Sashe 50
Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda ta shiga Bata iskeshi ba,Zama tayi taci Hanjinta ta koshi sannan ta mike ta nufi kitchen a gaggauce tayi musu jellop din cous-cous Dan lokaci ya kure kunun Aya ta hada ta sa firji,Koda ta Gama anyi magrib Bata tsaya wanka ba Saida ta yi sallar magriba sannan tayi Koda ta fito ana kiran isha'i Dan haka ta shafa Mai tare da saka rigar data ware Dan yin sallah tayi sallarta,bayan ta idar ne ta shirya cikin wasu riga da siket English wear marasa nauyi light makeup tayi kasancewar ta me son yin kwalliya,ta fuskanci baya son shigowa gida sai yayi sallar isha'i Dan haka Zama tayi a Palo tare da kunna TV ta kamo tashar Arewa24 tana kallon shirin dadin kowa,Bata jima da Zama ba taji alamar shigowarshi,Saida ya karaso Falon sannan cikin cool voice tace mishi sannu da zuwa,amsawa yayi a hankali sai dai ya kafeta da idonsa Wanda yasa ta Kara sunkuyar da kanta kasa.
Shi kuwa ganinta yayi tayi wani masifar kyau kodai mutanen sunzo ne🤣.
Sam Bata San barinsa wajen ba illa jin Kara rufo kofar shi dataji.
Ya Dan jima sannan ya fito sanye da jallabiya da alama wanka yayi,Shima zaman yayi ya maida hankalinshi ga kallon,yaji muryarta tana fadin,
Nan za'a kawo ma abincin ko dinning zaka ci?
Shuru yayi da kamar bazai amsa harta fidda ran amsawarshi daga baya taji yace muje inci acan din Kar in Bata Miki guri ko.
Batayi magana ba ta mike ta nufi dinning area din kusan lokaci Daya suka Isa .
Bayan sun Gama cin abin cin sun dawo falo Basu jima da Zama ba bacci ya dauketa batare da saninta ba Wanda sai wajen asuba data farka ta ganta kwance saman jikinshi a kan gado sai taji kunya,a ranta ta furtaa Allah yasa Bai ganni Ina shararar da miyan bacci ba.
***********
Sannu sannu rayuwa na tafiya haka ta kasance a gidan Habeeb,inda yanzu kusan watan Dije uku da Fara kwanan Habeeb dakinta,sai dai a wannan zaman Dije ta Fara fahimtar halayyar Sajida,domin ta fahimceta a gaban Habeeb wani salo take nunawa na musamman tare da kulawa akan Dijen,sabanin inya fita da farko tana tsayawa taita Mata tambaya ya tsakaninsu da Habeeb,da taga Dijen ta ramfo ta takan Gaya Mata abubuwan da zasu hanata bacci,sai kawai ta canza lale dataga ya fita Nan fa zata hau zazzaga wa Dije kudirinta tare da fada Mata tun wuri ta tattara ta bar gidan inba haka ba sai tayi data sani.
Sam Dije Bata kulata ba Kuma ta fadawa kowa ba
*****
Yau ma fitarsa kenan Sajidar ta iskota har bangarenta,ta shiga zaginta tare da fadin inta Isa ta fito wallahi saita babbala ta,Kuma saita dauje Mata baki tasan Habeeb ko an fada Masa bazai yadda ba.
Ita Kam Dije yanzu Bata Tata take ba ta kanta takeyi Dan wani irin kasala takeji kwana biyu,ita mamaki ma take Bata wato ita Kuma nata salon kenan.sam bata zaci haka daga gun Sajidar ba ganinta wayayyiya amma Kuma yanzu ta birkice gaba Daya.
Yau Kam kin tafiya tayi ta dinga surfawa Dije zagi,wadanda har Saida sukasa Dijen zuge gilashin windo ta mayar Mata da martani.hakan ya kara harzukata tayitayi har ta gaji ta koma bangarenta.
Da daddare bayan Habeeb ya dawo,Bata ko Bari yaci abinci ba kasancewar dakin Dije yake ta shigo falon ta zauna,Dan yanzu ace duk wadda keda girki a ci abinci bangarenta.
Bayan sunci sun koshi yasa wadda ita dole tasa ta ci ga mamakin Dije gani tayi Sajida ta rike ciki tare da fadin wayyo Allah na shiga uku dear pls ku taimakeni kanwata wayyo zan mutu marata..........
Mamaki ne ya Kama su duka cikin tashin hankali duka suka nufota,rurrufe ido kawai takeyi tare da Kara ambatar wayyo marar ta cikin rudewa ya ciccibeta Dije ma hijabi ta dauko ta rufa musu baya suka nufi asibiti.
Suna zuwa babu Bata lokaci ya shiga duba matsalar Bai gama gani ba yaga jini na biyowa ta kasanta dai dai Nan Kuma bincikensa ya Nuna Masa lallai Sajida maganin zubar da ciki Tasha.
Innalillahi wa'innailahir raji'un! Kawai yake furtawa to meya hada sajida da maganin zubar da ciki,jikin bangon dakin ya jingina Wanda ya ya Fara wasu hawaye a fili ya furta why? Sajida? Meyasa Kika aikata hakan abinda ya zuwa yanzu nake lissafin zuwansa duniya.
Jin shirun yayi yawa yasa Dije bude dakin ta shiga,yanayin data ga Sajidan ciki ya daga Mata hankali ganin jini na biyowa kafarta,tana juyawa taga Habeeb na kuka,cike da mamaki da Kuma firgici tace.
Meya faru?
Yaya meya sameta haka ?
Ka duba halin datake ciki ka taimaka Mata Mana!
Khadeeja sajida ta cuceni,Sam Bata kyautamin ba,cikina,jinina,mafarkina,shi ta zubar min.
Subanallahi Dije ta furta.
Garin Yaya?
Ban sani ba Nima Ashe dama Bata Sona?
Ah ah Yaya jeka taimaketa Dan Allah she's need your help pls!
Ko kallonta beyi yasa Kai ya fice .
Jin maganarsu takeyi kamar a mafarki,Dan haka ta Mika hannu ta shafo zaninta Jin da gaske jinin ne ke binta tare da wani azababben wani ciwon Mara Daya taso Mata lokaci Daya wata Kara ta saki ta sumeeeeee........
Wohoho!
Ku biyoni Dan Jin ya hakan ta kasance dama hausawa sunce in zaka Gina Ramin mugunta ginashi dai dai Dan watakil Kai zaka fada😜
*Insha Allah Zaku dinga jina kullum zan Gama muku kafin axumi.*
*Alkalamin khady* ✍
[7/8, 9:10 AM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*AWESOME WRITER'S ASS..* 🏮
(Palace of excitation n'd pleasant writer's)
*TAME GARI*
NA
khadeeja Usman
5⃣5⃣
Cike da tashin hankali Dije ta fito daga dakin,kacibis sukayi da Naseer Wanda yaga lokacin da suka fito daga gida,ya lura kamar ba lafiya ba,hakan yasa ya biyo sahun su,cikin rudewa Dije ta shiga fadin,
" Pls Yaya Naseer ka taimaki Anty sajida, ban San meya sameta ba,Amma tana bukatar taimako"
Bai wani tsaya tambayarta Ina Habeeb ba ya nufi dakin dayaga ta fito,itama binsa tayi da gaggawa.
Koda ya shiga ya isketa cikin wannan yanayin tabbas ya razana shima,Dan haka wayarsa ya daga ya Kira doctor yusuf yasanar dashi abinda ke faruwa.
Bayan zuwan doctor yusuf din,
Fita Dije tayi ta jingina da kofar tare da kuka,tana tunanin to meya Sami Sajida haka?
Kusan mintuna talatin suka dauka kafin suka samu jinin ya tsaya,kowannensu cike da mamakin abinda suka gani,sai dai shi Naseer ya tahallaka faruwar hakan ga Dan uwansa,Dan yasanshi Sarai tun farko yace shi a ra'ayinshi bayason matarshi ta haihu da wuri,to Amma ai ya sanar dashi kwanaki cewa Sajida nada ciki,Kuma ga dukkan alama yayi matukar farin ciki da faruwar hakan Wanda a lokacin shi kanshi Naseer din har Saida yayi mamaki,aikuwa ya Zama dole yaje yaji dalilin faruwar lamarin dandai a yadda gwajinsu ya Nuna musu Sajida maganin zubar da ciki tasha.
******
Ba Wanda Habeeb ya sanarwa Sajida na asibiti daga Iyayenta har nashi,Wanda su Naseer sun dauka ya fada shiyasa Basu wani damu ba ganin wai ba Wanda yazo tunda dare ne,shi Naseer gida ya wuce ya bar su a asibitin Dan yaso magana da Habeeb Amma yanayin Daya ganshi shiya tabbatar mishi akwai damuwa,shiyasa ya kyaleshi.
Shima Habeeb din hakan take a gurinshi,inda yaja hannun Dije wadda keta rokonshi akan yabarta ta kwana a asibitin Amma ko kulata beyi ba,ya sata mota suka tafi gida.
*****
Tun asuba Dije data tashi Bata koma bacci ba ta tsaya ta gyara ko'ina tare da yin abincin da zasu asibiti dashi,Sam takasa gane matsalar dake faruwa, domin tana ganin jiya Habeeb kwana yayi beyi bacci ba, duk juyin datayi saita ganshi tsaye ko zaune Yana safa da marwa har aka Kira sallar asuba yayi alwala ya fita masallaci,acan Suka hadu gaba dayansu har Daddy Nan Daddy yaji Naseer na tambayar Habeeb ya jikin sajida.
Amsa masa yayi da cewar,
" da sauki"
"Assha" cewar daddy!
"Meya sameta?"
"Dan zazzabi ne Daddy Amma taji sauki"
"To Allah ya bata lafiya"
"Ameen!
Direct asibitin ya wuce Dan so yakeyi yaji ta Yaya hakan ta faru,sai dai Koda ya Isa ya tarar an Kuma Mata allurar bacci,wadda sai Nan da kusan awa Daya zata saketa,kujera yaja ya zauna ya zuba Mata ido Yana Mata kallon tuhuma.
Itako Dije Jin shuru Bai dawo ba yasa ta tabbatar da ya tafi asibitin,Dan haka ta shirya itama ta dauki abincin da zata Kai a basket ta shiga part din mama mariya ta sanar Mata, kasancewar Daddy na part din mamy ne,yasa mama mariya ta kirashi a waya ta sanar dashi,yayi mamaki kwarai da Jin Wai asibiti Sajida ta kwana Amma Habeeb Bai fada Masa ba dazu a masallaci,nan yace to suyi gaba ita da Dijen shima gasu nan zuwa.
Hakan ko akayi habu driver suka sa ya kaisu.
Suna Isa direct dakin suka nufa.
Yana Nan zaune yaga ta Fara motsawa alamun zata farka,sannu a hankali yaga ta bude idanunta fes,sannan ta fara kalle-kalle,har idonta ya sauka akansa,so takeyi ta tashi Amma sai taji jikinta yayi Mata wani iri,ba kwari.
A hankali yayo tattaki ya iso bakin gadon a tunanin ta taimaka mata zaiyi ta tashi sai Jin maganar sa tayi Yana fadin,
"Dama Sajida Ashe bakya Sona?"
"Ashe duk cewar da kikeyi kinfi kowa kaunata,da son ganina cikin farin ciki Ashe karya kike yi?"
"Laifin me na aikata Miki da kika zabi salwantar da gudan jini na,farin cikina a yanzu Wanda na tahallaka dukkan burikana akansa!"
"Meya hadaki da maganin zubar da ciki? In bakya son haihuwar ai saiki sanar Dani,ni Kuma zan durkusa na rokeki ki fadi ko nawa zan biyaki harki haifamin shi,Amma sai da Kika bari nasawa raina nima na kusa Zama uba sannan Kika Sha abinda yayi sanadiyar zubewar cikina, wallahi kin cuceni bazan ta......"
Sallamar su Daddy da su mama mariya da sun Dan jima da yawa amma dayake Daddy ya kirata yace suma suna hanya shine suka tsaya jiransu Dan su shiga tare....
*Toh fa! Ana wata ga wata,ku biyoni Dan Jin ta Yaya kaddara ta sauya lamarin Sajida har reshe ya juye da mujiya*
*Alkalamin khady* ✍
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*AWESOME WRITER'S ASS..*

5⃣6⃣
*Kuyi hakuri na rashin jina da bakuyi ba jiya,mun Sami matsalar wuta ne,Kuma ko yauma charji na kadan ne zanyi muku abinda ya samu*
****************