← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 59

Sashe 53

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun ranar da suka koma gida ta shiga tsananin damuwa domin kuwa ko abinci Bata ci Banda kuka ba abinda takeyi,mahaifinta yayi rarrashi harya gaji domin shi baisan ainihin abinda ke faruwa ba,illah kawai sunce Masa Habeeb yayi tafiya ne shine tasa damuwa a ranta danya tafi da amaryarsa.Hakuri ya shiga bata tare da nasihohi da haka har tafiya ta kamashi ya bar kasar.

Yauwa kamar kullum tana zaune a dakinta duk ta bi ta rame ta fita hayyacinta,mahaifiyar ta ce ta shigo dauke da faranti a hannunta abinci ne da ruwa tare da lemo Mai sanyi,Saida ta ajiye ta Sami guri ta zauna sannan ta kalli sajida data gyara zamanta tare da sunkuyar dakai.

Cikin bacin Rai mahaifiyar ta ta Fara magana, wato ke bakyajin magana ko? Kin bi kinsa tunanin banza da wofi a zuciyarki Akan wani banza namiji,yanzu ke a haka kike son mu tunkari abinda ke gabanmu,kin San ko Ni kaina inajin takaicin abinda ya faru Dan koba komai in waiga in kalleku zagada zagada keda kannenki gabana ai dole gabana ya dinga faduwa,tunda kin samu kin auru ai bazan Bari inyi gangancin da Zaki fito ba,ba boka ba malam Amma wallahi Saiya shigo hannu Dan haka ki kwantar da hankalinki ki samu ki murmure mu tunkari yakin Dan muyi nasara.

Sosai taji dadin maganganun mahaifiyarta Dan haka ta saki ranta taci abinci tare da kudirewa ranta saita Rama abinda Habeeb yayi mata.,tunda ya kasa Mata uzuri.

**** *****

Tayi cikin farin cikin komawarta dakinta,da farko Naseer shareta ya shiga yi,Saida ta dinga kwantar da Kai tana bashi hakuri, albarkacin cikin jikinta ya shiga tausaya Mata kasancewar cikinta ya tsufa sosai suna jiran hukuncin ubangiji ne,

Zamansu da Zainab kadaran kadaham babu Mai shiga shirgin wani in Naseer baya Nan Amma in Yana Nan saika rantse da Allah ba Wanda ya fisu hadin Kai,hakan yasa hankalinshi ya kwanta har wata Yar kiba yayi.

*****

Tun sassafe yasa ta shirya suka wuce asibiti,sawa yayi akayi Mata duk wani gwaje_gwajen Daya Dace,inda result ya tabbatar tana dauke da ciki,sai dai akwai maleria fever dake damunta,sosai yayi farin cikin kasancewar cikin dan haka ya kasa boyewa,ko kadan Bai fada Mata ba illah lura datayi Yana cikin farin ciki sosai.

A zuciyarta ta furta to kodai farin ciki yakeyi da ciwon nata ne!

Dan haka cikin kulawa ta kalleshi tare da fadin,

"Wai Ni me yake damuna ne da akamin test?

Murmushi taga yayi abinda ya dada kular da ita kenan Dan haka tace au ciwon nawa ma abin dariya ne kenan?

Ah ah abin farin ciki dai.

Na shiga uku Yaya dama ana farin ciki da ciwon mutum?

Sosai ma kuwa ya Bata amsa tare da mayar da hankalinshi ga tukin da yakeyi,

Ji yayi tasa Masa kuka tare da fadin ai Ni dama nasan wallahi karya kakemin da kacemin Wai kana Sona Ashe kiyayyata dakai har takai haka! Ina ciwo kana murna shikenan Nan ta fashe da kuka.

Baiyi Mata magana ba har suka karaso gida suna zuwa,ko Gama parking baiyi ba ta bude murfin ta fita,Yana Gama parking din yabi bayanta Dan yasan wannan chakwakiyar dole ya warwareta.

*Alkalamin khady* ✍
[7/9, 8:59 AM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*AWESOME WRITER'S ASS..*🏮
(*_palace of excitation n'd pleasant writer's*_

*TAME GARI*

NA

Khadeeja Usman

5⃣9⃣

Koda ya karaso ya tarar da ita harta karasa daki tana zaune saman kujera tana kuka,shuru yayi yayin Daya zuba mata idanu,sannan ya zuba hannu a aljihu,ya jima tsaye a haka,ganin kukan nata yayi yawa zai iya sata ciwon Kai Wanda hakan matsala ne ga rayuwarta yasa shi matsawa kusa da ita ya zauna tare da dagota,

"Haba my lovely sister,meye abin kuka Kuma? Uhmmm fadamin kinji! Ya karasa maganar Yana jawota jikinshi.

"Bawani your lovely sister ,kawai ka kirani da your hated sister,ai na fahimci komai yanzu wallahi baka Sona tunda har kake murna da ciwona".

"Ai ciwon naki ne na Dadi ne shiyasa".

Kara fashewa tayi da kukan,wato dama ana ciwon dadi?

"Sosai ma kuwa".

"To ta Yaya"?

"Yauwa to bara kiji yadda hakan ke faruwa,Amma saikin share hawayenki,kinji ko my....

Share hawayen ta shiga Yi harda gyara zama,to na daina kukan ta fada a Dan shawagwabe,yanayin yadda tayi maganar Saida tasa tsikar jikinshi tashi,Dan haka sosai ya jawota jikinshi ya mannata Nan ya cire Mata gyalen data yafa ya ajiye a gefe,dankwalin ma cirewa yayi Nan ya shiga shafa gashin kanta ,sosai yanayin yayi musu Dadi su duka,hakan har ya shagaltar dasu da mantawa da batun bayanin ciwo,sosai ya shiga shafata yayin da yake bin ko'ina na jikinta yana kunna light,tuni suka birkice inda ya kinkimi abarsa suka antaya bedroom din su,Saida suka tabbatar sun samawa kansu nutsuwa,sannan kowa yaje ya tsarkake jikinshi.

Ba wani jimawa zazzabi ya rufeta,hakan yasa ya tuna da maleria da akace tana damunta,wadda yasan dole sai anyi treated dinta,fita yayi ha hado Mata tea Mai kauri,Saida ya tabbatar ya Dan huce sannan ya tasheta ya dinga Bata a baki,ko Gama Sha batayi ba ko ta shiga kwara amai,Saida ta amayar da duk abinda ta Dan Sha sannan ya kamata yakaita toilet ya wanke Mata jikinta ya daukota kamar wata babydoll,sosai tayi mamakin ganin ya zage Yana gyara gurin batare dako kyankyani ba,Saida yaga gurin ya koma neat kamar ba abinda ya faru sannan ya dawo yaci gaba da Bata sauran tea din,anyi sa'a batayi Aman ba,tana Gama Sha ya Bata magani Nan ne ma tasoyin gaddama Saida ya lallabata sannan ta karba Tasha.

Ji yayi tace,"baka fadamin dalilin dayasa ake murnar ciwon mutum ba".

"Ai na dauka kin Manta ne kin hakura da ji".

"Ah ah! Ni ban hakura ba Ina son ji Dan Karin ilimi,

Kumatunta ya Kama yaja tare da fadin,"yarinya me wayo".

"Amma ai kin San me ake nufi da aure ko"?

"Ah ah! Ni ban sani ba".

"Toh naji baki sani ba,Amma ai kin San burin kowacce mace in tayi aure ta haihu ko?Amma ban San ko ke bakya so ba".

"Kan balastin! Injiwa yace maka bana so! Ga kawata can rufaida saboda Bata haihu ba har yanzu uwar mijinta ta tsaneta, wallahi nafi son na haihu,kawai dai Dan nasan Kai bakason ka haihu Dani ne shiyasa bakamin yadda akeyi a Sami ciki.

"To ya akeyi a Sami cikin?

A bazata taji tambayar Amma saita maze tace Nima ban sani ba Amma nasan da kanamin yadda kayiwa anty ai Nima Dana Sami ciki.

Shafa gefen fuskarshi yayi tare da sakin murmushi,sannan yace," to yanzu idan nace Miki kinada ciki to ya zakiyi?

Zaro ido tayi tare da fadin,"ta Yaya ma hakan zata kasance?

"Ta yadda nake bi da ke,shiyasa Kika ga Ina murna da rashin lafiyarki,domin na tabbatar nayi ajiya anan ya karasa maganar Yana shafa cikinta,.

Rasa me zatayi tayi,farin ciki ne kome ohoo,illah sinke kanta da tayi Wai ita kunya,jawota ya karayi jikinshi,tare da fadin kin gamsu yanzu Ina Miki abinda ake samun ciki,kin San dai bazai yiyu inyi Miki filla-filla a banza ba ko?,Kara rukunkumeshi tayi tana boye fuskarta sosai ya shiga shafata har baccin Daya zame Mata na gado ya saceta.

Kulawa sosai take samu daga gareshi da soyayya inda har take mamakinsa da yadda taga yanayi,Dan wani lokacin sai tayi da gaske yake fita aiki kullum rokonshi ta kula Masa da baby'n Shi.

*******

Yau Yusrah ta tashi da nakuda kasancewar tun safe aka kaita asibiti,Amma Bata haihu ba sai wajen karfe Daya, alhamdulillih ta haihu lafiya tasami da namiji,sosai kowa ke murna tare da Nuna farin ciki, Naseer baki yaki rufuwa hakama Zainab,wadda itama take dauke da nata Dan matashin cikin,kusan zance kowa yayi farin ciki da samun haihuwar inda mamy da Daddy sosai suka Nuna murnansu,sai washe gari aka sallami su bayan an tabbatar da lafiyar su,daga baby har Mai jego, direct mamy ta wuce da ita part dinta inda sam hakan baiyiwa Naseer Dadi ba.

Kwana biyu da haihuwa da safe su mamy na zaune itada da yusrah da wasu danginsu,yayin da Dije da Zainab keta kiciniyar aiki duk da mamy nata yada musu magana,ità Kam Dije dama dauriya kawai takeyi Dan zazzabi takeji.

Sallama suka ji inda suka juya gaba dayansu Dan Jin muryar Mai sallama,Sajida ce da mamanta,bayan sun zauna a mutunce su Zainab suka gaishesu inda ga mamakin su sukaga sun amsa cikin sakin fuska,har kasa sajida ta tsugunna ta gaida mamy,inda ta amsa ba yabo ba fallasa Dan haushinta da takeji na zubar da cikin da tayi,Basu nuna sun damu ba Nan suka yi Mata barka,sun dau lokaci shuru zuwa can maman sajida ta Miko medium akwatin da suka shigo da ita shakare da kayan baby,sosai fuskar mamy ta shakare da farin ciki,Nan fa ta Fara Saida tikitin godiya,kallon juna sukayi,suka kyafta ido sannan maman sajida ta Fara magana.

"Haba hajiya ai wannan ba komai bane yiwa Kai ne,Kuma ko ita Sajida ai Dan kaddara ta gifta ne wadda Saida muka fita da ita waje likita ya tabbatar Mana da cewa a I wani magani aka zuba Mata na gargajiya Mai hadarin gaske a lemo Tasha,shi Kuma Habeeb Bai wani tsaya dogon bincike ba ya yanke hukunci Wanda yasan yanZu duniya ta lalace kana tare da makiyinka ma baka sani ba,to yanzu dai Alhamdulillih ta Sami sauki likita ya tabbatar Mana da hakan,Dan haka yanzu ma zuwan namu da biyu ne,munzo ne bisa umarnin Mai gidan yace a karbo takardar Dan tasamu tayi aure zaman haka bashida amfani dan gashi Nan Dan ganinta da akeyi a gidan yasa an Fara tururuwar zuwa yanzu ma Dan gidan president ne ya makale.

Haba hajiya wane Kuma batun saki,Dan Allah bar wannan maganar,ai gara ya zauna da ita da ya zauna da dangin kauye,kada ki damu,yanzu ma ba inda zata tayi zamanta dakinta,Ni Dama nasan makarmashiya aka shirya,to abin ya karye naci dubu sai ceto,zai dawo ma ya sameni Kinga ki tafi kawai ki barta,ki bawa Alhajin hakuri.

"Ai da nace gara a rabun zaifi"!
Chapter 53 · 0% Book details