Sashe 56
Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk abinda sukeyi Dije na kallonsu Amma ta share,tabaryar da muciya ta dauka,inda ta shiga aiki kamar yadda sajida tayi Mata,sosai tayi barna itama har Saida ta gaji,su kuwa su Sajida da zarar sunji karar fashewar abu sai su Kara curewa waje Daya.
Zama tayi tana maida numfashi,sannan ta Fara magana tana fadin,yanzu aiki ya kammala saura yiwa bil'adama bille,
Jin abinda tace yasa su Sajida rudewa da neman mabuyar datafi ta inda suke,kansu ne ya hadu ji kake kummmmmm, kowacce hannunta tasa ta toshe bakinta tare da matso kwallar azaba,a cikin wannan halin Sajida tayiwa Laila alamar ta Bata wayarta,da kyar ta lalubo ta cikin hand bag ta Mika Mata, number Habeeb tasaka ta shiga kiranshi cikin rudewa,Kira wajen biyar tayi Masa amma Bai dauka ba Nan ta Kara tsinkayo muryar Dije tana fadin yauwa Bari mu tashi mu Fara aiki Dan mu kammala da wuri,saboda yau zamuyiwa Mai martaba gyaran fuska.........
*Alkalamin khady* ✍
[7/9, 9:03 AM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*AWESOME WRITER'S ASSO....*
( _Palace of excitation n'd pleasant writer's_)
*TAME GARI*
NA
Khadeeja Usman
6⃣3⃣
Banda zufa ba abinda ke karyo musu gaba dayansu,wayar ta sake Kira tare da fadin "Dan Allah ka dauka Mana",tana Fadi tana yarfa hannu,harta Kiran ya Kara yankewa Bai dauka ba,Nan suka Kara jiyo muryar Dije tana fadin,
"Wai Kuna inane,Akuyatu"?kuyi sauri ku Kira su aunty arwanatu,da Yaya lugudanatu,ke nama Manta in ki biya ku taho da tumakatu 'yar sarkin wanzamai,da kawu kwaya-kwaya Dan Naga yafi iya irin na zamani,ku iso da wuri Dan Allah Kar Mai martaba ya gaji da jira ya Fara tsinke gashinshi da hannunshi.
Sosai cikin sajida ya bada wani sauti,ji kake kuuuuuuuu.....kallonta takai ga Laila taga yadda ta hada zufa ga wani marayan kuka da takeyi,tasa hannunta ta toshe bakinta,da sauri Sajida ta Kara Danna lambar Habeeb Allah Allah takeyi ya dauka.
Shikuwa Habeeb silent yasa wayarsa ya shiga wata tearter ne,kuma koda ya fito ya Manta Bai maidata normal ba,sai zuwa can ya tuna ya daukota,Yana daukowa Kiran sajida na katsewa, kasancewar bayada number,yasa shi niyyar sharewa,Amma Kuma Saiya ga missed calls Kuma da number,hakan yasa shi tunanin Kiran number yaji ko waye,Yana Kira kuwa yaji muryar sajida cikin tashin hankali tana fadin,
"Please Habeeb come and help us,wlh zata kashemu,Wai bille zatayi mana,Dan Allah ka taimaka kazo Yan......Bai ko karasa Jin abinda take fadiba yaji wayar ta yanke.Cikin kidima ya fito a office,kacibis sukayi da Naseer ya shiga tambayarshi lfy?,Sam yakasa bashi amsa illah fada mishi da yakeyi sun zo...sun kawo ziyara,cike da rashin fahimtar idan maganar sa ta dosa ya kalleshi Dan neman Karin bayani,Amma Ina! Har yakai parking space ya shiga mota,cike da mamaki yabi bayanshi shima a tashi motar, kasancewar ba Wanda yasan abinda ke faruwa a gidan hakan yasa kowa dayaji irin horn din da ake bugawa hankalinsu ya tashi,duk suka firfito suka tsaya Jin Mai zai faru.
Direct part din Sajida suka ga Habeeb ya nufa a guje,kowa Saiya rufa Masa baya,gani sukayi ya tsaya cakkkk....kome ya tuna oho?
Baya yayi sannan ya jawo Naseer ya tura shi gaba tare da fadin,
"Please bros ka taimaka ka shiga wallahi mutanen khadeeja ne suka tashi sun rutsa Sajida a ciki,ban San meke faruwa ba,Dan tunanina kada Susa tayi abinda zai Kai ga salwantar abinda ke cikinta,kaga ba ita kadai ba......katseshi yayi ta hanyar fadin,
"Ai wallahi Inka ganni a lahira kaini akayi,ka Manta irin azabar da muka Sha,sannan kakemin maganar Wai in shiga to Kai me zai Hana ka shiga tunda matarka ce a sunfi saninka a kaina"....
"Ba Wai batun haka bane,kaga Kai ka fini abin Nan shine nace,me zai hana Kai din ka shiga Inya so in kaga abinda ke wakana saika kiramu" ya karasa maganar kamar zaiyi kuka.
"Anki shiga din' nace Anki shiga din,wato Kai kaki Ni ka turani,toh Baga su mamy ba,su shiga Mana Dan ban San a yanayin daka iya riskarsu ba,Dan haka su da suke mata,Kuma manyanmu,su Fara shiga kawai mugani.
"Dan uwarka bazan shiga ba,Ni nace yaje ya auro irin aljanu,aiga 'yar uwarta Nan ita ta shigan Mana,sai Ni ko,salon a je a hada Dani tunda kun gaji da ganina to alkur'an ba inda zani,Jin muryar su mamy na tashi yasa su Sajida bare baki tare da sakin ihu.Sosai Habeeb ya Kara kidimewa,inda ya nufi kofar kamar gaske,Yana tabawa yajita Gam,Dan haka ya shiga murzawa,
Muryar Dije ya jiyo tana fadin,an Gama ranka ya Dade za'a hada harda na wajenma,ai da gudu Habeeb ya kwasa ya nufi bakin gate su mamy ma duka suka rufa Masa baya,suna kaiwa Nan suka tsaya maida numfashi,mamy ce cikin mayar da numfashi ta shiga tambayarshi meya sa shi gudu,?
Shima cikin haki yace, cewa sukayi Wai a hada damu".
Dafe kirji mamy tayi tare da fadin,
"Me za'a hada damu din?
"Nima ban sani ba,Amma Inaga salon azabar su ne na aljanu".
"Oh ni karima na shiga uku Wai ma waya tabosu ne?"
"Wallahi mama Inaga sajida ce Dan ga motar kawarta nana da alama tare suka jangwalo su".
To basai abin ya Kare akansu ba mu miye namu a ciki,cewar yusra dake kokarin sauke Sudais tana mikawa Naseer, Zainab ce tace ai kun San lamarin iska,su kan me uwa da wabi sukeyi.Haka dai suka tsaya curko curko,ganin hakan yasa baba Mai gadi ya karaso tare da tambayar su meke faruwa,sosai suka Masa bayani,inda ya tayasu jimami tare da fadin akwai shawara in kun amince,me zai Hana maza fade ta muji.
" Dama nace Mai zai Hana a kirawo irin malaman Nan masu rukiya! Kwarai kuwa ka kawo shawara cewar mamy Bari na Kira malam buba,ai ko tsayawa batayi taji me zasu ce ba ta matsawa malam buba Kira,Yana dayawa ta sanar dashi ya zo gidanta ba lafiya zai cire aljanu,Nan yace Mata Yana zuwa.
Sadaf Sadaf suka dinga tafiya kamar barayi,har suka karasa bakin kofar,suna zuwa da kyar Habeeb ya Dan matsa ta gefen window Wai ko zai gano wani abu,Amma ba halin ganin Dan ko Ina a rufe yake ruf,
su kuwa su Sajida,suna can Banda kuka ba abinda ba sukeyi, musamman da sukaji Dije na cewa a hada Dana wajen ai duk sai suka Kara karaya.
Itako Dije Saida ta tabbatar ta huta sannan ta yunkura tare da fadin,Yaya gurguwa tashi muje mu Fara kaddamar da aikinmu,tana mikewa ta shagide kafa da mere baki ta dauko lafciciyar wukar Nan ta cikin set din wukake,wato ta Sara Kashi,ta nufi bayan kujerar,Sajida data Dan zuro Kai Wai taga ya ake ciki taga Dije a haka ai saita mike tayi tsalle saman kujera,hakama laila,Nan suka shiga zagaya falon,itako Dije dada karkacewa ma takeyi tana fadin,haba bil-adam ku tsaya Mana ayi muku komai cikin sauki,na yantse a hankayi janyi muku,Kuma bajan bayi jininku ya juba a kasha ba duk Jan lashe.....wata uwar sufa Sajida tayi Saida hannunta ya bugu,Amma Bata ko tsaya Jin zafin da taji ba ta nufi kofa Allah ya Bata sa'a ta murza key ta bude,tana fitowa su Kuma saiga su mamy da malam buba............
🤔
To fa me zai faru kuma gaba! Ga malam ga aljanun Dije
😂😂😂🤣🤣🤣
*NIDAI BA RUWANA YASEEN*
*ALKALAMIN KHADY* ✍🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
AWESOME WRITER'S ASSO..
( Palace of excitation n'd pleasant writer's)
TAME GARI
NA
khadeeja Usman
hakika duk inda masoyi yake yanada Dadi,masoyana kune abin alfaharina, khadeeja novel fans daga 1 har zuwa 10 na yaba da kokarin comments dinku,da sauran group din da nake ciki,Ina alfahari da dukan masoya tame gari nagode sosai masoyana 😘
6⃣4⃣
Yana gaba su mamy na binsa a baya kamar barayi,itako Dije sunata faman zagaye ita da Laila a falon,Dan cewa tayi an Kara musu karfin hukunci yanzu Kam harda aski za'a musu,umarni ne daga Mai martaba.
Ganin shigowar su mamy,yasa Laila wage baki iya karfinta tana ihu,tana Kiran azo a taimaka Mata,Wanda sai a wannan lokacin Dije ta ankare da jama'ar da suka hallara a falon.Ji tayi ance malam gata Nan cewar mamy tana Nuna Dije,itako Dije ganin haka yasata sulalewa kasa tare da rufe ido Wai ita ta Suma.
Shi kuwa malam tunda ya kyalla ido yaga Dije Fara tas da ita,gashi tayi 'yar kubul- kubul,fatar ta sai sheki takeyi,saboda jaririn cikin dake jikinta,hakan yasashi lasar baki kamar tsohon maye, musamman Daya Kai duba zuwa kirjinta ganin yadda yake cike.
Juyowa yayi ya fuskanci su mamy tare da fadin,"gaskiya Hajiya lamarin yarinyar Nan babba ne,domin aljanun dake kanta sunada mugun yawa,Dan wallahi bazan boye muku ba 'yan daba ne akanta,Kuma 'yan daban ma rukakku,masu zukar wiwi.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,yanzu dama a aljanu akwai 'yan daba?"cewar mamy.
"Sosai ma kuwa hajiya,Kuma su matsalar su 'yan Sara suka ne,dan haka sai anyi da gaske kafin a fidda su daga jikinta,Dan haka sai kunyi hakuri kun Dan fita daga waje,Dan ba karamin artabu zamusha dasu ba",ya karasa maganar Yana gyara babbar rigarshi,tare da Kara Saba jakarshi a kafada.
Mamy ce tafara ja baya,tare da kallon sauran,Nan kowa yayi hanyar waje, Banda Habeeb Daya kafe,yace ayi komai a gabansa,Saida mamy ta janye shi tare da fadin inshi yagaji da rayuwa,to su suna sonsa a raye,badan ya so ba yabi su suka fita,bayan malam yabada umarnin a kulle kofar ta waje har Saiya bada umarnin a bude tukunna,aikuwa hakan akayi,duk suka fita yayin da shi Kuma ya sauke jakarshi ya nufi inda Dije ke kwance.
Tsaye yayi bisa kanta Yana me Kara Kare Mata kallo,Wanda hakan da yayi yasa Dije Dan bude ido Daya,karaf idonta ya sauka kan fuskarshi Yana lashe baki,ji tayi kamar ta tashi ta zura a guje,domin tasan yau asirinta ya Gama tonuwa.Tana tsaka da wannan tunanin taji hannun mutum a jikinta Yana shafata,tare da fadin,"gaskiya Hajiya kin biyani,yau can kwashi gara Danni dama nafi son irin wadannan iskar masu bugar da mutum,yanzu Dana Shaka Mata hodar Nan zansha budirina,inta dibar lamari,Ina Jan lokaci irin wannan yarinya haka.....jar fata kamar baturiya.