina kada kizo inga laifinki kin san hausawa sunce mu dangin miji ba'a iya mana

kallonta sajida tayi tare da nazarin yarinyar wannan yarinyar fitinanniya ce ta qarshe amma zanyi maganinki ta fada a ranta........

naso inyi muku yafiv haka amma kaina ciwo yakeyi bacci😚

*vote*
*comments*[3/14, 9:18 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀

TA ME GARI

1⃣7⃣

nayi adungure na wulwula na heqo na mazgo gaisuwa ta tare da jinjina ga dukkan masoya ta me gari tare da jinjinar ban girma ga members na khadija. fans novels 1 da khadija fans novels 2 ina ganin comments dinku gaskiya kuna yin dije da yawa 😘

miqewa tayi ta tabi bayan sajida wadda ke ganin ikon Allah ganin da gaske take bin nata zatayi yasata juyowa tare da fadin

haba qanwarmu ai kya tsaya inyi dawainiya dake ko iya na yau ne ko a matsayinki na bakuwa kamar yadda kk fada

dakatawa dije tayi tare da fadin ah ah matar yaya bawai fa wani dalili yasa nace ki bari in nemawa kaina d'a'amin ba kawai sai dan kin san iyawa mutum sai Allah kuma gashi naga bakisan da zuwana ba kada in saki wahala kije kawai ki kula da mijinki dan naga alamar ke yake jira bakin ciki ya cika masa zuciya kije ki rarrasheshi

kallonta sajida tayi tare da fadin wane irin bakin ciki kuma ?

ah bakin cikin zuwana mana shin wai be baki labarin abinda ke tsakaninmu ba?

dammmm gaban sajida ya fadi cikin karfin hali tace meye tsakanin kun ?

ah lallai da sauran ku tunda har yanzu be fada miki ainihin sahihin abinda ya hadani dashi ba

zuciyar sajida fa tafara cunkushewa jin yarinyar na ambatar wai alaqa tsakaninta da habeeb shin me hakan ke nufi?wace alaqa ce kuma?to ko dai ya so yarinyar ne ?kai no habeeb dake son babbar mace wadda ta iya tattali irinta me zaiyi da wannan berar wadda inba kayan fitina da jaraba ba ba abinda ta ginu akai dan haka cikin dan hade rai tace ai ke yakamata ki sanar min alaqar ba shi ba

kallonta dije tayi ta nazarci matar tun dazu ta karance ta akwai kishi dan haka saita kiyasta a ranta kawai inta yi mata wani rashin kyautarwa wlh ta hakan zata azabtar da ita

itako sajida haushin yarinyar ta tsinci kanta da ji dan sai yanzu ma taga meye dalilinta na tsayawa ta biye mata yarinyar da bata wuce sa'ar kausar ba autar su dan haka saita sa kai da niyyar ficewa daga dakin muryar dije taji na fadin

.yauwa Aunty jeki bashi haquri ni bawani dadewa zanyi ba zan koma gida amma dan Allah a dan taimaka a qara yawan abincin gidan kar ayi la'akari da girman mutum shi ci ba'a nan yake ba kada ki ganni siririya wlh rainon kauye ce dan haka a taimaka kada a tauye ma cikina hakkinsa kuma kada ki manta kice masa ya baki labarin zuwansu qauye last

ko ta kanta sajida bata bi ba tasa kai ta fice itama ta fito sajida na kokarin shiga dakinta ta tsinkayi muryar dije na fadin

aunty inane madafa?

kamar ya ?

ashe fa matar yaya 'yar gayu ce na manta wlh

i mean kitchen?

nuni sajida tayi mata da hannu inda tai shigewarta daki

tana shiga dije ta kwashe da dariya tare da qarasawa kitchen din ruwan tea kawai ta hada tasha dan duk jikinta ciwo yakeyi har yanzu musamman gurin da nasir ya riqeta a nan ta shanye shayin ta gama ta koma masaukinta tare da bude jakarta ba kayan bacci ciki dan haka ta kwanta abinta a haka da kayan yusra🤣

tana shiga dakin ta sameshi gaban mirrow yana fesa body spray a dan hade rai ta qarasa ta karba ta shiga fesa masa duk yana lura da yanayinta kasancewar ta mace me iya tattali da soyayya sajida ta waye kwarai ta san hanyoyin mallakar miji cikin sauki ba boka ba mallam tasan kissa kala kala hakan yasa ta mamaye zuciyar habeeb domin shi dama dan son rayuwa ne kuma saiya samu me tarairayarsa duk yadda yake da jin kai da miskilanci to fa a gaban sajida tamkar yaron goye yake kuma yana iyajin zai iya mata komai a rayuwa dan haka koda yaga yanayinta yasan akwai damuwa damuwar kuma bazata wuce akan zuwan dije ba dan yasan sajida akwai kishi dan haka saida yabari sun gama shirin kwanciya kafin ya jawota jikinsa cikin salon tasa soyayyar ya shiga fadin

what's wrong with my princess ?

uhmm ?

shuru tayi kafin zuwa can yaji tace

mece sahihiyar alaqarka da khadija?

cike da mamakin tambayar datayi mishi yace kamar ya ban fahimta ba inaga ai kinfi kowa sanin matsayinta a gurinmu ko?

hmmm amma ai tace in tambayeka ainihin sahihiyar alaqar dake tsakaninku wai a kauye shine nake son jin ko akwai wata a qasa ne

murmushi yayi a zuciyarsa tare da fadin lallai yarinyar nan bala'i ce ko ince annoba ifritu wato tayi nazarin hallayar sajida harta zurma ta ita kuma duk da girmanta da shekarunta ta kasa fahimta wannan akwai shegiyar yarinya wato so takeyi ya bata labarin abinda tayi musu a qauye abinda ya barshi a sirri baya fatan matarsa tasan abin kunyar daya faru shine take son fallaso shi ai wlh gobe korata zaiyi gidan nasir suje can su karata tunda su sun saba wristilling da ita

jin yayi shuru ne yasata fadin kayi shuru baka bani amsa ba

oh baby matsala wlh wlh kinji na rantse miki wlh babu wata alaqa tsakanin mu in ba matsayinta na qanwa garemu ba ke ni wlh banma santa ba sai zuwan da mukayi time din da muka dawo nigeria daga nan tsohon nan ya hadomu da ita shine silar zamanta a gidanmu so banda wannan alaqar banga wata ba amma ban san dalilinki na tambayata ba

hmm ai dole in tamvaya ganin yadda kayi mata dazu a gidan naseer kuma gashi yanzu ta dawo nan amm.......shiiiiiii ya fada tare da dora yatsan shi a saman lips dinta haba baby ya kk son maidani baya ne me kk tunani namijin dake da mace kamarki shine zai iya hango wata to kisani wlh inda ana ciro zuciya to dana ciro mikitawa kinga yadda nake sonki nake ji dake ke wlh ni ko wacce mace kallon 'yan daudu nake musu kuma ma in zaki hadani da wata ina laifin ma ki hadani da ta kwarai saiki hadani da hambirin hayam wlh kin cuce ni kin san yadda na tsani yarinyar ma kuwa wlh sbd daddy yasa nake raga mata kuma bana son raini shiyasa kika ga ban. fiya shiga shirgin kowa ba sai naki ke kadai keda habeeb kisawa ranki ko'a lahira bazan miki kishiya ba bare gidan duniya da sai naga wadda taimin zan aura dai ko ? to duk ba wadda tayimin sai fadimatuz zahra'u sajida,batula,Aliya,kamila,sharifa,zakiyya.....zai ci gaba ta katse shi ta hanyar mannewa da jikinshi tare da aika masa da rikitattun sakonnin da suka sa ya kasa qarasa wa ya shiga maida martani ita ko ta dage wajen ganin ta biyashi tukwicin kalamansa masu tsadar gaske a wajenta nan suka lula duniyar masoya

Asuba ta gari

*******

ana kiran sallar asuba a kunnen dije koda ta farka tayi sallah ta yi addu'ointa kamar yadda ta saba kafin daga baya ta miqe ta afka kitchen break fast me rai da motsi ta hada sannan ta jera saman dinning kafin ta koma daki wanka tayi tare da shiryawa cikin unifoam dinta sannan ta fito saman dinning ta nufa ta fara karyawa amma bataji alamar mutan gidan sun shirya fitowa ba gashi har kusan 7:15 sai da ta gama karyawa tsaf kafin ta miqe ta nufi dakin dataga sun shiga jiya

kwankwasawa ta shiga yi

ya akayi ne waye ?

taji muryar sajida na fadi

au to bakuwar gidan ce naga shuru ne me gidan be fito masallaci ba shine nace bara in sanar muku ana shirin tada sallah ya gaggauta koya samu jam'i don kin san sallah in rana ta fito ba kyau gara a yita da duhun asuba

bude qofar sajida tayi tare da kallon dije jin abinda ta fada mata wato dai so takeyi tace basa tashin asuba kenan shine ta fada a fakai ce ganin ta cikin shirin makaranta yasata fadin to tasalla munji mun tashi ai a bari mu gama kimtsawa sai mu fito ko?

ah ah in dan ta dije anty ku koma bacci nidai kiramin me gidan a sallameni in tafi naga zan makara

gyaran murya yayi daga bayan sajida shirye yake tsaf cikin kayan suit ash colour sunyi masa kyau matuqa cikin hade rai yace lfy nake jin hayaniya
Chapter 17 · 0% Book details