Sashe 23
Tame Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tunani tayi taga ko ba komai bai kamata tayi musu haka ba coz wannan fannin da ban amma kuma sai dai naseer yafi habeeb dan shi ya karaya da wuri ya bada kai bori ya hau dan haka nan ta shiga kici kicin kunce igiyar amma ta kasa tana tsaka da haka ta hango habeeb ya nufo gurin da take gadan gadan cike da mamakin yadda akayi ya fito ta kwasa a guje tayi hanyar gate ya so binta amma ya kasa dan shi bazai iya gudu ba sam duba da yadda yaga ta zura a guje kamar iska na qara mata gudun
kwafa yayi tare da qarasawa bakin kofar su habeeb da suma suke ta leqe ta window kamar maguna cikin dan zafi yace kai kuma dayalla malam saika bude ta kitchen ka fito sam naseer ya ma manta da wata qofa ta baya ta cikin kitchen sai yanzu sim sim ya juya ya nemo key din ya bude ya fito yana fiwo ko kallonsa habeeb beyi ba ya juya ya nufi bakin motarshi shima ganin hakan yasa be tamka mishi ba ya shiga tashi motar shima suka fita
ita ko dije cikin sa'a tana fitowa daga gidan ta ga motar makarantar su aikuwa ta afka aka wulla da ita
***
sam yarasa mafita game da lamarin dije yarinyar da gani kasan batada lfy duba da yanayin kiriniyarta da fitina gashi yanzu inya ce ta koma gida daddy zaiga kamar da wani abu ko ma yaga laifin mamy duba da yadda mamy ke nuna kin dangin daddy to yanzu meye mafita? yana tsaka da wannan tunanin naseer ya turo kofar office din tare da sallama
amsawa yayi tare da yi masa nuni daya zauna suyi magana
zaman yayi duk da shima yana son suyi magana dashi dan ita ta kawo shi amma bari ya fara jin tashi
bayani ya shiga koro mishi akan dije nan yake tambayarshi meye mafita ,?
wlh nima maganar dana zo da ita kenan gaskiya ya ksmata asan abinyi ni a ganina tunda dai yarinyar nan irin naci ce dangin laquwa kawai mu haqura ta zauna din kamar yadda ta nuna ta na son zaman tare damu sai dai mu kiyaye bata mata rai tare da duk wani abinda mukasan zai sa sabani tsakaninmu tunda dai kaga ita dangin ifritai ce da an tabata sai mutum yaji jiki mu samu mu gagganda mu aurar da ita cikin qankanin lokaci dan na fuskanci batada wani wayo kaga saimu dan sami wani galmashuran mu hadata dashi mu lallabata cikin salama a rabu lfy
Ajiyar zuciya habeeb ya sauke tare da fadin to ai duk ba wannan ba a ina zata zauna ? dan ni gaskiya zamanta zai kawomin matsala da sweety na duba da yadda yarinyar ke da rawar kai ita kuma sweety na ga kishi kuma ma ni bana son harkar hayaniya wlh ni ko kallon yarinyar nayi gabana faduwa yakeyi kada taje taci gaba da gayyato aljanun nan suna watanda da kayan gidana dan kaga ko na jiya fa maimakon suzo da nasu to nawa fa duk suka nakasa
jimmmmm naseer yayi ya shiga nazarin maganar habeeb lallai fa akwai matsala to ammaai ko su aljanun in ka lallabasu basa cutarwa a cewarsa
dan haka ya nisa yace wannan ba matsala bane saita zauna inda nake ko?
Alright indai kaga ba wata matsala ai shikenan amma wlh yarinyar nan ko yau dana kamata inaga saina kusa kasheta
dariya naseer yayi yace ka kusa kasheta ita kuma ta kasheka gaba daya ba ko kuma tasa ka kukan.....bari dai nayi shuru ya fada yana rufe baki tare da dariya qasa qasa
to dadin abin dai kowa yanada abin fadi
gaskiya ne amma na wani yafi na wani ba naseer ya fada yana qoqarin miqewa dan tafiya shima miqewar yayi yana fadin na sa an kira me gyaran doors din nan inaga ya zuwa yanzu an gyara
ok ya fada tare da sa kai suka fice gaba daya
*****
itako dije sam ta manta ma da tsiyar data shuka sai da aka kusa tashinsu ta tuna dan haka ta shiga tunanin mafita kawai in koma gida ince wa daddy nafasa zaman nan shi yafi min alkhairi dan wlh wannan me siffar mugun dawan ya rikeni kwanana ga kare yaje ma yayimin rauni a zo aurena a ragemin farashi
to wai ke dije yaushe kika fara tsoro ne kece fa uwar mazga jahannama ga fasinja dije Annoba fitinatu cewar wani bangare na zuciyarta
ke banza da ne nake amsa wannan sunan amma yanzu tunda na fara shan ruwan alwalar la,asar naji nafara sanyi ita kadai take ta surutunta a zuciyarta har aka tashi ta shiga motar komawa gida jikinta a sanyaye
ta jima zaune a unguwar nesa da gidan taki shiga kamar abin dole danma suna ci suna koshi a makarantar amma da yau taci ubanta da yunwa duk da tunanin matakin da habeeb zai dauka a kanta ya hanata sakewa taci abincin
*niko nake su dije anyi laushi ne*😂
tana nan zaune har magariba ta gabato ta hango dawowar su habeeb nan ta shiga neman mafita zuwa can kuwa ta saki murmushi dan tunawa da tayi da wata dabara
qafar wandonta ta shiga nadewa duka biyu zuwa gwiwa ta bubbuda qafafu ta gyara saiti shi kuwa musa ya wangale gate motocin na shiga yayin da matan masu gidan kowacce ta fito dan tarbar mijinta anci kwalliya dan tarbar miji suna gama shigewa musa ya fara qoqarin maida gate aikuwa dije ta kwaso a guje ta nufo ciki yana gaf da ida rufewa ta afko kamar an jefota tana fadin ku gudu gasu nan ku gudu ku gudu ai musa be ko tsaya qarasa turawa ba ya afka dakinsa ya banko ji kake garam
su kuwa mata anata kwarkwasa sun nufo parking space inda mazajensu suka parka suna qoqarin fitowa sukaga ahigowar dije na fadin ku gudu gasu nan ganin yadda take a sukwane yasa naseer da yusra kwasa suma a guje inda sajida ta juya itama da niyyar guduwar shims habeeb haka ji kakeyi kummmm kawunansu ya hadu yayin da hancin habeeb ya fashe jini ya fara biyowa itako sajida bakinta ya bige shima har da jini amma ko ta kan juna basu bi ba suka shiga rige rigen tserewa yayin da ita uwar gayyar tuni ta shige parlor ta tsaya tana mayar sa numfashi a wannan yanayin suka shigo suna kokarin danna kofar da aka gyara dazu suka aa key nan habeeb ya sunkuya tare da safe kai jin jini na bin gefen hancinshi ita ko sajida sai yanzu taji zafi kamar kada ta taba aikuwa taji baki yayi suntum dan da nan jambakin datasa ya hade da jini da maiko abin saiya qarawa bakinta style 😂
sun jima haka kowa na mayar da numfashi kafin dije ta dago ta dubi sajida taga yadda lokaci daya halittar bakinta ta sauya aikuwa duk yadda taso hadiye dariyarta kasawa tayi sai da ta dara dariyar da takeyi ne yasa habeeb dagowa dan tambayarta me takewa dariya ai kuwa shima yayi tozali da bakin sajida da ya samu qarin armashin kwalliya.....
*wayyo cikina*
😂😂😂🤣🤣🤣
*na kasa qarasawa*
*
*Alqalamin khady*✍
[3/14, 9:52 PM] El~hajj: 🌀🌀🌀🌀🌀🌀
TA ME GARI
NA
khadija usman
2⃣3⃣
shi kanshi duk yadda yaso ya maze kasawa yayi duba da yadda yaga bakin sajida lokaci daya ya koma kamar na jaba sam yama manta da ciwon nashi nan shima ya shiga dariya
sajida kuwa ta zubawa sarautar Allah ido ganin duk su biyun shi da dije sai babbaka dariya sukeyi hakan yasa tayi tsammanin ko abinda ya biyo dijen ne ya shige jikinsu dan haka saita fara ja baya tana neman hanyar shafcewa
cikin dariyar harda rike ciki ya nunata da yatsa ya na fadin kin ganki kuwa sweety kin kalli yadda bakinki ya koma kuwa ?
tabawa tayi da hannunta taji yayi suntum sai yanzu na fuskanci meyake yiwa dariya itako dije cikin dariyar ta juya kallonta ga habeeb tace wlh yaya kaima bakaga hancinka ba har ya malkwade shafawa yayi shima ya danji zafi sai yanzu ya dan nutsu kafin ya rike kansa ya samu guri ya zauna tunawa da yayi da gudun da suka sheko to ko uban me ya koro yarinyar oho
cikin wannan yanayin ya dago da kyar yace ke su waye suka biyo ki ne?
tsayar da dariyar tayi kafin tace ba fa wasu bane qawaye na ne na skull shine mukace ayi rige rigen zuwa gida to shine fa na sheqo a guje.......
dukansu sakin baki sukayi suna kallonta inda zuciyar su ta shiga sama da kasa kowannensu yama rasa abin cewa tana gama fadar haka kuwa ta juya tayi cikin daki tana dariya
dukansu sun kasa magana sajida da ya zuwa yanzu takejin kamar ta shake yarinyar ta mutu kowa ya huta takeji wannan jaraba har ina yanzu duk wannan gudun famfalakin data sa su ashe shirmenta ne na banza da wofi dama ga haushinta da take ji tun safe tama rasa hukuncin daya kamata tayi mata
haka shima habeeb ransa ya gama dagulewa wato ma duk wannan gudun data sa su ashe kawai na iskanci ne yanzu dubi yadda ta mayar masa da bakin mata tamkar na jaba duk soyayyar da aka kwadaita masa yau amma yarinyar nan tayi masa bakin cikinta tunda ta yaya zai fuskanci wannan bakin na sajida a haka