← Book details Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 59

Sashe 42

Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa Daddy Yana Gama musu jagora tare da Nuna musu kowanne sashi na bangaren amaryar sa wayarsa ta Fara ruri alamun Ana Kiran sa,hakan yasa ya fito ya nufo wajen,sai da ya gama wayar sannan ya nufo wajen daya hangi su mamy Amma ya Nuna Bai gansu ba Dan ya Kara kuntata musu Dan yasan ya zuwa yanzu sun shiga kidima da wani yanayi na kasa tantance meya ke faruwa.Yana fitowa ya hange su kuwa yashe a kasa,ita ko yusra h tana duke,cikin ko in Kula ya karasa inda suke,duk da yaga halin da suke ciki Amma ya Nuna Kamar Bai damu ba,Daya daga cikin direbansa ya Kira,cikin kankanin lokaci kuwa sai gashi Nan ya Kira su Habeeb yace suzo su taimaka asa uwarsu da matansu a mota akaisu asibiti.

Dukansu hankalinsu ya tashi ganin halin da suke ciki,musamman Naseer Daya san Yusrah nadauke da ciki Kuma yaga halin datake ciki,babu Bata lokaci suka sasu a mota suka nufi asibiti dasu,shi ko Daddy baiko bi ta kansu ba Dan ya San ya zuwa yanzu abinda ke damunsu kishi ne,Kuma burinsa ya cika,Dan haka Ya fito da waya ya Kira Hajiya baturiya yace Mata ya maganar da sukayi fatan komai ya kammala.

Amsa Masa tayi da an Gama komai ya zuwa yanzu dama jiran wayar sa takeyi.

Shikenan zuwa goben sai ayi komai ko?

Shikenan Allah yakaimu

Ameen!

Nan sukayi sallama ya Kira restaurant din dayayi order abinci cewar su kawo yanzu,aikuwa ba Bata lokaci sai gashi sun kawo abinci Mai Rai dai lafiya,Nan fa mutanenmu suka shiga kwasar gara da harrakawa.

***********

Itama yusrah kafin a karasa asibitin ta karasa sumewar hakan yasa ko da suka Isa duka daki Daya aka Basu tare dayi musu taimakon gaggawa kasanceawar tun suna hanya suka Kira Yusuf dayake Yana asibitin suna zuwa kuwa aka antaya wa su Hajiya mamy zurkudediyar alluran bacci,bayan an Gama musu duk abinda ya kamata an tabbatar sun farfado.

Suna asibitin Daddy ya Kira su yace su zo Yana son ganinsu.

Sun Dan jima kafin su zo suna zuwa yajasu part din mamy.

Bayan sun zauna ne yaga sun nutsu yayi gyaran murya tare da Yin addu'oi na musamman sannan yafara magana.

Nasan a matsayinku na 'ya'ya agareni nayi muku abinda ku kuke ganin ban kyauta muku ba,duk da cikinku babu Wanda ya nunamin hakan baiyi Masa dadi ba sai dai nasan kunyi shuru ne Dan kuyimin biyayya,Alhamdulillah naji dadi Kuma nayi farin ciki da Allah yabani yara masu biyayya

"Allah yayi muku albarka".

Ameen!!

Suka amsa gaba daya

Sannan Daddy yaci gaba,kuyi hakuri da auren Dana daura muku batare Dana tambayi Ra'ayin Daya daga cikinku,ko kuna da ra'ayin Kara aure ko bakuda shi,to banayi hakan bane Dan wani abu,ko dan na Bata ran matanku da mahaifiyarku ,sai dai nayi ne Dan gyara da duba duk abinda zai je ya dawo Nan gaba idan nabari abinda matanku da mahaifiyarku sukayi yaci gaba da faruwa,shiya sa nadauki wannan matakin,to Amma Ina son ku sani,Kamar yadda ban nemi izininku ba nadaura muku aure,haka Suma yaran da aka daura muku auren dasu babu wadda aka nemi Jin ra'ayinta Kuma suka amince,to dukanku munji dadi da kukayi mana biyayya Allah yasa yadda kukayi mana Allah yabaku masu Yi muku Kuma.

Ina son Kamar yadda kuka mini biyayya ku rike amanar da Allah ya Baku ku Kula da matanku,kuyi adalci tsakaninsu,ku tabbatar kunyi adalci dan gudun tashi da shanyayyen barin jiki ranar gobe kiyama,ku rike amanar da kuka dauka kuyi kokarin sauke nauyin dake rataye a wuyanku,Allah yayi muku albarka ya albarkaci aurenku da zuriyarku baki Daya,Ameen!!

Nan yaci gaba dayi musu nasiha Mai ratsa jiki da zuciya,sai da ya gama kafin ya shiga sanar musu plan din daya shirya akan su mamy har sai sun gane kuskurensu,Nan ya fada musu shirin dayayi gobe,dukansu sunji sun Kuma gamsu Dan haka ya fada musu plan dinsa na farko Daya shirya.

Kuyi managed

*Alkalamin khady* ✍
[3/18, 8:07 AM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*AWESOME WRITER'S ASS..* 🏮
(Place of the excitation n'd pleasant writer's)

*TAME GARI*

NA
khadeeja usman

4⃣6⃣

Kamarya!! Na kwantar da hankalina,bayan Ina ganin gayyar mutanen garinku a gidana,wato bayan wannan kodaddiyar Mai zubin mayun,harda Karin mutum biyu aka samu,no wonder,ashe shiyasa na dinga mafarkai kaje gidan marayu da sansanin 'yan gudun hijira ka debo mutane ka kawo su gidan nan,Ashe wannan gayyar ne suka bugo Mana sammako,ni wannan rashin son 'ya'ya irin na saude da inusa ban San Ina zasu kaishi ba,inba haka ba 'yar kwaya Daya ku gagara riketa,duk nasan kwadayi ke dawainiya da su,shine wato Dan sunga ita ta samu gurin Zama shine harda tattago wasu da hadota dasu,to wallahi Sam bazan lamunta ba dole su tattara su koma inda suka fito a yau basai gobe ba.Ta karasa maganar tana wani huci,idonta na kan mama mariya dake hakimce kan kujera,Jin maganganun da mamy ke Fadi yasata harde kafa Daya kan daya.

Duk abinda ta fada baisa Daddy ya Nuna Mata bacin ransa ba ko kadan,Dan yasan abinda zataji yanzu shine zai daga hankalinta,ya wargaza nutsuwarta,dan haka cikin sanyin murya ya Fara Mata magana.

Haba uwar gidana,me yayi zafi haka,kada fa ki Manta kece sarauniyar gidan gaba Daya Kuma shugaba a cikin gidan,ai irin wannan Bai Dace da tauraruwa Kuma lantarkin gida ba,Dan haka kiyi hakuri kizo kisamu guri ki zauna kiji me zan fada muku.

Wani sanyi taji a ranta,Wanda yasata sakin karamin murmushi ya lura da hakan,ita ko a zuciyarta tana ayyana idan har Zama suka zo yi to kuwa saita maida su kamar bayi,Dan duk masu aikin gidan sallamar su zatayi,daga mazan har matan Kai har maigadi ma,da wannan tunanin ta karasa ta zauna tana karkada kafa da hura hanci,Nan surukan suka shiga gaisheta,sabanin yusrah data mike ta fada jikinta tare da sakin kuka Mai sauti.

Cikin kidima ta shiga tambayrta me aka Mata ?

Cikin kuka ta Fara fadin wallahi mamy kice Masa ya sakeni,Dan wallahi bazan Kara Zama dashi ba,mugune Azzalumi Wanda Bai San kima da darajar soyayya ba,wallahi na tsaneshi,idan har Bai sakeni ba wallahi zan kashe shi daga shi har matsiyaciyar yarinyar.

Ban gane ba? Wace yarinya ce wannan da take Neman tarwatsamin farin cikin yarana?

Nuna Zainab yusrah tayi da hannunta.

Au! Au! Kice ku naku shirin na musamman ne,wato da tuggu da makirci Kika iso gidan,shine daga zuwanki yau Kika Fara shiga tsakanin Mata da miji ko? To wallahi baki Isa ba,inma uwarki ce ta kitsa Miki daga wannan bakin kauyen naku to kisani zaman maraya Dana karkara akwai bambamci,to Wai ma uwar me Kika kulla da har yaran da suke masifar son junansu kamar Laila da majnun suka samu sabani,har take cewa ya saketa?

Mamy Wai aurenta yayi.

Ke bana son iskanci wanne irin aure Kuma?to kodai kema kin shiga tarzomar mafarkin ne kamar yadda nayi?

Sajida dake zaune take Jin tamkar zuciyarta zata tsake ta fito,Dan ji takeyi duk wani abu da zasu ji to ko Rabin abinda takeji bazai kaiba,Amma sanin abinda ta shiryawa zuciyarta yasa ta danne tare da sakin murmushin dayafi kuka ciwo tace,tabbas mamy ba mafarki yusrah tayi ba gaskiya ne cewar duk mazajenmu sun Kara aure kamar yadda Habeeb yayi mun bayani, sakamakon rashin Jin maganar su da mukayi muka baro kauye Wanda sai yanzu nakejin tabbas bamu kyauta ba,abinda mukayi am........

Ke dayalla dakata ni bama na fahimtar ki sosai,shin mazajen naku ne suka Kara auren batare da ni mahaifiyar su na sani ba ? Shin Kuna nufin kucemin Kuma daga kauye suka dauko matan nasu? Kai wallahi karya ne.

Wallahi mamy gaskiya ne abinda Anty ta fada Dan Dana yiwa Naseer magana Akan inbai sakeni ba saina fada Miki sai yace ai harda kema anyi Miki Wai ina kyautata zaton ma itace wannan zaune kusa da Daddy.

Wayyo! Wayyo! Na shiga uku ni karima,kishiya da girmana Hamisu da gaske ne abinda suke fada? Ka fadamin inji ni aka yiwa kishiya,? Kishiya ma daga kauye? Wallahi bazai yiyu ba,nasan shirin mahaifinka ne,Dan ya tozarta ni,ni da zuri'ata,wallahi Bai Isa ba saina warware wannan mugun kullin da akaimun,yanzu na fahimci abinda ya faru,Amma yanzu zanyi maganin abun,Ina son yanzu ba sai andau lokaci ba Kai Habeeb da Naseer a matsayina na uwar data haifeku,ku warware wannan tsinannen auren yanzu ku sakar musu yaran su kafin nima nasan abinyi akan tawa,ta karasa maganar tana huci.

Dukansu kallon juna suka tsaya yi,yayin da shi Kuma Daddy ya tsaya Yana kallon mamy Dan yayi tsammanin fiye da hakan ma daga gareta,Saida maganganun data fada akan mahaifinsa sun Bata ransa Amma shi yasan matakin dauka yanzu.

Magana nake muku cikin tsawa ta fada,wadda dukan su su hudun suka shiga yanayin damuwa shikam Naseer a yanzu ji yakeyi daya saki Zainab gara tace ya saki yusra Dan ko zagin data Masa ya Isa ya saketa,shi kuwa Habeeb duk da baijin wani son Dijen a ransa Amma baijin ya tsani auren ko ita kanta,Kuma shi a tsarin shi ma babu saki ko da wa ya aura,Dan haka duk sukayi shuru.

Wallahi idan har baku sake su ba yanzu-yanzu na rantse da Allah saina tsine muku...

Ke kuma ki sani adadin sakin da sukayi kema adadin naki kenan! Cewar daddy Daya Mike cikin bacin Rai,yasan inda a abinda mamy ta tsana Bai wuce ace tabar gidansa ba,matar da ko 'yan uwanta Bata son zuwa wajensu,Dan haka ta girziza da jin furucinsa Wanda yasata saurin dagowa ta kalleshi.

Yes! nasan kinji abinda nace,

Yanzu Alhaji kana nufin idan yaran Nan suka saki wadannan 'yan kauyen Nima sakina zakayi?

Tabbas kuwa sakin ma uku!!

Idan Kuma na janye fa?

Aurenki na Nan.

Shikenan na janye furucina Amma Kai kana ganin kayimun adalci? Kayiwa yaran adalci?

Wannan ke kike ganin haka Dan haka na sallami kowa ku tashi ki tafi maganar da naso yi ayita wani lokacin,kuje Allah yayi muku albarka.....

*Alkalamin khady* ✍
[3/18, 8:08 AM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*AWESOME WRITER'S ASSO..* 🏮
(Place of the excitation n'd pleasant writer's)

*TAME GARI*

NA
*Khadeeja usman*

4⃣7⃣

Sam yusrah kin yadda tayi ta koma dakinta,inda mamy ta goya Mata baya tace tayi zamanta har saita Gama aiwatar da shirin datake yi akansu.Shiko Daddy Yana lura dasu Amma ya zuba musu ido yace gara ma ayi hakan an samu ragin wata fitinar.
Chapter 42 · 0% Book details