← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 59

Sashe 24

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

itama sajida a nata bangaren hakan take domin yau ta kudiri aniyar shayar da shi soyayya ta musamman amma sai gashi wannan matsiyaciyar yarinyar ta bata masu shiri ji yadda hancin mijinta ya wani maude abin haushin ma ga gobe yusuf zai zo da matarsa yanzu haka zasu zo su gansu sun canza kamanni kai wannan yarinyar Allah ya hadata da marurun rayuwa wannan jaraba har ina ga yadda ta kwaso a guje wlh ita ta dauka ma 'yan boko haram ne suka shigo anguwar ashe wai shirmenta ne gashi dai ta zama budurwa amma ba hankali tana tsaka da wannan tunanin taji muryar habeeb cikin dariya yana fadin sweety duk tunanina ne hakan ya fada yana me qara kunshe dariya iya kuluwa ta kulu amma itama data kalleshi taga yadda hancinsa ya wani bude yayi dirimm dashi ai saita fara dariyar itama ganin tana kallonsa tana dariya yaga yadda bakinta yakeyi shima sai dariya

haka suka dinga yi sam sun manta da dije wadda tun da ta shiga daki itama ta zube ta fara tata dariyar ganin yadda lokaci daya halittar mutan gidan ta canza gashi ta kubuta daga hukuncin laifin dazu sai da tayi me isarta ta miqe ta shiga toilet tayi wanka ta canza kaya kafin ta fito falon

koda ta fito bata iske kowa falon ba da alama sun shige ciki dan haka kai tsaye ta bude kofar ta fita ta shiga jido kayanta tana kaiwa dakin datake kwana

sai da ta gama tsab kafin ta duba saman dinning taga an shirya shi tsaf da abinci mai rai da motsi komawa tayi tayi sallar magrib inda ta zauna tana karatun kur'ani har aka kira isha'i tayi kafin ta miqe ta fito falon bata iske kowa ba nan ma da alama masu gidan basu da niyyar fitowa dan haka ta zauna ta fara harraka abincinta sai da taci ta koshi sannan ta kai plates din data bata kitchen ta dauraye su kafin ta koma falon ta zauna kenan kuma saita mike ta fice daga part din gaba daya

su kuwa masu gidan suna can cikin daki zazzabi ne ya rufe sajida yayin dashi ma gwaskan kansa ke masa ciwo ko yunwar ma ba ji sukeyi ba dan sajida ta rasa bakin cin abincin ji takeyi ya zuwa yanzu kamar bakinta ba'a fuskarta yake ba dan haka da kyar sukayi sallah suka kwanta aka shiga zaman kurame

part din su naseer ta nufa tana zuwa ta shiga bubbugawa a wannan lokacin suna zaune a falo sunyi jugum suna jiran ko ta kwana jin ana buga kofar yasasu kallon juna amma kowa ya kasa motsawa nuni naseer ya shiga yiwa yusra data je ta duba waye hararsa tayi tare da maqe kafada alamun taki din bata rai yayi wai shi me gida ya zare ido alamun ta tashi amma taki jin anata bugawa ya lallaba ya miqe cikin sanda ita ma yusra ta mike ta qarasa daga bakin bedroom dinta a cewarta idan abun gudun ne saita shige daga nan

kamar barawo yazo sata haka naseer ya dinga sanda kafin cikin murya me kamar rada ya ce waye?

ni ce cewar dije

jin muryar dije yasashi fadin lfy dai ko?

eh lfy ta bashi amsa tare da fadin fatan dai duk kuma lfy kuke

bai bata amsa ba illa sauke ajiyar zuciya da yayi tare da bude kofar ya ko ganta tsaye murmushi ta sakar masa tare da rabashi ta shiga ciki ya mayar da kofar ya rufe amma besa key ba saboda tsaro inji shi yusra dake can kurya tana kallon duk abinda ke faruwa har dije ta samu guri ta zauna kafin ta dan dawo falon tana yake nan dije ta gaisheta dukansu suna son su tambayeta meya faru dazu suna jin tsoro dan haka sukayi gum ganin babu me niyyar magana yasa dije takalo hira daga um sai um um haka aka dinga hirar itako dije da ba gajiya takeyi ba ta dinga digo da hira ganin da sukayi batada niyyar shuru yasa duk suka bingire suka shiga baccin karya ganin datayi sunyi bacci yasata miqewa ta fice batako tashe su ba su kuwa masu baccin karya ashe na gaske harya sacesu basu sani ba karshe dai nan suka kwana

****

tun asuba da dije ta tashi tayi sallah bata koma bacci ba wardrope ta bude ta shiga jera kayanta ciki tunda ita batasan da maganar zamanta gidan naseer ba dan haka ta shirya kayanta tsaf komai ta ajiye inda zata buqata dakin yayi kyau matuka data qara gyarashi kasancewar yau friday yasa take son shiga school da wuri dan da wuri suke tashi ta fuskanci 'yan gidan basa tashin asuba a cewarta dan haka ta ce bari ta samawa kanta abin kari ta wuce abinta

ga mamakinta koda ta fito saita iske saman dinning da kayan jiya karasawa tayi ta bubbude taga yadda ta barshi jiya haka yake to ko me ya hanasu cin abinci oho ita harta manta ma da abinda ya faru jiya dan haka saita shiga kitchen dan samawa kanta abinda zata ci harta yi niyyar yin nata ita kadai sai kuma taga rashin dacewar hakan duk da batasan dalilin yin hakan da sukayi ba amma dai tasan ba haka kawai bane dube dube ta shiga yi ganin botikin gyada da tayi yasata fasa dafa tea ta dama kunun gyada cikin qankanin lokaci ta gyara wake tare da markada shi ta soya kosai lafiyayye ta fito falon dashi ta kwashe kayan sama ta mayar kitchen ganin abincin ba abinda yayi yasa ta juyeshi ta sa a friedge tana fitowa ta ga sajida ta fito da alama bata jin dadi ganin yanayinta cikin kulawa dije ta shiga gaisheta ta so ta shareta amma saita amsa da kyar itako dije bata kawo komai ba ta dauka ko ciwon ne ya jiki aunty dije ta kara fada

hararar ta tayi qasa qasa bata ko amsa ba ta nufi kitchen dan sama musu abinda zasu ci dan da yunwa suka tashi

ganin da dije tayi ta nufi kitchen yasata fadin Aunty ga abin kari na hada mana gaba daya naga kamar bakyajin dadi

jim tayi kamar ta shareta sai kuma ta tuna da masifaffiyar yunwar da suke ji dan haka cikin hade rai bako walwala ta dawo ta nufi dinning sai yanzu ta lura da ba abinda ta dafa jiya da yamma amma bata damu ba ta juya ta nufi daki bata wani jima ba saiga shi sun fito ita da habeeb dukansu yau inka gansu babu wata walwala a tare dasu

gaisheshi dije tayi ya amsa ba yabo ba fallasa itako dije a ranta tace dama kun saki ranku dan indai nice tunda na ce zan zauna a gidan nan ko naman jikina zaku na yanka saina zauna din

kujera taja ta zauna nan ta zuba kunun ta a cup ta dibi kosai a plate bata ko kalli inda suke ba ta fara afkawa cikinta

bakaramin dadi yaji ba ganin kunun gyada da kosai yana son kunu sosai kowanne iri hakama kosai itama sajida tsintar kanta tayi da son cin kosan wanda ada sam bata ko son jin sunansa bare ace taci

zuzzuba musu tayi nan suka shiga aikawa kasa da hanci ba qaramin dadi sukaji ba su duka dan haka ko bakinsu ba'aji dije ce ta cinye nata kosan ta miqa hannu da niyyar debowa cikin kula danta qara taga wayammm

binsu tayi da ido inda ta kalli plate din gaban kowa taga shi habeeb saura uku ita kuma sajida sauran daya bata ko tsaya wata wata ba ta dauke nsu gaba daya cikin sauri suka kalleta amma ko'a jikinta taci mayar gabanta ta zauna ta fara ci

habeeb ne yayi qarfin halin fadin ke wannan wane irin iskanci ne mu sa''aninki ne ?

ah ah amma kuyi haquri naga ne ai ana barwa qarami dan ragowa ko zai bukaci kari to ku kuma naga kamar bakusan babba da yaro ba gashi ni ban koshi ba kuma ciki be san ayi masa kara ba musamman cikin kauye tunda ya riga ya saba da hatsi shiyasa na yi muku haka amma idan baku koshi ba ai naga akwai duk kayan hadin a gidan ni da ba manomiya ba kuma ban nemo na kawo ba bare ace zan hana kaga sai chair lady ta shiga ta qara maku wani tana gama fadar haka ta miqe ta shiga dakinta danta shirya ta wuce school

dukansu binta sukayi da ido sajida data gama kuluwa tace wai ni dear tsoron yarinyar nan kk yi ko kuma me? ta yaya kana gani yarinya tanawa mutane rashin mutumcin dataga dama amma ka kyaleta

to ke me zai hana ki dauki mataki ya fada yana me kokarin mikewa dan barin gurin

au hakama zakace ko?

to shikenan zan kuwa dauki matakin kamar yadda kace amma wlh matakin dazan dauka baxai yiwa kowa dadi ba dan ni ba ruwana da wata alakar dake tsakaninku ko kuma ran daddy'nku da zai baci wlh baxai yiyu ba ni ban haihu ba amma a fara kawomin jidalin dangin miji tun yanzu duka yaushe mukayi auren da har za'a wani kawomin wata watanma dangin dangarera inda ma qanwarka ce uwa daya uba daya amma cousin wlh ma an raina min hankali ta tafi gidan naseer mana ko dole sai nan yarinya sai jaraba da fitina baki kamar reza tunda ta diro gidan nan narasa kwanciyar hankali daga ni har sauran jama'ar gidan amma kun kasa daukar mataki ji yadda ka tsaya qanwar cikinka tana fada ma magana to wlh yau zanyi maganin
abun ta fada tare da kokarin miqewa shi kuwa habeeb da tunda ta fara magana ransa ya fara baci tsaye yayi ya zuba mata ido

itako dije ta fito kenan da niyyar tafiya ta ji sajida na sababi tsayawa tayi tana kallonta har zuwa lokacin data mike ta nufo ta gadan gadan tana kumfar baki

a inda dije take bata ko matsa ba ganin sajida ta nufota yasata fadin um um Aunty um um fa ina tausaya miki wlh kada ki qaraso

sajida da masifa ta rufewa ido ko jinta bata nuna tayi ba sai qara nufota takeyi yayin da dije tana daga inda take tafara dariyar mugunta abinda yabawa habeeb mamaki da tsoro kenan........
Chapter 24 · 0% Book details